Showing 111001 words to 114000 words out of 180150 words

Chapter 38 - A Tsakankanin Soyayya Book 1 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

26 Sep 2025

2449

kofar bedroom dinta da key sanan tadawo ta zauna ta share fuskanta tass, anatse tace "Aneesah na?" "uhm" ta amsata ahankali, sake daurewa Ammi tayi ta hana kanta kuka tace "kina ina yanzu haka a ina kika samo wanan wayar dakike kirana da ita? Tuntuni kina inane eh? Ina polisawan nan suka kaiki?" dan shiru tayi kaman bazata ce komiba saikuma ta dake zuciyarta nawani irin tafarfasa tace "prison! Ina gidan yari Ammi!" wani irin kuka dayazo ma Ammi yasa da sauri tadau pillow gefen gadon ta taushe bakinta tana kuka sosai, yarta ne Alhaji zaikai gidan yari? 20yrs old mace Alhaji zai aika prison? Me Aneesa tamai? Mai Aneesa tamai? Jibi yanda gidan yari yadawo mata da y'a? Dudda bata ganinta amma jibi muryan yarta, Alhaji ya cuceta bazata taba yafemai ba, Aneesan ta ce yanzu tai rayuwa a gidan yari? Tai wahala taga ukubobi na rayuwa haka? Ko hanyar gidan yari batasani ba amma tanajin labarin gidan yari tunko tana Amarya. Takai almost one minute ba tace komiba kafin ahankali ta janye pillow ta ijiye cikin wani irin muryan ban tausayi Ammi tana girgiza kai tace "how are you Aneesah na? Are you fine? Are you okay? Me suka miki achan? Sun wahalar dake?" gyadama Ammi kai tayi kaman tana gabanta cikeda dakewa tace "lafiyata kalau karki damu Ammi" gyadamata kai Ammi kawai tayi kaman tana ganinta tana mugun mamakin Aneesan, tasan she's just forming tasan karya take mata, tanaji a jikinta yarta ta wahala, tasha azaba, murya chan kasa tace "kina ina yanzu?" kallon hanya tayi tace "ina hanya ansakeni daga gidan yarin suka jefar dani wani mutumi yadaukeni zai kaini asibiti saikuma na farka yanzun nan" da sauri Ammi tace "kika farka? Suma kikayi?" girgixa kai tayi tace "Ammi karki damu, lafiyata kalau" "innalillahi wa innailaihi raji'un Aneesah, Aneesah, Aneesah wayyo Allah na zuciyata zan mutu" Ammi tama rasa natsuwarta sai sambatu kawai take tana kuka sosai da sauri Aneesa ta katse wayar dan inta cigaba da sauraron yanda Ammi ke kuka Ammi will just break her heart ne, kifa kanta tayi ahankali kan cinyoyinta mutumin nan nabinta da kallo, dudda wayan ba'a speaker takeba yana tsintar some maganganun Ammi cikima harda yanda Ammi ke kuka tana tambayanta meya sameta sosai yaji sun mugun bashi tausayi dudda baisan wacece itaba but hakanan yaji ajikinshi something da kuma situation ne yadawo da ita wanan yar daban.







Ringing da wayar ya shiga yi Aneesan taki dagokai balle ta dauka yasa ahankali yace "answer the call, ur Mum is calling again" katsewa wayar tasake yi wani wayan yakara shigowa ganin batada niyyan dauka yasa ya matzo ahankali ya karbe wayan daga hannunta ya kalli screen din kafin yay picking yakara a kunne. Cikin kuka sosai Ammi tace "Anee....sah na" ahankali guy din yace "Assalamu Alaykum" da sauri Ammi tace "bawan Allah waye kai? Ina y'ata?" ganin yanda duk Ammi ta daburce yasa yace "calm down Mum relax, sunana Dr Zaid, a per-term Dr prison din da yarki take, I only come idan akwai any surgical issues daza'ama prisoners, yau na shigo nai surgery bayan nagama naga anyi releasing yarki a sume, I could not leave her that way is against my professional code of ethics shine na dauketa with the hope nakaita asibiti aka dubata tana farfadowa saita nemi iyayen ta but kafin nakai saita farka, relax am not a bad person bazan taba cutar yarki ba dan nima inada kanwa mace sanan inada y'a mace shekarunta biyar aduniya bazan so wani ya cutanmini su ba, yanzu tell me kina ina nakaiwo miki ita nasan Abuja sosai dan wurin zuwana ne" ajiyan zuciya Ammi tasauke ta goge fuskarta tace "bawan Allah nagode maka, yanzu taimako daya nakeso kamin so nake ka tayani kaita Park, kasata a motar kaduna gidan kanin babanta zata" da sauri yace "kaduna Mum, ai am going back to kaduna yanzu haka, kin yarda dani natafi da ita kokuma na kaimiki ita Park din?" dan shiru Ammi tayi kafin ahankali ta nisa tace "na yarda dakai kodan diyarka dakacemin kanada, ka kaimini ita kaduna zan sanar da Baffan ta zai sameku ya karbeta ahanya" ahankali yace "to shikenan" zai katse wayar Aneesa tadago kai ta fizge wayar daga hannunshi ta kara akunne cikin wani irin murya tace "nace miki inaso naje kaduna ne Ammi?" shiru Ammi tayi kafin tace "keda gidan nan har abada Aneesa, ki tafi wurin Baffan ki nima zanzo nasame ki a wajen, duk wanda ya cutar mini dake nabarsu da Allah, Allah baya bacci no need for you to come back here and cause issues nasanki, ki barsu da halinsu, watarana sai labari kinji, kiyakuri, kije wurin Baffan ki kijirani anan, am coming for you okay" gyadamata kai tayi ta katse wayar ahankali tana huci. Kunna motar yayi yaja ta gefen ido yake kallonta ta mugun bashi tausayi ganin yanda take goge kwalla tana fighter tahana kanta kukan amma takasa, ganin yanajin tausayinta over yasa ya maida hankalinshi kan tukin dayake yi baisake kallonta ba.




Number Baffa Ammi ta nemo ta kira, ringing daya ya dauka, ahankali Ammi tace "barka da warhaka Baffa" "barkan mu dai Maman Aneesa" dan shiru Ammi tayi kafin ahankali tace "Baffa ansaki Aneesa yau tana hanyar zuwa kaduna, zan turama number mutumin daya dauketa, Baffa ka kulamin da Aneesah, Baffa Aneesa need strick care gidan yari Alhaji yaturata, zadaika ganta dakanka, Baffa rayuwata nacikin kunc....." takasa magana sabida yanda kuka yaci karfinta, haushin ta sosai Baffa yakeji amma ayanda Ammi ke kuka sai jikinshi yamai sanyi yasan koshi baikai Ammi jin bakinciki faruwan komiba, murya chan kasa cikeda lallashi yace "kinga, kinga Maman Aneesa, calm down komi yay tsanani maganin shi Allah, wanan jarabawa ce da yardan ubangiji kuma zamuci, dan haka kiyihakuri, kuma karkiji komi akan Aneesa Allah yakawo ta lafiya koma me tadawo yarmuce ahaka zamu rungume ta da hannu bibbiyu sanan we will shape her to our like, addu'a kawai zakiyi tamata kinajina, kul karna karaji kinyi kuka kan zancen nan tunda ansakota Alhamdulillah, duk wata matsala da sauki ce da yardan Lillahi, share hawayenki" ahankali Ammi tasa hannu ta share hawayen tass ta sauke ajiyan zuciya, murya chan kasa tace "Baffa sai magana ta biyu" da sauri Baffa yace "oho ina jinki" ajiyan zuciya tasake saukewa tace "Baffa alfarma nakeso, inaso ka saidamin da shanayen Aneesa guda biyu so nake kabani dubu dari sauran kudin inaso kayi amfani dasu ka shigarmin da kara kotun musulunci anan kaduna, inaso araba aurena da Alhaji, dubu darin zan biyashi kudin sadakinshi dasu" shiru Baffa yayi tunda tafara maganan harta gama saida tace "kanajina Baffa" da sauri yace "inajinki" anatse yakira sunanta. "Rukayya" yanda yakira sunanta kai tsaye yasa Ammi tagane he's so serious dan he hardly call her name direct. Anatse Baffa yafara magana. "Rukayya na isa dake, sanan inada iko dake, kinada wani irin matsayi na yar uwata najini dabazan iya tsayawa ina ganin zakiyi shireba na barki, nasan kin tsani Alhaji sabida abinda yama Aneesa, bari kiji wata magana aduk lamarin nan laifin Alhaji guda nake gani, shine dabai tsaya yasaurare muba, kisaka kanki atakalmin shi, daga ke har Alhaji kunyi boko, yan boko kuma mutanene dasun yarda da technology, babu yanda za'ayi mutum kaman Alhaji yaga camera yakama abu haka bayan ya kalla kuma yace bahaka bane, tunda har yagani da idanunshi ga Aneesa nasaka poison bazai taba yarda ba itabace dole kuma ya hukunta ta, kar abin nan yasa kice zaki nemi saki, babu kyau saki, kin riga kinsa Aneesa tadawo wajena hakan dakikayi kin kyauta tabarmai gidanshi, Ke kiyi zamanki kicigaba da rayuwan aurenki, ki rubuta ki ijiye nina fadamiki wata rana Alhaji saiyazo yasa guiwanshi akasa yabaki hakuri, gaskiya bata boyuwa fa da dadewa, komujima komu dada gaskiya zata bayyana, Allah zai warwaremuku komi, zai wanke Aneesa dake, bama ke kadaiba, Alhaji harnan kaduna saiyazo ya roki Aneesa gafara, nidake bamusan gaskiyaba Allah zai bayyana mana gaskiya, kiyi hakuri bazan taba baki goyan bayan ki kashe auren nan kifito ba, amma kiyakuri dan ke wacce aka cutace, Allah zai bimiki hakkin ki kowaye awanan lamarin sai Allah yatona musu asiri dai dai, daya bayan daya namiki alkawari, Aneesa kiyita mata addu'a, kimata fatan samin miji nagari na aurar da ita muhuta kinji Rukayya kiyahakuri" hawaye Ammi ta share bataso tama Baffa gardama hakan yasa tace "shikenan Baffa nagode" "yauwa, Allah yamiki albarka, kituramin number kinji" to.
_*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



5️⃣4️⃣

_07012181461 chat me up in kinason wanan book din_



.........
Dady yakai almost 20min awurin a tsaye yana mamakin what just happen yanzunan tsakanin shida Aliyu, inda yabari Aliyu ya kona kanshi da yaya zaiyi? Da ina zaisa ranshi, dagokai yayi ahankali ya kalli ma'aikatan wajen cikeda sanyi jiki yace "agyara wajen nan dan petir nada hatsari sosai" sanan yawuce yana tafiya ahankali ahankali duk jikinshi yay sanyi sosai yana kallon yanda matayenshi ke tashi daga window dasuke leke suna komawa ciki yadauke kai yawuce shashin shi yafada kan kujera.


Agurguje Aliyu yay wanka kusan sabi uku sabida yadena warin petir din sanan yafito, agurguje yake shirya wa dan baiso yabata lokaci, 3quater na gucci yasaka da wata dark brown paco robbani logo print shirt daya haska fatar shi yafito da kyanshi, fesa turare yayi yasa takalmin shi na prada sanan yadau car key dinshi yana dingishi yafito yay flat din Dady babu alamun wasa akan fuskanshi, ahankali yatura kofan dakin da sauri Dady dake kishingide kan kujera yatashi yazauna da kyau yana kallon Aliyun kaman yau yafara ganinshi, har gabanshi Aliyu yakaraso ba yabo ba fallasa yace "Wani prison ka kaita Dad?" yadanyi shiru yana kallon Dady kafin ahankali yace "zanje nadauko tane" sosai Dady ke mamakin shi dansai yanzu yakara ganin son Aneesan akwance kan fuskar Aliyun, ahankali Dady yanisa yana kallon fuskanshi dasaiyau ya yarda da maganan manya cewa abinda kafiso shiyafi baka matsala banda haka ace duk wanan abin dayake ma Aliyu bayagani, yazaci in Aliyu ya warke yaji meyayi he will be proud of him yarungumeshi yace I love you Dad, you are the best saidai yaga akasin hakan, sabida shine fa ya kulle Aneesa amma duk bayagani, yarinyar dataso aikashi lahira saima haushin shi dayake ji, ahankali yace "Zilanious prison take" dago idanu Aliyu yayi ya kallai irin kallon nan na Dady zaka iya aikata haka kafin ahankali yajuya kawai yafita daga flat din Dady na binshi da kallo yawuce yafita abinshi batare daya waigoba koya juyoba.







Yayi tafiyan almost 30min sanan yakai prison din shima da taimakon Google map, parking yayi yafito yana zare bakin glases din idanunshi kafin ya shiga ciki hargaban kanta inda wata guard take ga katon book din rubuta name of visitors a gabanta, tun kafin Aliyu yakaraso inda take take wani irin jarababben kallonshi wani irin dan gayune yau haka yazo prison dinsu, turaren shi daya fara mata sallama yasa tadawo daga yar gajeran tunanin datake, tace "Well done Sir, barka da zuwa yallabai, wakazo gani?" girgiza mata hannu yayi alamun he's not here to visit anyone, cikin kwantacciyar muryanshi yace "am here to pick up someone da akai releasing" da sauri tace "what's her name sir?" "Aneesah is her name" zaro ido tayi ta kallai tace "Aneesah barkono? Ai indai itane ansallame ta tun dazu about 30-38min ago ma kam" dukan wajen yayi cikeda cinrai zaijuya yawuce tace "Sir excuse?" dan juyowa yayi ya kalleta, murmushi tayi tace "don't be offended zan dan yimaka personal tambaya ne" gira daya yadaga mata batare dayay magana ba alamun go on am all ear, murmushi tayi tace "Sir you are so cute wlh, please wats your relationship da Aneesah" dan tabe baki yayi ganin tambayan gulma ce yace "am her husband to be, and Aneesah is Cutie than I" da sauri tace "no way wlh, kai kaga kyan ka kuwa gaka fari kaman jinin bature, kafita kyau" ahankali yace "I will take that as a compliment, as 4 me tunda nake I've never set an eye on a lady that is as beauty as Aneesah ba in my life, she is the definition of Queen of heart, excuse me" yajuya yafice daga wurin da saurinshi ya shige mota yana duba agogon wayanshi maybe hala to takai gidama, dawani irin sauri yaja motar baida burin daya wuce yadaura idanunshi akanta and apologise to her on his father's behalf.


Ahankali sallan la'asar takama shi ya tsaya yayi sanan yakoma mota gabanshi na faduwa yakosa yaga Aneesan, parking yayi a compound dinsu ysauko daga motan yana dingisawa yay flat din Ammi, sallama yayi tareda bude kofan falon, Ammi ce kadai zaune kan kujera sai bowl dake dauke da sliced fruit masu sanyi da fork ta tasa agaba tana kallo takasa ci tadago kai tana kallon Aliyun, da sauri Aliyu yamaida kofan yarufe yakaraso gabanta tareda tsugunnawa yadafa hannun kujeran yace "Mum am just coming back from the prison ance tuntuni aka sallamota inkika fitarmin da novel waje Allah ya isa ban yafemikiba





Ina take Mum ta iso ne? Yay maganan yana waige waige ko ina kozai ganta kafin ahankali yajuyo da kanshi ya kalli Ammin kaman yanda take kallonshi yace "Mum tadawo? Kodai Dad baisa asaketa bane? Bari naje nasame shi" yay maganan yana mikewa tsaye zaitafi yaji ankama hannunshi, ahankali yajuyo ya kalli Ammin, ganin yanda take kallonshi yasa ahankali ya tsugunna yace "Mum, menene Mum? Baisakota bako kibari naje nasame shi" girgiza mai kai Ammi tayi ahankali tace "yasaketa Aliyu, amman Aneesa da gidan nan har abada tagama zaman shi" wani irin faduwa gaban Aliyu yayi yace "wat! Mum! Ina kikasa taje? Mum bazan iya rayuwa babu Aneesa ba, am sorry Mum bangaya miki ba, I love Aneesa sosai, I want to marry her, please Mum kisata dawo gida I promise you zan wanke Aneesa agaban kowa I will prove her innocent" tunda ya ambaci kalman so Ammi ke kallonshi jitayi kaman ya sosa mata inda ke mata kaikayi ko kadan bataso ta tsaneshi but idan tacigaba da zama tana tuna abubuwan da mahaifinshi yamata zata gaggasamai maganganune hakan yasa tamike tsaye ahankali tareda daukan bowl din fruits dinta zata wuce da sauri Aliyu dayakeji kaman zai zare yace "Mum dan Allah ki tsaya, please just tell me ina kikasa Aneesan taje? Mum dan girman Allah kifadamin wlh Mum kaman zuciyata zata fashe dan Allah karki rabamu, I love Aneesa and she loves me too, Mum aure zamuyi, Mum inason Aneesa sosa......." "Aliyu!!!" Ammi tawani irin juyowa tareda kiran sunanshi ta hanyar dakamai tsawa, da yatsa ta nunashi tace "karna karajin, karna karajin ka furta kanason y'ata, karna sakejin kace y'ata na sonka, Aneesah bazata taba aurenka ba har abada, bazan taba bada y'ata ga yaron wanda ya kulle min itaba, Aneesah tama barmuku garin gabaki daya bazaku kara ganinta ba that I promise, sanan ka tashi kafita daga flat dinan kafin raina ya mugun baci, get out! " Ammi ta dakamai tsawa tareda mai pointing kofa, ja idanun Aliyu sukayi kallo daya zakamai saiya baka tausayi kaman kamishi kuka, baki yabude zaiyi magana Ammi tace "I said out Aliyu" juyawa ahankali Aliyu yayi saida yakai bakin kofa ya tsaya yajuyo ya kalleta yace "nasan kina fushi Mum, and you have the to be, no body wish yaga an kulle mai da agaidan yari bama police station ba, Mum kisani ko banyi danke ba nothing is going to stop me daga wanke abin sona Aneesa, I will prove to everyone that Aneesah na is very very innocent someone putted everything, saina wanke Aneesah, and flat dinki kike korana ko saina dinga zuwa Mum, saidai in kiyita korana kullum" yay maza ya share hawayen daya zubomai yajuya yafita.
Da sauri Ammi tajuya tai sama maganganun Aliyu sun tabata ba kadan ba, takusa kuka daurewa tayi ta zauna akan gadonta tana goge kwalla.
Duk wacce ta karanta batare data biyaba Allah ya isa, duk wacce ta fitar da book dinan waje Allah ya isa ban yafeba.


Tunda yay nisa a tafiya take bacci, har Baffa yakira sukai magana yacemai a express road zai tsaya ya jirasu dan gidansu na danaba ne duk batasani ba bacci take kaman wacce tai shekaru batai bacci ba, taji dadin AC sosai, sosai yake gudu ana kiran sallan magrib ya shigo kaduna-Abuja express road, wayarshi yaciro yay dialing number Baffa, ringing daya Baffa ya dauka yace "sannu Malam, sannu da kokari kun shigo express road dinne?" "eh Abba mun shigo" da sauri Baffa yace "to shikenan ka karaso ina tsaye bakin titin zaka ganni nasaka jallabiya mai ruwan goro da bakar hula, akwai carbi a hannuna dan daga masallaci nake" "to" ya katse wayan yacigaba da tukin yana kallon gefen titi, yay tafiyan kusan minti uku sanan yahango Baffa dattijon kirki yana tsaye bakin titi yanajan charbi yanabin kowacce mota daya wuce da kallo, horn ya danna mai hakan yasa Baffa yadaga hannu da sauri, yadan karyo kwana ya parking daidai baki bakin anguwan da Baffa ke tsaye ya kashe motan tareda fitowa, Baffa da sauri yamikamai hannu yace "sannu danan, Allah yasaka da alhairi" kasa karban hannun Baffa yayi saidai ya tsugunna yace "barka da warhaka Abba daftan mun sameku lpy" murmushi Baffa yayi yace "Alhamdulillah, tashi, tashi, Allah shi albarka" tashi tsaye yayi yace "bacci take tunda muka shiga hanya gatanan" yay maganan yana bude dayan door din Baffa biyeda shi abaya, Aneesa yagani babu ko dankwali akai gashin nan yarufe fuskanta yabar kadan, tana sanye dawata koriyar riga tagidan yari da koriyan dogon wando, sai kambas fari daya dawo brown shima duk na gidan yarin ta takure jikin kujera tana bacci wani irin tausayi data bama Baffa ko baisan lokacin daya tsugunna gaban motar ba, ahankali yakai hannunshi ya yaye gashin fuskar nata yadaura hannunshi kan fuskanta zafi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login