Showing 45001 words to 48000 words out of 61846 words

Chapter 16 - Nakasa B Kasawaba Book 2 Complete Hausa Novel

Ali ne ya ƙira."
Ɗago kai Adda Rahama tayi tare da cewa.
"Akan maganan auren ne ko?."
Kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
"Ƙwarai kuwa, koda na faɗa masa cewa, babu wacce ayanzu Saifuddeen ɗin keso, cewa yayi wannan ba uzuri bane, za'a ne mamasa ko acikin dangi."
Idanu Saifuddeen yaɗan zaro waje, kasancewar yana kallon Ummin nasa, hakanne yasa ya fahimci me take faɗa.
Murmushi Adda Rahama tayi, ɗan satan kallon Saifuddeen ɗin tayi, cikin kulawa tace.
"Hakan ma yayi, tun da dai shi yace bashida zaɓi."
Hayatuddeen ne ya ɗago kai tare da duban Ummi, cikin nutsuwa yace.
"Acikin dangi kuma tab, nikam dai banso Hamma ya yi auren dangi, to idan ma hakane ae ga nan Amina da Asma'u, duk suna sonshi, musamman  ma Ameena, dake bala'in sonsa ae sai ya zaɓi ɗaya acikin su ko?."
Ɗan jim Ummi tayi, nan kuma tasaki murmushi, cikin gamsuwa da kalaman Hayatuddeen tace.
"Tabbas, ka ga kuwa ni na manta ma da batun Ameena, gaskiya yarinyar akwai hankali, sannan kuma tana da kirki sosai, don ko lokacin da yake jinya a Hospiatal ɗin Abuja, ta kula dashi sosai, gaskiya na yaba da hankalinta sosai tana son Babana."
Duban Ummi Adda Rahama tayi tare da cewa.
"Okay wannan nurse ɗin ba, gaskiya nima yarinyar ta kwanta min arai, sai-dai kuma wacece Asma'u, don ban shaida ta ba."

Carab Hayatuddeen yayi inda yace.
"Wata jarumar film ne, kinma santa ae, wannan Asma'u Ahmad Matawalle wanda take rawa da waƙa, tauraronta yana haskawa sosai."
Idanu Adda Rahama ta ɗan zaro tare da cewa.
"Mai rawa da waƙa kuma? chab awani gidan? gaskiya a'a, Ameenan dai tayi, don ƴar gidan mutumci ce da dukkan alama, kuma Saifuddeen da yawan kishi ai bazai iya aurenta ba."
Cikin gamsuwa Ummi tace.
"Tabbas nima Ameenan tafi kwanciya min arai, don dai ita Asma'un kam sam batayi ba, don idan ma muka zaɓeta bamusan da wanne ita kuma zata zo ba, duba da irin lalurar da yake fama da ita ma, sam baidace ya auri wata ƴar nanaye ba, wanda suka saba cuɗanya da maza, ko yaushe suna cakuɗe da maza awaje guda ga Saifudden da ɗan karen kishi, balallai ma yasamu ingantacciyar kulawa daga gareta ba, Ameena ɗin dai ita muka zaɓa."
Nan Adda Rahama ta jinjina kai cikin gamsuwa.
Shikuwa Saifuddeen daya duƙar da kanshi kasa, sai alokacin ya ɗago, kasancewar bai kallesu ba, hakan yasa baiji mai suka tattauna ba.
Madanannin wheellchair ɗinsa ya danna, kai tsaye yanufi hanyar barin falon, don yagaji so yake yaɗan je ya kwanta ya huta.

Yana fita Ummi ta dubi Hayatuddeen wanda keta aikin zubawa cikinsa abinci, cikin kulawa Ummi tace.
"Hayatuddeen bani wayarka."
Adaburce ya ɗago kansa, kasancewar yakai loman abinci bakinsa, hakanne ya sakashi ƙwarewa, take tari ya sarƙesa, da mamaki Ummi ke kallonsa, yayinda Adda Rahama kuma keyi masa sannu, botle water ta miƙo masa, nan ya amsa haɗe da kafa bakin goran abakinsa, saida yasha sosai kafun yaji ya samu relief,   cikin kulawa Ummi tace.
"Sannu, haba kaima sai cikawa cikin ka abinci kake babu ko tsayawa, tayaya bazaka ƙware ba, bacin abincin ba guduwa zaiyi ba, kana abu kamar mara gsky."
Shiru yayi tare da ƙoƙarin neman hanyar barin falon.
Dubansa Ummi tayi tare da cewa.
"Ina kuma zakaje? bacewa nayi kabani wayarka na ɗau number'n Ameena ba."
Jin haka yasashi sauƙe gagarumar ajiyar zuciya,  zaro wayar daga cikin al'jihun wandonsa yayi, nan yashiga contact ɗinsa, inda ya laluɓo number'n Ameena'n, nan ya miƙawa Ummin nasa.
Tsab Ummi ta kwafe number'n Ameena'n, inda ta sanya awayanta, kana ta miƙa masa wayarsa, haka ya wuce sama sumu-sumu, daganinsa kasan bashida wadataccen gaskiya.

Nan Adda Rahama da Ummi suka ci gaba da tattaunawa akan sabon auren da za'a ƙarawa Saifuddeen ɗin, sai ayanzu ne suma suke ganin cancantar yin hakan, saboda Zaleeha ta gujesa, tana ganin cewar shi nakasashshe ne, yayinda su gani sukeyi dan shi nakasasshene yasa ta gujeshi sannan babu wata mace wanda zata iya zama dashi, hakan yasa dole ne ma su Aura masa Ameena, tun da dai ita tana son shi, sun tabbatar da cewa kuma zata kula dashi. Sun ɗan taɓa hira kafun Adda Rahama ta tafi, Ummi kuma ta nufi ɗaki ta kwanta, bayan taƙira Bappa Ali ta sanar masa zaɓin da tayiwa Saifuddeen ɗin, sosai shima Baffa Ali'n yayi na'am da batun, nan take yaƙirayi Baba Malam ya sanar masa, da batun,  sosai Baba Malam yaji daɗi, don kuwa ko ba komai hakan da sukayi sun karramasa.

Saifuddeen kuwa yana shiga ɗakinsa, ya soma rage kayan jikinsa,  ƙarasawa gaban tankamemen bed ɗinsa yayi, nan ya sauƙa akan wheellchair ɗinsa, inda ya hau gadon.
Lumshe idanunsa yayi tare da jawo blanket ya rufe jikinsa,   maganar ƙarin auren nasa daya dawo cikin kunnensa ne, ya sashi jin wani ɗaci a maƙoshinsa, sam shi baima ɗauki abun agaske ba, yasan suna faɗa ne kawai, amma shi ina yaga ta wani ƙara aure, shiru zaiyi ya ƙyalesu, yasan nan da kwana biyu suma zasu daina batun.

Yana nan kwance, yaji vibration na wayarsa, don dama akusa dashi take.
Kasancewarsa wanda bayajin magana, ko kuma wani sauti, hakan yasa koda yaushe wayarsa a vibrate take,  domin ta hakanne kaɗai zai gane cewar an turo masa saƙo, domin idan kunnensa baya ji, to ai jikinsa naji, don aduk sanda wayan ke kusa dashi, ko kuma take jikinsa, to zai jita tana rawa, hakan kuwa alamane na cewar an turo masa saƙo, ɗaukan wayar yayi tare da dubawa, ganin  saƙon na Ummin sane ya sashi buɗewa.
Number'n wayane arubuce da kuma rubutu aƙasan sa kamar haka.
"Wannan number'n itace number'n matar da na zaɓa maka amatsayin wacce zaka aura, saboda haka kayi saving ɗinta."
Yana gama karanta saƙon ya tashi zaune cikin hanzari, jiyayi gabansa ya faɗi, cikin sauri ya jawo rigarsa wanda ya cire, nan ya sanya tare da hawa kan wheellchair ɗinsa, ahanzarce ya nufi part ɗin Ummi'n dan yafa lura su da gask suke nufin ƙara mishi auren.

Koda yaƙarasa falon ta bai ganta ba, kai tsaye yanufi bedroom ɗinta.
Tsayawa ajikin ƙofar yayi, tare dayi mata knocking,  Ummi dake kwance jin ana knocking yasa ta tashi ta zauna, murmushi tayi don tasan cikin biyu za'ai ɗaya, ko Saifuddeen ko kuwa Raleeya.
"Shigo." Ta faɗa ataƙaice.
Da sauri ya tura ƙofar ya shiga, Ummi na ganinsa taɗan tsume, tare da dubansa.
Ƙarasowa yayi har gabanta, inda ya kamo duka hannayenta, kansa ya shiga girgiza mata, alaman "a'a."
murmushi tayi tare da cewa.
"A 'a me? bazakayi auren ba ko kuwa me? ko bakason zaɓin danayi maka, ba kuma zaka iya karɓanta matsayin zaɓina ba?."
Shiru yayi tare da ɗan lumshe idanunsa, kansa ne ke sarawa, cikin body language ɗinsa, yace.
"Bawai zaɓinki bane banaso Ummi, ni auren ne banaso, ki dubeni ki gani fa, tayaya zan iya rayuwa da mata biyu, ko kun manta abun da Dr. ya faɗa ne, ina ɗauke da nakasa banjin cewa, zan iya bawa mata biyu kulawan daya dace dasu ba."
Dariya Ummi tasanya, tare da dubansa, saida tayi dariya sosai sannan taɗan soma tsagaitawa, shikuwa Saifuddeen kafeta yayi da idanunsa, tare da sanya mata fuskan tausayi.
Ɗan tsagaitawa da dariyan Ummi tayi tare da cewa.
"Ikon Allah, Yau kuma Saifuddeen kaida kanka kake ƙiran kanka da Nakasashshe? duk saboda ance ka ƙara aure shine har ka aminta cewar kai nakasashshe ne, har kuma ma kake ƙiran kanka da hakan, tsawon lokaci ban taɓa ji kaƙira kanka da wannan sunan ba, amma yau sai gashi da bakinka ka faɗa, ka kuma nanata.  hmmm lallai ma kuwa to wallahi in sha Allah auren nan babu fashi, sai anyi shi, na kuma gama yi maka zaɓi, umarni ne idan kuma kace a'a, shikenan saika ƙira surukin naka wanda ya yanke hukuncin, kace masa kai bazaka bi umarninsa ba."

Idanunsa ya lumshe, jin zuciyarsa yake tayi masa nauyi, a kasalance, cikin yanayi marar daɗi yace da Ummi, ta sanar dashi, "Wacece zaɓin nata?."
Nan Ummi tace.
"Idan yana buƙatar sani, zai iya zuwa ya tambayi Adda Rahama, zata sanar dashi koma wacece."
Jin haka yajuya yafita jiki a mace, yana mai saƙawa ransa to wacece ina take ina suka samota da zasu liƙa mishi ita, tuno babu in da zai samu amsoshin duk waɗanan-nan tambayoyin sai wurin Adda Rahma.
Ae kuwa kaman jira yake cikin sauri ya juya ya fice daga cikin ɗakin.
Kai tsaye ɓangarensa ya nufa, inda ya kimtsa kansa,  koda ya fito text message ya turawa Ahmad kan cewar yana son ganinsa.
Kasancewar Ahmad ɗin na cikin gida, hakan yasa mintuna kaɗan sai gashi ya fito.
Cikin body language Saifuddeen ɗin yace da Ahmad.
"Ya kaishi gidan Adda Rahama."
Sanin kwanan zancen yasa babu musu, Ahmad ya ɗauko musu mota, nan suka shiga, inda ya jasu zuwa gidan Adda Rahaman bayan sun biya jonapwd sun ɗauƙi ishaq wanda a zaton Saifuddeen ishaq zaibi bayanshi.

Koda Adda Rahama ta gansu batayi mamaki ba, don tun kafun zuwansu Ummi ta ƙirata ta yi mata bayanin komai.
Tray ɗin drinks masu sanyi ta dire agabansu, Ahmad ne ya ɗauki kwalin exotic ya miƙawa ishaq kana shima ya ɗauka inda yasoma kwankwaɗa, don shi fes yakejin ransa bashi da wata damuwa.
Hakama ishaq da shi yafi kowa jin haushin Zaleeha, kuma Babanshi ya mishi bayanin son ƙarawa Saifuddeen aure da Baban Zaleeya ya shiryawa.

Saifuddeen kuwa fuska ya marairaice, duban Adda Rahama yayi, tare da ɗaukan wayansa, cikin message ɗin Ummi ya shiga, nan ya nuna mata fuskar wayar, tare da yi mata alaman tambaya, kan cewa.
"Wacece? Ina take?".
Murmushi Adda Rahama tayi masa tare da cewa.
"Miye abun tada hankalinka haka ne Saifuddeen? da ka nutsu ma don amaryar taka ba ɓoyayya bace awajenka kasanta."
Cikin son ƙarin bayani ya zubawa Adda Rahama'n fararen idanunsa.
Duban tsab Adda Rahama tayi masa, kana cikin nutsuwa tace.
"Nasan kasan Ameena ae, wannan nurse ɗin da ta baka kulawa, lokacin da kake jinya a Abuja, kafun ku wuce India, to ita ce dai Ummi ta zaɓa maka, nima kuma nayi na'am don yarinyar akwai hankali, Masha Allah.
Ka tuna har gida tazo itada Mamanta suka dubaka da jiki."

Idanunsa ya zazzaro waje tare da jujjuya kai da ƙarfi sosai yashiga mamaki, lokaci ɗaya yaji kaman an watsa masa ruwan zafi, amamakance ya ɗan ƙanƙance idanunsa, cikin yanayin maganarsa wanda ya saba, wato body language yace.
"Allah ya sauwaƙe ni dai na auri wannan Ameenan, mezanyi da ita bazawara ce fa!."
Cikin tsananin mamaki Adda Rahama ta dubeshi,  kallonsa tayi da kyau tare da faɗin.
"Kai Saifuddeen banda sharri bazawara kuma? wa ya faɗa maka cewar bazawara ce?".
Murmushin gefen baki yayi, tare da jijjiga kansa, in a body language ɗinsa yace.
"Impossible!, nine zan auri bazawara? chab hmmm Allah ma ya sauwaƙe, sam banason sauran wani wlh Allah ya kiyasheni suɗe ƙashin da wani ya rigani tsotsa."
Baki Adda Rahama ta buɗe fuska cike da tarin mamaki sauƙe a jiyan zuciya tayi tare da cewa.
"Wai nikam wayace dakai itaɗin bazawara ce?."
A shagwaɓe ya rubutawa Addan nasa.
"Ae basai an faɗa min ba, duk ckekken Namiji in dai ya nitsu idan mace bazawara ce zai gane ta ido, kuma nayi imani cewa Ameena bazawara ce, saboda haka ni dai bana sonta wlh bazan iyaba, ba kuma zan aure ta ba."
Ahmad da Ishaq kam dariya sukeyi sosai fahimtar abinda yake faɗin.
Baki Adda Rahama ta taɓe, inda ta gyara zamanta, dubansa tayi da kyau,ido cikin ido tace.
"Naji koma dai bazawara ce, ita Ummi ta zaɓa maka a matsayin mata, sannan da kake ta maganar cewa, ita bazawara ce, kai ɗin dakake magana saurayi ne kai? inace kaima bazawarinne tunda dai kayi aure."
Bakinsa ya turo gaba, a shagwaɓe ya narke fuska, cikin body language yace.
"Wallahi ni banason Ameena, yarinyar da idanunta abuɗe suke, ta fa riga da tasan Namiji, sannan kuma har yanzu ni matashin saurayi ne, tayaya ma zan yarda na auri Ameena."
Duban Adda Rahaman yayi tare da kamo hannunta, cikin yanayin daya saba musu alaman magana yace.
"Kin sanni tun ina ƙaramin yarona ma ko ta yaya bana amfani da tsohon abu, hatta kaya idan ya kasance gwanjo ne bana sawa, sannan idan yakasance wani ya taɓa amfani da abu, bana kuma amfani da abun, a iyaka tsawon rayuwata nafison komai sabo, koda wajen zama ne nafison sabo, banason wanda wani ya taɓa amfani dashi, harta mota ko wayar hannu, ban taɓa sayan second ba, komai na nafison yakasance sabo, ko lokacin da nake makaranta, ko yaushe ni nake zuwa first a acikin aji, bana taɓa yarda nazo second akomai na, to me yasa yanzu zan yarda na auri mace second hand? sauran wani, wanda wani ya cakalkala ya bari, ragowar wani fa Adda tunda nake gidannane kawai nataɓa sayan abu second hand kuma kin san shima saida na sabunta mana shi, bazan iya auren sauran waniba kinfa san inada kishi."
Kansa ya girgiza tare da cije laɓɓansa.
Baki buɗe Adda Rahama ke kallonsa, sosai take mamakin ƙarfin hali irin na Saifuddeen ɗin.
Shikuwa Ahmad da shaq dake gefe sai ƙyalƙyala dariya suke tayi, don sosai show ɗin na Saifuddeen keyi musu daɗi.
Ajiyar zuciya Adda Rahama ta sauƙe tare da cewa.
"Koma menene dai Ummi ta gama magana, kuma ta yanke hukunci, wanda mu dukan mu mun gamsu, ta kuma ce zata sanar wa Bappa Ali, don asamu ayi bikin cikin gajeren lokaci, kaman yanda Baba Malam ya buƙata, kai da za'ayi maka auren gata ma, miye na damun kanka, sadaki, kayan aure, komai da komai, duk fa Baban Zaleeha yace ya ɗauke ma, wannan kaɗai bai isa saka farinciki ba, auren huce haushi fa zaiyi maka."
Jan kujeransa baya yayi, inda ya kwaɓe fuska, nan ya dubi Ahmad yace dashi.
"Su tafi." kana ya ja hannun ishaq
Shidai Ahmad dariya kawai yake, har hakan yaso ƙular da Saifuddeen.
Haka dai suka dawo gida, bayan sun sauƙe ishaq ko amota Saifuddeen fuskar nan tasa aɗaure take tamau.
Suna isowa gida, kai tsaye part ɗin Ummi ya sake komawa.
Ganinsa yasa Ummi kafesa da ido, cikin sanya fuskar tausayi, yayiwa Ummi alaman cewa.
"Shi bayason Ameena, saboda bazawara ce, sannan kuma shi tsoronta ma ya keji, gata da kallon tsiya, sai kace mayya, gaba ɗaya idanunta abuɗe suke."

Dubansa Ummi tayi, tare dayin dariyar zuci batayi mamakin jin cewa Ameenan bazawara bace, saboda kafun isowarsu Adda Rahama ta kirata tasanar mata.
gyara tsayuwa tayi tare da cewa.
"Allah mai iko, yau kuma Saifuddeen  kai ne me tsoron mace? uhmm saboda bakason auren ta  shiyasa kake tsoronta ko?"

Sake shagwaɓe fuska yayi, duk yanda yaso Ummi ta fahimce sa, ƙiyawa tayi, daga ƙarshe ma juyawa tayi ta koma cikin ɗaki.
Ganin haka yasashi komawa part ɗinsa, ransa duk ba daɗi, wani haushin Ameenan nema duk ya cika masa zuciya, wannan rana haka dai yayi bacci zuciyarsa duk ba dadi.

Washegari.

Yana gamayin break fast ya shirya kansa, inda ya ɗauki Sule driver suka nufi gidan su Ishaq, don tun adaren jiya ya tsara cewa zai je yasamu Dirankaɗi da maganar, wato Baban Ishaq kenan."
Koda yaje Ishaq ne yayi masa jagora zuwa falon mahaifin nasa,  bayan sun gaisane Saifuddeen yayi masa bayanin duk wani abun daya kawosa, ta hanyar yi masa rubutu a laptop ɗinsa.
Koda Dirankaɗi ya karanta murmushi yayi tare da duban Saifuddeen ɗin.
Cikin son basa ƙarfin guiwa yace.
"Tayaya kake tunanin cewa, bazaka iya auran mata biyu ba? Kai jarumi ne Saifuddeen, saboda haka kada kasa wani damuwa aranka zaka iya."
Nan fa Saifuddeen ya tubure masa kan cewar lallai shi bazai iya ba, ganin haka yasa Dirankaɗi ɗaukar wayarsa, inda ya ƙira Bappa Ali, shi kuma Ishaq dariyan Saifuddeen ɗin kawai yake.
Gaba ɗaya abun da Saifuddeen ɗin ya faɗa, shi Dirankaɗi ya maidawa Bappa Ali, nan Bappa Ali yace da Dirankaɗi, ya faɗawa Saifuddeen ɗin, aure babu fashi, tunda Baba Malam da kansa ya yanke hukunci.
Koda Dirankaɗi ya faɗawa Saifuddeen ɗin, take yace.
"To Baba nifa banida kuɗin auren ma in da ba sadakanta iyayenta zasuyi ba".
Nan Dirankaɗi da Ishaq suka saka dariya, dubansa Dirankaɗi yayi tare da cewa.
"Ae dama ba kaine zaka sayi komai na auren ba, auren gata za'ayi maka ae."
Haka duk yanda Saifuddeen yaso ya kaucewa auren, Dirankaɗi da Bappa Ali sunƙi basa dama, dama shi Baba Malam baisan wainar da ake toyawa ba.
Dole haka Saifuddeen ya dawo gida, zuciyarsa cike da tunani kala-kala.

Haka akayi ta kai ruwa rana da Saifuddeen inda yaketa cemusu wai aifa Dr yace bazai iya zama da mata biyuba, Ya Adnan kuma yace a a ba wani Dr daya faɗi hakan.

Ɓangaren Baba Malam kuwa, tuni ya turawa Yaya Ahmad kuɗi, kan cewar ya bawa Aunty Lubna ta shiga cikin shoprite na Abuja, tayi musu sayayyan kayan lefe,  wanda za'aiwa Saifuddeen sabon aure dashi.
Yaya Ahmad  ne yace da Baba Malam ya amshi kuɗinsa,  shi zai haɗa lefen da kansa,  nan Baba Malam yace "a'a so yake komai na auren yayi da guminsa, da kuma haƙƙinsa, don ya ƙudurta aransa cewa, auren huce haushi da kuma gata zai yiwa Saifuddeen ɗin."

Can ɓangaren Zaleeha kuwa, rayuwarta mai sauƙi take gudanarwa acan garin na Numan, zuwa yanzu bata da wani abinci sai kayan fruits,  dangin su apples da kuma ayaba, goiba dabina sai su water meloon, acikin ƴan kwanki kaɗan ɗin, tuni abubuwa da yawa sun sau ya mata, zuwa yanzu abu biyu ne ke damunta, wato tana jin can ƙasan zuciyarta bata son gudowan da tayi tana kewan kowa hatta su Ummi tana kewansu, ji take kamar ta koma amman da zaran ta tuna ta koma ɗin sai taji kanta yana juyawa sai taji ta gigice lokaci ɗaya taji kamar an ɗaure mata zuciyarta.

Sai kuma nata soyayyar mutumin da har yanzu takasa sake sanyashi acikin idanunta, sosai soyayyarsa ke ƙara ninkuwa acikin zuciyarta, dashi take kwana kana dashi kuma take tashi, yayi mata tsaye acikin rai.

Yanzu ma zaune take akan katifarta, laptop ɗinta ne agabanta, inda ta saka earpiece akunnenta, wani series film take kallo acikin laptop ɗin nata, don tahakane take samun rage kewa, wayarta dake gefe ne ta soma ƙara alamar shigowar ƙira, sunan Balkeesu ne ke yawo akan screen ɗin wayar, saida ta kusa katsewa ta ɗauka tare da kara wayar akan kunnenta.
Daga can ɓangaren Balkeesu tace.
"Mutanen ƙauye."
Baki Zaleeha ta taɓe tare da faɗin.
"Ya akayi ne."
Balkeesu kuwa dariyar dake cinta arai ta danne tare da faɗin.
"Lafiya lau, ya kike kwana biyu ina ƙiran number ki baya tafiya."
Ajiyar zuciya Zaleeha ta sauƙe, cikin halin rashin kulawa tace.
"Maybe matsalan network ne."
Dariya Balkeesu tayi inda cikin zuciyarta tace.
"Ko kuma matsalan wuta ba." Afili kuwa cewa tayi.
"Dama Rabeel ne yace nayi miki magana,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login