Showing 78001 words to 81000 words out of 180150 words

Chapter 27 - A Tsakankanin Soyayya Book 1 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

26 Sep 2025

2436

ke saukowa daga stairs tana sanye dawani baby pink hijab iya guiwa daga gani irin nazaman gidan nanne tasa wata yar shimi da straight skirt mai tsagu ta gefe daya, fuskanta da dan lema lema alamun daga wanka tafito kaya kawai tasa tana tafiya ahankali, tundaga kan yatsun kafafun ta dake dauke da fararen kumba yake kallo gasunan ajere gwanin ban sha'awa yake kallo har zuwa kan side slit din skirt din da idan tana tafiya yake fito da fatar yar kafarta dakeda kwanta cen gashi kaman irin yarannan dabasu san wahala ba wani irin serious murdamai cikin shi yayi dayasa yadauke idanunshi daga kan kafar nata yamaida kan fuskarta sabida wankan datayi har wani extra glow fuskarta yakara kan normal glow dinta karasa saukowa kasan tayi batare data kalli indama sukeba shi dama Abdul kallon match abinshi yake baima kufada itaba hanyar kitchen dinsu tayi ahankali tabude kitchen din ta shiga, kallon stairs Aliyu yayi ganin babu mai zuwa yasa yatashi daga kan kujeran yay kitchen bude kofan yayi ya shiga da sauri Aneesa dake kokarin daukan plate ta juyo suka hada ido maida kofan yayi yarufe ya shigo kitchen din dauke kai tayi daga kallonshi dan wani irin haushin shi takeji tadau kulan da Ammi tace ta zuba mata abincin ta gudun karyay sanyi tadau chokalin dinan abinci zata diba, ahankali ya tsaya agefenta yana kallon abincin datake shirin diba murya chan kasa yace "Aneesah nah!" wani abune taji yatokare mata zuciya sabida yanda yakirata kokarin diban abincin take tamasa a plate takasa hakan yasa ta ijiye kulan cikeda tsiwa ta kallai tace "karka kara cemin Aneesan ka, no karma kakara kiran sunana, na fadamaka baruwan ka dani, kuma ka koma inda kafito kabarmana dakinmu, su baby kakide, mutum kato dashi ana cemai baby, a'a ba baby baibo" ta harari bango tajuya tadau kulan abincin with annoyance kaman shi yamata laifi tana kokarin diba, dudda shi ba ma'abocin yin soyayya bane but from the look all he sees is jealousy a fuskan Aneesa so that means Aneesa na sonshi harma tana kishin shi, wani irin dadin yaji, hannunshi yamika ya fizge kulan abincin datake yin dambe dashi da sauri ta kallai tana kokarin danne feeling of kukan da takeji tamikamai hannunta cikeda masifa tace "kabani kulana" make mata kafada yayi yana karanta sakonni daban daban dake kwance akan fuskanta, cikin fushi tace "zan hadaka da Ammi na, kabani kulana nace" sake make mata kafada yayi ya ijiye kulan kan fridge dake bayanshi kafin ahankali yatako yazo dab da ita yana kallon fuskanta kasa jure kallon dayake mata tayi ta dauke kai ta matsa gefe zata wuce tafita da sauri yatare ta ta kusan fadawa kirkin shi hakan yasa takoma baya da sauri zuciyata na boiling takasa daga ido ta kallai sabida kwalla daya taru a idanunta, cikin wani murya chan kasa mai kama dana lallashi yakira sunanta. "Aneesa" hannu tasa da sauri kanta akasa ta share hawayen dasuka dan zuvo dan bataso yaga hawayenta taki dagokai. Ahankali yace "I love you so much Fateema, you are the only one in my heart, ke kadai zuciyata ke tsananin kauna daga ranan da idanuna suka ganki, I love everything about you, am sorry the way I treated you back then, please kibani dama na nunamiki irin son danake miki, zaki aureni Aneesa?" batare data kalleshi ba tace "Allah kyauta na aureka" lumshe ido yayi dan ya tsani kalman, Murya chan kasa yace "kina sona?" cikeda tsiwa tace "banson ka, mezanyi da masifaffe" ita kanta batasan mesa takemai tsiwa hakaba kuma bahalinta bane kawai tsiwan zuwan mata yake, dan murmushi yayi tareda cizan bottom lips dinshi yana kallonta yace "to mesa kike kishina?" da sauri tadago idanunta dahar sundan chanza kala ta kallai tace "me ruwana dakai dazanyi kishinka? Allah kyauta" murmushi yayi tareda dan juyamata gira yace "okay tunda bakisona bari inkoma wajen maisona nama barta ita kadai nabiyoki" wani irin kashine ya tokare mata makogoro batason ta furta kalaman dasuka cikamata baki amma saida suka fito. "kamafi ruwa guda, su baby kakide, ba baby ba bobo rubbish" ta finciki plate din datadan zuba rice aciki kafin ya fizge kulan tazo zata wuce kaman zata fashe, fashewa yay da dariya ya kama hijabinta da sauri tajuyo ta kallai idanunta sun cika da hawaye sosai tace "ka sakenmin hijabi kona cire maka hijabin na barmaka" dan ware manyan idanunshi yayi cikeda tsokana yace "zaki iya bari naganki da dan singlet din dake jikin ki?" da sauri ta kalli jikinta tayaya yagane singlet tasaka ajiye plate din abincin tai da sauri ta maida hannayenta tacikin hijabin tana turo hijabin gaba dan ya kwanta mata ajiki dayake hijabin robaroba ne karyaga jikinta ta ballamai harara zuciyanta na tafarfasa tace "kawuce kabarmana kitchen dinmu kona hadaka da Ammi na" ta kawad dakai tana kunkuni tace "wanan katoton ne wai baby" murmushi yayi sosai yace "inba ga tsoroba kifada da karfi naji" ko kallonshi batayiba, daukan kulan abincin ta yayi cikeda tsokana yace "bari na kaima babyna abincin nan" da sauri tadago kanta ta kalli kulan daya dauka yana rufe marfin da kyau hawaye ne suka cika idanunta gam tare kofan tayi tareda mikomai hannunta tabude baki zatai magana saiga hawaye sharr sun zubo da sauri tasa hannu tashare hawayen tace "wlh bazaka kaima wata abinci naba, Ammi ta dafa ta ajiyemin, babu wacce zata cim.....mi...." takasa magana sabida yanda bakinta ke rawa saiga wasu zafafan hawayen sharrr da sauri ta daura hannunta akan fuskanta tarufe fuskanta tana kuka mara kara bataso yagani hawaye nabin hannayenta, wani irin rawa zuciyan Aliyu yafara jiyake kaman yakamata ya rungume ta and assure her cewa ita kadai yakeso ita kadai ne azuciyanshi, ahankali ya ijiye kulan akan fridge ya tsugunna ahankali tareda kai guiwanshi kasa yana kallon fuskanta yanda har lokacin take kuka sabida yanda kafadarta ke rawa, hannayenshi yakai ahankali ya daura akan guiwowinta hakan yasa ta janye hannunta daga kan fuskarta daya gama wankewa da hawaye idanunta harsunyi ja sundan kankamce ta kallai, girgiza mata kai yayi ahankali, Murya chan kasa yace "am sorry for making you cry I was only trying to show you that kinaso na just dat you hate some part of me, and I promise to change for you, bazan kara miki fadaba, I will take care of you, I love you so much, let's build foundation of love da babu wata ko wani dazai iya gizgixata, let's build SOYAYYAN da ATSAKANIN TA babu wata SOYAYYA data isa ta shigo, Ina miki tsan-tsan so, son aure, I want you to bear my children, I love you Fateema, I love you you Anebaby, stop crying I belong to you ke kadai, wipe your tears kona goge miki?" makemai kafada tayi tareda sa hannu ta goge fuskan nata tass tana kallonshi ita kanta batasan ya akayi take sonshi ba, bama tasan lokacin data fara sonshi ba kawai taga tana sonshi dama haka so yake, murmushi yayi yanaji kaman yay kissing nata yace "bazaki ce na tashi ba Baby" dan murmushi tayi akunyace tareda rausaya kanta tace "ka tashi" tashi yayi ahankali tareda daukan plate dinta yadau kulan yazuba mata abinci sai kallonshi tabaya take, spoon yadauka yasa mata akan abincin ya mikamata yana kallon fuskanta ahankali tasa hannu ta karba batare daya sakin mata plate din gabaki dayaba yace "bakice min kinaso na ba" akunyace ta fizge plate din tajuyamai baya tareda sa hannu zata bude kofan ahankali tace "ni banson lazy man, I want My Aliyu to be the strongest man alive on earth, unbeatable, champion, kai karfi kaman wanda muke gani a TV suna wrestling da masu zuwa gym, ni banson lazy I want to see the strong you" tadan juyo tamai wani irin kallo dayasa numfashin shi yakusa tsayawa tace "until then amsan dakake so kaji bazakaji ba" tabude kitchen din da gudu tafita yabita da kallo yana murmushi kafin yadan shashafa gemushi yace "fair enough, I can do anything just to win your heart Anebaby".

_duk wacce takaranta batare data biyaba Allah ya isa__*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



3⃣7⃣


Fita tayi daga kitchen din da sauri, hada ido sukayi da Abdul dake kan kujera yana rikeda remote din TV yana murmushi, dauke kai tayi da sauri tai hanyar stairs daidai Ihsan tafito sabida gajiya d jiranta datake tayi a daki tace "ainazaci afalo kikecin abincin shine nace barina biyoki" girgiza mata kai Aneesa tayi, cikin yar siriruwan muryanta tace "a'a, mukoma daki" juyawa Ihsan tayi sukai sama.

Ahankali ta zauna kan gadonta rikeda plate din abincin tana murmushi tana juyawa tana tunanan kalaman Aliyu dake ratsa mata zuciya, tana wani irin karajin maimaicin kalaman shi a kunnuwanta, tabatan da akayi yasa tadago kanta da sauri Ihsan ne kaman zatai kuka tace "kinki kulani, ba Momma tacemin mun zama friends ba, kodai bakisona ne a matsayin kawarki" da sauri Aneesa ta girgiza kai tareda ajiye abincin agefe ta zare hijabin jikinta ta ijiye tace "laaaa, no bahaka bane ina sonki a matsayin kawata sosai ma" murmushi Ihsan tayi cikedajin dadi tana kallon jikinta, wani milk color shimi tasaka ya kwanta a jikinta bulbul ya bayyanar da kirjinta sosai kaman zasu yaga sufito, murmushi tayi tace "to yaushe zakizo gidanmu ki kwana?" ahankali Aneesa tace "nima bansaniba amma zan tambayi Ammi da Abba insun barni zanzo I promise" murmushi Ihsan tayi tace "to shikenan dau abincin ki to kici hudu takusa zaku koma islamiya kumako" gyadamata kai Aneesa tayi ta faracin abincin haka Ihsan keta mata hira babu labarin makarantan su dabata bataba harta cinye abincin hira takemata, kwalama Aneesa kira da Ammi tayi yasa ta amsa da sauri. "na'am Ammi" daga tachan Ammi tace "kin manta zaki islamiya ne ko" da sauri ta kalli agogo hudu saura minti biyar, da sauri Ihsan tace "la mun manta tashi da sauri ki shirya" tashi tayi ta shiga bayi tadauro alwala tazo tai sallan la'asar sanan tai wajen wardrobe dinta, wani dogon rigan yar kanti tadauka baki ne color tasaka, tazaro wani clean ironed mustard color hijabinta har kasa tasaka tasaka safa sanan tadauko wani dan babban jakanta ta kwashe littatafan da aka bata aciki ta rataya ta kalli Ihsan dake ta binta da kallo itadai tanason wanan Aneesan tarasa mesa, waya Aneesa ta mikamata tace "gashi samin number ki zamu dinga WhatsApp" sakamata number Ihsan tayi sanan tarakota suka fito afalo sukaga Ammi da Momma sai hira suke Momma tace "har anfito yan islamiya to adawo lafiya" Ameen tace tana kallon Ammi dake binta da kallo batare datace mata komiba, turobaki tayi a shagwabe tace "Ammi bazakimin addu'a ba" dariya Ihsan tayi tace "laaaa ashe kina shagwaba katuwa dake" murmushi kawai Ammi tayi tace "wanan Ihsan, aina kosa Allah yakaimu ranan aurenta nayi na tarkatata nakaita gidan mijinta nagaji" kaman zatai kuka tace "niba inda zani ina tare da Ammi na" dariya dukansu sukayi Ammi tace "bazaki wuce kitafi ba kin tsaya surutu sai kinyi latti, kyasha dukan latti, adawo lafiya to Allah kiyaye, banda wasa kuma adage da karatu" bye tama Ihsan sanan tawuce tabude kofa tafita daga dakin already taga har yara sun cika wurin motar ana jiran driver yazo yabude su shiga, ahankali take tafiya tana nufan parking space din kaman ance ta daga kai da Aliyu suka hada ido dake gaban shashin shi yana mata wani irin kallo yay folding hannunshi a kirji, dauke kai tayi kirjinta na bugawa tarasa mesa kirjinta ke bugawa duk inta ganshi kasa daurewa tayi tadan dagokai ta kallai sake hada ido sukayi har lokacin itayake kallo kaman zai cinyeta da idanu, samin kanta tayi da dagamai hannu kaman wata yar koyo taimai waving hand din alamun bye da sauri ta kalli hannun nata kaman ma batasan lokacin data dagashi ba, dan murmushi yayi tareda lumshe ido yabude su ahankali yana kallonta ahankali yay waving nata back irin waving dinan na yaron dabayason maman shi tafita, dauke kai tayi da sauri tadena kallonshi dan hakanan taji yawani irin bata tausayi kaman zuciyanta da nashi na communicating, kaman zuciyanshi nace mata karki tafi kidawo ki zauna dani.

Karasawa wajen motan tayi har direba yabude yaran duk sun shiga Hajar ne kadai agaban motan, wani matsiyacin kallo tama Aneesan tace "gasu agola nan anzo" daidai Aneesa takaraso wajen Rauda dake cikin motan dan ciwon cikin yasaketa sosai yanzu tace "kai Anty Hajar wlh babu kyau fa" ta kalli Aneesa datai kaman batajisu ba tasakin mata murmushi tace "shigo ki zauna Aneesa" murmushi itama tamata dan sai yanzu ne tagane Rauda itace yarinyan data taimaka ranan data fara ganin Aliyu sarkin kallo sai kallonta yake kaman baitaba ganintaba, shiga cikin motan tayi ta zauna kusada Rauda, Hajar ta shigo itama sanan direba yarufe kofan yakoma gaba ya shiga yaja.






Ahankali Rauda tasa hannunta takarbi hannun Aneesa data danyi wani zanen lalle ta around kumbunan ta tace "wow Aneesa wanan wani irin zanen lalle ne? Bbu kodaya a hannunki saita wurin yatsun ki it really looks nice, waya miki ya bala'in burgeni, waya miki?" murmushi Aneesa tayi tana kallon yatsun nata zanen datayi ne da bikin Ammi saitama Ammi kuma lalli mai kyau, ahankali tace "ninayi" "iyye kin iya lalle ne daman?" gyadamata kai tayi tace "na iya, kinaso namiki?" da sauri Rauda ta gyada mata kai tace "inaso mana, sosai ma" ahankali Aneesa tace "shikenan duk randa kika shirya zan miki wanda ma yafi wanan kyau" washe baki Rauda tayi tace "nagode, Awani aji aka saki dazu a hadda?" ahankali tace "aji hudu, islamiya ma aji hudu" bangaje mata kafada Rauda tayi cikeda jin dadi hira irin na kawayen nan tace "iyye ajinmu daya ashe, nima dazu dasafe cikina keta ciwo saisa banjeba wlh" ahankali Aneesa tace "sorry Allah ya sawake" cikeda damuwa Rauda tace "kema kinayin ciwon ciki idan zakiyi?" gyadamata kai Aneesa tayi batare datai magana ba she's not just comfortable sabida Hajar dake wurin, dan tana ganin yanda Hajar ke hararanta itada Raudan kaman ta bubbuge su, cikeda damuwa itama Rauda tace "sannu kinji Aneesa, ance inkai aure yana denawa" "dalla malama kimana shiru ko kina maganan iskanci agaban yara" Hajar tafada cikeda masifa, cikin tsiwa Rauda tace "to wai me ruwanki dani Anty Hajar, yaran sunsam menake cewa ne, kinamin wani ihu saikace nayi dake" ta harari gefen side din Hajar din, murmushi Aneesa tayi hakan yakara harzuka Hajar tace "dan ubanki nikekema rashin kunya?" cikeda rashin kunya Rauda tace "karki kara zaginmin uba nidai, Dady na nagida yana hutawa abinshi kina duramai zagi, kuma ai badake nakeba daga ina firana da kawata saikiyi ta zagina, dakenayi? Neman tsokana kawai" kwashe wa da dariya yaran motan sukayi, wani mugun kallo Hajar tamusu hakan yasa at ukai shiru, Hajar tai kwafa tace "zamu koma gida kaman Mama taji komi" dauke kai Rauda tayi tacigaba da hira ta da Aneesa batakara cemata komiba harsuka kai makaranta suka tafi ajinsu a binsu.



***

Wuraren magrib suka shigo gidan, derevan su yay parking yafito tareda zagayowa yazo yabude musu, saukowa sukayi Rauda ta dubi Aneesa data sauko bayan ita tace "saida safe ki gaishemin da Mummy, gobe zanzo na gaisheta kinji, bari naje part din Ya Aliy...." fizgan hannunta Hajar tayi kaman tafizgo barauniya tace "dan ubanki bazaki ba, ba Mama tahanaki zuwa bangaren shiba" cikin tsananin jin haushi Rauda tace "wai me haka Anty Hajar, wlh kisakeni kona hadaki da Dady me ruwanki dani sai samin ido kike kina sauraron conversation dina" cikin fushi Hajar tadunkule hannu ta sakin mata mugun dundun abaya da har Aneesa saida tajishi har cikin ranta sabida karan dayayi dumm! wani irin ihu Rauda tasaki kaman zata fasa gidan tai kasa tana bankarewa daidai Aliyu ya shigo gidan daga masallaci, rike ciki Rauda tayi dan har cikinta taji dundun tasaki wani irin mugun kuka tana kama cikinta, kaman Aneesa zatai kuka ta kalli Hajar dake huci kaman wata kumurcewatu😎 tace "me tamiki zaki mata wanan dukan bayan kinsan cikinta naciwo" da yatsa Hajar ta nunata tace "ke kalleni nan am 25 niba tsaran wasan ki bace, ba ruwanki idan nida kanwata na fada agol...." wani irin wawan mari da aka dauketa dashi yasa takasa karasa kalman dazata fadi tadago idanunta da sukai mata dishi dinshi tsabagen zafin marin tana sosa wurin ta kalli wanda ya mareta Aliyu ne yana sanye dawata white riga mai dark blue short hands sai dogon black jean dayasaka kamshin turaren shi yabi yacika wurin, hanunshi yadaura kan wandonshi yana kwanto belt dinshi dama bala'in haushin ta yakeji tun ture Aneesa datayi dazu tafadi, cikeda rashin kunya Hajar ta kallai tana ganin belt din dayake shirin kwancewa ita tafi karfin tagudu tace "wlh karma kasake kayi gigin ciro belt dinan kace zaka dakeni dashi agaban kannina kajamin raini agaban yaran da aka haifesu jiya, meruwana dakai nasan kane shiga shara ba shanu, wlh ka zaulamin belt dinan saina hadaka da Mama na tafito ta ramamin mugu kawai" wani irin zuciyane Aliyu yaji tarufe shi ya tsani rashin kunya, ahankali Aneesa ta saukar da kanta kasa jitake kaman tarufe Hajar da shegen duka yanda takema Aliyu rashin kunyan nan harda zagi.




Karan saukan belt da ihun Hajar dataji yasa ta dagokai, takoina Aliyu ke zubama Hajar duka kaman dama anbashi contract din dukanta ne, murmushi Rauda tayi tana share hawayen daya gama wanke mata fuska ganin Ya Aliyu na rama mata, ihu sosai Rauda take tana kiran maman su. "wayyo Allah na, Mama, Mama, Mama kinga Ya Aliyu ko, Mama zai kasheni" fara bude kofofi matayen Dady sukayi suna kallon yanda Aliyu ke kilan Hajar dake ihu da magriban nan, bude kofa Mama tayi jin ihu da hayaniya atsakar gida idanunta ne sukaci karo da Aliyu na dukan Hajar da belt gasu Rauda da sauran yaran gidan jikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login