Showing 9001 words to 12000 words out of 180150 words
Chapter 4 - A Tsakankanin Soyayya Book 1 Complete Hausa Novel
akwai drinks masu sanyi dat means Dady duk Yasaka an saka, tadauko drink tadaura akan tray da glasscup goran ever water tafito, yana kwance afalo sanye da pyjamas farare yay filo da cinyar Dad suna hira kasa kasa dako ita bata iyajin abinda suke cewa sai murmushi yakema Dad, karasowa tayi dauke da tray taja table ta dauramai abincin akai ta zauna agefenshi tace "ci abinci yayan mu" tai maganan tana rikemai hannu, kanta ya shafa ahankali tareda yatsine fuska yace "is too hot I can't eat it bari yahuce, ya school Angel?" murmushi tayi sosai tace "fine Yayan mu, ina 100level computer science education, ni course din wuya yakemin Yayan mu sosai" zaiyi magana Dady yamike tsaye yana gyara babban riganshi yace "bari naje na watsa ruwa na kwanta tunda kun manta dani" dariya dukansu sukayi kafin ahankali yace "good night Dad" murmushi yayi yace "yauwa Yarana, saida safenku, dazaran tafara damunka da surutu ka kadota dan kasha gajiya ga Rauda aku kuturu ce" dariya tafashe dashi taboye fuskarta abayan Aliyu tace "Yayan mu ai banda surutu ko" dan murmushi yayi yace "don't mind Dad ya iya shairi" hararan su Dady yayi yawuce yafita daga dakin, abincin ya kalla yace "go and bring another fork let's eat together" , ware ido tayi saikuma tanunamai cikin ta tace "kar cikina yafashe ni nakoshi, ci karage saina rufe nakai kitchen" daukan fork din yayi yafara ci ahankali, kafeshi da ido tayi ganin yamata bala'in kyau, rabonta dashi kusan 1yr kenan yanzu, ya kara kyau ya kara kiba, yakara cika da zati, gadan gemun daya tara dan kadan dake shining tsabagen gyaran dayakeji, sosai tai nisa akallonshi bama tasan harya gamaba saida ya dungure mata kai sanan ta farga tareda kyalkyace dariya takalli abincin tace "harkagama harya isheka dan wanan zakaci?" ruwa yadauka yakai baki yace "yeah, am ok, dauka kikai kitchen kidawo" dauka tayi tai hanyar kitchen shikuma yacigaba dashan ruwan goran dake hanunshi, dawowa tayi tasake zama kusada shi kaman zata cinyeshi tun tana karama take mugun son Ya Aliyu, shima haka yakeji da ita duk cikin kannenshi itace ta isa tazo bangarenshi ta shiga ko ina tafito, tun tana karama inhar yana nan yana daukanta sufita yasiyo mata abubuwa dayawa sudawo, ita kemai girki ta gyaramai bangaren shi, da ita kadai yake shiri duk fadin gidansu, tashi yayi daga kan kujeran da sauri ta tashi itama, hanunta yakama sukai hanyar bedroom dinshi abakin gado ya zauna ya nuna mata daya daga cikin akwatunan da bodyguard suka shigomai dashi yace "take it to your room" wani irin murmushi tamai ta tashi da sauri tai wurin akwatin, zama tayi a kasa ta kwantar da akwatin tabude, turarukan matane guda hudu adan mini fine bag, sai wani kit da sauri ta dauka ta bude agogo verosky ne da bracelet dinshi, ihu tayi dan tadade tanason abun batada shi, sauran kayan kuma riguna ne masu kyau na mata ciki da singlets, cikin tsananin farin ciki ta dago kai dan tamai godiya taga haryay bacci yana saukar da numfashi ahankali.
Murmushi tayi ta kwashi kayan ta mayar cikin akwatin ta hadasu tsaf tarufe ta tashi takaraso gaban gadon daya ke kwance ta tsugunna ta kafamai ido tana tunani, sosai takeson Ya Aliyu sama da duka yan uwanta, su 21 ne yaran Dady, Ya Aliyu shine first born agidan, itama ta girma batasan maman shiba but Anty Hajar tasanta dan tana around 6yrs ta rasu, hawan jini yakasheta, Mama ta taba fadamusu Aliyu yakusan haukacewa da Ummin shi tarasu dan ya shaku da maman shi sosai, bayan Ya Aliyu sai Maman su ta haifi Anty Hajar, sai ta haifi har maza biyu amma duk suka rasu bayan sunzo duniya, sai ita, sai kaninta dukansu mata guda 6, amaryan Dady yaranta mata guda uku, sai ta tsakiyar itama yaranta mata guda Takwas, bawasu manya bane dayake gasan haihuwa ake agidan, daga ita sai Anty Hajar ne kawai manya duk sauran yaran yarane basu wani tasaba. Deep down tausayi sosai Ya Aliyu kebata bana wasaba gidan nan kowa ya tsaneshi harda Maman su itacema oga, she's sure ayanda Mama ta tsaneshi inda zata sami hanyar kasheshi zata iyayi, ita tarasa meyay musu meya tsaya musu? Maiya kare musu wanan mugun tsana haka daga ina? Gashi baima dawani magana, bayama kulasu sabida yanda ko kaunar ganinshi basayi duk sun rabashi da kaninshi, itama da karfi da yaji tanunama Mama itafa saita kula Yayan su koda ba mahaifiya daya ta haifesu ba ubansu daya ai, kuma jini guda ke yawo ajikinsu, Ya Aliyu is just somehow that she can not even define, he's very cool saiyaga daman kulaka zai kulaka, sanan yanada fushi yanada bakar zuciya but he's always keeping calm baimaso yana fushi, gashi baida kwari komi ahankali yakeyi sanan shi mata basama gabanshi, shi kawai gashi nanne soo somehow, sa'oinninshi maza by now suna cikin kogin soyayya koma sunyi aure sun ijiye iyali shiko batamaga alamun sha'awan aure tattare dashiba ko halinsu Mama ne dayagani yasa yadauka duk haka mata keda bakin hali ya tsani aure oho but she just wish, hope and pray Ya Aliyu will meet the love of his life soon and experience that feeling of knowing someone out there is dying for you, is crazy for you, and can do anything for, love feeling is just the best ne, tarasa mesa duka matan Dady dukansu ukun bazasu soshi and hold him like a Son ba why, yanzu kenan duk yaron da mahaifiyar shi zata mutu tabarshi haka zaiyi rayuwa kowa na kyaranshi? This isn't right at all.
Tashi tayi ahankali jikinta duk yay sanyi taja jakanta tareda kashemai wutan dakin tafita ta rufemai kofan falo tawuce part dinsu, ahankali tabude kofar su gudun kar Mama taji ta maida kofar tarufe sanan tadaga akwatin dan karyay kara tai dakinsu, bamata kunna wutaba ta lallaba ta ijiye akwatin gefen gadonta ahankali kaman munafuka, fincikota dataji anyi saida tadan saki gajeren fitsari kunna wutan dakin akayi taga Yayarta Hajara ne tsaye jikin kofa sai maman su data mugun daure fuska tana rike da ita, sosai jikinta yafara rawa hakan yasa tace "M...Mama menayi?" hannu Mama tasa ta dauke ta da lafiyayyen mari ihu tabude baki zatayi Maman su tace "wlh, wlh kikamin ihu ubanki yaji ya shigo dakin nan saina miki abinda bantaba mikiba tunda na haifoki duniya" gyada mata kai tayi tsabagen rudewa tasa hannu takama bakinta tana kuka sosai mara kara, cikin mugun fushi Maman su tace "wato dan ubanki tunda Aliyu yabar garin nan nahuta yanzu yadawo kin fara, Rauda ni, ni, ni nan uwarki karimatu in tsugunna in haifoki kifito tanan Rauda" ta daura hannu gaban zanin jikinta tace "nasha azaban nakuda na kwana biyar, bayana kam har tofin yaasin akamini tsabagen yanda kika shirya karyashi kafin ki fito, sanan dakika tashi fitowan kika fito ta kafa nasha bakar azaba nice yau Rauda kike nunamin wani kasurgumin katon banzan namiji, mai kama da basamuden chan yafi ni ni mahaifiyarki, iyye Rauda? Nasaki ki daukomin zanin gado, Rauda ni zaki watsarma da wankakken zanin gadona fari kal akasa sabida kinga Aliyu, dan ubanki ciki daya kuka fito da Aliyun?" shiru Rauda tayi bata bata amsaba sai uban hawaye dake fitowa daga idanunta, cikin tsananin fushi Mama takara kamo gaban rigan ta bakinta na kumfa tace "kibani amsa, ciki daya kuka fito da Aliyu?" girgiza mata kai tayi cikin kuka tace "Yayan mune Mama" wani mahaukacin mari Mama takara sharara mata tace "dan ubanki menasha taraku nake fadamuku? Aliyu ba dan uwanku bane, babu ruwan ku dashi yanda baida uwa hakama baidaku, kuba yan uwanshi bane, haka zai karake rayuwanshi baisan dadi da soyayyan dan uwaba, ku dauka ko jini vaku hada dashi ba, yaron da ubanku ya fifitashi kan kowa na gidan nan uban me za'ayi dashi eh?" cikin kuka sosai Rauda tace "amma Mama shi aka fara haifa a gidan nan, kafin dukanmu, kuma Dady na nuna yafi sonshi ne sabida duk kunki bama marayan yaron soyayyar mahaifiya dukkun tsaneshi, maiya muku? Bai taba zaginki ba, bai taba miki rashin kunya ba, inya gaisheki baki amsawa bama kya kallonshi saisama yadena, duk kun rabashi da kowa, Anty Hajar ma bata gaidashi duk kun hana kaninshi gaidashi saidai idan sunga Dady ne zasu gaidashi, haba Mama kiji tsoron Allah, _d'a na kowane_ maiya muku eh? Idan yanzu kika mutu akamana haka yaya zaki dingaji akabari" shaketa Mama tayi ahaukace jitake kaman ta kashe ta tace "nikike kirama mutuwa Rauda akan Aliyu? Ba dangin iya bare na Kaka, saidai ke kimutu baniba kinji shegiya wacce ta debo jinin dangin ubanta mai bakin zuciya" ganin idanunta na juyawa yasa Anty Hajara da itama take mugun jin haushin kanwar nata sabida taurin kanta tazo ta cire hanun Mama daga wuyanta tace "ya isa haka Mama" cikin fushi da mugun masifa jikin Mama har barbar yake tace "Hajar ki barni na kasheta, baidai tafison wani kato akan uwarta ba, goben nan zakiji kishiyoyina sun faramin habaici na haifi munafuka, zataci ubanta ne saisa gwara ai aurenta da Khamis ta tattara tabar gidan nan ta tafi gidan mijinta nahuta inba hakaba bakin cikinta zai kasheni ne, dama Khamis din yacemin gobe zaizo yadauke ki kufita kibishi kufita dan kin gama zaman gidan nan balle kije kinama wani kato girki kega kuku yakarata chan daci a restaurant shidai da gidan ubanshi ba amma wlh bazaici abincin gidan ubanshi ba zan gyara miki zamane Rauda" ahankali Hajara trying to calm Maman su down tace "ya isa Mama kiyakuri, Bazata sakeba" dan shiru Maman tayi tana kallon yanda Raudan taduka tana kuka sosai mara kara kafin tai kwafa ta kalli hadadden akwatin data shigo dashi tace "kuma shegen akwatin nan kona shege zanyi" tasa hannu zata dauki akwatin da gudu tarike akwatin cikin kuka tace "Mama dan Allah ki barmin abuna" hannu Mama tasa zata fizge akwatin tarike gamgam tana kuka, cikin kunan rai Hajara tace "wai bazaki saki akwatin ba Rauda kanin ubanki ne yabaki akwatin, kisaki akace" cikin kuka sosai ta girgiza musu kai taki saki dan son abubuwan ciki takeyi sosai, Mama jitayi kaman ta kashe Rauda tahuta zata jibgeta Hajara tai sauri ta tare tasa hannu ta daki hanun Raudan tace "sake shegen akwatin" ta hankadeta tareda fizge akwatin tamikama Mama dan ayanda taga mama tasan zata iya jima Rauda ciwo ayanda ta zuciyan nan. Karban akwatin tayi ta kalli Raudan dake kuka kaman zata mutu tai kwafa tajuya tafita daga dakin tsaki Hajara tayi ta balla mata harara tahau kan gadonsu cikeda takaicin Raudan tai baccinta, sosai Rauda taci kuka harta godema Allah ahaka bacci yay awon gaba da ita awurin.
_*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_
_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤
_✍🏿M Shakur_
5️⃣ & 6️⃣
_how to pay your subscription fee_
_*zaki turo 300 ta account dina 3107021073 first bank aisha Muhammad, saiki turo evidence of payment ta WhatsApp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting*_
_*for those da prefer su tura kati, you can also send MTN card na 300 ta WhatsApp number na 07012181461 saina loda nasaki a group din danake posting ATSAKANKANIN SOYAYYA_
_Free page_
Sallame salla Ammi tayi
sake kwalamata kira akaro na uku tayi. "Aneesa wai bazaki tashiba, idan kika bari nazo dakin nan sai jikinki yay tsami, kindaisan abubuwan dake gabanki yau ko" da kyar ta iya bude ido jin Ammi na masifa tana kiranta jiya taci aiki a shago bana wasaba saisa tagaji haka, dama duk jumma'a haka take uban aiki a shago dan masu zuwa party nazuwa placing order dayawa kuma duksaitayi, da kyar ta sauko daga gado har bata gani da kyau tana dafa bango tafito daga dakin tafito Ammi tabita da kallo tai tsakar gida bayi ta shiga dan lokacin har gari yasoma wayewa fitowa tayi tadauro alwala takoma daki tadau hijabi ta sanya, akusada Ammi ta tsaya ta kabbarta salla, data idar tai karatun Al qur'ani sanna ta sallame ta gaida Ammi ahankali, amsawa Ammi tayi tace "tashi kije kidaura ruwa a wuta" gyadama Ammi kai tayi ta tashi ta zare hijabin jikinta tafito daga dakin tai kitchen wuta ta kunna ta daura pot din ruwan wanka dake cikeda ruwa tadau tsintsiya ta share tsakar gidan fess sanan ta shiga dakin dakin Ammi ta tattaro ta gyara sanan tawuce nata dakin ta gyaro shima tahada da falo ta gyara tafito da dattin ta kwashe, tadawo ta kunna turaren wuta sanan tafito tasauke ruwan daya soma shirin tausa daga wuta ta daura dumamen tuwo tahada ruwa ta shiga bayi, wanka tayi tana fitowa ta sauke tuwon dayayi tasa miya sanan tai dakinta, mai kawai tashafa tadau doguwan riganta na gida baki ta zura tafito lokacin wajen 8 nasafe ta zuba abincin ta dan tasan Ammi bata breakfast early tadawo ciki ta zauna kusada Ammi tafara cin tuwon dayay dadi miyan harda wake aciki, ahankali takeci harta cinye sanan ta kai kwanon kicin ta wanke hanun ta ta dauraye baki tadawo ta zauna kusa da Ammi, da hannu Ammi tanuna mata dakinta tace "daukomin purse dina" tashi tayi tai hanyar dakin Ammi tafito rikeda wata bakar purse ta zauna kusa da Ammi tamika mata karba tayi tabude purse din ta ciro kudaden dake ciki wanda suke na Aneesan na lallen datakeyi take tara mata dubu biyarne Ammi tamika mata tace "kije kisiyo kayan lallen, sanan kisiyo handglove banson yanda kike bata hanunki haka, kiyi sauri kidawo dan nasan anjima kadan yan lallen zasu fara zuwa yau asabar kina gida" karban kudin tayi tana kallon agogon bangon dakin ganin Takwas da rabine yanzu yasa tace "karfe tara kasuwan lallin ke budewa, Ammi ki faramin tsifan kafin lokacin" tai maganan tana zare hulan kanta tulin kitson kanta datai shuku na hannu yawani zubo har gadon baya, hulan data cire Ammi ta daura ta mayar mata tace "sokike kije kasuwa dakai daya da rabi, aga nan yay kato nan yay kadan, Tara zaki fita yanzu takwas darabi minti talatin yayma kitson nan kadan, yanzu jeki fara shiryawa ne, kafin kigama shirin lokaci yayi" kaman zatai kuka ta tashi tai hanyar dakinta, sip dinta tabude tadauko wani gogaggen atamparta riga da skirt dakeda dilli dillin ja, sai ta dauko jan hijabin ta dayakai mata har guiwa ta maida sip din tarufe tacire rigan jikinta ta shiga shiryawa, riga da skirt din yay mata kyau sosai gaban madubinta taje ta shafa hodanta tadau man baki tashafa a lips din sai abin yay kaman tasa pink lipstick, dawowa tayi tadau hijabin tasaka daya kwanta a fuskarta tadau karaman jakanta tafito, baki Ammi ta tabe tace "kasuwan aka cima kwalliya haka yan mata kodai nai siriki ne akasuwan" akunyace tace "laaaaa Ammi" dariya tadanyi ta dauke kai cikeda kunya tadau kudin dake gefen Ammi tace "nifa hoda kawai na shafa Ammi" tura kudin tayi cikin jaka tayi har lokacin taki kallon Ammi tace "natafi Ammi" "adawo lpy, ki adduan fita daga gidafa, kuma adaga kafa kar aje ana yauki akasuwa hmmm" Ammi tafada cikeda zolaya, murmushi sosai tayi tasa hijabi tace "to, Ammi idan yan lalle sunzo kice sujirani bazan dadeba" "shikenan, saikin dawo, kiyi addu'an fita daga gida" ficewa tayi daga dakin tai addu'a tafita daga gidan.
Around 8:40Am Hajar tabude dakin nasu ta shigo tana kallon Raudan dake kwance kan gadonta idanunta sunyi suntum suntum tace "kije Mama na kiranki adakinta, Khamis kuma yazo yana falo" ko alamun tashi batayi ba hakan yasa Hajar tamata ihu. "wai bazaki tashi kije kiran da mama ke mikiba mara kunya" tashi tayi ahankali tana turo baki tafita daga dakin, dakin Maman su ta shiga, Mama na zaune kan katafaren gadonta ta mimmike kafafun tana shan farfesun kaza, watsa mata harara tayi tace "sai yanzu kikaga daman zuwa rasakunyar beran tanka" ahankali tace "ina kwana Mama" hararanta Mama tasake yi tace "daban kwana ba zaki ganni anan ne?" matsar da farfesun tayi gefe ta sauko daga gadon, gaban wardrobe dinta tayi tabude taciro wani sabon dinkakken atampa na mustard da brown anyi dinkin riga da skirt sai mustard veil da mustard flat shoe mai kyau, mika mata Mama tayi cikin daure fuska tace "ai tun asuba kikai wanka, gasunan shirya anan yanzu nan Hajar zatazo tamiki kwalliya kitafi yana falo" karban kayan tayi ahankali ranta abace ta cire rigan ta ta shiga sakawa ahankali, rigan ta tsaya tana kallo yanda net ne daga ta kirjin ana hango boobs dinta, hannu tasa a wurin ta dago kai ta kalli Mama da itama ita take kallo cikeda masifa tace "miye to?" cikin dan shakakkiyar muryanta tace "ana hango kirjina Mama is net" harara Mama ta watsa mata tace "naga dai Khamis zaki aura har ubanki yasan da zancen, banda haka Khamis dandan Yayata ne na yarda da tarbiyan shi, yaro mai natsuwa da hankali ga kunya, me kike nufi mai zaimiki? Besides wanan dinkin mai net din wuyan ai shinaga yan mata ke yayi yanzu saisa na bada amiki irin shi dan haka karki kara cemin komi" daidai lokacin Hajar tabude kofar dakin ta shigo dauke da kayan kwalliya murmushi sosai Mama tayi tace "kaga yar albarka maijin maganan uwarta, bazaki taba ganin mara dadi ba arayuwanki Hajar saidai kiga daidai, yimata kwalliyan sutafi sai dare yau" murmushi Hajar tayi jin ddin maganan maman su, taja kujera ta zaunar da Raudan data dawo kaman gunki ta shiga mata makeup din, cikin 5min tagama mata sosai tai kyau, tadau gyalen ta yafa mata a kafada tace "tashi kuje" kallon gyalen tayi kaman zatai kuka tace "ahaka Anty, jibi kirjina fa" mugun kallo Mama ta watsa mata tace "barganin kinyi gayu bazai hana na lallasaki da safen nan ba, dan ubanki inya gani aike zai aura ballema Khamis baida kallon nan, wuce muje" ta tasata agaba sukai falo kanta akasa, wani kyakyawan