Showing 114001 words to 117000 words out of 180150 words

Chapter 39 - A Tsakankanin Soyayya Book 1 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

26 Sep 2025

2440

rau yaji kaman wacce ke zazzabi, murya chan kasa yakira sunanta "Aneesah, Fateema, Fateema" ahankali take motsi da ido jin ana kiranta kafin tabude idanunta duka ta saukesu kan Dr zaid dake bayan Baffa tsaye ya rungume hannu a kirji yana kallonta. "Aneesah" kiranta dataji an sakeyi yasa tasauko da kanta kasa ta kalli gabanta, Baffan ta tagani a tsugunne yadaura hannu kan fuskarta kaman yau yafara ganinta yama kasa cewa komi, ahankali tace "Baffa" kallonta Baffa ya tsaya yi yakai almost 2min abubuwa da dama nakai komo a zuciyan shi kafin yamike tsaye yamika mata hannu yace "sauko mutafi gida wanda yakawo ki karmu tsareshi dare nayi" yunkurin tashi tafito tayi taji kanta kaman zai cire sabida ciwo, tashi tayi ahankali tana dafa kujera idanunta na jujuyawa cikeda karfin hali tafito daga motar, kafafunta ne suka fara rawa kafin tasa hannunta ana Baffa tai baya luuu zata zube da sauri Baffa yatareta yana salati. "innalillahi wa innailaihi raji'un Aneesa" da sauri Dr yazo wurin yatsun shi biyu yadaura kan wuyanta yace "ta sume batada lafiya, Inane gidanku Abba" da sauri Baffa yace "kasan layin nanne kadan" "shigo mota da ita na sauke ku inada kayan aiki mukaje saina dubata" adan rude Baffa yace "kai likita ne?" gyadamai kai yayi Baffa ya shiga motar ahankali rike da ita yarufo musu kofan ya zagaya ya shiga yatada motan Baffa na nunamai harsuka karasa wani gida dakeda dogon dakali agaban gidan, sai wata yar Honda da tayoyin gabaki daya sukai less pake a kofar gidan, parking yayi yafito Baffa yafito rikeda ita yace "mushiga ciki likita" boot Dr Zaid yabude yaciro wani akwatin aiki sanan yabiyo bayan Baffa shiga gidan sukayi babban gidane sosai mai fili daga ta wuraren zauren kiwo ake awurin shanaye da awakai ne da aka garkame su dayawa, sai kuma tsakar gidan sai dakunan dakenan ajera guda shiga, sallama Baffa yadoka yana kwalama matarshi kira yabude wani daki dababu komi ciki saiyar katifa akan gado maidan kyau ahankali ya kwantar da Aneesah ya kalli Dr Zaid dake tsaye yace "zoka dubata likita" karasowa Dr yayi yana sanya stethoscope a kunne yazo yadubata sanan ya dago kai yace "abani ruwa Abba" da sauri Baffa yafita, ganin Baffa yafita yasa da sauri Dr Zaid yaje wurin kafarta wando nta yaja sama nan yahango wukake har guda biyu a jikin safanta kwashesu yayi duka yajefa cikin aljihun wando shi hakanan yaji bayaso susan tana yawo da wukake ko ahaka ma jibi yanda tsohom nan da mahaifiyar ta suka dawo ai zasu shiga damuwa sukaga abinda tazama, drip yadauko da allurai yay aciki sanan yamakala mata yana cikin makala mata Baffa ya shigo tareda matarshi datadan mayyanta rikeda ruwan tace "subhallahi Aneesa ce haka, Allah yabaki lpy" takaraso tace "ga ruwan likita salla nakeyi ne dazu dakika shigo" karban ruwan yayi bayan yagama samata drip din sanan yay dipping hand dinshi inside the water yaciro yakai kan fuskarta yana shafawa wani irin ajiyan zuciya ta sauke kafin ahankali tabude idanun dasuka kankance ta daura akanshi, wani irin faduwa gabanshi yayi da sauri yatashi tareda rufe akwatin shi yadauka tareda juyowa ya kalli Baffa yace "zan tafi Baffa jikin zai sauka dan nai allurai a ruwan danake karamata, inhar jikin bai saukaba ka kirani gobe da safe saika kawota asibitin danake aiki, amma yanzu abata abinci taci sanan tai wanka ta tsaftace ko ina harda wanan gashin nata zataji dadin jikinta" "baza'a yiba din m we ruwan ka dani eh?" cewan Aneesa data farka cikeda karfin hali, dukansu juyowa sukayi suna kallonta barinma Baffa daida gabanshi yay mummunan faduwa dayaji yanda tai magana, tashi tayi ta zauna cikeda karfin hali tana kallon drip din cikin fushi tace "kazo kacire abunan ko wlh na tashi saina fedeka" ahankali Zaid yajuyo yazuba mata idanu kallo daya yamata yagane dudda uban karfin halinta inta tashi tafiya biyuma sunmata yawa saita sake zubewa ta sume dan babu abinci acikinta, Baffa daya kasa magana yana kallonta Zaid ya kalla yace "abata abinci Abba da madara tasha, saida safen ku" wani irin yunkurin tashi Aneesa tayi da sauri inna tace "a'a mutuniyata ihakuri zauna bakiga bakida lafiya ba" ta kalli Baffa cikeda saiyasa tace "Mai gida aje asayomata madaran, likitan mu gode" "niban godeba wlh" Aneesa tafada tana ballamai harara juyowa yayi ya kalleta kafin yadauke kai tafice daga dakin yana mamakin masifan yarinyar.
_*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



5️⃣8️⃣





Wani irin zaro idanu Maman Rauda tayi tace "innalillahi wa innailaihi raji'un Rauda!" takasa gasgata abinda idanuwanta ke gane mata.

Aliyu ko motsi kirki yakasa saima wani irin rike Raudan tsam dayayi ajikinshi yakara barinta yanajin yanda take wani irin nishi akunne shi, arude Dady ya shiga kiciniyar karbanta yace "Rauda, Rauda Gadanga bani ita kaga" fitowa sauran polisawan da sojojin sukayi aka tsaitsaya ana kallo ahankali Dady ya karbeta jini na fitowa ta gefen bakinta tana wani irin nishi, taushe baki da hannu Hajar tayi tana kuka sosai, arude Dady da hankalin shi ke gab da fita daga jikinshi yace "call the Dr Aliyu, call him" ya kalli Raudan datake wani irin nishi hawaye na fitowa daga idanunshi yace "stay with me kinji y'a, u will be fine okay, likita yanzun nan zaizo, yayanki zai kira Dr" yay maganan yana dagakai ya kalli Aliyun daya fitoda waya amman yama kasa tabawa tsabagen rudewa yakasa dena kallon Raudan yanda jini ke fita tawajen scissors din yanabin interlock din tsakar gidan, Dady zaiyi magana yaga Rauda tadaga hannunta ahankali tana rurrufe idanu ta mikama Aliyu wani irin zubewa Aliyu yayi kasa ya kama hannunta gam saiga hawaye sharr da sauri ta girgixa mai kai tana wani irin nishi da kyar tabude bakinta dake fitar jini sosai tace "no crying uh'uhn, be strong for me, be a very strong man Ya Aliyu, k.....kada...wo namiji, inaso kahada kan kowa na gidan nan let's our family be united, no more sluggishness ka...ji" da sauri Aliyu yadaga kai wasu hawayen nazubomai sosai, murmushi tadanyi cikin tsananin azaba ta lumshe ido ahankali tace "D....a..d" da sauri Dady daya daurata kan cinyarshi yace "na'am Rauda na" hannun Aliyu tasake rikewa da kyau tace "Ya Aliyu na son Aneesah ka auramai ita, Dady!" tasake kiranshi da sauri Dady da muryanshi ke rawa sosai yace "na'am Rauda" dan shiru tayi takasa magana saikuma tabude idanunta ta kalli Hajar dake tsaye tana kuka sosai tana kallonta, murmushi tamata ta kalli Aliyu dake rikeda hannun ta hawaye nabin idanunshi, murmushi tamai tace "in Aneesa ta haifi Baby girl zakasa sunana Ya Aliyu?" dawani irin sauri Aliyu ya gyadamata kai hawaye na gangarowa daga idanunshi ya matse hannunta yace "yes Rauda, I will name her princess Rauda, the best, the most sweetest and the most caring little sister in the world" murmushi tayi sosai da saida duka hakoranta dasuka hade suka bayyana, hannunta daya rike ta shiga kiciniyar kwacewa hakan yasa yasaki hannun yana kallonta ahankali takai hannun kan idanunshi ta lakato hawayen dayake yi tareda girgiza mai kai tace "daga yau no more shading tears, no more crying over any abu dake damunka, kome kakeso kome kedamunka ka tashi tsakar dare ka gayama Allah, show the world ba old Ya Aliyu bane, u are strong, u are a fighter, u are capable, I hate seeing you cry, karka kara kaji" hannunta dake kan fuskarshi ya damke wasu hawayen na shirin fitowa ya hannasu ya fuzar da iska heart dinshi nawani irin strengthen and getting tough, wani irin ajiyan zuciya ta sauke sanan tajuyo da kanta ahankali tazubama Maman ta da officer yarike gam ido, yanda take kallon Mama yasa jikin Mama ya shiga rawa saita saki wani irin mugun kuka tace "kiyafeni Rauda, dan girman Allah kiyafen, kiyakuri, nayi nadama, inda nasan kezan sama da banyi ba wlh" wani irin numfashi Rauda ta shigayi tarike hannun Ya Aliyu gam da sauri ya kalleta, numfashin ta shiga yi da sauri da sauri ta juyo ta kalli Aliyu tana wani irin nishi lips dinta na rawa da sauri Dady yace "call Dr Aliyu" arude Aliyu ya shiga neman number Dr, ahankali Ammi ta tsugunna Dady yabita da kallo, hannunta ta daura kan goshin Raudan dake wani irin nishi jinin na bulbulowa sosai tana kallonta tace "la'ilaha illallah, Muhammadu Rasulullah, la'ilaha illallah Muhammadu Rasulullah" duka wajen daukan kalman akayi ana bata ahankali bakinta yadauka tayi kafin ta lumshe idanunta rup, hannu Ammi tasa tacire dankwalin kanta dayake babbane ta warware tarufa matashi ta kalli daga Dady harsu Aliyu dake jiran tacemusu wani abu ta girgixa musu kai alamun takoma ga mahallicinta.
Wani irin uban ihu Maman su Rauda tayi. "wayyoooooo Allah na na shiga uku na lalace, Rauda, na shiga ukuuuuuuu, mena aikata ni Kareema? Na kashe y'ata? Wayyo Allah na, wayyo Allah na, wayo wayo" juyowa Dady yayi da jajayen idanunshi ya kalli officer yace "dan Allah kufitar min da matanan daga gidan nan" turata cikin mota akayi tanaji tana gani aka fita da ita.

Kafin kace me mutane sun cika gidan da anguwan ma makil, bayan sallan la'asar akai jana'izan ta aka kaita makwancin ta.


_Ya Allah ka jikin dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya, Ya Allah ka gafarta musu, Ya Allah kakai haske kabarinsu, Ya Allah kasa sunhuta, Ya Allah muda bamu riga munkoma gareka ba Ya Allah kasa mu mutu muna musulmai, Ya Allah kayafemana kurakuran damuka aikata, Ya Allah ka karemu zuwa hanya madaidaiciya. Ya Allah ka dubemu badan muba badan halinmu ba ka warkan da alumman ka daga wanan cuta ta corona virus, Ya Allah ka kawomana karshen ta, Ya Allah ka tsaremu ka tsare alumman musulmi gabaki daya, Ameen Ya Rabbil Alameen_


_*Good Morning GGM*__*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



5️⃣9️⃣

_How to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta WhatsApp number na 07012181461 sainai adding naki a group din a tsakanin soyyayya. For those dabasu da account zaku iya tura katin MTN ta WhatsApp number na 07012181461_


_*see in bakida kudi karma kisake ki karanta littafin nan dan wlh banyafe miki ba zaki biyani hakkina alahira*_

_*keda kika biya access fee kikai joining group dina danki karanta littafi ba littafina kika siyaba so bakida anything kimin sharing book waje, saisa nai free pages, masu neman free pages kuje Wattpad dina "mamanshakur" and read, inhar kika fitarmin da littafi waje wlh keda Allah, Allah baya yafe hakkin wani sai in shi ya yafe miki*_






_kaduna_
Sanin batajin dadi yasa Baffa yahana Inna karta tadata da asuban ya shiga dayan dakin yatado yaranshi maza guda uku dasuke gida, Khaleelu, Ibrahim da Mubarak sukai alwala suka dunguma suka wuce masallaci.


Wuraren tawas nasafiya Baffa ya shigo gidan yabar yaranshi a makarantan asuba da akeyi a masallacin, inda matasa maza da mata suke haduwa amusu karatu sai karfe taran safe ake tashi. Da sallama ya shigo gidan yatsaya wajen akuyoyinshi da shanaye yana dubasu ya kwalama Inna kira. "Maman Hamma" daga kitchen Inna ta amsa. "na'am mai gida kadawo?" "kinbama awaki dusan kuwa?" tana juye tafashashen ruwan zafi a kullin koko data dama tace "eh najuye mai gida" shikadai Baffa ya shiga magana yana dudduba awakan yace "shine sukemin kuka kaman basu ci komiba da safen nan" tashi yayi ya kakkabe hannunshi tareda wankewa dawani ruwan dake cikin botiki sanan ya yarfe hannu yana tafiya cikin gida, Inna daya hango a kitchen tana kokarin hada musu kari yasa yay dakin da Aneesa take da sallama ya yaye labulen tareda tura kofar dakin hasken rana ya shigo dakin ya sauka akan fuskarta, dan motsi tayi sabida hasken daya hasko fuskanta da kyau, karasowa ciki Baffa yayi ganin karin ruwan yakare dayake nurse din jiya tanunamai yanda zai cire mata koda yakare kafin likitan yazo yasa yakarasa yakama hannunta tareda ciremata ya zauna ata baki bakin gadon yana kallon fuskanta yana tunani, gabaki dayan Aneesa da mahaifinta take kama banbancin su shine bata dauko hasken fatar shi ba saita dauko bakin fatar mahaifiyarta, bala'in tausayin yarinyar yakeji yarasa mesa ga mahaifiyarta tai aure, ga abinda mijin mahaifiyar yamata, in sha Allah kome zaiyi sai yayi mata dan yaga tafara walwala tadawo kaman da, zai mata duk wani abu dazai mantar da ita wahalhalun datasha gidan yarin nan dudda baida karfi amma duk inda zai samu saiya samo danya bata jin dadi. Ajiyan zuciya ya sauke yakai hannunshi ya daki filon da kanta kekai bude idanunta dake cikeda bacci tayi tai kini kini da rai kaman dama fada suke, murmushi Baffa yayi yaja hancinta da hannu yace "nine ke tashinki, tashi kiga gari yariga yawaye" yay magana yana dagata danta zauna, ahankali ta tashi ta zauna, hannunshi yakai yataba wuyanta yace "ya kikeji yanzu? Meke miki ciwo?" murya chan kasa tace "bakomi" shiru yayi ganin yanda take amsa shi dai dai kaman tana fada dashi, kaman ance dole saita amsashi, ahankali yace "tashi kije kidauro alwala kizo kiyi sallan safiya" tashi tayi tafita daga dakin tana tafiyarnan daidai kaman yar gidan sarauta tafita tsakar gidan daidai Inna tafito daga kitchen rikeda katon botikin kokon data dama, cike da fara'a ganin Aneesan tafito ga doguwan riganta data bata ya mugun yimata kyau gwanin ban sha'awa yasa tace "har kin tashi ne yar arziki, ya jikin?" ko kallon inda take Aneesa batayi ba tawuce abinta ta buga kofan bayin kaman dashi take fada kofar yabudu ta shiga ciki takara bugo kofan, kofan yarufe, karkada kai kawai Inna tayi tareda yin murmushi taji zafi amma batawani ji zafi ba tasan ba laifin ta bane, ta yaye labulen babban falonta ta shiga ta ijiye botikin a tsakiya tareda kwaso kofuna na robobi irin masu marfin nan ta zuzxubama kowa sanan tafito takoma kitchen din tana hadama Baffa dumamen tuwon jiya, ta hadamai asamiran shi tai dakinshi, fitowa shima Baffa yayi daga dakin Aneesan jin Inna na kwalamai kira......





Inkinsan bakida kudi karma ki karanta min littafi dan wlh banyafe miki ba, duk wacce ta karanta bata biyaba Allah ya isa.
Fitowa Aneesa tayi daga bayin bayan tadauro alwala daidai lokacin yaran Baffa sun shigo gidan, dawowan su daga islamiyan safe kenan suna dan hiransu, Khaleelu da Ibrahim sun girmeta, Khaleelu yanzu yanada 25yrs, saurayine kawai yanada karamin jiki ne dan jikin Innan su yadauko saisa baka gane ya girma, sai Ibrahim shikuma yanada 23 shi yamafi Khaleelu girma inka gansu zaka zaci shine babba dan har gemu gareshi gashi ustazu yanada kokarin sosai a fannin islamiya shi capinta ne, sai Mubarak wanda yake sa'an Aneesan yadan bata watanni da bazasu wuce uku ba zuwa hudu, washe mata baki dukansu sukayi ganinta tafito daga bayi, tun jiya da daddare suke so suje dakinta Inna tahanasu akan batada lpy, wani irin mugun tsaki Aneesa taja ganin yanda suke kallonta suna washe mata baki kaman tace sumata dariya. "mtswwwwww" tawuce tagabansu tai dakinta batare data kallesu ba, da sauri Mubarak dake sa'anta yace "kai badai ni kikama tsakin nanba yarinya? Wlh saidai su Ya Ibrahim kikamawa dan lallasaki zanyi mara kunya kin san halina ai yanda nake daddakaki in munzo Suleja" Aneesah harta shiga daki taji maganan Mubarak din karaf a kunenta da sauri ta daga labule tafito ta tsaya abakin kofa da kyau tana kallonsu daga wurin ta kalli Mubarak tareda nuna kanta da yatsa cikin kunan rai tace "dani kake wayan nan maganganun?" da sauri Mubarak shima cikin zafin kai irin na saurayin dake tasowan nan yace "a'a da wata nake tunda akwai wata bayan ke a tsakar gidan ne" kwafa Aneesa tayi tace "Allah yasoka dan inda dani kake da banga abinda zai hanani parke ma bakin nan dakai magana dashi ba, dogo ba hankali kawai" cikin fushi Mubarak yataso zaiyo kanta Khaleelu baban wansu yarike shi yace "me haka bakasan bakuwar mu bace? Aneesa cefa dakuke wasa tare lokacin da ake zuwa da ita datana yarinya, ka manta Aneesan da Abba ke kwasan mu muje Suleja ganinta, me haka? Common yar uwan ka ce, share, forget" cikin fushi Aneesa tace "barshi karma ya share baisanni bane, zan gwadama hankali yaro, dogo ba hankali kawai" cikin fushi Mubarak keson kwashe hannunshi daga hannun Ya Khaleelu yace "Ya kagani nitake cema dogo ba hankali ko, wlh takara cemin dogo ba hankali saina fasamata baki wlh kuwan" da sauri Aneesa tace "shege kafasa ance dogo ba hankali, kazo inhar kai dan halak ne" wani uban tsalle Mubarak ya daka ya fizge hannunshi yay cikin gidan ganin yana tahowa yasa Aneesa ta shiga waige waige, wukan data hango a makwarara inda aka kai kayan wanke wanke yasa tai wurin da gudunta ta tsugunna tadau wukan ta rike da kyau ta kalli Mubarak din dake zuwa kaman namijin zaki tace "kazo kaga wlh saina maka barakaka" da sauri Mubarak yakarasa gabanta batare daya damu da wukan data daukaba dan yasan duk wargi ne yasa hannu yadaga zai kifamata mari Aneesa ta daddage tayanki fatar hanunshi da wuka, atare daga Khaleelu har Ibrahim sukai ihu dan duk basu zaci zata iya amfani da wukan ba sukayo kansu da gudu.





Wani irin ihu da Mubarak yayi yakoma baya yasa da sauri Baffa dake zaune kan yar kujeran dakinshi yana sauraron labarin BBC hausa na safiya yana kallon Inna na zubamai man shanu kan dumamen shi itama tana sauraron labaran da yakeji ya rage karan da sauri yana gyara zama jin kaman yaji ihu, hayaniya dasuka ji na yaransu yasa atare suka Mike tsaye da sauri,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login