Showing 90001 words to 93000 words out of 180150 words

Chapter 31 - A Tsakankanin Soyayya Book 1 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

26 Sep 2025

2444

musu ya shiga Maman su Rauda ce agaban flat dinta da Rauda agefenta dake mata rubuce rubuce, bin motan sukayi da kallo, parking yayi yafito yazagayo yabude side din Aneesa yana murmushi, ahankali tafito da kafafun ta, turomai baki tayi tace "to ka matsa so kake nabuge ka" dan shiru yayi yana kallon fuskanta, murya chan kasa yace "kinsan wani abu?" da sauri ta girgixa mai kai tace "menene" murya chan kasa kaman maison yin gulma yace "ina sonki sosai Aneesa, yau zan fadama Dady, nakosa na aureki" murmushi tayi tarufe fuskanta da hannayenta tace "nidai ka matsa na wuce" ahankali yace "bakice kina sona ba yau?" batare data bude fuskanta ba tace "kai da kake ta ihu ne kanka dan dauki dan karfe ne zance inaso hu'um, nisai kadawo mai karfi kaman zaki sanan zance ina sonka" ahankali ta zare hannunta daga fuskanta tadan kalli fuskanshi yanda yake kallonta da shagwababbun idanun nan tace "inaso kazama my lion, Boldest and bravest saida aji tsoranka badai ka kajiba, baka ganni ba, kataba ganin power na kuwa?" da sauri ya girgiza mata kai yana danne dariyan dayake ji, kyawawan idanunta tadazan zaro tace "kai namiji ne dana nunama, amma inada babban power, kaga ko a bakery mu in a day sainai baking su meat pie da cakes na buhu data saisa nakeda karfi, ranan nan nakusan yima Fatima duka" da zaro ido yayi surprisingly gyadamai kai tayi tace "yes tsokana take takan Yusuf security saurayinta namin magana toni mai ruwana dashi ninace yazo yamin magana aiba nibane ko?" ta kalleshi tana jiran amsa, gyadamata kai yayi tacigaba da zuba tace "shine tazo aiko nadau babban bowl nabita da gudu tafita daga bakery" ta kyalkyace da dariya harda tafi, this is the first time take sakin mai surutu haka ta masifan burgeshi ahankali yakira sunanta. "Aneesah" tsayar da dariyan tayi tadago kai ta kalleshi, wani irin luu yamata da ido ahankali yace "I love you so much, I will tell Dady about our love yau" ta gefenshi tayi tai hanyar flat dinsu da gudu tana murmushi ko lura dasu Mama daketa kallonsu batayi ta shiga flat dinsu, Booth Aliyu yabude ya kwalama mai sharan tsakar gidansu kira kayan daya saima Aneesa yanunamai flat dinsu yacemai yakai shikuma yawuce flat dinshi dan bacci yakeji sosai.


Kayan da Ammi taga an shigo dashi yasa ta kalli Aneesa tace "wanan kayan fa" dan zaro ido tayi kaman wata mara gaskiya tace "nima bansani ba Ammi nadaiga yanata siyansu dazu" ajiyan zuciya Ammi ta sauke tana tunani saikuma ta kawad da tunanin hala Alhaji yace yadingayin haka, koma bahakaba yaron nada hankali danya saima Aneesa abu bawani abu bane dukansu Dady yarike a matsayin y'ay'a a yanzu.

Karfe hudu driver ya kwashe su zuwa islamiyya koda daddare data dawo batama iya tsayawa taci abinci ba sai bacci, da Ammi ma ta shigo tadata suzo suci abinci kasa tashi tayi tai nisa a baccin haka Ammi tafito tafadi ma Dady da Aliyu, abincin da Aliyu bai iyaci da kyau ba kenan sabida bata a wurin yaso yaga fuskarta kafin yay bacci amma baiganta ba, ture abincin yayi yamike tsaye da sauri Ammi tace "ina zaka bakaci komiba ai" murmushi ya kakalo ma Ammi yace "na koshi ne Mum, ban wani jin yunwa, saida safe ku" "say your prayer before sleeping okay" gyadama Dady kai yayi yawuce yafita.



Yau gudun kar Ammi tamata fada da sassafe ta tashi tai salla tai karatun Al 'Qurani saida gari yay haske sosai sanan ta shiga gyaran gidan har zuwa kasa, a kitchen taga Ammi na hada breakfast ahankali tace "ina kwana Ammi na" "kin tashi lpy yi sauri kikarasa gyara falon da baranda sai kizo muhada breakfast inaso kiyi wanki kyau kayan wankin mu sundan taru" gyadama Ammi kai tayi tacigaba da gyara falon harta fitar da sharan waje Aliyu tagani kan 34 degree hyper extension yana excerise yanda taga yana nishi saida hawaye yatarun mata a idanu, he's doing all this sabida ita, lumshe idanu tayi ahankali tace "ina sonka sosai Ya Aliyu na, I love you wlh" tsince yan datti gaban dakin tayi dan bataso ma yaganta tabude kofa tadawo daki, kitchen ta shiga alalen gwangwani taga Ammi nahadawa shidai Dady bai cika wani son abincin yan gayun nan as breakfast ba yafiso yaci lafiyayyen abinci a gida wanda koyaje office bazai damu dawani abinci ba, shi dama aka'ida sai biyu yakecin abinci safe da dare bayacin na rana awurin aiki, yau shida kanshi yacema Ammi tamai alale na gwangwani yana bala'in jin dadin girkin Ammi shidai he's so lucky Ammi is just good takowani fanni in bed hulala Ammi is a killer, a girki kuma wuhuhu she's a murderer, dan she murder anything she cook karyane kace kaci bai hadu ba, wuraren 10 suka gama Aneesa ta jera komi a dinning lafiyayyen alalen manja ne na gwangwani da akayi da kifi sai kunun gyada mai kauri, sai ruwan sanyi irin abincin nan ba'a hadashi da juice, sama Aneesa takoma dantai wanka Ammi kuma tadau waya takira Dady, ba'a wani jimaba Dady ya shigo sanye da suit necktie dinshi a hannu rungume Ammi yayi a kunnenta yarada mata "I will miss you yau da daddare, Ina kaunar ki yallabiyata, kin gamamini alalen?" gyadamai kai Ammi tayi takama hannunshi takaishi kan table zama tayi ta zauna a gefenshi ahankali yace "ina yaranmu suke?" daidai lokacin Aliyu ya shigo ya watso ruwa yasa jeans da riga murmushi Dady yayi yace "oh jama'a Gadanga na yadage, yaro duk yabi yanabama kanshi wahala iyye" murmushi yayi yaja kujera yazauna yana kallon Ammi yace "good morning Mum" "morning Aliyu, sannu kaji, Son anya baza'a rage excerise dinan ba kuwan yamaka yawa?" girgixa mata kai yayi yace "Mum ni inaso nayi please karki hanani" cikeda so Ammi tace "don't worry, kacigaba but saisa saisa okay" "sure Mum" murmushi Dady yayi yana sama Ammi albarka a ranshi, ahankali Aneesa ke saukowa maroon hijabi tasa har kasa, kafeta da ido Dady yayi for the first time hakanan saiyaji yama Aliyu sha'awan yarinyan, Aneesa nada natsuwa gata ustaziya, har cikin gida yawo take da hijabi, karasowa tayi akunyace ganin kowa na kallonta tace "ina kwana Abba na" cikeda fara'a Dady yace "kin tashi lafiya yarinyar Abban ta" Aliyu tadan kalla kafin ta dauke kai tace "ina kwana Ya Aliyu" myrya chan kasa yace "how was your night little sis" murmushi daga Ammi har Dady sukayi jin sunan daya kira Aneesa dashi kafin Ammi tamike tai serving kowa sanan aka shiga cin abincin Aliyu da Dady santi kawai sukeyi, Dady ne yagama yafara musu sallama yatafi office sai Aliyu shima sallama yama Ammi yatafi flat dinshi soyake yasake wanka da ruwan zafi dan jikinshi ciwo yakemai na bala'i.

_duk wacce takaranta batare data biyaba Allah ya isa ban yafeba, in kinason book dinan kimin magana ta watsap 07012181461_
Clearing dinning Aneesa tayi ta shiga kitchen dinsu tai wanke wanke ta gyara ko ina tsaf sanan ta shiga dakin Ammi kayan Ammi dasukai datti ta kwashe a basket sanan tawuce nata dakin ta kwaso nata kayan tsaf sanan tafito tazura hijabi, afalo taga Ammi zaune tana duba wani littafin azkar tace "Ammi natafi wanki a laundry" kallan kayan wankin Ammi tayi tace "banda neman tsokana kowa kika gani a laundry ki gaidashi banson hayaniya nasan halinki Aneesa banda neman tsokana" dariya tayi tace "Ammi aini baruwana dasu" tabe baki Ammi tayi tace "ki
gayama wanda baisan halinki ba masifaffa, wuce kitafi" fita tayi daga dakin tana dariya tai hanyar laundry da Dady yanuna musu yace "anan zasu dinga wanki" shiga laundry tayi babu kowa sai manya manyan washing machines har guda uku na LG, girgiza kai tayi tace "masu kudi na sha'ani ahaka still yan wanki ke zuwa suyi, inada wanan agidana ai bana bukatan masu wanki" tsayawa tayi agaban washing machine din tana kalle kallen neman yanda ake kunnawa dan wlh bata iyaba, wani button ta danna wani irin kara da washing machine din yayi batasan lokacin data saki wani irin ihu tarugo da gudu gab taci akaro da mutum atare daga ita har Aliyun data bangaje suka saki ihu. "auhhhh" rike ciki Aliyu yayi kaman zaiyi kuka yace "wayyo Allah na marana, ta tayarmini da ciwon mara na" dudda tana fama dajin zafin bigewan datayi amma bai hana yanda Aliyu yay kaman zaiyi kuka yana cewa wayyo Allah ta famamai ciwon mara bata dariya ba, wani irin fashewa tai da dariya hakan yasa yay shiru yana dafe maranshi yana kallonta yay kaman zaiyi kuka yay kini kini da fuska murya chan kasa yace "ni kin fama min ciwon marana sanan kuma kinamin dariya" sake ware manyan idanunta Aneesa tayi cikeda dariya tace "to maza na ciwon mara ne" tasake kyalkyacewa da dariya, ganin yanda take dariya gwanin ban sha'awayasa a shagwabe yace "ai is because of sit up din danake yi na exercise ne yasamin serious abdominal pain, its hurt badly" tsayar da dariyan tayi tana kallonshi yanda yay maganan ya mugun bata tausayi ahankali tace "sorry kaji" gyadamata kai yayi yana kallon fuskanta kafin kaman sun hada baki atare sukace "what are you doing here?" dariya dukansu sukayi ganin sunyi magana iri daya atare, da sauri Aneesa tace "I go first, nazo nai wanki ne kaifa?" dan yatsine fuska yayi yana kokarin mikewa tsaye yace "Dady yace nazo nadubamai wani necktie anan" kallonta yayi yace "mesaki gudu haka?" washing machine din data kunna ta nunamai dake kara har lokacin, karasawa wajen yayi ya saita mata komi ya kalli kayan data kwaso a basket ya juye a washing machine din sanan yarufe yana kallon fuskanta kaman yau yafara ganinta, murguda mai baki tayi tace "nika dena kallona"

_duk wacce takaranta batare data biyaba Allah ya isa_
Matsowa yayi kusa da ita yakawo bakinshi daidai saitin kunnenta ahankali yace "I wish I can, I love you so much Anebaby, bakice min kinasona ba" murmushi tayi tareda juyamai baya ahankali tace "mesa baka zuwa aiki kullum kullum kana gida eh?" ahankali shima kaman yanda tai magana yace "gajiya nakeyi, saina kara girma zan fara aiki" dan kallonshi tayi saikuma ta dauke kai tace "ni kadinga zuwa aiki, I want you to be my strong working class Man, inta kallonka inajin dadi"._*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



4️⃣3️⃣




Dan shiru yayi na yan seconds kafin ahankali yace "is that all you want namiki koda wasu abubuwan kuma?" da sauri tajuyo tai facing nashi tace "kaga ko inaso da asuba idan katashi kaje mosque kai sallan ka a jam'i bayan ka idar kai azkar kai karatun Al 'Qur' ani saika dawo gida ka chanza kaya kazo gym kai training sosai harsai zufa ya wanke ka sanan saikaje kayi wanka, dazaran kayi wanka saika shirya office saika shigo flat dinmu na ganka naji dadi araina sai muyi breakfast tare, bayan munyi breakfast tare saiku fita tareda Dady katafi office, around 4 idan kadawo kai wanka ka chanza kaya saika fita ball irin yanda samari sukeyi da yamma sai bayan magrib saika dawo gida kasake yin wanka kahuta shikenan abinda nakeso" tamai wani irin murmushi tana kallon fuskanshi, shidai inhar zai dinga ganin wanan murmushi a fuskanta always inkuma har abinda takeso kenan zai iya mata kome takeso aduniyan nan, he love he has for Aneesa knows no boundary, lumshe ido yayi yabude yace "shikenan I will do anything for you Fateema na" murmushi tayi akunyace tana boye fuska murya chan kasa yace "kinsan ni menake so kimin?" da sauri tadago kai ta kalleshi tana girgizakai, ahankali yace "banson kikarama any namiji magana in your life, kowani taimako ko help kikeso komin ina nake ki kirani I will come, banson kowa ya rabeki, zan iya kashe duk wanda yazo yace yana sonki, kisa har lahira, u are my wife Aneesa, Ke gonata ce baby wanda ya isa yazo yace zai shiga gonata ko zai hada wata mu'amalat da ita, promise me I will always be the man u will always love till eternity" gyadamai kai tayi ahankali murya chan kasa tace "namaka Alkawari Ya Aliyu na" murmushi yamata yace "inaso nafada ma Dady ina sonki I want to marry you" makemai kafada tayi alamun a'a, kaman zaiyi kuka yace "why now?" ahankali tace "kaga Ammi na da Abban ka basu dade dayin aure ba mubari sundanyi kwana biyu saimu fadamusu, kumani inaso nai jamb har University nafara ko 100 level ne saimuyi aure" girgiza mata kai yayi kaman zai sakin mata kuka yace "zan iya jira kiyi jamb din tunda ending of this month ne but bazan tsaya jiranki har kifara University ba, ni nakosa nai aure, nakosa kizama matata ki haifan mini plenty babies" murmushi tayi akunyace zai sake magana washing machine din ya shiga kara din din din, alamun yagama wankin tass, kashe machine din yayi yaciro mata kayan yasa mata a bucket yace "muje backyard muyi shanya" daukan mata bucket din yayi itakuma ta dauki empty basket din suka fita har sunkai wurin kofan fita tace "laaa Ya Aliyu ka manta bakadau neck tie din Dady dayace ba" murmushi yayi yace "bakin mantan dani duniyan danake ba, am coming" ajiye bucket din yayi yawuce yakoma ciki tanabin bayanshi da kallo ganin haryadan soma chanza mata daga fara excerise dinshi, akasa ya hango necktie din kusa da kofan wani dan daki haka da suke zuba su omo da hypo abubuwan dai wanki , tsugunnawa yayi yace "gat u" yadauka harzai tashi idanunshi suka sauka kan kafafu hudu tacikin dakin omon, da alamu akwai mutane a wajen kenan all maganganun dayayi da Aneesa angama saurara kafafun babban mace dana yarinya dayagani ne yasa bai bude kofan ba yatabe baki yamike tsaye yasami Aneesa abakin kofa sukai backyard a binsu ko ajikinshi.


Ahankali Mama tabude kofa tafito Hajar datai kini kini da fuska biye da ita tace "nidama Mama naga yanda yake yawan kallon yarinyar, harda jiyama dasuka dawo, ashe sonta yake saisa ya wulakanta Nafisa" shiru Mama tayi tayi mugun nisa atunani, tabata Hajar tayi tace "Mama kinko maji menake cewa kuwa? Tunanin me kikeyi haka?" kallon Hajar Mama tayi for few seconds tace "Hajar lokacin koyama Aliyu lesson yayi and yarinyar nan dakike gani is what am going to use, shekara da shekaru ina harin yaronan Allah bai bani damaba yau da Allah ko yasa mukaji conversation dinsu is a sign cewa kome zanmai yanzu zanyi nasara" murmushi Hajar tayi cikeda jin dadi tace "Mama ki ramamin dukan da mugun yamini, sanan ki rama hana auren Rauda dayayi da Nazif," gyadamata kai Mama tayi tace "uwa ta auri uban d'a, idan kuma nabari d'an ya auri yarinyan uwan aiza awayi gari mun rasa komine, duka kadaran mahaifinku maidama Aliyu da yarinyar nan su ubanku zaiyi to bazata yuba" dan rage murya tayi kafin tace "kawo kunnenki kiji Hajar" da sauri Hajar ta mikama Maman nata kunne cikeda kosawa taji me maman zatace, wani magana maman tafadi mata akunne a mugun tsorace Hajar ta fizge kunnenta ta kalli fuskar Maman tata tace "Mama kisan kai?" rawa jikinta yafara tana girgizakai tace "a'a gaskiya Mama, kema kinsan banson Ya Aliyu, na tsaneshi sosai kome zamumai mumai banda kissan kai Allah yahana wlh, a'a I always support you Mama kema kin sani but wanan no, kashe shifa Mama zamuyi how? Haba kashe rai nidai a'a Mama" wani mugun harara Mama ta watsa mata tace "dan ubanki kina dagamin murya so kike ajimu?" da sauri tace "sorry Maman mu, ai babu kowa a wurin, mama kinga dai karki kara furta maganan" dan dariya Mama tayi tana kara kallon koina ganin babu ko mahaluki daya yasa tace "listen to me jor, angayamiki banda hankaline? Bakiji kalmata ba zamuyi amfani da yarinyar nanne babu ubanda zaima san damu, we are going to use one bird to kill two stones, kinga dai yanzu daga maman ta har babanku babu wanda yasan da soyayyan su ko so is a good thing gwara mu aiwatar da abin kwanan nan tun kafin asan da suna soyayya, kawo kunnenki kiji plan dina" kunnenta Hajar tabata Mama tamata wasu maganganu dagokai tayi tareda gyadama Maman tasu kai duk tai wani iri harga Allah batason abinda Mama ke shirin aiwatar wa but Yaya zatayi hannunta Mama taja sukai daki tace "don't forget abinda nafada miki yanzu aikin ki shine samusu ido and watch all their moves, kibar komi a hannuna I will not involve you in this kinji" tai maganan tana bude kofan dakinsu suka shiga inda Rauda da sauran yaran ke kallon cartoons, daure fuska Mama tayi dan haryau bata amsa gaisuwan Raudan sanan tawuce dakinta Hajar tabita abaya suka shiga suka rufo kofa, tabe baki Rauda kawai tayi tacigaba da kallonta abinta.




Yau asabar yaune second week din Ammi agidan Dady, wani irin rayuwa take ginawa itada Dady dako Aliyu abin burgeshi yake, tuni Dady yamata kyautan wata dalleliyar mota, dan Ammi is every with a plus arayuwan shi, she gives him happiness, kwanciyan hankali da komi, kome yace yanaso shi zai ci idan yanacikin matsala he don't need to say it Ammi na ganin fuskanshi zata gane ta lallasai, in bed kuwa kullum saiyay sumbatu saisa ko kadan baya iya daga mata kafa, gurxanta yake kaman ba gobe.

mai fitarmin da littafi waje, wlh ban yafemiki ba, Allah kuma yana kallonki
Wani irin soyayya Aneesa da Aliyu sukeyi asirrace na fitan hankali, yanda take juya Aliyu yanda takeso ko saika rantse tamai asiri ne kowani abun, idan tacemai tanaso yay kaza she don't need to repeat it zaiyi saisa itama ko kallon maza batayi dan she really really love Aliyu da duka zuciyanta, Sosai Dady ke bala'in mamakin chanjin Aliyu all of a sudden dudda yaso dagowa kaman soyayya suke da Aneesa amma dai ya share yasan komeye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login