Showing 6001 words to 9000 words out of 180150 words

Chapter 3 - A Tsakankanin Soyayya Book 1 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

26 Sep 2025

2417

manya manyan bottle din wine da glass cups, suna ganin shi sukai ihu. "you are late Leo" haka suke kiranshi da Leo tun farkon shigan shi school idan za'a kira sunan shi Aliyu saidai suce Aleo shine friends dinan nashi kawai suka cire A din farko suka radamai Leo, zama yayi kusada black guy din Wanda shikadai ne yay kama da dan Nigeria cikinsu sauran duk da turawa ne. "ahhh wash, my legs" black din dake kusada shine yace "where are your guards Dady's boy?" daga yanayin yanda yay maganan zaka gane tsokanar shi yake nema hakan yasa sauran suka fashe da dariya sosai, hararan su yayi yace "I came alone" "whowhowhow! Kai nawa, lemme just call this a white lie right guys?" ya tambayi sauran mazan atare sukace "yeah, is a white lie" sukahau dariya ganin iskanci sukemai yasa ya kalli bar attendant din wurin yace "non alcoholic wine pls" da sauri mutumin yajuya dan zuwa daukomai, juyowa yayi ya kallesu ganin duksun tsareshi da ido suna shan shishan su yace "wats up guys?" wani daga cikinsu ne cikin harshen turenci dan duk da turenci suke magana yace "magana muke akan irin matan damukeso mu aura in the future, I personally Leo want to marry sangartacciyar yarinya, yarinyar yar gayu mai kyau wacce tasan gata, yar gidan masu kudi, kai wacce irin mace kakeso ka aura Leo?" daidai lokacin bar attendant din yakawo mai wine din dayay requesting karban wine din yayi daya zubamai a glass cup, Bash dan Nigeria dake kusada shi ya kalli wanda yama Aliyu tambayar yace "me kake tambayar Leo irin matar dazai aura, kaima kasan Leo ready made yar gata zai aura, am sure yarinyar president zai aura?".







Tabe baki yayi jin maganan da Bash yayi yakai wine dinshi baki yana kara shigewa cikin kujera da kyau, ganin baida niyyan magana sun saba dama da iskancin shi yasa daya daga cikin turawan mai suna Frodd yace "ni inaso na auri matan data girmeni sosai at least tabani 10 good yrs" atare dukansu sukai kallai harda Aliyu dake sipping red wine dinshi, daga musu gira yayi yace "yes, idan ka auri wacce ta girmeka tafi riritaka, tafi kula dakai, tana kuladakai kaman dan kwai cus it took her a very long time kafin tasameka so u will be well taken care of, you are just like an asset awurin ta" dariya dukansu sukayi banda Aliyu da yadanyi murmushi kana ganinsu kasan suna enjoying hiran dasukeyi abunsu ganin yana murmushi yasa sukace "come onnnnnn Leo tell us yours" dan bude ido yayi ya kallesu saikuma yay murmushi ya daga glass cup din hanunshi yana kallon wine din yay shiru kaman yana tunani dan fuzar da iska yay kadan ya gyara zaman dayay akan kujeran mai kama da kwanciya ya daura glasscup din akan kirjinshi yace "I don't think I will ever get married but if I will matar danake so na aura" yay shiru yasa hanunshi yacire glasscup din daga kan kirjinshi yadaga sama tareda bude idanunshi ya kalli glasscup din dayake dan girgizawa ahankali yace "inaso na auri mace dat is not from a wealthy home, rich girls are too stupid and proud I hate them" ya yatsine fuska kadan cikin sassanyar muryanshi yace "I want a hardworking smart girl mara son jiki a kazar kazar girl" yasake yin shiru yana girgiza cup din yace "a good cook, obidient and gently being, a girl that She sees me for me, I want Inner Beauty in a lady not facial, if her heart is beautiful am okay" yay dan shiru kafin ahankali yace "I want a girl that am naturally attracted to, attraction is the basis of love and marriage, and if the spark isn’t there, it’s something that’s really hard to fake" yay shiru yace "a girl that is not too expose mai kunya, yarinya mai hankali da taimako" yadanyi shiru kafin ya yatsine fuska ahankali yace "I just want a girl that will beat my imagination, I want a girl that will beat all this qualities I listed and be more and more and more" dan murmushi yayi ya ijiye glasscup din yace "anyway nasan they're no such girls on this earth, so I ain't gonna stress myself with marriage, nowadays girls are too lousy guys" yasake yatsine fuska agajiye duk dariya sukahau yi Bash yadan buga kafadarshi yace "u are just talking ne, irinku har kuka kukema soyayya, aure maybe ma duk saika rigamu aure muna nan dakai" kabar da hanun Bash din yayi yay hamma yana duba rolex din hanunshi ganin kusan 1:30 nadare yace "night guys am sleepy, I will be travelling tomorrow" atare duk sukace "where to?" tashi yayi ahankali yace "home" Yajuya ahankali yana daga musu hannu yay waje, bacci yakeji bana wasaba da kyar yakai parking lot aka budemai mota ya shiga ya kwantar da kanshi jikin kujera ya lumshe ido sai bacci.





Murmushi bodyguard dinshi yayi kawai bayan yarufe kofan motar baiga laifin babanshi ba dayake hadashi da security komi Aliyu yakeyi a shagwabe a sangarce kaman ba namiji ba, kaiwa gida sukayi yay parking suka fito ya zagayo yabude kofan yadan bubbuga kujeran yace "we are home sir, wake up lemme take you to bed" bude ido yayi ahankali ya kallesu ahankali yatashi yaziro kafafunshi kasa bodyguard din zai rikeshi ya harareshi cikin bacci yace "don't touch me" yay gaba suna biye dashi har upstairs yabude dakinshi ya shige yafada kan gado batare daya cire takalmi ba, ciremai takalmin bodyguard din sukayi sanan sukaja bargo suka rufemai jiki ya rage karfin AC, dayan kuma ya kashe wutan dakin suka juya suka fita already tun dazu da rana suka hadamai kayan dazaiyi tafiya dasu gobe.
_*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



3️⃣


_How to subscribe_
_*zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turamin evidence of payment to WhatsApp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting*_

_*zaki iya turo katin MTN 300 ta WhatsApp number na 07012181461 sainai adding dinki a group danake posting*_


_Free page_


Da asuba ya tashi da kyar shima sabida alarm din gefen gadonshi ne daya saita yatadashi, tashi yayi ya shiga bathroom, yadade aciki kafin yafito cikin wani blue bathrobe, zama yayi abakin gado ya shafa manshi mai kamshi a tsanake sanan yatashi wardrobe dinshi yaje yabude yaciro wani black belted cotton poplin cargo trouser da wata farin logo print t-shirt na Ambush yadauko yasaka, yabude bangaren rigunan sanyin shi yana tunanin wanda zai saka kafin yajawo wata logo embroidered wool fleece jacket itama ta Ambush, yasaka rigan tazauna ajikinshi tamai kyau sosai, yadau designers turarukan shi ya fesa sanan ya shimfida dadduma yay salla yana sallame wa yaji ana bugamai kofa, yatsine kofa yayi sanin mayun nanne, da kyar cikin isa da izza yace "come on in" bude kofa bodyguard din yayi rikeda wata yar karaman tray da small mug of hot coffee kekai, karasowa gabanshi yayi ya ijiye tray kan dadduman yace "have this sir, we are leaving in the next 10min" daure fuska yayi yace "where is d other guard? Lucas is his name right?" yay maganan yana mai alamu da yatsa ayangance, gyadamai kai bodyguard yayi yace "yes he's Lucas, I left him outside he's packing out luggage to the car" yatsine fuska yayi as usual yatashi daga kan dadduman yahau kan gadon yazauna yamai pointing coffee da yatsa alamun yabashi ysha, daukan coffee yayi da sauri ya mikamai karba yayi yakai bakinshi yay sipping dan ficili ya zare daga bakinshi batare daya kalli Guard dinba yace "where is my phone? Dad dina yakirani?" "your phone is here sir" yakarasa kusa da bedside lamp yadau wayarshi dat was lying there yadauka ya danna wayar dababu any security lock ajiki yace "No sir, babu miss call din kowa" dan kwafa yayi baisake cewa komiba yacigaba dashan dan coffee ayangance sanan ya gama yatashi ahankali yay gaba bodyguard din ya gyara ko ina sanan ya kashe wuta yabiyoshi waje harya shiga mota yawuce ya shiga gaba suka wuce Airport.





Sai fushi fushi yake sabida Dad baikiraba shikuma bazai kirashi ba saisama yabarma bodyguard din wayar dan yasan in yana hanunshi zai iya yakirashi, ya tsani British Airways dan sunada wani banzan dabi'an batarma da mutum luggage saisa tun jiyan yasa suyi booking air France, sai tunanin uban zaman dazaiyi cikin jirgin yake inhar basuyi stopover ba flight dinshi is 18hrs flight inkuma jirgin ya tsaya for fueling ko cleaning kokuma wani dai emergency, kokuma weather issue zasu iya 20hrs or more than sef saisa he came prepaid yasa kayan sanyi idan ya shigama he will request for a blanket or showel duk wanda suke danshi gaskiya shi bazai saka pyjamas din airline ba, kuma yanada matsalan jin sanyi sosai, checking in sukayi suka karbi ticket sukai departure lounge basu wani dadeba suka fara boarding karfe 7:15 jirgin su yadaga sai kallon lokacin yake yana kokarin hararo wat time is it yanzu a Nigeria, dan Nigeria is almost 9hrs ahead of California, dan murmushi yayi ganowa dayayi yanzu darene a Nigeria probably hala Dad yay bacci saisa bai kirashi ba.





8:40 na dare jirgin su yasauka a Abuja, fitowa sukayi kana ganinshi kasan yagaji sosai saukowa suka farayi bodyguard dinshi biyeda shi, wuraren Tara suka gama komi suka fito ta arrival sai kalle kalle yake ya tsaya chak dan baiga wani nashiba baiga wani direban gidansu ba baiga Daddy ba, wani irin haushi ne yakamashi yamikama bodyguard hannu alamun yabashi wayarshi, karban wayan yayi dayariga ya kunna mai ya shiga dialog Dan kiran Dad dinshi, fizge waya yaji anyi daga hanunshi da sauri yadago kai wani magidanci ne kamansu daya sak dan shima farine sol alamun tsufa daya bayyana tattare da magidancin ne zaisa kawai kagane ba yan biyu bane uba da d'a ne, dudda fushi yake da Dad amma baisan lokacin dayasaki wani murmushi ba yawani irin rungumeshi ba so tight yace "Daddd dy" murmushi sosai mutumin yayi yana bubbuga bayanshi yace "na'am Aliyu na, sarkin zuciya, Aliyu an mazajena" dariya daga shi har Aliyun sukayi sanan yasake shi ahankali yana kallonshi kaman yanda yake kallonshi yace "muje kahuta kagaji da yawa karka fadi" sukai wajen mota bodyguard na binsu abaya, motoci biyune bodyguard suka shiga dayan Daddy da Aliyu kuma suka shiga motar Daddy, kwanciya yayi ya daura kanshi kan cinyar Dad yana yatsine fuska, kallo baban nashi ya binshi dashi yana mamaki yaushe Aliyu zai chanza yadawo namiji, son jikinshi da rashin kuzari is too much, hanunshi ya chusa cikin kanshi yana mishi head massage yace "sannu kaji Son kagaji sosai ko?" gyadamai kai yayi idanunshi a lumshe yace "bakaine kawani ce mutum yadawo ba, I need hot bath jikina kaman an kakkaryani Dad" "tooofah, sannu yaron kirki, muna zuwa gida zakai wanka kaci abinci saikai wanka abinka" gyadamai kai yayi a shagwabe yana sauke ajiyan zuciya yanajin dadin yanda Dad kemai headmassage din.





Agaban wani babban gida sukai horn wani soja yabude musu Gate din, tashi yayi ahankali ya zauna yana kallon babban gidan nasu da babu kowa a ciki, shiga ciki sukayi sukai parking bude musu kofar motar akayi, ahankali suka fiffito daga motan yana kallon gidan, babban gidane dake dauke da manya manyan flat flat guda hudu, sai daga tachan dayan bangaren kuma wani babban flat guda daya ne, shidai babu yanda zaiyi da Dad ne amma harga Allah baison dawowa Nigeria ba, ya tsani gidan mahaifin shi sosai, he hates this house with all his heart, dafashi da akayi yasa yadaga kai ya kalli Dad din yadan turo baki kaman mai shirin yin kuka, murmushi Dad yamai tareda sumbatan goshinshi yace "all is well Aliyu am here for you kaji relax, muje" gyadamai kai yayi suka fara tafiya bodyguard kuma nawajen mota suna fito da kayayyakin su daga boot, wata yar budurwace doguwa dabazata wuce 20yrs ba sanye dawata doguwan rigan atampa tafito daga wani daki dasuke kira da laundry tariko wani white folded zanin gado a hanunta tajuyo, ganin Aliyu tareda Dady yasa ta tsaya chak tareda bude baki cikeda mamaki danko kadan Dady bai sanar dasu zai dawoba, tsayawa Aliyun yayi shima yana kallonta da idanunshi dake cikeda gajiya, murmushi Dady yayi yace "gata wajenka nan ai banfada mataba I want to surprise her taganka kawai kaman daga sama" murmushi sosai yayi yana kallonta batare dayace mata komiba ya daga mata gira daya alamun kallon fa baki sanni bane? Watsar da zanin gadon tayi akasa tsabagen rudewa tasa hanunta takai kan saman idanunta ta murza idanun irin ta kara tabbatarwa ba gizo idanunta kemata ba sanan tabude su, tagadai still dai yana tsaye inda yake kusada Daddy dake sanye da babban riga that means Yaya Aliyun tane, wani irin ihu tayi dayacika gidan. "Yaya Aliyuuuu, Yaya Aliyu oyoyo" ta tafi dawani irin mugun gudu hakan yasa yabude mata hannu da gudu taje tai wani irin tsalle tafada jikinshi ta rungumeshi sosai her heart couldn't contain her happiness sai kuka, hakan yasa Dady yace "kagamin shagwababbiyar yarinya, kin wani dane jikinshi zaki karyamin shi saikuma ki sakinmai kuka dukshi kadai, haukatashi kikeso kiyine daga dawowan shi, cikashi" kojin maganganun Daddyn suma batayi sai kuka take bayanta ya shafa ya bubbuga alamun tai shiru, jin karan bude buden kofofi wanan nabin wanan yasa yadago kai matayen Dadyne kowacce tadan leko dakai daga flat dinta ga yara manya da kananu duk sunaso sufito suga ihun mai akeyi a tsakar gida sun hanasu fita, fuskarnan bayabo ba fallasa duk sai kallonshi suke kaman yau suka fara ganinshi, babban cikin matan ne tadan tabe baki tace "ahhhh manyan baki su Aliyu ne agarin, mutanen turai saukan yaushe ko sanarmana ba'ayi ba, hala cinye dan gwal din zamuyi maigida" tasake tabe baki tana kallon Rauda da har lokacin ke rungume da Aliyun tace "sannu da zuwa Aliyu, kekuma ina zanin gadon danace kikawo min uwar shishigi?" kafin Rauda tai magana Dad yace "ahadama Aliyu lafiyayyen abinci Kareema" dan juya ido tayi tace "haba Alhaji saida abinci yakare kasan yawan yaran gidan nan gasuda shegen ci barin ma yaran Amaryan ka, aida kafadamana zaizo dasaimu saka dashi a girki, shi yaro kasan bacin abincin yan aiki yakeba dasai ace suhadamai koyar Indomie ce, kaga kumani wash Allah" tadan yatsine fuska tana dafa kafarta tace "kasan ina fama da wanan ciwon kafan bazan iya shiga wani kitchen ba Alhaji sanyin kashi dazaran dare yayi saidai kaji kasusuwana nakiran salla" shiru Dady yayi yana kallonta baiso yay hayaniya agaban Aliyu da dawowan shi kenan baiso yatadamai da hankali da sauri Rauda ta tashi daga jikin Aliyun tace "nizan ma girki kaji yayan mu, maizan dafama?" kafin ma yay magana Kareema tace "wai bazaki wuce kidau zanin gadon chan dakika watsar akasa kije ki shimfidamin agado ba" wani mugun kallo Daddy ya watsa mata yace "kije ki dauka dakanki, girki zatama dan uwanta" Daddy ya kalli Raudan datai zuru zuru dan tsoron masifar uwarta take Yace "wuce je store ki dauko all abunda zakiyi amfani dashi kizo side din Aliyun kiyi girkin awajen" gyadamai kai tayi tace "to Daddy" tama Ya Aliyun murmushi tajuya da sauri tawuce, Dady ya kalli sauran matan biyu dasuka tsaya suna kallonsu yace "duk baku iya gaisuwa bako" ko wacce da kallan nata reaction din dasukayi da kyar sukace "sannu da zuwa Aliyu" ko amsasu Aliyu baiyiba Yajuya yay part hanyar side dinshi, Amaryan Dady mai suna Amina tace "yaro baisan ya gaida manyan Shiba saidai asa manya su gaidashi sabida sonkai, mumadai Allah bamu y'ay'a mazan nan, kuma kar wata takara kiran yarana " dan juyowa Dady yayi ya kalleta jin yanda take jefanshi da kananun magana ta shige dakinta baice komiba amma wlh duk zasuci ubansu yasan maganin su, shida sune su zuba indai kan Aliyun dudda sun haifamai yara zai iya sakin yan bura'uba yakawo nany su kulamai da yaranshi, billahillazi duk wanda zai tabamai Aliyu marayan danshi nan mara uwa sai yay yakin biafra da mutum.
_*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



4️⃣


_how to subscribe_

_*zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turomin evidence of payment to WhatsApp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting*_

_*Zaki iya turo katin MTN 300 ta WhatsApp number na sainai adding naki a group din danake posting*_



_Free page_


Bangaren Aliyun Dady yabude da wani card, ya shiga Aliyu dake tafiya ahankali biyeda shi, hadadden dakine nagani na fada, an gyara komi tsaf sai shining furnitures din keyi dan Dady yasa an gyara komi, zama yake shirin yi Dady yace "a'a Son aje ayi wanka eh dan saurayin baban shi" gyadama Dady kai yayi kaman zaiyi kuka yay hanyar bedroom dinshi daidai lokacin Rauda tashigo falon rike da katon basket data lodo all abinda zatai amfani dashi tamai girki, ganinta yasa Dady ya washebaki yace "yauwa yar albarka, shiga kitchen ki hadamai" "to Dady" tace tana leken Aliyun dake shirin shiga daki, hada ido sukayi tasaki wani murna tawuce kitchen. Sea food pasta takeso tadafamai dazaiji shrimps sosai, ruwa tasaka a wuta ta rufe pot, sanan tasa wani pot a wuta tana hada tomato sauce, ruwan na tafasa ta zuba spaghetti danya tafasa tacire, in less than 30min tahadamai hadadden spag dayaji shrimps sai kamshi yakeyi.




Wani hadadden plate ta dauko ta zubamai tasaka a tray, tabude fridge dinshi taga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login