Showing 63001 words to 66000 words out of 180150 words

Chapter 22 - A Tsakankanin Soyayya Book 1 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

26 Sep 2025

2426

sauri takoma cikin gida Baffa yakoma waje ko minti daya ba'a yiba shida Dady suka shigo zauren tareda Baffa dakin su Baffa yabude ma Dady yace "shiga ka zauna na aika Aneesa takirata, cikin gidan mata sun cika abinka da gidan sha'ani" shiga ciki Dady yayi ya zauna yana murmushi yanadan girgiza kafa yawani irin kosa yaga Ammi ta shigo.

Har gaban kofar dakin Aneesa takawo Ammi dake wani irin jin kunya sosai sanan tawuce takoma cikin gida da gudu, bin bayanta da kallo Ammi tayi tana sauke ajiyan zuciya kafin ahankali tasa hannu tabude kofar dakin ta shiga ciki ahankali da sallama, mikewa tsaye Dady yayi yana yana gyara babban riganshi dayasha lafiyayyen aiki yana kallon Ammi, kasa jure kallon daya ke mata Ammi tayi hakan yasa ta saukar da nata kan kasa, ahankali tashigo tana taku daidai anatse har gabanshi kafin ta tsugunna ahankali zata gaidashi da sauri yawani irin riketa batare daya bari ta tsugunna ba yadago ta tashi tsaye tayi tana kallon fuskarshi kaman yanda shima yake kallonta wani irin kyakyawan runguma yabata tareda sata a kirjinshi da kyau yahada da malummalum da hannuwanshi yawani irin zagayeta yana sauke ajiyan zuciya ahankali tareda lumshe ido yana shakan dadaddan kamshin turaren dake tashi daga jikinta, lamo Ammi tayi tana sauraron yanda beat din zuciyar shi ke sauka a natse it feels gud to be back, bakaramin natsuwa taji ya shegeta ba da wanan runguman dayamata ba, sunkai kusan 5 minutes a rungume da juna kafin ahankali Dady ya dagota tareda tallabe fuskarta yana kallon simple makeup din da Aneesa tamata yace "karki kara cewa zaki tsugunna ki gaidani kinji Matata" gyadamai kai Ammi tayi tareda dan lumshe ido tabude su ahankali, ahankali ya sumbaci goshinta tareda rike mata hannu yay kan kujeran dayake ya zauna sanan ya zaunar da ita gefenshi yajawo kanta ya kwantar akan kirjinshi yanadan shafa mata baya, Murya chan kasa ta yanda daga ita sai shi zasu dinga jin abinda suke cewa yace "Alhamdulillah, ina tsananin farin ciki da wanan ranan Rukayya, I feel blessed dana same ki a matsayin mata sanan ina rokon Allah daya bani ikon kula da ke da yaranmu biyu yanda yakamata" gyadamai kai Ammi tayi kanta na kirjinshi tace "Ameen" murmushi Dady yayi yakama hannu ta da Aneesa tamata lalle yana shafawa lallen ya masifar mai kyau murya chan kasa yace "Rukayya anya zan iya hakura har kiyi satin dayan danace zan baki kiyi dan kikarasa shirye shirye kuwa?" yay dan jimm sai chan yace "ana daura auren nan dana ganki yanzun nan a matsayin mallakina, matata wacce nakeda iko da ita sainaji bazan iya daurewa ba kuma banso ko kadan na takura miki wlh" daya yanda yake maganan dudda kanta na kirjinshi bata ganin fuskarshi tasan yana cikin damuwa ne and one thing datama kanta alkawari shine kaman yanda har mahaifin Aneesa yakoma ga Allah yabonta da kyawawa dabi'unta yake haka zata kasance ga Dady, she will never give room dazaisa Dady yay complain akanta ba, zatabi mijinta zatai kyautatamai, zata karenshi sanan ta kare dukiyar shi, ta kula da komi nashi domin al jannar ta na karkashin tafin kafanshi ne, ahankali tadago da kanta daga jikinshi ta kalleshi tace "kayakuri kadagamin kafa kabani yau kadai sabida nasamu na hada komi nawa, inyaso gobe saikazo ka daukemu mutare, nima nakosa na kasance tareda mijina abin sona, sanan abin alfaharina, uba ga yarana biyu Aliyu da Aneesa, an dagamin kafan nahada komi yau Abu Aliyu?" Ammi tai maganan tana shafa gemushin har zuwa kumatun shi ahankali with love and compassion, Dady jiyayi kaman kanshi zai tarwatse arayuwan shi yanason mace data iya lafazi masu dadi da taushi sanan da sanyaya ran mai gida, matan shi babu abinda suka iya arayuwan su banda habaici da yada magana, wani zubin sukamai habaici saiyaje office yafara rubutu zai ma gane bakin zaren habaicin, just at yanda Ammi tanunamai he's in total control of her, what a submissive wife sanan akarshen maganan tace mahaifin yarana biyu tasake karyawa da Abu Aliyu, tsabagen yanda maganan tamai dadi baisan sanda yajawo ta yadaura ta kan jikinshi ba, ahankali ya sumbaci bakinta ko kadan Ammi bata hanashi ba yakai kusan minti daya yanayi anatse kaman zai cinyeta sanan yasaketa yakai bakinshi saitin kunenta yace "nagode Gimbiya ta, Allah yamiki albarka Rukayya, gobe karfe hudu bayan sallan la'asar zan aiko motoci akawomin abin sona Ummu Aliyu, Abu Aneesa na tsummayan Ummu Aliyu ina sonki Rukayya sosai, don't ever change wayan nan kyawawan dabi'un kinji abin sona" gyadamai kai tayi tace "naji abin sona Abu Aneesa, I love you wujiga wujiga, zan iya tafiya ko yallabai baigama daniba tukunna" washe baki Dady yayi yana dariya irin ta manyan nan feeling bossy yace "a'a Yallabai baigama da Yallabiya ba, yadai kusa, kafafuna sunmin tsami ne sosai nafi awa biyu a tsaye wajen daurin auren nan" tashi Ammi tayi daga jikinshi tace "wai wai bari muga kafan" zama tayi a gefenshi tareda dan dukawa takamo kafan Dady dake sanye da cover shoe ta daura kan cinyarta, ahankali ta zare cover shoe din Dady sai kallonta yake kaman zai hadiyeta safan tacire ta ijiye kan hannun kujera tasa hannu ta ahankali ta shiga matsamai feet din Dady ya lumshe ido sosai yakejin dadin yanda tamai, almost 20min tadauka tana mammatsamai kafan harsaida dan gyangyadi yasoma saceshi tun yana kallonta sanan tasaka mai safa ta mayar ma da takalman shi ta ijiye kafan ahankali gudun kar ta tasheshi sanan ta matsa kisada shi tashafa sajen shi bude ido yayi tareda kama hanunta ya sumbaci hannun yana murmushi yace "nabaki izinin zaki iya tafiya kar anemeki" wani irin rausayar da kai Mami tayi tace "godiya nake mai gida" har bakin kofa yarakata yabude mata kofa tafita tana mai murmushi tai cikin gida, guda kawayenta suka shiga yi suna mata kirari Aneesa sai dadi takeji kaman zata mutu haka aka wuni sai bayan magrib baki suka fara tafiya Aneesa ta gyara gidan tass Ammi taje tai wanka da ruwan turare dana yan magungunan data hadama kanta dan Dady yabata kudi dasu tasaisai abinda take bukata na gyarani jiki.



Washe gari koda gari yawaye daidai da tsinke Aneesa bata bari Ammi ta daga ba ita ta gyara ko ina tahada ubansun abinci a big pot dan tasan anjima kadan zasuyi baki, sanan ta hura wani wutan ta daura ruwan wanka kafin tawuce ta shigo daki tai wurin Ammi, kallonta Ammi tayi tace "sako hijabi kije wajen Maman Aisha ki kiramin ita, sonake ragowan abincin nan da baban ki yakawo ayi biki dashi duk tazo ta kwasa ko" gyadamata kai Aneesa tayi tace "zataji dadi sosai kuwan Ammi dama baban su yanzu baya aiki" hijabi tasa taje takira maman su Aisha tare suka dawo ita tawuce kitchen tadaiji yanda maman su Aisha keta godema Ammi harda kukan ta, girkin takarasa taje tai wanka tadawo daki dama tariga ta ijiye kayan dazata sa tai gayu sosai yauma lacey takara sawa pitch wayaga ansami lace daban daban kyau tayi.

Wuraren bayan la'asar din kaman yanda Dady yafada motoci suka cika anguwan kaman za'azo daukan budurwa, Momma ce tazo da kawayenta guda uku suka shigo dakin kebewa tayi da Ammi dataji tana so sosai dan kallo daya kacal tama Ammi tasan zatafi sauran matan Dady hankali ta shirya Ammi tasa mata alkyabba akan hadadden lapaya dake jikinta sanan aka hadu da kawayen Ammi yan anguwa aka kai Ammi mota, Momma ta turo bodyguard ciki Aneesa na nuna musu kayansu dazasu kai mota akwatin nan su dayan abubuwan dasuka tattara duk suka tafi dashi tadauko dogon hijabin ta har kasa pitch tasa da takalmin ta mai kyau look so decent and magical tafito ta kulle gidan tajefa key cikin jaka tazo da sauri motan da akasa Ammin ta aciki Momma dataji tanason Aneesa tace "zoki zauna wajen maman ki" da sauri tazo dan dama tafiso ta zauna wajen Ammi ba dayan motan ba, motan daga Ammi sai momma sai kuma ita, kawayen momma na motan farko su kadai, sai motan karshe kuma kawayen Ammi ne aka dau hanyar City Abuja. Aneesa sai kalle kalle take oh yanzu zasu koma new gidansu ne.




Agaban wani katafaren tangamemen gida da sojoji guda uku ke waje akai horn wani soja daban daga ciki yabude musu kofa suka shiga, tundaga Gate Aneesa ke kirga manya manyan flat din dake makeken compound din, bata taba ganin hadadden gida hakaba ko gidan dataje kwanaki tai lalle albarka, babu kowa atsakar gidan saidai kofa dataga ana bubbudewa kaman an hada baki ana lellekowa, a parking space akai parking da sauri direban yafito ya zagayo yabude musu itadai Aneesa sai kallon ikon Allah take, Momma ce tafara fitowa ta kalli Aneesa dake murmushi bakinta yaki rufuwa tace "fito daughter" ahankali Aneesa tafito da kafar damanta dake cikin safa ta ijiye akan interlock din dake kasan gidan wani irin faduwa gabanta yayi tareda wani irin sanyi dataji ya shiga tundaga kasan kafan nata har zuwa brain dinta, "menene daughter?" tambayan momma yasa tadawo daidai murmushi tayi tace "kashina ne yay kara kas kas Mommy" dan dariya Momma tayi tace "gajiya ne kin aikatu saisa anjima kafin ki kwanta saikiyi wanka da ruwan zafi zakiji dadi" gyadama Momma kai tayi tafito gabaki daya wani irin iska ne taji yakada ta harsaida hijabinta ya shiga rawa ga sanyi daya ziyarci kowani gaba na jikinta, fito da Ammi Momma tayi Ammi tafito daga motan wani irin guda Momma tasaki kaman dabiyu tai gudan kawayen Ammi suka fara wake kawayen Momma na amshi suna tafi akai hanyar flat din Ammi itadai Aneesa na gefen Ammin ta, Rauda dake falo dukta kosa yafito ta kalli maman su datai kini kini da rai itada hajar suna keke ta window tace "Mama please kibarni naje na ga sabuwar matan Dady" dakuwa Mama tamata tace "inkin isa kifita kigani, mai bakin hali, mara mutunci yarinyar dabata kishin uwarta" tabe baki tayi tawuce fuuu tai dakinta cikeda fushi dajin haushin Mamansu.
_Duk wacce takaranta batare data biyaba, Allah ya isa, keda Allah, mai son book tamin magana 07012181461_

Abakin kofan flat din Ammi Momma ta tsayar da kowa ta kalli daya daga cikin kawarta dake rike dawani buta irin butan da dinan na silver dake cikeda ruwa tace "kawo butan Hauwa tai alwala sai a shiga daki" Ammi suka ba butan ahankali Ammi ta tsugunna tafara alwala ana guda ana wake saida ta gama tass sanan aka sa tai bismillah aka bude kofa ta shiga da kafar dama kasa kulle baki Aneesa tayi dataga dakin da akace na Ammin sune, dakine mai benefa a tsakiya, innalillahi komi na dakin sabo fill ga kamshin furniture's nan ko ina, kawayen Ammi ma kasa shiru sukayi sai masha Allah ake, azuciyoyin su suna ashe saisa taki aure jira take saita zaba takuma dirje, wanan gidan arxiki haka dole tai zaman kusan shekara sha tara ba aure gashinan yanzu ai yabiya ta chasko Alajin Allah kice bana sai makka su Rukayya da yarta. Sama sukayi da Ammi yayinda ake shigo da kayansu ciki har dakin Ammi suka kaita dayaji kaya gawani lumtsetsen gado royal, Momma takama hannun Aneesa suka fita daga dakin Ammi su biyu kacal wani daki dake kallon na Ammi tabude dakin yaji kaya ga fenti baby pink ta kalli Aneesa dake kallon ko ina tace "ga dakin ki nan" wani irin ware manyan idanunta Aneesa tayi ta nuna kanta tace "yanzu wanan hadadden dakin ne nawa Mummy?" gyadamata kai Momma tayi tace "eh naki ne daughter" wani irin rungume Momma Aneesa tayi tana tsalle tama manta batasaba da matan da kyau ba tsabagen murna tace "thank you, nagode nagode nagode Mummy kinji" sai kuma tasaki kuka sosai Momma taji Aneesa ta burgeta dan itama kaman Dady take tanason appreciative person komin kankanin abu ka nuna kaman a maka kyautan makka ne abun namata dadi, hannu tasa ta share hawayen datake tace "mena kuka? So kike maman ki ta shiga damuwa?" da sauri ta girgixa mata kai tace "Mummy dadi nakeji am happy, Ammi na is happy, kina sonta kuma Abba nason ta, jibe gidan da kuka bamu saisa nake gode miki, thank you so Mummy kinji Allah yabiya muku bukatun ku na alkhairi" rungume ta Mummy tayi kadan sanan tasake ta tana kallonta kaman mai tunani sai tace "kinsan menene?" da sauri Aneesa ta girgiza kai Momma tace "zan miki kawa, ko dayake bari Ince namiki kawa y'ata ce sunanta Ihsan, she's your age mate zan taho da ita nan gobe, ai zaki dinga zuwa gidana hutu ko" da sauri ta gyadama Momma kai tace "eh zan dinga zuwa Momy" "gud, yanzu stop crying zomu koma wajen maman ki kinji" murmushi tayi tace "to" Momma tace "to acire hijabin mana ustaziya ai anzo gida ko" gyadama Momma kai tayi ta zare hijabin tareda linkewa ta ijiye kan gado duk Momma na kallonta sai taji Aneesa ta kara burgeta abinda Ihsan bata iyaba kenan kome tacire daga jikinta saidai ta yar, hanunta ta kama suka wuce suka koma dakin Ammin ba'a jimaba Momma tafito ta sauka kasa dan kiran Dady ta sanar dashi matan shi basu kawo musu abinci ba ga baki, ko ruwa basu kawoba, fada Dady ya dinga yi danya fadamusu suyi harda ijiye musu kudi, hakuri Momma tabashi tace ya sharesu yanzu zatasa kawayen ta sudafa, ita da kawayenta ta tattara sukai store din gidan suka shiga girki mai rai da lafiya.




Wuraren 8 na dare Dady da Aliyu suka shigo gidan ganin Aliyu zaiyi hanyar part dinshi yasa Dady yace "let's go Son ka gaida new Mum dinka" yatsine fuska yayi ahankali yace "not today Dad, mutane sunyi yawa a shashin, am having headache inaso nadan kwanta".



_duk wacce takaranta batare data biyaba Allah ya sakamin, mai son book dinan should chat me up 07012181461__*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



3️⃣2️⃣




Fuskarshi Dady ya shafa yana kallonshi kaman maison gano wani abu cikeda damuwa yace "Gadanga na are you okay?" murmushi ya kakalo yace "yes Dad am fine, bari naje nai bacci, my regards to new Mum" gyadamai kai Dady yayi yace "love you Son" murmushi Aliyun yayi yace "I love you too old man" yawuce da gudu, dariya Dady yayi cikeda sonshi yace "zakaci gidan kune nine old man din" yajuya yana tafiya yace "kagamin yaro in karo amaryata yana cemin old man" yacigaba da tafiya yana kiran number Momma bamata amsaba tafito tazo wurinshi kudade masu yawa yabata yace "gashinan kibama wayanda sukazo, motoci na jiransu su fito amaida su gida" ahankali tace "to Yaya, nima zan wuce gobe zan zo, nama Aneesa alkawarin kawa so zan kawo mata Ihsan" dariya Dady yayi yace "I see, shikenan Allah kaimu gobe, ki kadomin wanan mai kunen kashin" dariya Momma tayi tace "Abdul shi zanma saka ya tukomu" da sauri Dady yace "kafin kiwuce ki kawomin Rukayya da Aneesa bangare na zan hada su namusu magana ne" da sauri Momma tace "to Yaya" tawuce tai hanyar flat din Ammi shikuma Dady yawuce flat din sauran matan shi yana fadamusu azo shashin shi harda yara sanan yawuce part dinshi, wanka ya shiga yay da ruwan zafi sanan ya shirya cikin simple jallabiya fara mai kyau dayadan fito da tebanshi ya feffesa turare, jin hayaniya afalon shi na yara yasa yagane sun soma zuwa, karasa shiryawa yayi tsaf yadauko faran hulan kwankwasa kaji hadisi yasa sanan yafito daga bedroom dinshi ya sauko kasa yana kallonsu da sauri kananun yaranshi na wurin Amaryan shi Amna da Ashna suka rugo da gudu. "oyoyo Dady" , murmushi yayi ya tsugunna ya dauke su dukansu sai jan gemunshi suke yana murmushi yana satan kallon duka matayen nashi dasuka zauna akan manya manyan kujerun nashi ko wacce tai kini kini da rai adole an musu kishiya barin ma Amarya, dan murmushi yayi ya kalli yaranshi su Rauda dasu hajar da sauran yaran dasuka dan tasa duk suna zaune akasa akan makeken carpet din wasu na wasa wasu na hira, karasawa yayi ya zauna akan kujeran wacce take nashi ne babba yana wasa da yaran suna dariya Rauda na murmushi dan ita bataga rashin sonsu da Dady bayayi ba da Maman su ke fada, wai Aliyu kawai yakeso ayaranshi, ita bataga hakan ba yanson su, yanason duka yaranshi, dankome suke so yana musu yana wasa dasu, Aliyu maraya ne, basu sonshi, basu kula dashi basa bashi abinci, sun tsaneshi ba dole yakula dashi da kanshi ba.


Cigaba da wasada yaran Dady yayi daidai yana jira yaji any of matayen nashi wata tagaishe shi amma basu gaidashi ba, sai kumbure kumbure suke, cikin fushi Maman su Rauda tace "wai wa muke jirane haka ake batamana lokaci" cikin fushi da kunan rai Amarya tace "ganemin fa, kya tayani tambaya sai, an shanyamu saikace kayan wanke ko yar gidan sarki muke jira ai sai haka" baki Dady yabude zaiyi magana Momma tabude kofa suka shigo itada Ammi dake sanye da hijabi har kasa sai Aneesa, itama sanye da hijabin ta har kasa tana gefen Ammin ta har wajen kujera Momma takawo Ammi da Dady yabi da kallo tace "ga kujera ki zauna" zama Ammi tayi ahankali tadan dago kanta ta kalli Dady dake kallonta cikeda natsuwa da tsantsan girmamawa tace "ina yini Alhaji, barka da dare" har wani irin lumshe ido Dady yayi da Ammi ta gaidashi muryanta na ratsa kowani bangare najikinshi, kafin ma yabata amsa ta juya ta kalli sauran matan dan kallo daya ta musu tagane matayen Dady ne tace "ina yinin mu" zama Aneesa tayi gefen kafar Ammi tace "ina yini Abba" murmushi sosai Abba yayi yace "lafiya lau daughter na, ya gajiya" cikeda kunya tana kare fuskarta da hijabi dan dakin da mutane da yawa tace "Alhamdulillah" sanan ta kalli matayen da Ammin ta ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login