Showing 30001 words to 33000 words out of 204120 words

Chapter 11 - Gurbin Ido Book One Complete Hausa Novel

gyada tana sakin siririn murmushi,sannan ta fara takawa zuwa rumfar yuuman,gabanta yana dukan uku uku,batason ta hadu daada mahaifiyar ibrahim,bare shi ibrahim din kansa,ita daya tasan irin jan kunne da kums gargadi da tasha daga wajen inna furera,ba shakka banda akwai qudurin da innar keson cimmawa ma,babu abinda zai sanyata ta kawo musu sarqar.

"Wa'alaikumussalam,shigo mana" anni ta fada tana zubawa maimunatun idanu sanda take sanyo kai cikin dakin,idanunta ya sauka ga gefe wuya da kuma kunne zuwa kuncin maimunatu karo na barkatai a yau din,ita din bata jiya bace ba kuma ta yau bace,wannan tabon tun dazu data kalleshi ta tabbatar da cewa na duka ne,to amma me yarinya kamar maimunatu tayi da za'ayi mata irin wannan dukan?,me aka saka akayi mata wannan dukan dashi?,sai taji ranta yana baci abinda.bai faru ba a yanzu.

Ita din wata irin macace da bata qaunar zalunci ko kadan,ko kai waye,ko yaya kake da ita,matuqar ta fuskanci kana da dabi'a ta zalunci yanzu zaku raba hanya.

Gaban annin ga durqusa,tasa hannu biyu tana miqa mata sarqar,anni ta miqa hannu ta karba

"Hukumullahi...ni nayar da ita,tabbas,to kinga basan ma ta fadin ba banda Allah ya tsananta rabo yanzun kin ganta kin kawomin,da haka zan yita bulayin nemanta" anni ta fada tana sakarwa maimunatu murmushi,zuciyarta da ruhinta cike da soyayya da kuma kaunar maimunatun,halayenta mabanbanta ne da halayen sauran al'umma,abar yabo ce ta gaske kuma a zahiri,godiya ta yiwa maimunatun sosai,tans juya abun a ranta ta tayar da sallah.

"Anni.....gaba daya yau tunani ya sanyamin ke agaba,komai yayi zafi maganinsa Allah anni,aci gaba dai da addu'a,wataran komai zai warware in sha Allahu" yuuma dake ajewa anni kwanon tuwo ta fada,don idan annin tazo har ta koma babu ruwanta,irin tasu cimar takeci,takan ce ko a gida rashin samun me tsaya mata da irin cimar ne yadda takeso,amma ita bata da kamar irin abincinsu.

Ajiyar zuciya annin ta sake tana miqe daya qafar tata data jima a lanqwashe ta fara yi mata tsami

"Ramatu,inajin wani abu a jikina tattare da yarinyar nan"

"Wa fa?" Yuuma ta tambayi anni tana tattara hankalinta gareta

"Maimunatu"

"Ohhh.....maimunatu?"

"Ita.....tun dazu da mukayi magana dake ramatu nake juya zancan cikin raina,da magaribar nan bayan yarinyar tazo ta kawomin sarqa ta,sai gaba daya tunani ya damfaru a kanta,na lura da irin dabi'un da nake buqata tattare da yarinyar,ta hada juriya haquri da kuma amanar da zata iya zama da ja'afar,dabi'u da kuma halayen da tabbas zata iya dawo da ja'afar yadda yake ja'afar dinsa"

"What!" Laila dane kwance ta fada cikin rata,har maganar tata taso ta fito fili

"Me anni ke fada ne?,ta manta waye ya ja'afar?,ta manta waye yaa J?,the classic and unique guy?,ya ja'afar fa ake magana da wata bafulatanar ruga?,saura kadan ta miqe ta zauna,amma sai taci gaba da kwanciya,tanason jin yadda maganar zata kaya.

Dukka idanunta yuuma ta fidda tana duban anni

"Anya kuwa anni?,bakiyi ragon tunani ba?ja'afar fa?"

"Me yasa kika ce haka ramatu?,ko hasashe na bai hasaso dai dai kan dukka nagartarta ba?" Kai yuuma ta girgiza a hankali tana juya abun a ranta,bai kamata tayi shuru ba wani abu ya kasance daga baya kuma ta zama abar zargi ba daga kowanne bangare,abu me muhimmanci ta fara gayawa anni wace ainihin maimunatu tukunna

"Dukkan abinda kika hasaso akan halayen maimunatu haka suke,yarinyar har tafi haka ma,dukka rugar nan sunsan da wannan,saidai wani baqar al'ada da jahlici gami son rai sun rufe musu idanu basa ganin wannan,bari na gaya miki wace maimunatu tun daga tushe,wanda ba kowane cikin rugar nan ya sani ba,domin kuwa,ni din,nice qawa qwaya daya tilo da mahaifiyarta keda ita a rugar nan,wadda bata da kamata,wani rikici da ya faru tsakanin gidan da gidan nan yasa bappa ya yanke huldata dasu saboda wanzar da zaman lafiya,abinda ya rabamu kenan da shatu,har zuwa sanda ta koma ga mahaliccinta" kai anni ta gyada tana bada hankalinta zuwa ga yuuma,yayin da itama yuuma ta nutsu sosai ta fara yima anni magana

"Furera mahaifiyar gaje,waddda kukayi ciniki a hannunta,mata ce ga jauro,wadda keda yara biyu dashi,macace mara mutunci ta gasken gaske,wadda ba kasafai ake tabota ta qyale ba,me son abun duniya ce da kuma masifar son 'ya'ya,asalinta bafulatanae gembu ce,jauro ne dan wannan rugar,muna zaune tare da ita tsahon shekaru,kwatsam tayi baquwa,wadda ta shigo rugar nan tare da furera da taje ganin gida,matar itace shatu,wadda tazo da diyarta maimunatu......sun shigo tare da tarin dabbobi wadda dukka dabbobin nan mallakin shatu da diyarta maimunatu ne,amma kuma a idanun kowa dabbobi na furera ne,don a haka ta gayawa kowa wannan labarin,ta shaidawa mutane cewa gadonsu dama taje gida karbowa ta taho dasu,ta kuma hado da wadda zafa dinga mata kiwo tana biyanta wato shatu,abinda zai baki mamaki,shatu ba kowace bace a wajen furera face 'yar uwarta da suke uba daya,bata da ikon musawa ko qi,saboda a sannan shatun na cikin wani yanayi na tashin hankalin rayuwa,tana neman mafaka,mahaifin maimunatu baqo ne,irin baqin dake shigowa garin na gembu saboda huldar kasuwanci da kuma yawon buda idanu,a nan yaga shatu ya kuma tsaya kai da fata sai daya aureta,a nan garin ya barta saboda ta nuna tafison zama cikin danginta,yana zuwa yana ganinta yayi mata kwanaki ya koma,mutum ne mai arziqi,don haka gida na alfarma ya ginawa shatu,ya zuba mata dukka kayan alatu da more rayuwa,ta yadda gidan shatu shi ya zama abu kwatance da kuma burin kowa cikin garin nasu,wannan ya haifar da hassada daga zuciyar 'yan uwanta da suke 'yan uba,saboda ita shatu su biyu mahaifiyarsu ta haifa a gidan,ita da 'yar uwarta sa'ade,kusan jinin dakinsu ne haka,sannan kuma da baiwar zallar kyau da Allah yayi musu fiye da sauran 'yan uwansu,itama sa'ade nata mijin me hali ne sosai,hakan ya sake haifar da zallar 'yan ubanci a tsakaninsu,saidai sunata dannewa saboda suna rabarta suna kuma samun akhairai da abun duniya daga wajenta,kasancewarta ba mai rowa ba,a haka ta haifa maimunatu,dukka alhaji na zuwa wajenta ne yayi mata satittika ya tafi,bayan ta.haifi maimunatu yake maganar zai kaita taga danginsa,saidai kuma wata tafiyace ta taso masa,wanda ya dauki tsahon watanni kafin ya dawo,koda ya dawo din kuma shima yana da niyyar kaita,har sun shirya sun saka rana,yace zai taho takanas daga kano ya dauketa. Shiri sosai shatu tayi domin zuwa ganin surukanta,ta shirya maimunatu da kyau wadda ke samun gata kamar babu gobe,itama haka,saidai haka ta yita jiran alhaji amma shuru babu shi babu dalilinsa,nata da wayar hannu bare ta nemeshi,haka tayita zaman jiransa har dare yayi ta fidda tsammani,ta sanyawa ranta qila wani abune ya tareshi,ta barwa gobe. To washegarin ma dai haka ta yita jiransa shuru babu shi babu labarinsa,haka wata washegarin,wasa wasa sai ga kwanaki nata tafiya shatu bata sake ganin gilmawar alhaji ba,abun ya daga hankalinta qwarai da gaske,tafi tafi watanni suka fara shudawa shuru babu shi babu dalilinsa,ga ciki da ya bayyana a jikinta,ita dai ta yarda da alhaj dari bisa dari,saboda iya tsahon zamata dashi tsakaninsu ita dashi babu komai sai son barka,mutum ne mai son addini da kuma kiyaye dokokin Allah,kusan a wajensa shatu tayi karatun addini mai dan dama wanda ta dinga koyawa maimunatu,duk da a sannan ta sanyata makarantar islamiyya da boko,amma kamar tasan yadda rayuwa zata juya musu,sai take zama duk bayan sallar magariba take mata nata karatun,ganin cewa yarinyar tana da budaddiyar kwanya dake saurin kwashe karatu,don tun bata isa sakawa a makaranta ba ta sanyata,tace tayi wayon acan,hakan yasa adan lokacin ta samu karatu me yawa,tana cika shekara tara zata shiga ta goma ta gama primary,mahaifinta nada niyyar yi mata shirin shiga makarantar gaba wannan abun ya faru"

*Follow my arewabooks account for more new pages*

HUGUMA
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: *13*


Tunda gari ya waye take zaune tangaram tana duban qofa zuwa window,tana lissafa wucewar mintuna da awanni da yatsun hannunta,wucewar kowacce daqiqa bugun zuciyarta ne ke daduwa,ta kalli qullin kayanta da ba komai bane a ciki illa fararen kayan saqinta,wadanda su daya ne abinda ta mallaka take kuma ji dasu,Sallamar da taji da baqin murya ya tabbatar mata ranar barinta rugar yayi,karon farko da zata fita daga rugar tun sanda suka shigo ita da mahaifiyarta.

Laulo ne ya leqo yayi kiranta,sai ta miqe riqe da qullinta tabiyo bayansa,saboda tasan cewa abinne yazo wai inji mai tsoron wanka.

Laila da yuuma ne tsaye a tsakar gidan,lailan cikin ado take dake nuni da zallar ilimi dukiya da kuma wayewa,ta qaraso a hankali ta gaida yuuma dama lailan,dukka suka amsa mata da sakakkiyar murya.

Sosai inna furera ta kama kunnuwanta,har data dafe gefen fuskarta saboda tsananin zafi

"Banda dauke dauke,banda mugun hali,iya abinda aka kaiki shi zakiyi,kada ki yarda a kawomin qararki,idan haka ta kasance kuwa kashinki ya bushe" kai take gyadawa da sauri don ta samu ta saketa,duka yuuma da laila sai da zuciyarsu ta motsu,saidai kowannensu da sauqi,saboda sunsan taqi kadan ya rage ta rabu da wannan rayuwar .

Sanda suka qaraso gaban motar tsaye tayi kawai tana qarewa motar kallo,tana qissima yadda zata tsinci kanta a ciki,wai yau itace zata shiga wannan abar?.

"Ki shiga maimunatu,anni na jiranmu" laila ta daga kai daga danna wayar da take ta yiwa maimunatu magana,ajiyar zuciya ta sauke sanda ta shiga motar,saidai gaba daya a takure take saboda rashin sabo,sai da suka koma ta gidan yuuma suka dauko anni sannan suka juya suka nufi hanyar barin rugar gaba daya.

Duk inda suka gifta sai maimunatu tabi wajen da idanu,tana jin wata kewa tana ratsata tun yanzu,tana jin wani yanayi mara dadi cikin zuciyarta,tana qissima yaushe zata dawo?,yau ko gobe?,ko kuma ta tafi kenan tafiya ta har abada?.

"Ki saki jikinki maimunatu,ki sanya a ranki zaki je kiyi rayuwa ne irin ta kowanne yaro dake gaban mahaifiyarsa" anni ta fada bayan ta karanci damuwa da tunani daya cika kwanya da zuciyar maimunatu,qas tayi da kanta tana jinjinashi,sannan tasa hannu a fakaice ta goge qwallar dake shirin sauko mata,babu abinda yake dawo mata sai wani lokaci can baya da suka baro garinsu na gembu ita da daadarta shatu zuwa wannan rugar,a zahiri rayuwar sam mara dadi ce,to a yanzun gata ra cira daga nan din zuwa wani wajen,an mata bushara da kyautatuwar rayuwarta,to amma kuma sanin haqiqanin yadda zata kaya din sai ubangiji,sanin gaibu sai Allah,ko wacce irin qaddara ce cikin wannan tafiyar kuma?.

_ku biyo alqalamin 'yar mutan huguma_


Sosai maimunatu ta bude idanunta tana kallon hanya,a wancan lokacin da suka shigo garin akwai qarancin shekaru,shekarunta basu kai haka ba,don haka ta dinga kallon hanya abinta,tun daga cikin rugarsu har suka fito suka dauki hanya dodar.

Bayan 'yan hirarraki motar ta dauki shiru,bacci yayi gaba da anni,haka ma yahaya,sai ita sai driver,sai laila data nutsu ta tattara hankalinta kan waya,ta karanci yadda laila ke son waya,daga dan qaramin sanin data yi mata,ta saci kallonta kadan sai kuma ta sake maida hankalinta ga titi,tana kallon yadda ubangiji ya shimfida qasarsa.

Wani sashe na ranta kuma cike yake da mamaki,gashi dai tafiya suke,amma kamar a tsaye suke a waje daya,banda tana ganin yadda suke wuce dazuka da bishiyu tabbas da zata ce ba tafiya suke ba.

Awa biyu cur sukayi suna tafiya kafin anni ta farka,ta sanya drivern ya shiga dasu cikin wani gari,sukayi sallah,kafin su idar kuma saiga yahaya nan ya shigo musu da takeaway,wanda suka wuce dashi mota,suka dora tafiyarsu.

Tunda ta karba ledar abincin take hannunta a riqe ba tare da ta ci ba,abinci ne data jima rabonta da irinsa,tama manta lokacin,tun a zamanin da suke muhallinsu ita da mahaifiyarta,cikin ranta take tantamar anya abincinta ne?,bata sake budawa ba saida laila wadda ta gama cin nata ta kalleta

"Ki buda mana maimunatu kici?,ko bakison irinsa?" Dan qaramin murmushi ta saki ta girgiza kai,sai ta buda ledar a hankali,laila ta bita da kallo,wani irin kyau fuskarta ke fitarwa fiye da wanda take dashi duk sa'ad da tayi murmushi,janye idanunta tayi,tana gyara zamanta yadda zataji dadin ci gaba da danne dannenta,zuwa lokacin maimunatu ta fara kaiwa cikinta abincin.

Yawan wanda yaci sai yasa ta dinga jin kunyar suga ledar,ita kanta tayi mamaki qwarai,amma kuma daga bisani da taga laila sabgarta take a tab dinta,anni kuma ta koma baccinta sai ta sake itama.

Duk yadda taci burin ganin hanya tun daga adamawa zuwa gombe amma sai da bacci yayi mata tsiya,tana gama cin abincin jikinta ya mutu murus,tsohuwar yunwar data jima a jikinta ta kwanta,tsohuwar gajiya kuma ta shekara da shekaru,basussuka baccin da batasan adadin yawansu ba suka taso mata haiqan,bata shirya ba baccin yayi awon gaba da ita.

*GOMBE STATE*

*_G R A GOMBE_*
_DR SULAIMAN KUMO ROAD_


_Dr marwan khalid akko residence_


Katafaren gida ne wanda ya amsa sunansa ta kowacce fuska,irin ginin da aka yishi ba don alfahari fariya ko taqama gami da almubazzaranci ba,gini ne na ma'ana da sanin rayuwa da kuma abinda duniya ke ciki,duba daya zaka yiwa gidan kasan cewa daga zubi da tsarinsa ginin ya zaunu matuqar zaunuwa,hakanan yakan dauki hankalin mafiya yawan jama'a,tun baka ma shiga cikinsa ba.

Gidane dake dauke da sassa guda hudu,biyu na matan gidan,daya kuma mallakin me gidan,yayin da daya bangaren ya zama mallaki ga mahaifiyar me gidan wato haj maryam Farooq kumo.

Gaba daya gidan mallakin dr marwan khalid akko ne,babban limamin gombe gaba daya,shararre kuma sanannen dan kasuwa,wanda Allah ya yiwa baiwar arziqi dama dukiya gaba daya,gami da tarin ilimin addinin islama wanda shi ya kaishi ga zama cikakken dr,hakanan ta fannin boko din ma ba'a barshi a baya ba.

Wani irin mutum ne da Allah ya yiwa baiwar kwarjini da kuma farinjini,mutum ne me amfani da ilimin addininsa ainun,mai yawan taimako sadaka da kuma kyauta ma gaba daya,dukka sirrin nasararsa ya ta'allaqa ne ga mahaifiyarsa,jajirtacciyar uwa da bata daukan raini ko kuma wargi komai qanqani,tsayayya akan 'ya'ya da kuma jikokinta.

Marwan shine babban d'a a wajen haj maryam anni,hakan ya sanya yayi mata matsuguni cikin gidansa tun bayan rasuwar mahaifinsu,kuma dama shi din mutum ne mai matuqar qaunar mahaifiyarsa

da kuma qawa zuci,hakan ya sanya itama haj maryam anni ko cikin yaranta tafi ji dashi,duk da cewa dan fari ne ba auta ba,autansu alhj sagir yaso daukarta ganin kamar shi yafi dacewa,amma gaba daya ya hanasu hakan,yace shi yafi cancanta tunda shine babba.

Matan Dr marwan akko biyu,akwai haj Aishatu,wadda take da yara bakwai dashi,diyarta ta farko macace mai sunan anni wato maryam suna ce mata maama,sai ja'afar d'a na biyu a wajenta,wanda ya zamto halitta mafi soyuwa a wajensu,duka sauran mata ne,salma,hafsa,nadiya,safina,sai autansu namiji khadim,daya dakin kuwa dakin amarya umamatu tana da yara hudu ne,suma din mata ne,fa'iza ce babba,sai khadija,zahra'u,sai mai sunan yuuma rahama suna ce mata baby.

Tsakanin aishatu da suke kira da amma da kuma umamatu da suke kira da ammy zama ne na fahimtar juna da kuma zaman lafiya dai dai gwargwado,yadda Allah ya dorawa kowa son ja'afar haka ammy ke qaunarsa,shi din dan gidanta ne tun farkon zuwanta gidan,amma kuma ta tattara ta miqa mata shi,shima kuma ya dauketa kamar uwa a gareta.

*_Ja'afar marwan khalid akko_*


matashin saurayi kuma matuqin jirgin sama,mai jini a jika,wanda Allah ya yiwa baiwar qira ta jiki,bashi sahun dogaye ko kuma gajerun maza, moderate ne,yana da murjajjen jiki mai siffar qarfi dake nuna shi din ma'abocin gym ne,kalar fatarsa ruwan tarwada ce,wadda ta samu kulawa ta gasken gaske take bada wani irin launi mai daukan hankali matuqa,baya tara suma kamar yadda shi din ba ma'abocin yin aski bane,saidai yadda yake barin sumar kansa zuwa habarsa da kuncinsa abun yana da matuqar qayatarwa da kuma daukar hankali,Allah ya zuba masa wani irin mugun kwarjini wanda yake qara masa kyau haiba da kuma cikar kamala,yana da wani irin farinjini na musamman,bawai a wajen mata kawai ba,a'ah.....hatta a wajen al'ummar gari gaba daya.

Dan gayu ne na gasken gaske,gayu wanda ake kira gayu bawai muna gayu ba,mai tsananin tsafta ne daya tsani qazanta dama qazami,yana da tsari da kuma dokoki da ya sanya ba kowa ke iya mu'amala dashi ba,kamar yadda shima bada kowa yake iya mu'amala ba.

Miskili ne ajin farko,irin miskilancin da zakayi tunani bebe ne ko kuma kurma,magana ko hira bata daga cikin abubuwan dake burgeshi,abu ne mai wuya ka zauna dashi kaji wata doguwar magana a bakinsa,sau tari yafi ganewa amfani da body language,kamar wani me ciwon baki ko kuma mara lafiya,yana da tsananin kamewa da kuma tsare gida,akwai jinin sarauta sosai cikin jikinsa,hakan ya sanya yake da izza da kuma rashin daukan raini,bai yarda da qasqanci ba,yana da neman na kansa sosai,mahaifiyarsa diya ce ga turakin akko,yana da matuqar girmama na gaba dashi,komai qanqantar shekarun daka bashi,duk da mutane da yawa sun masa shaidar wulaqanci da kuma girman kai.

Mutum ne mai tsanani ta fannin so ko qi,bai iya so ba,hakanan bai iya qiyayya ba,idan jininku bai hadu ba ka fita a hanyarsa kawai shi yafi maka alkhairi,yana tsananin son mahaifiyarsa fiye da kowacce halitta a duniya,mahaifinsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login