Showing 3001 words to 6000 words out of 61846 words
Chapter 2 - Nakasa B Kasawaba Book 2 Complete Hausa Novel
da kuma abinda kike Al'washin yi na cewa zaki kashe kanki ko?." shiru babu mgna sai wata zazzafar zufa data keto mata,
"To yanzu gaya min cikin mutun biyu da kika sa suka turo mana iyayensu wa kike so?."
kai ta jujjuya alamun babu.
Cikin fad'a Aminu yace.
"To uban wa yasa zaki had'a mana kayan mutun biyu, kin san aurenki saura kwana biyar meyasa zakisa Abdussalam turo iyayenshi." da sauri tace.
"Bani bace nace su kawo kayansu bafa."
a hatsale Habu yace.
"Waye to." cikin tsoro tace.
"Mama ce."
shiru sukayi sai Baba Malam ne yace.
"Uhummm". Malam Adam kuwa yace.
"To yanzu dai gwara mu zare hannunmu a kanki, gwara mahaifin naku ya tafi ya barku kiyi duk yadda kika ga dama ko."
cikin raunin murya tace.
"Dan Allah, Baba Malam kayi hak'uri na tuba, ku gafarceni,
Kayi hak'uri kada ka tafi, na yarda ayi auran."
cikin jin dad'i Malam Adam yace.
"Allah ya miki al'barka, tashi kije."
jiki na rawa ta mik'e ta tafi.
daga nan suka ci gaba da tattaunawa.
Nan Baba Malam ya bawa Habu umarnin cewa gobe da safe ya kwashe kayan su Abdussalam ya mayar musu.
Ita kuwa Zaleeha d'akinta ta wuce,
kana ta d'auki wayarta.
10:15 pm ta gani,
zuciyarta cike da bak'in ciki ta kwanta,
text tayi ta rubutawa da mugayen kalamai tana tura mishi har kashi uku,
sannan ta kira Bilkeesu ta gaya mata duk abinda ya faru,
nan bilkeesun tace.
Tana zuwa gobe dan mgnar bazata yiwu a waya ba.
Saifuddeen kuwa, kafin ta tura mishi texts d'inma yayi bacci sabida a gijiye yake.
Washe gari tun da sanyin safiya, Ahmad da Salisu suka shigo da masu gyaran gida,
dan sabunta fentin gidan.
Kai tsaye sashin wannan part guda biyun nan wanda yakeda ciki da parlour da dinning area, a tsakanin part d'in da komansu iri d'aya suka nufa.
In da nan Raliya da Ahmad suke a d'aya part d'in.
Nuna musu duk gyaran daya dace sukayi kamar farfasa steps d'in tsakanin parlour da dinning area, yadda wheelchair D'inshi zaibi ko ina a part d'in har zuwa cikin parlour'n nan mai 2 beedroom dan nanne zai zama turakarshi.
Suna gama nuna musu suka fara aikinsu,.
Su d'in kuwa kai tsaye cikin gidan suka nufa,
jin shiru parlour ba kowa yasa suka wuce parlour Saifuddeen,
suna shiga suka hangoshi kan wheelchair d'inshi mai azabar kyau. Ya bawa k'ofar shiga baya.
Ba jin takunsu zaiba bare yasan akwai mutane a bayanshi,
Wayarshi ya zubawa ido yana maimaita karanta text d'in da Zaleeha ta turo mishi a karo na barkatai.
Wani irin zaro ido Ahmad yayi lokacin da idanunshi sukayi arba da abinda ke rubuce a wayar, wani irin zazzafan numfashi ya sauk'e da k'arfi tare da...!
Littafina na kuɗine in kin karanta na sata kin san sauran in kina ɓuƙata turo katin mtn na raɗi uku kacal ta wannan number 09097853276 ko kuma ki biya ta asusuna na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa.
By
*GARKUWAR FULANI*
[9/9, 9:04 PM] +234 806 222 4030: Zazzafan numfashi ya sauƙe, da ƙarfi ya fusge wayar daga hannun Saifuddeen, sosai hankalinshi ya tashi ransa yayi mummunan ɓaci dan ganin kalaman da Zaleeha ta rubutawa Saifuddeen tacikin text message, wani irin ɓaƙin ciki da ɓacin raine suka tokarewa Ahmad maƙoshi, shikam baisan meyasa Saifuddeen ya maƙalewa Zaleeha ba, yarinyar da bata ganin mutumci da ƙimarsa ko kaɗan, yarinyar da ta maida rashin kunya man shafawanta.
Ɓata fuska Saifuddeen yayi tare da miƙowa Ahmad hannu, alaman ya bashi wayarsa.
Fuska Ahmad ya haɗe sam babu alaman wasa akan fuskarsa haka ya juya ya nufi hanyar fita daga ɗakin, da kallo Saifuddeen ya bishi, wani ɗan guntun murmushi ya sake, haƙiƙa yasan Ahmad sam bayason aurensa da Zaleeha, ya kuma san dalili, amma yasan nanda wani lokaci kaɗan Ahamad ɗin zai fahimta.
Cikin zafin zuciya haɗi da fusata Ahmad ya nufi ɓangaren Ummi.
Zaune Ummi take akan kujera gefenta kuwa Raliya ne zaune tana ta yabawa da koda d'inkunan zafafan laces ɗin dake gabanta, wanda Saifuddeen ne ya saya musu donyin fitan biki.
Murya can ƙasan maƙoshi Ahmad yayi sallama, inda ya kutsa kansa cikin falon, fuskar Ummi cike da fara'a ta amsa masa, saidai kuma yanayin yanda taga fuskarsa yasanya taji ba daɗi, domin Ahmad mutum ne me yawan fara'a, baƙaramin abu bane zai sanya kaga ya ɓata fuska.
Raliya kuwa ji tayi gabanta ya faɗi, sakamakon ganin mood ɗin mijin nata.
Zama Ahmad yayi akan sofa tare da tanƙwashe ƙafafunsa.
Dubansa Ummi tayi cikin sanyin murya haɗi da bayyanar da damuwarta tace.
"Ahmad lafiya kuwa?."
Ɗago idanunsa wanda sukayi jajur yayi ya kalli Ummin tare da miƙo mata wayar Saifuddeen dake hannunsa.
Amsan wayar Ummi tayi tare da kai dubanta ga screen ɗin wayar, wanda har yanzu screen ɗin keda haske bai ɗauke ba, wanda shi Saifuddeen azatonsa Ahmad baisan security ɗinsa ba, shiyasama yabar Ahmad yatafi da wayan, shikuwa Ahmad dama tun tuni yasan securityn Saifuddeen ɗin, don ranan agabansa Saifuddeen yacire wayartasa a security.
Idanu Ummi ta ƙurawa rubutun dake kan screen ɗin wayar, sannu ahankali take karanta saƙon, lokaci guda jikinta ya ɗauki wani irin rawa, take yanayin idanunta suka sauya daga farare zuwa ja, aƙalla ta maimaita karanta saƙon yafi sau uku, batare da ta sani ba, sosai zafafan baƙaƙen maganganun da aka rubuta cikin saƙon ke yawo acikin brain ɗinta.
Babu abun dayafi ɗaga mata hankali kamar inda Zaleehan ta rubuta cewa.
```"Ka turo iyayenka su janye batun aurena da kai! Su zo su kwashi wannan tarkacen da kasa aka tarkato aka kawo mana jidali. In kuma kaki yin hakan ka kuskura ka bari akayi auren nan aka kawoni mushen gidan kunnan to.
Wallah Allah kenan``` Saifuddeen, in ka bari akayi auren nan cikin biyu za'ayi ɗaya ko in mutu ko ks matu!!!."
Sosai tunanin Ummi ya tsaya cak, wani irin matsanancin tsorone ya daki zuciyarta, sosai kalaman Zaleeha suka ɗaga mata hankali, tabbas tanayiwa ɗanta Saifuddeen tsantsar so, bakuma tason wani abu da zai cutar dashi, tayaya ma amatsayinta na Uwa zata zuba idanu tana kallo ɗanta yakai kansa ga inda ake neman halakasa, tabbas acikin kalaman na Zaleeha tagano cewa bata ƙaunar Saifuddeen ko kaɗan, sam bazata taɓa bari Saifuddeen ya auri macen da take da bushashshen zuciya ba.
Hawayen da suka cika idanunta tasoma ƙoƙarin shanyewa, cikin raunin daya bayyana akan fuskarta ta dubi Ahmad.
Shi ɗinma Ahmad dubanta yayi, cikin rauni yace.
"Ina takaicin tsananin son da Saifuddeen kewa Zaleeha, bata sonshi Ummi sam bata ƙaunarsa, bata ganin ƙima da darajarsa, tun awaje tana faɗa masa mugayen kalamai irin wannan inaga kuma idan anyi auren? ba fata nake ba Ummi amma sam banason abun dazai wargaza mana farin cikin mu, Saifuddeen kamar jigo yake agaremu baki ɗaya, bazan iya zuba idanuna naga ya jefa kansa cikin mawuyacin hali ba, Ummi zuciyar Zaleeha tayi zurfi sosai wajen tsanar Saifuddeen, saboda haka zata iyayin komai idan ya aureta."
Ɗan tsagaitawa da maganan yayi tare da maida ƙwallan da suka cika idanunsa, ci gaba yayi da cewa.
"Ai Nakasa Ba hauka bace bare tace baida hankali bazata iya zama da shiba, kuma Nakasar Saifuddeen bashi yake nuna cewa ya kasa ba, mene aibun Saifuddeen Ummi? shin laifine don Allah Ya jarrabeshi da nakasa? ko kuwa laifine don yazamo kurma kuma gurgu, shi nakasashshe ba mutum bane kenan? Wallahi Ummi Saifuddeen bai dace da Zaleeha ba, saboda bata yarda da ƙaddara ba, hartanajin cewa ita watace, wacce ajinta ya ɗara nakasashshe, ta manta cewa da me lafiya da kuma nakasashshe duk halittar Allah Ne."
Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da sakin wani murmushi wanda yafi kuka ciwo.
Cikin tsananin tausayin ɗannata Saifuddeen da irin ƙaddaran da Allah Ya ɗauro masa tace.
"Inajin tsoro Ahmad, Inajin tsoron abun da zai faru nan gaba, bana fatan yarinyarnan Zaleeha ta cutarmin Saifuddeen cutarwa mafi muni."
Still ajiyar zuciya ta kuma sauƙewa, tare da miƙewa tsaye, duban Ahmad takumayi cikin sanyin murya tace.
"Ahmad zanyi abun da ya dace, abunda kowacce uwa zatayi dan kare rai da lafiyar danta zanyi abinda ya kamata ace tayi a matsayina na uwa!."
Tana gama fad'in haka ta juya ta nufi hanyar ɗakinta.
Tuni hawaye sun wanke fuskan Raliya, duk da cewa bata karanta saƙon da Zaleehan ta turowa Saifuddeen ba amma tabbas ta fahimci duk abun dake faruwa, daga cikin kalaman na Ummi da kuma mijinta Ahmad.
Dubanta Ahmad yayi, itama kallonsa take, yayinda hawaye ke tsiyaya daga cikin idanunta, shin menene aibun Hamman'ta don yakasance gurgu kuma kurma? shima mutum ne kuma Namiji kamar kowa, yana da cikakkiyar lafiyansa na ɗa namiji, sannan gurguntan sa bazai zama kasawa agareshi ba, don meyasa Zaleeha zata ƙisa?
Kai Ahmad ya girgizawa Raliya alaman ta daina kuka.
Kasa jurewa tayi, hakan yasa ta faɗa cikin jikinsa tare da sakin kuka mai sauti.
Rungumeta yayi ƙam tare da sake jawota jikinsa, nan yamiƙe tsaye tana ajikinsa suka nufi hanyar barin falon.
Suna fita suka yi karo da Hayatuddeen wanda shigowarsa cikin gidan kenan, sanye yake da white t shirt da kuma 3 guater jeans, hannunsa riƙe da wayarsa ƙiran Samsung yayinda kunnensa ke saƙale da earpiece, yana ganinsu yaɗan yi turus tare da turo bakinsa gaba, har acikin ransa shikam yagaji da ganin Yayar tasa Raliya da Ahmad manne da juna sunashan soyayyarsu kamar tattabaru, kullum haka yake ganinsu liƙe da juna kamar wasu tif da taya.
Hararansa Raliya tayi da jajayen idanunta, sake kwaɓe fuska yayi yana shirin yi musu halinnasa na shagwaɓa ne, Ahmad ya miƙo masa wayar Saifuddeen, batare da Ahmad ɗin yace komai ba yaja Raliya suka nufi ɓangarensu.
Da kallo Hayatuddeen ya bisu har suka ɓacewa ganinsa, bakinsa ya taɓe ƙasa-ƙasa yace.
"Hegu fitinanu, kuyi dai nima dana ƙara girma, ai dai zanyi auren nan ehe, don haka duk wani me ɗagamin kafaɗa ma gwara ya daina, nima ai zanyi auren bawai ba zanyi ba."
Haka ya nufi ɓangaren na Saifuddeen yanata ƙunƙuni aransa.
Koda ya ƙarasa part ɗin a parlour ya had'u da Salisu dake saurin fita, dan sunyi mgna da Saifuddeen kam batun Rashida na son su kai musu kud'in walima, so shine ya fita da sauri dan kai mata kud'in,
cikin girmamawa yace.
"Ina kwana Ya Salisu."
"Lafiya lau Auta ya sakalci."
Salisu ya amsa mishi ba tare da ya tsaya ba,
Murmushi Hayatuddeen yayi tare da cewa.
"Manyan angwaye sai b'are-b'are suke uwa hanji a langa."
yana musu tsiya ya wuce ya nufi bedroom d'in Hamma
Saifuddeen din nashi zaune ya sameshi akan wheelchair ɗinsa, inda ya tasa laptop ɗinsa agaba ƙiran company'n apple yana dannawa.
Akan cinyar Saifuddeen ɗin ya ɗaura wayar tare da yin super ya faɗa kan lallausan gadon na Saifuddeen, lumshe idanu yayi yana me shaƙan daddaɗan ƙamshin na Hammansa, aransa yana fata ace watarana shima yazama kamar hamman nasa.
Saifuddeen kuwa murmushi kawai yayi tare da ɗaukan wayar tasa ya duba, ganin still akan message ɗin Zaleeha yake, yasanyashi sakin murmushi, domin jikinsa ya basa cewa Ahmad bai cire wayan a security ba balle yayi amfani dashi.
Cigaba yayi da aikinsa,yayinda time to time yake sipping exotic juice ɗin dake gefensa.
A wunin ranan masu gyarannan suka gama komai na side d'insu Saifuddeen kafin azahar sun gama komai na side d'in masu buga kitchen cabinets ma sunzo sun shirya komai ras.
masu fenti kuwa sun fento ko ina na gidan luggu da sak'o da yake sunada yawa kuma akwai kayan aiki kafin magrib dai sun gama komai gidan ya zama sabo fil yayi ras sai shek'i yakeyi da k'amshin sabon fenti.
In da akayiwa gidan fentin Coral color iya rabi daga k'asa kuma dama tayis ne manne royal color hakan yayi masifar kyau ya haska gidan,
cikin gidan kuwa Side d'in Ummi pumpkin color akasa daga saman pop d'in daga k'asa kuma navy blue mai shek'i,
hakama saman inda Hayatuddee yake, inda Saifuddeen yake kuwa ba'a tab'abashi ba dan bai jimaba,
Sai inda Raliya take mai mak'otaka da inda za'a ake shirin sa Zaleeha, mint green and white akayi mata komai yayi ras, sai wojen part d'in duka da aka fente da dark brown and daga d'an k'asan kuma tayis ne manne a jikin ginin,
sai farfajiyar wurin da yakeda d'an zagayeyyen ma dai-daicin lambun da yakeda yabanyar grass carpet wanda yayi kore shar, sai bishiyar mangoro mai fad'i da tsananin duhu wanda yake baje kan bishi yoyin dabino da ayaba da gwaiba dake gefenshi dan bishiyar mangoron bata da tsawo sosai, a k'asan kuwa fulawowi ne jere wanda sune suka zama garkuwan wurin sai ya zama in kana cikin wurin baza'a hangoka ba, cikin wurin kuwa sai wasu fulawi masu halittar tim-tim in ka gansu kamar kujeru, kana ga kan pompoms guda biyu wanda dasu akeyiwa wurin ban ruwa, daga tsakiya ciluk kuma wani k'arfe ne mai tsawo wanda yake manne da fitilar sola mai d'an karen haske.
sai irin kujerun silver nan da ake ajewa a asibitoci da wuraren shak'atawa, kujerun ne suka zageye wurin da k'asanshi ke wadace da koriyar ciyawar, ga sanyin tsirrai gana ruwan dake gudana a wurin ga na inuwar bishiyar mangoro dana dabino da gwaiba, uwa uba ga sanyin bishiyoyin ayaba kusan guda biyar da suka zagaye wurin,
daga cikin wojen wurin kuwa an lailayeshi da intalak, sai babban baranda mai fadin da aka laileyeshi da tayis fari k'al.
kana cikin parlour kuwa yasha fenti purple and cerise color sosai parlour yayi kyau hakama cikin two bedroom d'innan, kitchen d'inta kuwa an k'awatashi da durowowi masu kalar pink and white sosai aka k'awata kitchen d'in.
komai fa yayi ras sai shek'i da k'amshi gidan keyi,
hakama fulawin gidan duk anbi an musu sassariya an dai-dai tasu,
garden dake bayan part d'in Ummi ma an gyarashi sosai,
gida dai ko yanzu amarya tazo...
Juyi take tayi akan makeken gadon nata, gaba ɗaya damuwa ya cika zuciyarta, wani irin zafi takeji acikin ƙirjinta, rumtse idanunta tayi, take wasu irin hawaye masu zafi suka kwaranyo daga cikin idanunta, ya zatayi? wazata kaiwa kukanta ya share mata hawaye? burinta shine koda mutum ɗaya ne ya fahimceta, amma ankasa samun hakan, sosai zuwa yanzu ƴan uwanta keyi mata kallon wanda aljanu suka kama, laɓɓanta ta ciza tare da sakin wani marayan kuka mai sauti, ta lura shi wannan nakasashen jikinshine a nakasashe zuciyarsa cike take da jarumta, dan ta fahimci duk baraza da ihu da hargowar da take mishi akan ransa da rayuwarshi a banza, babu alamun karaya bare fargaba ko d'igon tsoro, asalima sai tsoronshi dake cika mata idanu muddin ta kalli kwayar idanunshi koda na one second ne.
Juyi ta kumayi tare taune lip d'inta na k'asa ayanzu tafi buƙatarsa fiye da dacan baya, fatanta burinta, muradinta duk sun ta al'laƙane akansa, sam soyayya batayi mata adalci ba da ta jefata cikin mawuyacin hali, hannunta ta sanya ta dafe dai-dai saitin zuciyarta dake bugawa, tanajin sonsa na fusgarta, wani irin maganaɗisun ƙaunarsane ke ƙara janta akowacce rana, yaya zatayi da soyayyarsa dake ƙoƙarin fasa mata zuciya?
Ƙaddara tazo mata ayanda bata taɓa zata ba, ƙaddara ta zautar mata da tunani, har takai ga tanayin komai cikin zaucewar hankali.
Sosai tayi hugging pillow, ahankali taci gaba da rera kukanta, saida tayi kuka sosai kafun wani wahalallen bacci ya ɗauketa.
Washe gari.
Zaune suke su dukansu akan babban dinning table ɗin dake cikin falon, Saifuddeen, Hayatuddeen da kuma Raliya, sai Ahmad wanda shigowarsa cikin falon kenan.
Ahankali Saifuddeen ke tsakalan abincin yana kaiwa bakinsa, gaba ɗaya hankalinsa naga wayarsa dake riƙe ahannunsa, sosai yashiga busy tunda aka fara shirye-shiryen bikin, dan ma yanada tarin aminai dake ji da komai wani abinma sai dai kawai yaga anyi sosai suke shiryawa bikin inda ya kama yau saura kwana uku bikin.
Tunani yakeyi akan tirelar dake can harabar gidan nasu wanda aka kawo kayan Zaleeha. Tirelan cike yake dam da kayan Zaleeha wanda Ya Ahmad yayi mata komai na duniya wanda amare zasu buk'ata.
Wanda Habu ya bada shawaran kada a sauk'e kayan a gidansu a wuce dashi gidan Saifuddeen d'in acewarsa k'arin jidaline.
to koda ya gayawa Ahmad sai suka bawa driver'n tirelar hak'uri akan zasu biyashi abar kayan a ciki sai an gama gyaran side d'in amaryar sai su sauk'e kayan to su kuwa jin za'a biyasu yasa suka amince.
to an gama gyara a bisa tsarinsu dai gobe za'a zo a sauk'e kayan sannan tuni Salisu ya nemi masu had'a kayan su shirya za'a biyasu dubu saba'in kud'in aikinsu kana Maryam da Aunty Lubna zasu zo su kimtsa komai duk a goben...
Ummice ta ƙaraso cikin falon, cikin shirinta tsab, sosai tasha ado irin wanda ya bayyana cikar kamalarta, tana ƙarasowa cikin falon gaba ɗaya kallon ƴaƴan nata ya dawo gareta.
Ahankali Saifuddeen ya ɗago da kansa ya kalli Ummin nasa, ganin yanda tayi masa kyau yasanyashi sakin murmushi, tare dayi mata duban tsab, domin yaga alaman cewa fita zatayi.
Ƙarasowa dinning area'n Ummi tayi, hannu tasanya ta shafa kan autanta Hayatuddeen dake ta faman zuba wa cikinsa, spiring roll.
Fuska Saifuddeen ya kwaɓe tare da karyar da wuyansa gefe,
Matsanancin tausayinsa ne ya cika zuciyar Ummin, don sarai ta fuskanci abun da yake nufi, alamune dake nuni yanada yar damuwa can k'asan zuciyarshi wanda kuma baya son ta sani, ita kuwa in taga hakan bata matsa mishi kan ya sanar mata sai dai takanyi k'ok'arin sashi farin ciki, sai dai tasan yanzu koma menene aransa baya rasa nasaba da Zaleeha,
hannu tasa ta shafa kansa shima.
Murmushi yayi inda cikin body language ɗinsa yayi mata alaman da ina zataje.
Itama murmushin tayi tare da gyara tsayuwarta, duban ƴaƴan nata tayi dukansu, tare dayi musu bayani akan zuwanta Dukku da ta tsarashi yau da safe, sannan kuma ayau ɗin zata dawo, sosai suka ɗanyi mamaki sai-dai kuma sanin cewa ana tsaka da shirye-shiryen hidiman biki ne yasanya basu damu ba, don atunaninsu wani uzurine wanda ya shafi bikin zai kaita Dukkun.
Haka Ummi tayi sallama da su, inda dukansu suka rakota har compound ɗin gidan.
Saida suka ga tafiyarta kafun su dukansu suka koma cikin gida.
Kusan ƙarfe shabiyu da wasu ƴan mintuna Ummi suka iso