Showing 99001 words to 102000 words out of 180150 words

Chapter 34 - A Tsakankanin Soyayya Book 1 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

26 Sep 2025

2429

tafi wurin Abba? Kin fara abinci ko baki faraba?" muryanta narawa sosai tace "ban faraba....l...okacin" dan murmushi officer yayi yanuna mata katin maganin poison din yace "Aneesah sunan ki ko?" da sauri ta gyadamai kai, ahankali yace "kigayamin gaskiya, ni inhar mutum yafadamin gaskiya to komi na zuwan mai ta sauki inyamin karyane yakecin bakar wuya, a ina kika sami katin maganin nan? Kowani yabaki kisa karkimin karya bazan miki komiba, fadamin a ina kika sami katin nan? Wayabaki kisakama Aliyu a abinci?" girgixa kai Aneesa tayi hawaye ya gangaro tace "wlh, wlh nibansan katin maganin nanba, ni wlh banma taba ganinshi arayuwata ba wlh kuwan" hawaye suka zubo sharrr ta share da bayan hannu, murmushi Officer yasake yi yace "kin tsani Aliyu kin tsani Aliyu, luckily sai jiya babanshi yace kidafa mai abinci, sai abin yazama babu kowa adakin shine kika ciro magani kika samai danyaci yamutu hakane Aneesa?" fashewa da kuka tayi sosai tazo kusada Ammi tarike Ammi gam cikeda tsoro tace "Ammi kicemusu ni wlh bansan maganin nanba, ni bazan taba kashe Ya Aliyu ba wlh wlh kuwan" tafashe dawani irin kuka ajikin Ammi ahankali Ammi ke kallon Dady dayay shiru yana kallon Aneesan dake kuka girgiza kai yayi yace "No officer kubar yarinyar nan trust me something happen, Aneesa bazata iya kisa ba, dan ita tadafa abinci doesn't mean ita tasaka poison, banda haka ba itakadai ne agidan nanba sanan kowa anan can enter bangaren Aliyu" cikeda rashin kunya da rashin mutunci Maman su Rauda tace "me kake nufi Alhaji Aneesa bazata iya kisa ba to mune kenan zamu iya? Sonkai kiri kiri sabida yar gaban goshin kace, mukake zargi kenan mune zamu iya ko, nagadai akwai CCTV agidan aje aduba mana hakanan nifa na tsani zargi koba hakaba Amina" da sauri sukace hakane wlh, officer ne ya kalli Dady yace "Sir akwai CCTV agidan nanne?" gyadamai kai Dady yayi yace "akwai a compound dinan, banda haka akwai CCTV a bangaren Aliyu dashi kanshi baisani dashi ba, CCTV tareda kwan lantarkin dakinshi yake, nasaka ne sabida nasan matayena sun tsaneshi zasu iya komi akanshi saisa nasaka?" da sauri officer yace "ina zamuga footage din" "muje yana secret room dina" ya kalli matan yace "kar wacce ta tafi daki kujiramu anan" hanyar flat din Mama Dady yayi da Officer, wani irin murmushi Mama tayi zuciyata tai sanyi dama takira CCTV ne sabida tasa aduba, Dady yazaci shi kadai ysan password din shiga dakin baisani batun yauba tasan.



Dakin Mama sukayi sukai sama, agaban wani daki ya tsaya da handle din kenan kaman waya ga boturan dannawa, password din yasaka saiga dakin yabudu computers ne wurin shiga adakin, straight computer bangaren Aliyu Dady yanuna musu, officer ya zauna gaban computer yay rewinding back har zuwa footage din jiya, rewinding sosai yayi har zuwa daidai inda Aneesa tazo part dinshi ahankali yace "got it" tsayawa Dady yay akanshi ya shiga kallo kirjinshi na bugawa shigowa part din tayi rike da tray ta kalli ko ina kaman tana neman wani abu kafin suga tai tafiya da sauri ta shiga falon ta sauke tray din kan center table tana kalle kalle, sai sukaga ta chusa hannunta agefen zaninta basuga metayi ba sundaiga tafito da kwaya daya ta jefa a mug saikuma tadauko daya ta dagargaza kaman yanda ake dagargaza magi da hannu ta barbaza kan saman pancake ta kakkabe hannunta tadauka da sauri tai hanyar bedroom dinshi tabude kofa ta shiga dayake babu CCTV a bedroom dinshi basusan meya faru ba sundaiga chan tafito daga dakin aguje, baya Dady yayi zai fadi tsabagen yanda heartbeat dinshi yay weak polisawan suka tareshi suna salati wani irin fincike kanshi Dady yayi yafita daga dakin da mugun zuciya.







Tundaga yanda Ammi taga fuskarshi gabanta ya shiga faduwa ta shiga ambaton Allah, dawani irin zuciya Dady ke dumfaro su harya karaso inda suke tsaye hannu yasa yawani irin fizgo Aneesa dake tsaye kusada Ammi jikinta na rawa Dady baiyi wata wataba ya daga hannu ya watsa mata lafiyayyen mari "tass!" runste ido Ammi tayi dan har kashinta taji marin da Dady ya dauke Aneesa dashi, fashewa da kuka sosai Aneesa tayi tsabagen tsoro tamika hannunta tana kokarin kamo Ammi tace "wayyo Allah na Ammi, Ammi, Ammi, Ammi n...." zuba mata wani marin Dady yayi akaro na biyu da saita yasa tai shiru tai gum tama kasa magana sai dubu datake gani a idanunta cikin ihu da daga murya Dady ya jijjigata yace "me Aliyu yamiki? Meya miki kikeso kiashi lahira? Ubanwa yasaki kikashe min d'a??" yakara daga hannu zaikai mata mari na uku Ammi ta kirashi. "Alhaji" dago kai yayi ya kalli Ammi idanunta sunyi jajir suna shirin tsiyayar da hawaye, cikin raunin zuciya Ammi tace "kayakuri Alhaji ka kwantar da zuciyan ka abi komi ahankali, Aneesa bazata iya kisa ba, nasan abinda na haifa" cikin wani irin fushi Dady yace "nine makaryaci ko, kina zaton shiri nama yarki? Okay naji shairi namata a CCTV baya shairi ko to muje kigani" ya finciki Aneesa dahar lokacin bata gani sosai yay flat din Mama Ammi tabisu da sauri su Rauda dake kuka sosai da sauran matan Dady ma suka bisu har dakin cameran, shiga dakin Dady yayi rikeda Aneesa kaman wacce tai sata sauran matan ma da Ammi ma ta shigo cikin tsananin fushi Dady yace "play d footage back officer" dan bude idanu Aneesa tayi ta kafe computer da ido, wani irin faduwa gaban Ammi keyi lokacin da sukaga Aneesa ta jefa kwayar a mug da lokacin data dagargaza daya ta zuba akan pancake dakin yadau salati Mama tace "ga irinta nan ai, aure aure yau munga ranan aure aure, ka aurosu karufa mata asiri ka kawota gidanan da ita da agolan yarta, kahada yarta da namu gashinan suke son kashemaka d'a muda muke gidan nan shekara da shekaru ko kurjewa bamu tabasa Aliyu yayi ba amma gasunan dududu satinsu nawa a gidan just sati biyu da kwana daya" tajuya ta kalli Ammi tana mata tafi a fuska tace "to Allah yatona asirin ku, Allah yatona asirin ku kinyi amfani da yarki ta kashe Aliyu an kamaku, Allah saiya sakama Aliyu, butulu kawai murders, Aliyu daya dauke ku a matsayin uwa, andaiji kunya anji kunya, wlh hukuma ce zata rabamu daku, mutumin daya miki komi yafi fitaki kanmu harda siyamiki mota ne zaki kashema da" Dady jiyayi kirjinshi na tafarfasa kan maganganun Mama dan kaman tana sosamai inda kemai ciwone, cikin fushi Dady yajijjiga Aneesa dake kuka sosai yace "me dana yamiki Aneesa zaki kasheahi tell me the truth" fashewa da kuka sosai tayi tace "Abba wlh wlh, na rantse maka da girman Allah bani bane wlh, wlh kuw......" wani irin mari Dady ya kifa mata abaki saijini cikin ihu yace "stop lying! Stop lying kifadamin gaskiya, Maman ki tasa ki kashemin Aliyu kowane?" da sauri ta girgixa kai muryanta harbaya fita da kyau tsabagen kuka tace "wlh Abba banine ba, banine ba na rantse maka da girman Allah" cikin wani irin fushi ganin yanda take karya bayan ankamata dumu dumu yasa Dady yarufe ta da duka baji bagani tun Aneesa na ihu tana kiran Ammi hartazo takasa ihu ganin yana neman sumar da ita yasa officer da yaranshi suka rikeshi, yaciro ankwa daga aljihu yakama hannun Aneesa yasamata yace "with all the evidence damuka samu a kanki malama Aneesa, you are under arrest for attempt murder of Aliyu Muhammad Ibrahim you have the right to remain silent anything you say will be used against you" yajuya ya kalli Ammi dake kallon Aneesan dako numfashi bata iyayi yace "ki gayama yarki tafadi gaskiyan duk inda tasamo wanan poison din inba hakaba gidan yari ne makomarta" yaja Aneesan kaman yanajan kare sukai hanyar fita daga dakin Ammi ta tsaya still tana ma Dady wani irin kallo, duk fita akayi daga dakin akabi su officer dan aga inda zasuyi da Aneesa yarage daga Ammi sai Dady adakin, ko kallonta Dady baiyiba azuciye yazo zaibi tagefenta yawuce takama hannunshi tarike lumshe ido Dady yayi Allah kadai yasan iyason dayake ma Ammi dan tabashin nan datayi har brain dinshi yaji, kasa juyowa yayi hakan yasa ahankali Ammi ta zagayo ta gabanshi tasan Dady nacikin tashin hankali, ya acikin matsala saisa dudda uban dukan dayama Aneesa still tamai uzuri batason ko kadan taga bakinshi, ahankali tana kallon fuskan shi tai kneeling akasa ta hade hannayenta ta danne zuciyata sosai dan bata so ta karaya she needs to be strong and fight this battle for her daughter a yanzu Aneesa batada kowa sai ita she's all alone, Murya chan kasa tace "Alhaji nasan kana cikin tsananin fushi da bacin rai amma dan girman Allah ka sauraren" tadanyi shiru tana sauke ajiyan zuciya tadaga fuskanta ta kallai har yanzu idanunshi a lumshe kaman bayamason ganinta ne, Murya chan kasa tace "Alhaji bantabajin daidai da atom of hatred towards Aliyu ba, na rantse maka da Allah ubangijin mu, ubangijin Al arshi wanda ya busamana numfashi, ubangijin sammai bakwai, wanda ya halicce ni ya hallice ka ya hallici duwatsu da dabboni Alhaji bazan taba tunanin bama Aliyu wani abu danna halaka shi ko kokuma wani abu mai kama da hakan, haka zalika zan iya rantsemaka Aneesa ma bazata iya hakanba, am not justifying abinda Aneesa tayi bakuma kokarin kareta nakeba, but dan Allah ka yakuri, ka sauko da zuciyan ka, dan girman Allah kasaka asaki Aneesa she is too small tazata san rayuwan gidan yari kokuma rayuwan police station the trauma bazai taba barinta ba, Allah kayakuri ka janye case dinan kasa asaki Aneesa tadawo gida let's solve matsalan nan maturely, matsalan gidane let's solve it at home dan girman Allah kaji".





_follow me lemme walk on the journey of visuals can be deceptive wlh_
_*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_





_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤




_✍🏿M Shakur_



4️⃣8️⃣



_hello Fanmily, follow me on Wattpad at *mamanshakur* dan samin all littafai nai harda tsofaffin💃🏼_


_how to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment to watsap number na 07012181461, sainai adding dinki a group din a tsakanin soyyayya. For those dabasu da banki zaku iya turo katin MTN ta watsap number na 07012181461_

_Inkika karanta batare dakin biyaba keda Allah, ina binki bashi, kuma Allah ya isa_


_masu fitarmin da littafi waje, kuda Allah_



....
Bude idanu Dady yayi yadaura su kan Ammi saida taji tsoron yanda idanunshi yayi ja, ahankali yace "nafada kaman bakijini da kyau ba yanzu zan kara maimaita miki kiji da kyau, duk wanda yace zai tabamin yaro to wlh sai inda karfina yakare aduniyan nan, sanan kikace bincike? Binciken uban me za'ayi bayan ke dakanki kinga lokacin da shaidaniyar yarki ta barbadama yarona poison a abinci binciken uban me zanyi eh? Listen to me and listen very well Aneesa will pay for wahalan dayarona yakeyi mercilessly, dukan danamata anan kadan ne azaban dazansa amata saita gwammace dama mutuwa tayi da wanan azaban, kema kidage da addu'a Allah tashi kafadun Aliyu idan yarona yamutu banga abinda zai hanani karna saka arataya Aneesa harta mutuba, sanan banga abinda zaisa na withdrawing case dinan ba your daughter must be charged for attempt murder of my son" yana fadin haka ya kabar da hannun Ammi dake kan guiwanshi yay gaba zai wuce da sauri Ammi tabishi tasake rike guiwanshi tasa hannu daya ta share kwallan daya zubomata zatai magana saikuma tafashe da kuka sosai at this point takasa rike kukan kawad dakai Dady yayi dan baiso taga fuskarta ahankali cikin kuka sosai Ammi tace "Alhaji kayakuri, kayafema Aneesa, banda karfin ja dakai, banda karfin jadakai wurin hukuma, Alhaji Aneesa marainiya ce, kasan kannin mahaifinta ko kudin belinta kokuma kudin tara basuda shi kayakuri, kabi abinan ahankali, Alhaji koda Aneesa ce tayi hakan naji tunda dai Aliyu da ranshi yana numfashi bazaka iya yafemata ba?" da yatsa Dady yanuna ta yace "inhar akan Aliyu ne bansan yafiya ba, koda duka duniyan nan zasu taru bazan yafema yarki ba dan ta taba abinda yafi soyuwa agareni" ya tura Ammi yawuce yafita daga dakin, fashewa da kuka sosai Ammi tayi tama kasa tashi daga wurin takai kusan minti ashirin sanan tasauko kasa Mama da kishiyoyinta duk suna zaune suna ganinta suka kece da dariya hawaye ta share tawuce tafita daga dakin hanyar Gate tayi sojoji suka tareta sukace Alhaji yabada umarni kar abari tafita daga gidan haka ta lallaba takoma daki kuka taci bana wasaba ganin kanta yafara ciwo yasa tawuce ta watso ruwa tai alwala tazo tai sallan azahar tai addu'o'i tai addu'a Allah ya kare mata Aneesa saikuma kuka takasa hakura, ganin har dare ba labarin Aneesa gashi takasa bacci bataga Dady ba danbai dawoba yasa duniya tamata zafi tadau waya takira Baffa nan ta sanar dashi abinda ke faruwa tsaf tana kuka da kyar Baffa ya lallasheta ya sanar da ita gobe suna hanya, ranan saidai bacci barawo ya saceta bata iya bacci ba.


Inkika karanta batare dakin biyaba Allah ya isa
Wuraren karfe uku su Baffa suka iso Amma anhanasu shigowa Ammi itama anhanata fita, da waya tamasu kwatancen asibitin da Dady yake, nan sukaje suka sami Dady, faram faram Dady ya karbesu yakaisu sukaga Aliyun sun firgita da condition dinshi kaman wanda ke coma nan suka bijiromai da maganan Aneesa Dady kekaxewa yayi yahau xubomjsu ruwan bala'i kan saiyaga bayan Aneesa sun tsorata dan sunga new side of Dady sukai sukai dashi to yafada musu wani police station Aneesan take yaki yace "sai danshi ya warke tukunna suji yanda yakeji" ganin kaman ba Dady yasa suka juya suka tafi nan suka kira Ammi suka sanar da ita komi Ammi kuka harta godema Allah.

Hausawa sunce abu kaman wasa wai karaman magana tazama babba, yau kimanin sati biyu kenan Ammi batasa Dady a ido ba! Batasa Aneesa a ido ba! Gashi yahana abarta tafita daga bayama sojoji uku taga sunzo gaban flat dinta sun tsaya ko nan dachan ba'a bari ta tafito tana flat dinta, sosai wani irin zazzabi da ciwo yarufe ta bata iya bacci, kullum kaima Allah kukanta take, tana addu'a yabama Aliyu lafiya sanan ya tsare mata Aneesa aduk inda take yanzu ne tasan cewa manyan kasa masu kudi masu kudine, imagine Dady yasa ankulle Aneesa bamasusan a inda aka kulleta ba, duk police station dasu Baffa zasuje dazaran sunkira sunan Dady saidai ma akore su a karshe ma komawa kaduna sukayi dan duka kudaden su yakare akan zirga zirgan dasuka dingayi a Abuja.
Duk wacce takaranta batare data biyaba Allah ya isa.


Ahankali Dady yabude kofar flat din Ammi wani calm kamshin turaren nan yamai sallama dakin fess babu datti ko kada kaman ma ba'a rayuwa aciki, ahankali yamaida kofan yarufe yay hanyar stairs ahankali yake tafiya haryakai sama tsayawa yayi agaban dakin Ammi kaman mai tunani saikuma yasa hannu yabude dakin ya shiga da sallama chan kasa babu kowa adakin sai gadon dayagani yadan hargitse, kakarin amai dayaji yasa da sauri yabude kofar bayin Ammi dayagani tana amai yasa yace "subhanallah" ya shiga da sauri yakarasa inda take a tsugunne ya tsugunna tareda dafa bayanta zagin dayaji yasa yace "wat bakida lafiya" ruwa yadeba ya wanke mata fuska tareda zubamata ta kuskure bakinta tana kokarin mikewa tsaye yadagata tareda hadata da jikinshi ahankali ya sauke ajiyan zuciya ya danna bturin dazaiyi flushing aman sanan yabude kofa yafito da ita zaunar da ita yay abakin gado yatashi yadauko clean towel yadawo yazauna yana goge mata baki yana kallonta yay mugun kewanta yarasa me yasa yakasa tsanarta adaddafe yay sati biyun nan batare dayazo ya ganta ba dudda abinda yarta tama danshi, ajiye towel din yayi ahankali yanabin jikinta da kallo rigan bacci ne a jikinta mai V neck da sphagetti hand hakan ya bayyanar da kirjinta dayaga kaman ma sunfi da cikowa, ahankali cikin dan kakkausar murya yace "bakida lafiya shine baki sanar daniba mesa inda wani abu yasame ki fa?" wasu irin hawayen bakinciki ne suka zubomata ahankali tadago kanta ta kalleshi, bayan hannunta tasa ta share hawayen dasuka zubomata murya chan kasa tace "Alhaji akwai maganganu da dama araina wanda nasan koda zan maka su bazaka taba saurata ba, abinda nakeso nafadama nasan alarshin Allah na girgiza duk lokacin da aka fada" dan shiru tayi tasake share hawayen daya zubomata tana share majina, ahankali tace "Alhaji ina rokon ka dan Allah kasakeni!" wani irin sauka maganan tayi a zuciyan Dady kaman saukan kibiya. "ka saken, bazan iya zaman auren nan dakaiba, auren yafitan min arai, bazan iya zama da mutumin daya rabani da yan uwana ba yahanani ganinsu yahansu ganina, bazan iya zama da mutumin daya kullemin y'a ba bansan duniyan datake ba tsawon kwana goma sha shidda yau, Alhaji bazan iya zama dakaiba ka saken ka sallameni nabar maka gida inje innemi hanyar dazan kwato y'ata daga hannun hukuma, Aneesah na" tafashe dawani kuka da shikanshi Dady saida yaji kukan nata wani bangaren zuciyan shi nacemai bai kyauta ba wani bangaren zuciyan nagayamai yay daidai hukuncin abinda tana danshi ne ga Aliyu nan yanzu shirin fitar dashi kadan waje ake dan baya responding to treatment at all.
Cikin wani irin harzukewa Dady kaman zai mareta yace "okay ni da kuka cuta ban taba tunanin zan sakeki ba saike, bari kiji nafada miki Rukayya koda an rataye Aneesa ne bazan taba sakin ki ba, koda kece kikai laifin zan hukunta ki kema daidai shari'a bazan taba sakin kiba ban rabuwa da abinda nakeso, kome zakiyi kiyi ga fili gamai doki aurena dake mutu karaba wlh, mtswww" yaja tsaki cike da baccin rai yace "barima ma nanuna miki zaman aure ma yanzu muka fara" yay maganan tareda cire riga yana yarwa ahankali ya kwantar da Ammi dake kuka sosai ga jikinta zafi dudda haka bai hanashi sauke abinda ke damunshi ba dama a mugun bukace yake sai kewanta yake, itakadai yakeji acikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login