Showing 105001 words to 108000 words out of 180150 words
Chapter 36 - A Tsakankanin Soyayya Book 1 Complete Hausa Novel
shi murya chan kasa cikeda wani irin harshe yace "Gadanga na" hannunshi daya yazare daga kan kumatun nashi ya sharce hawayen dake zubomai ahankali yace "Aliyu na, my Hydar, Son, katashi talk to me mekake so meke maka ciwo eh? Are you okay are you fine, how are you feeling now, Aliyu na yimin magana" dan lumshe ido yayi yabude da muryanshi da bata fita sosai yana kallon fuskan Dady yace "Dad" wani irin hamdallah Dady yayi ya shiga kissing ko ina a fuskanshi tsabagen murna, dariyan da likitocin suka shiga yi yasa Dady yasaki Aliyu yajuyo ya kallesu yace "Dr tun yaushe yafarka?" "around 2:30 na dare, haryay brush, yya wanka, likitan abinci yazo yabashi yaci, munmai running scan komi lafiya lau I must admit yaronka is strong, matsala daya muka gano shine for now zaidan dinga dingishi sabida gefen abdomen dinshi da poison din yaci shima with the help of medication nan da one month zai warware yadena dingishin, yanzu dai zamu ajiyeshi muyi observing nashi for 12 hours inhar babu wani abu zamuyi discharging naku" hannu Dady yamika Dr cikin tsananin farin ciki yace "thank you Dr, thank you, thank you so much" gyadamai kai Dr yayi suka wuce suka fita daga dakin, zama Dady yayi kusada Aliyun yasake rungume shi jiyake kaman yahadiye shi sabida tsan tsan so sai godema Allah yake waya yadauka zai kira Momma saikuma yafasa yafison sugansu tare kawai surprisingly. Matse hannunshi da Aliyu yasa da sauri ya kalli fuskanshi yace "menene Son, mekake so eh?" lumshe ido yayi yabude dan drip din da aka samai yana sashi jin bacci sosai murya chan kasa yace "Dad An....Anee..s...." da sauri Daddy cikin fushi ya girgiza mai kai yana shafa gefen fuskanshi cikeda lallashi yace "is not time to be remembering the past, I know everthing Son, nasan komi Gadanga, nasan komi karka damu yanzu kahuta, u need to be back on your feet sabida nan da jibi mubar garin nan mukoma naija ana nemana a office sosai, karka damu I know everything" lamo Aliyun yayi ajikin Dady jin yasan komi ya lumshe ido yana ganin fuskar Aneesan ahaka har bacci yay gaba dashi.
_Agurguje kunce nawuce muku nan🤣_
Sai wuraren karfe biyar Dr suka gama komi ganin he's fully back on his feet yasa akai discharging dinsu bayan yasayo duka magungunan shi suka fito yana tafiya ahankali yanadan dingishi suka fito Dad yasashi a mota sanan yakoma gaba yaja motan har gida.
Parking Dady yayi yafito da sauri yabude ma Aliyu baya sanan yariko hannunshi ahankali Aliyun yafito yanadan dingisawa sukai ciki babu kowa a hadadden palor yana kwalama Momma kira, Ammi na kwance akan gado taji hayaniya muryan Dady dana Momma Aliyu yadawo an sallameshi, lumshe ido tayi ahankali tareda jan bargo tacigaba da karatun littafin azkar ta, bude kofan da akayi aka shigo yasa ta lumshe ido, akanta Dady ya tsaya yana kallon fuskanta ahankali yace "an sallamo Aliyu da yarki taso ta kaishi lahira sabida bakin zuciya, muje ki ganshi" bude ido Ammi tayi tai kaman bataji shi ba tacigaba da karatun ta, bargon data lulluba dashi Dady yaja ya yaye yace "bakiji menace bane Rukayya ko bakinciki kikeda farkawan shi" ahankali Ammi ta ijiye littafin koba komi she don't have anything against Aliyu dan Allah kuma zata badan mahaifinshi ba tashi tayi ahankali Dady yabi jikinta da kallo yana hadiye miyau yanda cikinnan ke karamata wani extraordinary kyau, hijabi tadauka tadaura kan riga da skirt din jikinta tazo zata wuce ta gabanshi batare data kalleshi ba yarike hannunta fizge hannunta tayi tajuya tafita har zuwa falon inda Aliyu ke zaune kan kujera ya rame sai Momma gefenshi, alamun tafiya dasukaji yasa ahankali Aliyu yadago kanshi har wani irin sauke ajiyan zuciya yayi ganin Ammi, wani irin murmushi Ammi tamai batare data iso wajenshi ba ahankali tace "Aliyu masha Allah, ya karfin jiki?" ahankali yace "Mum" murmushi Ammi tamai tana danne zuciyanta tace "na'am Aliyu na, Allah kara sauki, Allah yabaka lafiya gabaki daya, sanni kaji" gyadamata kai yayi yana kallon fuskanta juyawa tayi takoma ciki tabi ta gefen Dady dake bayanta ta wuce bedroom dinta batare data kalleshi ba.
Kwana uku suka kara agarin tunda Aliyu yaga Ammi ranan bai kara ganinta ba dan bata fitowa ko kadan koya tambayi Dad ina take sai Dady yacemai batada lafiya saisa bai kawo komi a ranshi ba, damun Dady ya dinga yi su dawo Nigeria dan wani irin kosawa yayi yasa Aneesa a ido, dudda Dady yaso sudan kara ko sati dayane dan yaso yama Aliyun siyayya suje shopping amma cemai yayi bayaso inyaje Nigeria zaisai kome yake bukata yakoma yay resuming office da gym dan wanna karan yanason yanuna ma Aneesa he's not that lazy Aliyu dahar take gani tafishi karfi, dahar ta raina he promise she will the new and the strong side of her Aliyu.
Private jet Dady yakara musu booking dan sosai Ammi batada lafiya laulayi take bana wasaba kodan tadade batai ciki bane saisa cikin kemata kaman cikin fari oho, shikanshi Dady tausayi take bashi, ko ajirgi tai amai yafi sau biyar dudda Momma batamata wani maganan kirki amma saida tamata sannu Ammi ta amsa da Ammi, Aliyu sai sannu Mum yake mata tamai murmushi, da kyar daga baya bacci ya kwashe ta, Dady ya kwantar da kanta akan kafadarshi.
Karfe sha dayan dare jirgin su ya sauka a Nigeria already bodyguard din Dady suna Airport suka kwashe su sai gida, Aliyu was so anxious yakosa yaga Aneesa, sai kallon hanya yake kaman yarufe ido yabude ya ganshi agaban Aneesa.
Gate aka bude musu suka shiga, babu kowa a tsakar gidan Ammi bamata tsaya jiran su ba tai flat dinta tabude, falon yay dan kura bedroom dinta ta wuce dan gyare gyare tayi dan batason datti sanan tawuce bayi tai wanka tafito tai salla shima adaddafe sanan ta kwanta sai bacci shima rabi rabi daga baya tashi tayi ta buga tagumi saikuma tafashe da kuku. "Aneesa, Fateema na kina ina? Oh am here ni mahaifiyan ki am helpless narasa ta yanda zan kwatoki amma bazan gaji da gayama Allah ba, Aneesa Allah zai saka miki kinji komawa ye yamiki wanan abin, Allah baya bacci ko kadan, nasan yana kallon kome yake faruwa" surutai Ammi tayi kaman wacce tazare kafin daga baya tadauro alwala tazo taita salla har bacci ya kwashe ta akan dadduman.
Hasken rana dataji akan fuskanta yasa tabude ido, Dady ne tsaye a jikin window ya yaye labulen, murmushi yamata yana ganin yanda take mussike ido yace "ajiyata nasaki bacci sosai, tashi kije ki dauro alwala kizo kiyi sal...." ko tsayawa jin meyakecewa ma batayi ba tawuce ta shiga bayi murmushi Dady yawuce ya sauka kasa kitchen ya shiga yasa ruwan zafi ya fasa kwai soyamata yayi dan yasan bazata iya girki ba ya hadamata tea mai kauri sanan ya dauro a tray yafito yay sama, dakinta yabude daidai ta idar da salla zama yayi kusada ita yana murmushi yace "ina kwana tunda yau baza'a gaisheni ba" dauke kai Ammi tayi, murmushi yasake yi yace "yau gaba akedani bazama amin dan masifan ba, to zokiyi breakfast nabaki maganin ki kisha" tashi Ammi tayi zata shiga bayi yakamota hakanan da karfi da yaji yadaura mata abincin taci bayan da ta iya sanan yatashi yafitar da plate din yadawo ya shiga bathroom dinta ya wanke hannu sanan yafito ya kalleta yanda take goge kwalla yace "zan dan fita, karki yi aikin komi mai aikin ki zatazo anjima ta gyara ko ina, tai mopping duka kuran, nima bazan wani dade ba, signing kawai zanje nama wani bill a chamber saina dawo" sanin bazata kulashi ba yasa yarufo mata kofan, tashi Ammi ta shiga wanka tafito ta shirya cikin wani atampa ganin tagaji d zaman daki yasa tafito falo.
_bangaren Aliyu_
Dayake yanzu kowaccen su shigema Dady take sabida abinda yafaru yasa kowacce ta shirya yaranta tsaf harda fesa turare sukace sutafi side din Ya Aliyu sumai yajiki murmushi Dady dayaci karo dasu lokacin daya fito daga flat din Ammi yay gaba.
In bazaki biyaba karma ki karanta dan wlh in kika karanta banyafe miki ba.
Aliyu na zaune afalo ya jingina da pillow yana kallon TV yana sanye da white singlet da 3quater yana shan yogurt aka bude kofa da sauri yajuya duk idan yaji anbude kofa yake juyawa dandauka yake Aneesa ce, yakosa yaga ta shigo gaidashi, kanninshi yaga suna shigowa daya bayan daya harda Hajar, ahankali yasaki murmushi yana kallon kofa yanajira yaga Aneesa ta shigo saibai gantaba, karasowa sukayi suna gaidashi. "Ya Aliyu ya jiki, Ya Aliyu Ya jiki" murmushi yayi ahankali yace "da sauki" atare duk sukace "Allah kara sauki" sanan suka juya suna fita kaman iya abinda akace su fadamai kenan su fice, Rauda ce kawai taki fita suna fita tadawo kusada shi hannunshi tarike mai tana kallon fuskanshi kaman zatai kuka tace "Ya Aliyu sorry meke maka ciwo yanzu?" hannunshi yadaura akan gefen cikinshi, ahankali tadaura hannunta awurin tana kallon fuskarshi hawaye yataru a idanunta sosai ahankali kaman zatai kuka tace "sannu kaji Ya Aliyu, Allah zai sakama, bantaba sanin haka Aneesa takeba, bazan taba yafemana ba wlh" tunda takira sunan Aneesa yake kallon fuskanta surprisingly harta gama sanan ahankali yace "Aneesah?! Me Aneesah tayi?" hawaye Rauda ta share kafin ahankali cikin gunjin kuka tace "yunkurin kasheka tayi amma Allah yatona mata asiri shine Dady yakira police sukai arresting nata" wani irin dukan kirjinshi da maganganun Rauda yayi saida yasa ya zauna da kyau yana kallonta kaman mai tuhuma yace "yunkurin kasheni how?" fashewa da kuka sosai Rauda tayi tace "poison tabaka Ya Aliyu, poison fa, nazaci tanada kirki sabida taimakona datayi ashe bakar muguwa ce makira" tafashe da kuka sosai, tashi Aliyu yayi dawani irin sauri yazura slippers yana dingishi yawuce yafita kaman ba shine mai jinyaba yay flat din Ammi bude kofan flat din yayi kai tsaye ya shiga Ammi na zaune kan dinning tana kallon yar aikin dake goge TV daga gani kasan tunani take, jin karan bude kofa yasa tadago kai hada ido sukayi da Aliyu ahankali tadauke kai, maida kofan Aliyu yayi ya shigo dakin shidama tun suna C.A from yanda Ammi keyi yaji ajikinshi kaman something is wrong ahankali yake tahowa harya karaso gaban Ammi, ganin yanda ta kawar dakai kaman ma ta tsani tasashi a ido yasa ahankali ya tsugunna agabanta, hannu yadaura kan guiwan kafanta yana kallon fuskanta murya chan kasa yace "Mum" kasa daurewa Ammi tayi saida tajuyo ta kalleshi danjin kiran tayi kaman Aneesan tace takirata, kallonshi tayi batare data cemai uppan ba, cikin wani irin low calm tone yace "ina Aneesa Mum? Where is Aneesa?" hannunshi Ammi
ta ture daga kan gwuiwanta kaman wanda ya soso mata inda ke mata kaikayi ta mike da sauri dan bataso tasaki kuka agabanshi tace "ka tambayi mahaifinka Aliyu, ka tambaye ni" tai maganan tana kokarin wucewa da sauri Aliyu ya chapke hannunta, cikeda masifa Ammi tajuyo saikuma tafashe da kuka sosai gwanin ban tausayi tace "Aliyu ka sakenmini hannu, mahaifinka yana azabtar dani kaima kazo kamin nakane, nagaji, nagaji, da ace zan fadi namutu dayafiye min da zaman gidan nan" yanda Ammi ke maganganun tana kuka sosai yasa Aliyu yaji hankalin shi ya masifan tashi irin tashin hankalin nan da d'a yakeji idan yaga mahaifiyarshi namai kuka, tashi yayi ahankali yajawo Ammi yazaunar da ita akan kujera tareda kneeling agabanta yasa hannunshi ahankali ya share mata hawayen datake yi kaman zaiyi kuka yana girgiza mata kai yace "kidena kuka mahaifiyata, stop crying Mum kidena kuka" bottle water dayagani kusa da ita yadauka yabude ahankali yamika mata, karba tayi ta kurbi kadan ta ijiye, hannunta yakama yarike gam yana kallon fuskanta, Murya chan kasa yace "Mummy menene? Talk to me meke faruwa eh, ina Aneesah? Ina Fateema take? Why haven't I seen her" kafa Ammi ta shiga girgiza wa tana cizan lebe inka ganta zaka iya mata kuka she looks so pained and hurt, kokarin danne zuciyarta take tace "Aliyu banda abin fadamaka all I know shine Allah ne yasan gaskiyan komi kuma watarana zai bayyanata, amma ni Uwa ce nakuma san abinda nahaifa ciki da bai, Aneesa na nada zafi tanada fada amma hakan baitaba subjecting nata to being a murderer ba, Fateema na ko kaza bazata iya kashewa ba balle kai, amman akace itace tabaka guba sabida itace ta dafa maka pancake da coffee, akace ita ta hallaka ka, baba....baban....ka yamata.....yamata....du..." takasa magana sabida kukan dayazo mata lumshe ido Aliyu yayi zuciyan shi na tafarfasa sama da d'a, sosai Ammi ke kuka kafin da kyar ta tsayar da kukan tanajan hanci tace "mahaifinka daya bani assurance yamin alkawari zai kasance mahaifi, uba ga Aneesa, zai tsaremin ita sa'an nan yakare min itane yadaga hannu yamata shegen duka sanan yasaka polisawa sukai gaba da ita, su....su Baffan ta sunzo Susan inda take yahanani ganinsu yahanasu ganin Aneesan har.....har....yau babu wanda yasan inda Aneesa take, I don't know inda yarinya na take, yau sati hudu da kwana shidda bansaka Aneesa a ido ba, bansan inda takeba, Aliyu am so hurt, kaman na kashe kaina, I hate my self, I couldn't help my daughter, bantaba sanin haka masu kudi suke nuna fin karfi ba sai akan mahaifinka, mahaifinka ya....." takasa karasa maganan sabida tsabagen yanda kuka yaci karfinta kasa daurewa Aliyu yayi yamike tsaye da sauri yajuya yafita daga dakin dan bazai iya jure yanda Ammi ke kuka sosai agabanshi ba direct flat din Dady yawuce yana wani irin tafiya kaman zaki ya daki kofar Dady da kafa.....
Duk wacce takaranta batare data biyan dari uku ba Allah ya isa banyafe miki ba.
Afirgice Maman Rauda databiyo Dady ciki yanzun nan daga dawowan shi tajuyo daga ita har Dady, ganin Aliyu ne yasa tai shiru batare datai magana ba dan bataso Dady yahanata kudin dayazo nema, Dady ne dayaga yanayin fuskan Aliyu yace "menene Gadanga na lafiya you look somehow" daga kafa yayi yataho direct har gaban Dady cikin wani irin yanayi na seriousness yace "Where do you take Aneesa to Dad?" kallonshi Dady yayi zaiyi magana Maman Rauda tace "me kake tambayar wacce taso kash....." cikin wani irin fushi Aliyu yadaga mata hannu strictly yace "am not talking to you Woman!" ya kalli Dad cikin daga murya da tsananin zuciya sabida yanda ranshi ya masifar baci yace "I said where is Aneesa Dad?" cikin dakewa da daurewan fuska Dady yace "tana inda yakamata paying for her crime attempt murder da aka kamata red handed" cikin daurewan fuska Aliyu yace "ba abinda na tambayeka kenan ba, I asked you Dad ina Aneesah?" "babu wanda zan fadamawa domin bazan taba yafema yarinyar dataso kashemin d'a ba harsai ranan da aka gama hukunta ta daidai da yanda constitution of Nigeria yafada" Kallonshi kawai Aliyu yake cikeda mamaki yace "Dad how can you even believe, tayaya ma zaka yarda cewan Aneesa can poison me eh? Daddd" tashi Dady yayi azuciye shima yaja hannunshi yace "muje kagani da idanunka angayamaka nima dafarko na yarda cewa small Aneesa zata iya hakane saida nagani da idanuna".
_*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_
_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤
_✍🏿M Shakur_
5️⃣1️⃣ & 5️⃣2️⃣
_how to subscribe_
_zaki turo 300 to account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment to WhatsApp number na 07012181461, sainai adding naki a group din danake posting_
Sukai flat din Maman su Rauda, agaban dakin CCTV Dady ya tsaya yasaka password sanan yashiga ciki Aliyu biye dashi da sauri Dady yay gaban laptop din kafin yatabe tabe ya kunna footage din ranan, ya tariyo har zuwa daidai inda Aneesa ta shigo part dinshi yace "gashinan ka kalla da idanunka" rungume hannu Aliyu yayi akirji yana kallon footage din tundaga yanda ta tsaya ta kwance zani ta zuba poison din takaimai har zuwa inda tafito da gudu daga flat din, pursing video Dady yayi ya kalli Aliyun dake kallon system din har lokacin rungume da hannayenshi akirji yace "you believe me now, ka yarda da magana ta ko, Aneesa wanted to kill you, taso takaika lahira and listen Aliyu kowaye yace zai tabaka a duniyan nan wlh sainaga bayanshi, Aneesa ba sai randa tagama biyan bashin offense dinta tsaf sanan zaku kara ganinta, I can't forgive yarinyar datasa dana yaje hell yadawo ba, pois......." hannu Aliyu yadaga ma Dady yana juyar dakai tsabagen yanda ya tsani Dady na ambaton Aneesa na neman kashe shi, yace "listen Dad, lemme even turn the table around na fuskance ka ta yanda ka fuskanci zancen" yay dan shiru trying to calm kanshi down danjiyake kaman zai kama da wuta yace "yes, na jika nakumaji dukkan bayanan ka naji yes Aneesa poison me and she tries to kill me and CCTV Camera ya kamata ta hanyar recording komi naji nakuma yarda" yay dan shiru yana sauke ajiyan zuciya kafin ya kalli Dady yanuna kanshi yace "Dady ni Aneesa taso takashe ko? And I think nine dindai yau standing right in front of you alive and healthy harma nake maganan nan dakai kaga koma miye abinda tasoyi bata cimma anniyanta ba, Dad ka saurareni da kyau" yasake yin shiru kafin cikin kakkausar murya yace "ni aka cuta ko nine nai going through all the pains of the poison, so Dad inhar hakane ni dinan da Aneesa taso takashe injika tabani poison na janye maganan, na yafemata sanan koma ina kasa aka kaita ka kira a saketa let Aneesa be reunited da mahaifiyar ta yauyau dinan" wani irin kallo Dady yamai yace "you must be very very silly Aliyu dahar zakai tunani zan iya sakin Aneesa sabida kace, I know the kind of pain you went through Aliyu, nine nasan wahalan dakasha, ikon Allah ne yasa kawai baka mutuba, Gadanga bazan yafema Aneesa ba wlh tunda taso cutar dakai saita biya bashin dataci sanan karka