Showing 54001 words to 57000 words out of 180150 words
Chapter 19 - A Tsakankanin Soyayya Book 1 Complete Hausa Novel
kafin daga bisanni tai bacci.
Wuraren biyun rana su Baffa suka iso kowannen su dauke da murmushi akan fuskar shi suka zazzauna nan suka shiga bama Ammi labarin binciken dasuka yo, Dady nada kirki ainun ga taimakon musulmai, sanan baida zalunci, matayen shi duka suna tare bai taba sakin mata kodaya ba, gidan shi ba'ajin kansu awaje atakaice dai basuji any bad halin Dady ba daidai da kwara daya, hakan yasa Baffa ya gyara zama yace "todai kinji komi, me kikace dan kiranmu yake jira, eh maman Fateema me kikace?" dan ajiyan zuciya Ammi tasauke kafin ahankali tajuyar da kanta ta kalli Aneesa dake bacci tai shiru kafin tafara zancen zuci. "hukuncin dazan yanke yanzu sabida kene Fateema na, I know, ni karan kaina nasan yanda zuciyar ki ta kwadaitu, tana neman wanda kowani safiyar Allah zaki kalla ki kirashi da Baba ko Abba ina kwana, kema ki sami wanda zaki kalla ki kira da mahaifi, bakomi zaisa na yarda da auren nan ba saidan inga farin ciki akan fuskarki, farin ciki wanda ni mahaifiyarki ce tasanyaki ciki, nothing beat seeing your child happy and as a mother I have to make you happy, zan yarda da auren nan for you Aneesa na dan naga yanda kikeson Alhajin nan banda hakaba ma ta sanadinki muka hadu" ajiyan zuciya ta sauke ta juyo da kanta ahankali ta kalli su Baffa dasuke jiran me zatace gyadamusu kai tayi ahankali tace "na yarda Baffa" wani iri washe baki da sukayi zaka dauka an musu bushara da aljanna ne Baffa yace "masha Allah Masha Allah, naji dadi, ina kuma rokon Allah daya sanya albarka awanan lamarin, ya kade fitina, yanzu Na sani tashi muje musanar dashi me akeciki kaga nasan zaiyi farin ciki sosai" cikin jin Dady suka tashi suka fita, dan murmushi Ammi tayi harga Allah tunda Aneesa ta nuna tanason Alhajin sai itama taji tana sonshi sosai bana wasaba kuma zata so ta kasance tareda shi har abada, dan dugo dakai tayi ta sumbaci goshin Aneesan dake bacci tana murmushi tanata kallonta ahankali tace "Allah yabaki miji nagari wanda zai soki sanan ya kulanmin dake aduniyan nan" karan dataji na shigowan message a wayanta ne yasa ta mike tsaye ta dau Jakarta dake kan saman drawer, wata savuwar number ce tatura mata sako, zama tayi abakin gadon tabude.
_Assalamu Alaykum, Rukayyah_
_Hakika yau kin sani cikin tsananin farin cikin dana dade ban shiga irinshi ba, naji amsan ki daga bakin Alhaji, Masha Allah, Alhamdulillahi Rabbil Alameen, alkawari daya zan miki shine bazaki taba samuna dacin amana ba, zan rikeki amana, Aneesa tadawo y'ata zan riketa amana sanan zan bata tarbiya amatsayina na mahaifi agareta, karkiji komi zan kasance miji nagari da zaki dinga alfahari dani akodayaushe. Ina kaunar ki sosai Rukkayah Sainazo_
_Alhaji Muhammad_
Dan murmushi Ammi tayi ta ijiye wayan tareda sauke ajiyan zuciya tana tunani wai yanzu itane zatai aure? Abinda bata taba kawowa zai faruba, Allah kenan dazaran yace lokaci yayi to yayin nefa, Allah sa mudace! Ameen.
Da sallama Dady ya shiga part din Aliyu, jin shiru bai amsaba TV ne kawai ke aiki a falon yasa yay bedroom dinshi, ahankali yabude kofan babu kowa a bedroom din sai kamshin da dakin yakeyi, fitowa yayi yana kwalamai kira. "Aliyu, Son, Gadanga na" fita yayi daga part din yana mamaki to ina yaje yaga motarshi ai, har zai wuce idanunshi suka sauka kan wani fine paint brush dake kasa, tsugunnawa yayi ya dauka yana murmushi yace "yau yan zanen sun tashi kenan jibi ya yarda wanan baima saniba" garden din dake side din Aliyun yawuce dan yasan anan yake zane, garden ne mai kyan gaske an gyara wajen iya gyarawa gawasu kujeru da table da aka jera awajen kaman wurin picnic, hango Aliyu yayi zaune kan wani dan kujera, yana sanye da gajeren wando na Paco Rabanne sai wani dark blue logo t-shirt na Marni kafanshi cikin wani white bedroom slippers, hanunshi rikeda paint brush yana 3D zane dabai riga yagama ba akan babban drawing board, kunenshi makale da head phone, jingina Dady yayi da bishiyar mango dake wurin yay folding hannu a kirji yana kallonshi yana murmushi Aliyu is damn gifted. 1st degree dinshi architecture yayi, 2nd degree dinshi kuma yay law, bai dade dagama masters dinshi ba, dukda first class yake fita, yanzu haka construction company dinshi is ready amma yaki fara zuwa office ko kadan baiso yana takuramai saisa ya barshi yasa wani PA dinshi yana managing wurin kafin Aliyu yay ready finally.
Ahankali ya sanya hanunshi dasuka dan baci da paint ya janye headphone din kunenshi batare daya waigoba yace "Dad why are you looking at me?" ware ido Dady yayi cikeda mamaki kafin yatashi daga jikin bishiyan yakara so inda Aliyun yake ahankali ya dafa kanshi yace "Son yan zanen ne yau suka tashi, mekake zanawa haka?" Dady yay maganan yana janyo dayan stool din dake gefe ya ijiye ata gaban Aliyun ya zauna yana kallon yanda paint din yabata rigan daya saka. "Aliyu" kallon Dady da sauri yayi yana tsayar da zanen jin yanda yakira shi, ajiye paint brush din yayi acikin cup din ruwan dake kan table yace "Dad, wat is it?" gyara zama Dady yayi yace "I want to talk to you" hannu yasa ya kashe headphone din da waka ke tashi daga ciki Aliyu yayi yace "OK, am listening" dan shiru Dad yayi kaman mai tunani, ahankali yace "aure nakeso zan kara Gadanga na" yay dan shiru yana kallon fuskan Aliyun ganin baiga wani chanji ko wani yanayin tattare dashiba yasa yace "Son kasan bana boyema komi ko, kawai sabida na kasance namijin da banso ina yawan sakin mataye nane bazan ma karya ba da tuni na saki duka mata uku nan danake dasu, basuda mutunci, basu da kirki, ga shegen son abin duniya, they've spoilt all my children Aliyu da yau inda zan fadi namutu yaran wanan ba ruwan su da yaran wanan, cikin dukan ku ku 20 daga kai sai Rauda ne Allah ya tsamo min, am worried Son, how many hours nake samu na zauna agida dazan samu nai uniting yarana, y'ay'ana iyye? Na auro jakunan mata babu abinda suka iya sai koyama yarana bakaken hali da tsanan junan su, mata uku amma banda ta arziki ko daya" yadanyi shiru dan ko kadan baiso yana tunawa da matsalolin gidanshi da hawan jininshi zai iya tashi, ahankali yace "I told you shekaran jiya abinda yasa nai latti was because I helped one woman da yarta batada lafiya na kaisu asibiti ne ko" gyadamai kai Aliyu yayi alamun eh, cigaba da magana Dady yayi yace "Aliyu when I saw how caring and loving that woman is towards her daughter I immediately saw myself in her, na yaba da natsuwan matar, sanan na yaba da tarbiyan data bama yarta, she's good, she's educated duka fanin boko da islamiya ahaka banma riga na tambayeta duka abubuwan data saniba tukunna, Ustaziya, kamilan mace, da natsuwa da kamala, ga fikra, all this abubuwan duniyan nan basu dameta ba, sosai naji ina sonta, nama yan uwan ta magana sufada mata tace ta yarda, dazaran an sallami yarinyar daga asibiti nakeso a daura auren, I don't wanna do anything dazai batama rai I need your support Gadanga na, should I go ahead and marry her?" dan shiru Aliyu yayi yana kallon mahaifin nashi deep down ya tsani yanda Dad ke aure but wani zubin baya blaming nashi danko shi kanshi baiga mata tagari acikin matayen ba, he just hope wanan will give his Dad the peace din dayake nema da kwanciyan hankali tunda dai yaga tsantsan son da Dady ke mata a idanunshi, dan murmushi dake karamai kyau yasakin ma Dady yace "marry her Dad, Allah sanya alheri" ajiyan zuciya Dady ya sauke tareda lumshe ido jiyayi duk wani nauyi da zuciyan shi yamai ya sauka baiso yay auren Aliyu bai yardaba saigashi ya yarda, cikeda tsananin farin ciki yace "thank you Gadanga na, zan kira Momman ka tahada min akwati, kaje gidan kuwa tunda kazo?" yatsine fuska yayi tareda girgiza kai, dan batarai Dady yayi yace "kabar zanen nan kawuce ka shirya, bodyguards dinka su kaika kanajina ko" ahankali yace "to" tashi Dady yayi yace "zan kira a gyara the flat that is next to mine, bari naje office" "bye Dady" "bye Gadanga" fita Dady yayi Aliyu yay shiru yarasa mekemai dadi aduniyan nan mugun so yake yaje asibitin but baiso yahadu da Ammi, Abdul yafado mai arai hakan yasa da sauri yatashi yay part dinshi wanka yashiga yafito ya shirya cikin wata hadaddiyar shadda yaja mota ko inda bodyguards din da Dady yace subishi baiyiba yafice abinshi.
Wuraren 3 na rana Dr ya shigo dakin rikeda leda dake cikeda magunguna yana kallon Aneesan data tashi zaune ta jingina da gado tana shan tea da Ammi tahada mata Baffa na zaune kusada ita rikeda plate da soyayyan kwai kekai tanaci, tarame sosai, raman saiya kara karamata kyau, lips dinta sukai pink suka tattare sosai bana wasaba, baki Dr yarike yace "iyye patient dina da bata son allura ne takecin dadi haka, mesa akabata? " dan murmushi Aneesan tayi akunyace, Baffa yace "yo kaiko bazaka barmin diya taci dadi ba, kukenan saiso kuna chakama mutum karfe daku za'a chakamawa da ansha kallo kuka wiwi zaku dinga yi fa balle yar diyata yar karaman nan" dariya duk akayi adakin Dr yakara so yana duba Aneesan ya bama Ammi ledan magungunan yace "an sallame ku, ga magungunan ta na narubu tamuku yanda zata dinga sha, ki kula da ita da kyau sanan a kiyaye kar sauro yacijeta sanan ta dinga shan maganin ta akai akai, kina yawan bata abinci mai Gina jiki, nariga na sanar da Alhaji nasallameku yama turo mota dazai maidaku gida motan na waje ku shirya sai a fitar da kaya" ya kalli Aneesa dake wasa da tea yace "Allah kara sauki my patient banda rashin ji da tsoron magani kinji ko" gyadamai kai Aneesa tayi tana murmushi ahankali Dr yawuce yafita, kayan su da dama a killace suke tsaf Ammi ta shiga gyarawa, shanye tea Aneesa tayi Ammi ta karba ta gyara komi Baffa ya karbi hijabin Aneesan daga hannun Ammi yasamata sanan yadaga ta tashi tayi ahankali yace "sannu kinji, sa takalmi" takalmi tasaka yana rikeda hannun ta suka fito shikuma Na Sani ya tsaya yataya Ammi kwashe kayan suka fito, da Ammi da Aneesa ne suka shiga jeep din da Dady ya aiko musu da shi sukuma su Baffa suka shiga tasu motar suka tafi gida sukai Suleja.
_duk wacce takaran ta batare data biyaba Allah ya isa_
_how to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 Aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watsap number na 07012181461, sainai adding dinki a group din danake posting_
Gaban wani babban gida Aliyu yay horn, budemai gate gateman din yayi yana ganin Aliyu yahau washe baki yana dagamai hannu, shiga gidan Aliyu yayi yay parking da sauri gateman din yazo daidai Aliyu yabude mota yafito, washe baki Gate man din yayi yace "sannu da zuwa Alhaji yaushe kadawo Nigeria" dan murmushi Aliyu yayi yace "nadan kwana biyu" cikeda barkwanci gateman din yace "shine bakazo bikina bako, ko Abdul fa yaje a kauyen mu akayi, sunan matata Talatu mesa bakazo ba" "dalla chan kawuce kabama mutane wuri bazoba ba din" sukaji muryan mace daga bayansu tana magana, juyo dakai daga Aliyu har gateman din sukayi wata kyakkyawan budurwa ce mai kama da Abdul sosai kana ganinta zaka gane kanwarshi ce tsaye gaban tap din tsakar gidan, wani irin mugun kallo Aliyu yamata dayasa da sauri tajuya zatai backyard cikin kakkausar murya Aliyu yace "come back here" juyowa tayi ahankali kaman wacce kwai yafashe mawa aciki ta tako tazo ta tsaya a gefenshi, gateman din yanuna da hanunshi yace "say sorry" dan turo baki tayi tace "toni Ya Aliyu menayi?" da sauri gateman din yace "tabarshi Alhaji, basaita bani hakuri ba, haka muke wasa da Hajiya ai ni natafi" cikin fushi Aliyu yace "karkaje ko ina" tsayawa yayi dudda baiso ba, Aliyu ya kalli yarinyar yace "kinsan Allah Ihsan idan bakice sorry ba saina kakkaryaki anan sanan zan wuce ciki" idanun Aliyun ta kalla ganin da gaske yake kuma tasan zai iya dukanta dan Ya Aliyu mugu ne kaman ya Abdul yasa ta kalli gateman din tace "sorry" hararanta yayi yace "bacemin daga gani" da gudu tajuya ta shiga falon su, kudi yaciro daga aljihu dabaisan yawansu ba yamikama gateman din da sauri ya karba yace "innalillahi wanan kudi haka Alhaji, me za'ayi dasu?" murmushi yayi yace "gudunmawata, agaishe da Amarya" wani irin ihu gateman yayi hakan yasa Aliyu yajuya yay ciki yanadan murmushi, mamaki yake haryau gateman dinan bai chanza haliba, daga murya gateman yayi yace "Allah baka mata kyakkyawa wacce zata dinga saka farin ciki kaman yanda kasani yau nagode Yallabai" ganin Aliyu yama shige ciki a binshi yasa yajuya yana murna.
Da sallama Aliyu ya shiga falon dayasha kayan alatu, wata kyakyawar matace zaune kan dogon kujera tadanyi kama da Dady kaman kanwar shi kokuma cousin dinshi, hanunta rikeda bowl din slice friuts ga Ihsan a gefenta idanunta sunyi jajir tana kumbure kumbure, hararan Ihsan din yayi yana tahowa yace "tashi daga wurin nan" tashi tayi daga kusada matar tai stairs shikuma Aliyu yazauna kusada Momma tareda karban bowl din fruits din hannunta yace "Momma na" tallabe mai keya tayi da hannu hakan yasa yadanyi kara. "aucch Momma zafi fa" hararan shi tayi tace "kamin laifi tunda kadawo bakazo ka gaidani ba sanan daga zuwanka zaka dinga cin zalun autana" yatsine fuska yayi yana kai fruits baki yace "Momma Ihsan batada kunya zan kakkaryata in batai hankali ba wlh" haba Momma tarike tace "ahhh lallai ba shakka to mafashi, kaji ko mafashi nace, daga kai har Abdul din duk wanda yatabamin auta saina rama mata wlh, yayyun banza yayyun hofi masu cin zalun kanin su kawai" dariya yayi sosai yatashi daga kan kujeran yana hawa stairs rikeda bowl din fruits dinshi batare daya tanka ba, Momma data binshi da kallo tace "gaurayen banza aje ayi aure anki sai mugunta, katada wanan mugafalin dabaida aiki sai bacci" dariya yayi yawuce wani daki na karshe a corridor, bude kofar dakin yay ya shiga hango Abdul dayayi yayi daidai akan gado yana bacci ba riga ajikinshi yasa yay kwafa yafito daga dakin ya kwalama Ihsan kira. "Ihsan" da sauri tafito daga dakinta tace "na'am, gani Ya Aliyu" "ehen get me a cold water, very cold one, wanda yafara kankara daga fridge" gyadamai kai tayi tasauka kasa ko 1min ba'ayiba tadawo rikeda ruwan sanyin a gora dayadan soma kankara tabashi tana kallon fuskar shi, bowl din fruit din yamika mata yace "take it to the kitchen" yawuce ya shiga dakin tareda rufo kofa, ahankali yake tafiya har gaban gadon yabude goran ya ijiye marfin ya kwantarda goran ruwan ya tsayayo abayan Abdul dake sharara bacci, ihu Abdul yayi tareda zabura yatashi zaune sabida masifaffen sanyin dayaji, fashewa da dariya Aliyu yayi yana komawa baya ya ijiye ruwan kan center table yana dariya sosai harda rike ciki, saukowa daga kan gadon Abdul yayi yadau ruwan yace "yasin saina rama" da sauri Aliyu yabude kofa yafita biyoshi Abdul yayi, Aliyu ya sauka da gudu ya zauna kusada Momma yace "Momma kinga Abdul ko zai watsamin ruwan sanyi" daidai Abdul ya iso shima ganinshi kusada Momma yasa yakasa karasawa wajen ya tsaya anan gaban stairs Momma dake kallonshi tace "kazo mana ishashe, sai shegen son bacci kaman zakara, ai koda baizo yatasheka ba dani dazo kaga ainihin tashi, nafadamaka bazaka kara bacci mai kyau agidana ba, kai aure kaje gidanka inkaga dama kai baccin kwana uku babu maidamunka kaida matarka ne, amma muddin anan gidanne to ko kagama baccin lafiya da lumana" yanda ya daure fuska yana kallon tijaran da Momma kemai agaban Aliyu yasa Aliyu ya fashe da dariya, keyanshi Momma ta tallabe tace "kaima harda kai ai" gwalo Abdul yamishi yace "Allah kara" turo baki Aliyu yayi kaman zai mata kuka, dan murmushi Momma tace "ga abincin ku chan a dining inkunga dama kuci, gaurayen banza" tashi Aliyu yayi sukayi sama abinsu ko takan abincin basubi ba._*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_
_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤
_✍🏿M Shakur_
2⃣9⃣
Zama sukayi akan gado Abdul zai fara masifa da sauri Aliyu yace "please jekai wanka inaso karakani hospital ne" da sauri Abdul yadaura hanunshi kan goshin shi yace "bakada lafiya ne Leo? Mekema ciwo?" girgiza mai kai yayi yace "am fine" "tome zakaje kayi a hospital?" kaman baiso yay magana yace "I wanna go see someone" kallonshi Abdul yayi irin anya Aliyu ne yay maganan nan kuwa dan yasan baida abokanai shi yanama shiga mutane ne dahar yasan wani dazaije dubawa a asibiti, ahankali kaman mai koyan magana yace "s...o..meo..ne? Someone Leo, waye someone kuma?" dan shiru Aliyu yayi yana kallonshi yarasa taya zai fadamai, dariya Abdul yafashe dashi yakoma kan center table yazauna yana daura kafa daya kan daya yana facing dinshi yace "shegen gora, koka fadamin gaskiya kokuma ko nan da chan like chan fa kofar dakina dinan da sunan rakaka wani wuri bazani ba, so tell me d truth" dan yatsine fuska Aliyu yayi yace "please now, kaga nagaji ni nai driving har nan hannuna duk sun sage karakani mana," da sauri Abdul yace "naji to tell me, who is someone, mace ne ko namiji?" hararan shi Aliyu yayi kafin yadauke kai murya chan kasan makoshi yace "mace" huuuuuu! Wani irin ihu Abdul yyi da ko Aliyu saida ya firgita yakoma cikin gado da sauri yace "are you okay me haka" hawowa gadon Abdul yayi