Showing 60001 words to 63000 words out of 180150 words

Chapter 21 - A Tsakankanin Soyayya Book 1 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

26 Sep 2025

2476

kwalama Aneesa kira. "Fateema" tashi Aneesa tayi da sauri tafita yana ma wurin zaure tace "sannu da zuwa Baffa" yar ledan hanunshi yamika mata yace "ga tsaraban kinan, jeki cema maman ki Alhaji yazo ta gyara yanzun nan zan shigo dashi" wani irin tsalle tayi tana murmushi tace "tom " dasauri tajuya takoma daki dawani irin gudu taje tafada kan jikin Ammi dake kan dadduma tace "Ammi Baffa yace kici gayu Abba yazo zai shigo dashi" hararanta Ammi tayi tace "to bismillan su mana wani gayu zanyi ni? Namasan shairin kine" ashagabe tana turo baki tace "ni Allah saikin yi, kinji Ammi na please" tai maganan tana daga Ammin tanajan hannunta tashi Ammi tayi tace "nidai nabani da dake Aneesa" dariya tayi sosai taja Ammin sukai dakinta ta zaunar da Ammi kan gado jikinta harwani rawa yake tabude sip din Ammi wani leshi taciro da sauri Ammi tace "lafiyan ki kuwa Aneesa? Da daddaren nan zansa leshinnan dake da nauyi?" kallon leshin Aneesa tayi tana murmushi tace "au hakane wlh Ammi murna nake banmasan me nakeyi ba" tabe baki Ammi tayi tace "kyaji dashi, mikomin wanchan doguwan rigan atampan" tamata pointing wani atampa mai kyau daukowa Aneesa tayi takawo mata sanan tace "yauwa bari naciro hijabin dazai shiga dashi" komawa sip din tayi Ammi kuma yacigaba da shiryawa, wani mustard hijabi taciro mai hula daya dace da doguwan rigan tajuyo har Ammi tagama sa kayan da sauri tawuce gaban madubi hoda ta dauko da kawalli da man baki, kallonta Ammi tayi ganin ta kwaso kayan kwalliya zatai magana Aneesa kaman zatai kuka tace "ni Allah saina miki" shiru Ammi tayi babu yanda ta iya, karasowa tayi ta shiga mata light makeup ta shafa mata man baki sosai Ammi tai kyau har tazo tanajin wani iri dan tamanta rabonta datai kwalliya haka, sallaman dasukaji nasu Baffa yasa Aneesa tace "kisa hijabin bari naje na gaida su" fita tayi da sauri daidai Baffa ya shigo da Dady dayaci manyan kaya na milk shadda sai kamshi yake bazawa, babban dadduman su dasuke shimfida ma baki Aneesa ta dauko ta shimfida tana murmushi tace "Abba sannu dazuwa" cikeda fara'a yace "lallai y'ata ta warke masha Allah, naji dadi, ya jikin?" "Alhamdulillah naji sauki Abba ka zauna" tanunamai dadduman zama yayi tareda yin bismillah, Baffa yace "jeki kira Maman ki saiki dauko tsaraban ki kizo musha a tsakar gida" gyadamai kai tayi tajuya da sauri tai dakin Ammi, Ammi na zaune kan gado tasaka hijabin tai kyau sosai kaman wata sabuwan amarya wani irin tsalle tadaka tafada kan jikin Ammi tana dariya, salati Ammi tace "innalillahi, Oh Allah, haladai kinyi alkawari ne saikin karyani kafin gobe da safe ko Aneesa" kyalkyacewa tayi da dariya tace "Ammi na wlh dadi nakeji, Baffa yace kije, nidai natafi, Ammi na kimai firan nan naki mai dadi" dukan da Ammi ta daga hannu zata maka mata yasa ta tashi da sauri tafita daga dakin tana murmushi ledan tsaraban ta tadauka Baffa dake kallonta yace "yauwa muje" murmushi Dady yayi yace "laaaa ni baza abani ba" da sauri tazo gaban shi tabude mai ledan tace "a'a Abba gashi kasha" tafada akunyace, dariya yayi yace "nagode Allah amfana" cikeda fara'a Baffa yace "yakara auki daharna fara kukan zuci zaka shanye mana kashu dinmu" dariya dukansu sukayi Aneesa tabi Baffa suka fita tsakar gida a binsu suka zauna kan tabarma suna hira suna sha.



Saida Ammi taji fitansu sanan ta tashi ahankali sosai takejin kunyan yanda Aneesa tamata gayu kaman wata yar yarinya, ahankali tayaye labule tafito falon kanta akasa idanun Dady kyam akanta ko kyaftawa ba yayi, karasowa cikin falon tayi zata zauna akan kujera Dady ya nuna mata gefenshi da hannu kan dadduman yace "zoki zauna anan Rukayya" dan dago kai tayi suka hada ido da Dady gyadamata kai yayi hakan yasa ahankali takaraso wurin dadduman ta zauna inda yake nuna mata kusada shi amma adan kwai gab tsakanin su.

Ajiyan zuciya Dady yasauke yana kallonta murya chan kasa yace "kinyi kyau sosai Rukayya" kasa dagokai Ammi tayi dan maganan yabata kunya murya chan kasa tace "barka da zuwa, ina yini, ya aiki" murmushi yayi sosai yace "baza akalleni ba Rukayya, idanuwana na kwadayin ganin fararen idanun nan naki masu sanyaya ma Muhammad Ibrahim zuciya" wani irin masifan kunya kalaman shi suka bama Ammi ahankali tadaure tadago kwayoyin idanunta dasuka sha kwalli ta daura akan Dady, wani irin lumshe ido yayi kafin yabude su ahankali ya kalleta murya chan kasa yace "godiya nake yallabiyata" sallama Aneesa tayi ta tsaya abakin kofa tana jiran abata izinin shigowa, ahankali Ammi tace "shigo" shigowa tayi dauke da best tray dinsu mai kyau da maltina mai sanyi ke kai sai kulan tuwo da miyan kuka dayaji wake da kifi da dan bowl dake dauke da ruwan wanke hannu sai goran ruwan Eva maidan sanyi Baffa yasiyo maltinan da ruwa, karasowa tayi ta ijiye tray tace "Abba ga abincin ka nan, Ammi na tadafa ai zaka cinye ko" da sauri yana kallon fuskan Aneesan yana mata murmushi yana masifar son yarinyar yace "kwarai kuwa, tunda Ammi ki tadafa ai dole na cinye harda side kwano" murmushi sosai Aneesa tayi tadan saci kallon Ammi data watsa mata harara tamike tafita daga dakin takoma wurin su Baffa.

Kallon Ammi Baffa yayi cikeda so ahankali yace "nagode da karamci, musamman kikamin girki dole na cinye abincin hasken idaniyata" murmushi Ammi tayi tasa hannu zata jawo tray dan serving nashi yace "zanci anjima kadan, yanzu lokacin kine bana cin abinci ba" murmushi Ammi tayi tama rasa mezatace itadai wanan mutum na kashe mata zuciya da kalamai.




Gyara zama Dady yayi yana facing Ammi dake wasa da yatsun ta yanda Aneesa keyi, ahankali yace "ina kaunar ki sosai Rukayya sabida ina ganin kaina aduk lokacin dana ganki, ayau nazo wurinki dauke da batu biyu danake so namiki masu mahimmanci" shiru Ammi tayi ta baci dukkan natsuwan ta sabida yanda taga yanatsu shima alamun maganan dazai mata mai ma'ana ne, dan ajiyar zuciya yayi yace "Rukayya banso mugina rayuwan mu kan karya kokuma yaudara, Inaso mugina rayuwan aure na amana da tsantsan kauna da jinkai, maganan farko dazan miki shine kome zaki gani agidana badaga wurina ba wurin matana kiyakuri bazan miki karyaba matana sai ahankali, sai ahankali kome zasu miki baruwanki dasu ba zaman su kikeba zamana kike, banso kiyi koyi da dabi'oisu, sonake nakara aure konadinga samin kwanciyan hankali daga wurinki" yay dan shiru kafin ahankali yace "sai magana tabiyu, marayan d'ana Aliyu shekaran shi ashirin da tara yanzu, mahaifiyar shi tarasu tun kafin yadan tasa, inaso kihada shi dashi da Aneesa kirike minsu amana Rukayya, matayena basa sonshi ko kadan abinci inba ina gidan nanba nace akaimai ba'a kaima, baida hayaniya ko kadan zaki ganshi, baida fada, baima cika magana ba, Komi nashi inaso yadawo wurinki, nabaki shi Rukayya kece mahaifiyar shi zuciyata ta yarda sanan ta aminta dake, kirike minshi amana kinji Rukayya hope ban hadaki da aiki babba ba?" dan murmushi Ammi tayi tace "ko kadan, d'a nakowa ne, baka hadani da aiki ba, nakuma gode da matsayin daka bani namaka alkawari zan kula dashi amana, bqzaka taba samuna da zalunci ko ha'intar shiba, na karba, na karbi Aliyu da hannu bibbiyu, Allah ya shige mana gaba" "Ameen" Dady yace yana wani irin jin son Ammi aranshi. Shiru duk sukayi suna kallon juna Ammi ce tafara breaking kallon ta nunamai tray tace "abincin ka zai huci kaci dan Allah" murmushi Dady yayi yace "ina zan iyacin abinci batare danasan ranan da zan mallaki Rukayya amatasayin matata ba uwar yarana guda biyu Aliyu da Aneesa" wani irin cute smile Ammi tayi batare data kalleshi ba, cikin wani irin murya Dady yace "idanuna na maradin wanan sassanyar kallon naki mai sanyayamin rai gimbiya" dagokai Ammi tayi ta kallai, ahankali yace "yaushe zaki bari na mallakeki kidawo mallakina?" ahankali Ammi tace "duk randa kakeso Yallabai" washe baki Dady yayi yace "yau Wednesday ko" gyadamai kai Ammi tayi, murmushi yayi yace "ran jumma'a nakeso adaura auren bayan antaso daga masallaci inyaso zan iya kara miki ko kwana biyu ne ko sati daya kigama shiryawan ku na mata saiki tare ko Gimbiya" dan murmushi Ammi tayi tace "hakan ma yayi, Allah yasamana albarka aciki" dan lumshe ido Dady yayi yabude yace "ina kaunar ki sosai Rukayya," yy maganan ahankali yana kallon Ammi kaman yana jiran tacemai wani abu murmushi sosai Ammi tayi tamika hannunta tadauko kulan abincin ta ijiye kusada shi tana kokarin budewa ahankali tace "ina kaunar ka nima Yallabai tun ranan dana fara ganinka" numfashin Dady yakusa daukewa da sauri yace "wayyo Allah na ban ruwa Rukayya zuciyata ta dadada dayawa, dole in kora da ruwa" murmushi sosai Ammi tayi tana girgiza kai tadauko ruwan tabude ta mikamai tana kallonshi kafa ruwan yayi abaki ya asha yana kallonta kafin ahankali ya mika mata goran, karba tayi tace "kaci abinci to" faraci yayi ba karamin dadi abincin yamai ba tass yaci ye tuwon hakan yama Ammi dadi ba kadan ba, ya wanke hannu yana share baki sanan ya kalli agogo goma saura tashi yayi yace "bari intafi, amma fara bani izinin tafiya tukunna" murmushi Ammi tayi tace "nabaka" "tom saida safe" gyadamai kai tayi tace "Allah ya kaika lafiya, nagode" har bakin kofa taraka shi yatafi su Baffa suka rakashi waje Aneesa ta shigo tareda rungume Ammi tana murna, yarane suka shiga shigo da jakunkunan na kayan kwalama daga baya kuma saiga su Baffa abinci tanasu suka ci suma suna mata maganan ran jumma'a za'a daura auren wai inji Alhaji. Karan shigowan sako dataji yasa tabude.
_na manta ban gayamiki ina tsananin kaunar ki kafin natafi ba, ina miki Son so, ki kulamin da kanki gimbiyata, Allah yamiki albarka, saida safe_
_Alhaji Muhammad Ibrahim_
Murmushi Ammi tayi ta ijiye wayan bata taba sanin zata karason waniba, bama tasan Yaya akai Dady ya sace mata zuciya ba kodan sabida yanda yakeson Aneesa ne? Kokuma sabida yanda Aneesa keson shine? Kokuma da iya maganan shi da halin taimakon shine? All she knows is tanason each and every single shade of him.

_duk wacce takaranta bata biyaba itada Allah, duk maison book dinan ta tuntubeni ta 07012181461 watsapp_
_masu fitarwa dama ku watstsatsu ne, saika kuka watsawa, ban yafemukuba kuma, rubabbu kawai_
_*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



3⃣1⃣



Gida suka karasa bayan sun tsaya sunyi sallan isha'i, thank God Momma bata falo dakinsu ya wuce direct dan ko kadan bazai iya tsayawa mata magana ba, ko takalmi bai cireba yafada kan gado yaja bargo yarufe tundaga kanshi har zuwa kafafunshi, inda ace zai biyema zuciyan shi kuka kawai zaitayi batare dayasan mezaiyi ya sanyayamai raiba, he's so soo maddd, so angry, ya tsani yaga Aneesa dawani tanamai magana jiyake kaman zai fadi yamutu, baima san tayaya zaiyi describing yanda zuciyan shi kemai zafiba idan ya ganta dawani, jiyake kaman ana daddatse mai zuciya da babban wuka, wani irin wahalallen bacci ne yay awon gaba dashi yana cikin tunani. Abdul ne yabude kofar dakin ya shigo zaimai magana yaga har yay bacci ya dunkule agado looking so innocent ko kayan jikinshi ma bai cireba yana sauke ajiyan zuciya daddaya, ahankali yazauna abakin gadon yana kallonshi yana tunani yaushe har soyayyan barkono yakama shi haka? Rashin amsan tambayan shi yasa shima duk yunwan da yakeji yaji takoma ciki ya kwanta gefen Aliyun shima batare daya cire kayaba nan wani shegen bacci yay awon gaba dashi.




Momma dake kitchen dasuka shigo ne tafito Ihsan dake biyeda ita tafito itama, Ihsan ta kalla tace "jeki kiramin su suzo suci abinci" sama Ihsan tayi bata wani jimaba ta sauko tana dariya tace "Momma duk sunyi bacci ko takalma basu cireba" girgiza kai Momma tayi tace "Aliyu da Abdul ai saidai Allah ya shirya domin kam duk kanwar ja ce" ta gyara zama tana kokarin daukan remote dake kan dayan kujeran tace "jekici abincin ki Ihsan".







Sai wuraren shadaya sanan Aneesa tabaro wurin Baffa dasuka wuce dakin zaure dasuke kwana itakuma tadawo daki, kulle kofa tayi dan tasan Ammi ta riga ta kwanta, dakin Ammi ta wuce straight Ammi na zaune kan gado tana linke kayan data cire, kallo daya tama Aneesan ta dauke kai, murmushi Aneesa tayi takarasa kan gadon ta zauna kusada Ammin, kayan ta karba takarasa linkewa ta tashi tai wajen sip din Ammi, sip din tabude tana kokarin maida kayan ciki tace "Ammi kinason Abban? Naga su Baffa sunce jibi ne bikin" tana maganan tana jera kayan a sip, jin Ammi ba tace komiba yasa ta juyo ta kalleta, hada ido sukayi da Ammi dake kallonta, washe baki tayi takaraso ta zauna kusada Ammi tareda daura hanunta kan cinyar Ammi tace "eh Ammi, bakice komiba" dan murmushi Ammi tayi tace "kina sonshi to Aneesa, ba dole na yarda ba" washe baki tasake yi tace "nagode Ammi na, Ammi kinga ko nizan miki lallen biki, in miki kwalliya dakomi ko Ammi" tabe baki Ammi tayi tace "nine zanyi wani lalle saikace bikin yar yarinya" kaman Aneesa zatai kuka tace "wlh nisaina miki, Ammi na mai shegen kyau kinji" tabe baki Ammi tayi tace "naji to, Allah kaimu da rai da lafiya" Ameen Aneesa tace haka tacika Ammi da surutu har Ammi tagaji tace mata tamata shiru kota maketa, gabaki daya tama manta da batun wani Aliyu daya bata mata rai dazu, bamata so ta tuna ko kadan, mamanta is getting married so she's super excited.




_masu iya magana sunce rana bata karya, saidai uwar diya taji........_

Yau dubannin jama'a wayanda suka halarci sallan jumma'a a babban central mosque in Suleja, wanda ya kunshi mutane da dama daga ciki harda abokanen Dady na wajen aiki da kasuwance, Aliyu, Abdul, dakuma Baban Abdul (mijin Momma), shi kanshi Dady dayaci wata fitinannan shadda wacce taci sunanta shadda, dakuma su Baffa da fuskokin su ke dauke da annuri, limami ya daura aure tsakanin Alhaji Muhammad Ibrahim da kuma Rukayya Hamisu, inda su Baffa da mutane da dama suka shaida sai murna ake ana hayaniya, sosai Aliyu ke murmushi he's trying his best yaboye damuwan shi dan baiso Dady yagane, today is a happy day for Dady baiso yaga any sign of something a tattare dashi ya shiga damuwa, yanada matsala daya addabi zuciyan shi ainun rabonshi da Aneesa tun ranan nan, yakira layin ta taki dagawa daga bayama kashe wayan tayi gabaki daya, gajiya ma Yayi da amsa gaisuwan mutane ganin kanshi yafara masifan ciwo ya kalli Abdul dake kusada shi shima yana sanye cikin shadda fara kaman tashi yace "am going home" da sauri Abdul yace "me haka? Kasan Dady zai nemeka ko" yatsine fuska yayi yace "stay kai, am having headache, inya tambayeni kacemai naje gida" yana yin maganan yay tafiya yana kallon Dady dake washe baki kaman anmai kyautan makka yana gaisawa da mutane, yawuce ya shiga mota yaja zuwa chan Abuja dan yasan koyaje gidan momma dake nan Suleja dakwai hayaniya kuma baison hayaniya ko kadan, yana danna mota cikin gidan Maman su Rauda na fitowa daga motar ta datai parking, wani natsiyacin kallo tama motarshi ko damuwa baiyi a yabude yafito yay side dinshi batare dayama inda take second look ba ballema yasan wats she's up to, kwafa Maman su Rauda tayi tace "inhar ban koyama Aliyu hankali ba aduniyan nan basunana Kareema ba wanan alkawari ne namaka, wlh kuwa" tai kwafa tawuce dakinta.

Bude part dinshi yayi ya shiga yaji ko ina na kamshin turaren wuta lumshe ido yayi yabude dan yana mugun son kamshi kuma yasan aikin Rauda ne hakan yamaida kofar yarufe yya hanyar bedroom dinshi, kaya yarage ya shiga wanka koyaji dadin jikinshi, baiwani jimaba yafito yana yatsine fuska sanye da bathrobe yafada kan gado tareda daukan wayanshi yana kallon number Aneesa yanaso yakira but yasan koya kira bazata dauka ba, ahankali bacci yay awon gaba dashi.





_Bangaren su Ammi, Suleja_
Yau jumma'a tun kafin a daura auren wuraren karfe takwas nasafe Momma da kawayenta suka kawo akwati guda goma inda saiti bakwai na Ammi ne dake cike da hadaddun kaya da an dinka wasu wasu kuma ba'a dinka ba saiti uku kuma na Aneesa ne da aka cikamata da kaya na yamma ta harda dogunayen riga Aneesa harda kuka, few kawayen Ammi na anguwan ne suka tarbesu itakuma Ammi taki fitowa har suka tafi anata guda daga baya aka daura hadadden abinci dan tun jiya Dady ya turo da motan kawo abinci Aneesa tama Ammi hadadden lalle bana wasaba ta shirya Ammi cikin wani lace mai kyau sky blue da fari ta rungume Ammi yafi sau dari sabida yanda Ammi tai kyau sanan takawo wani farin babban mayafi ta yafama Ammi, Ammi sai amsan gaisuwa take tana murmushi ka ganta itada Aneesa zaka zaci y'a da kanwa ne, Aneesa itama wani farin lace tasaka mai ratsin pink shima dadin ne yaaaimata takai aka dinka mata tai kyau telan dudda bai aunata ba amma chip chip yamata yafito da shape dinta sosai bana wasaba sai murna take ko ita ke aure albarka.

Wajajen karfe uku anguwan ya cika da maza da mawaka ana wake Dady, Baffa ne ya shigo ya leko ya kira Aneesa dake tsakar gida tana nan tai chan tama kasa zama waje daya da gudu tai wajen Baffa a zaure, baki Baffa yarike yace "wai wai wai, masha Allahu, ashe haka yar tawa keda kyau aida kyar naganeki wanan kyau haka" wani irin cute smile tayi cike da zumudi tace "Baffa an daura? Yanzu Abba yadawo mijin Ammi na?" tafada cikeda wani irin murna gyadamata kai Baffa yayi yace "kinsan mezakimin yanzu anjima zamuyi hira, yanzu jeki kawomin maman ki nan dakin mu ta zauna kifito, sabon baban ki keson yimata magana" da sauri Aneesa tace to Baffa tajuya da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login