Showing 168001 words to 171000 words out of 204120 words

Chapter 57 - Gurbin Ido Book One Complete Hausa Novel

Maida kansa yayi ya jinginar,ya rufe fuskarsa da tafin hannunsa yana dan lilo kan kujerar da yake zaune,gaba daya ita ke masa yawo tsakanin idanuwa zuciya zuwa qirjinsa,sau biyu yana attempting kwanciya,amma idan yaje sai yaji ya gaza zaman bedroom din,memory din data bashi yammacin jiya zuwa dare ke dawo masa,sai ya miqe tsaye yana kwasar wayoyinsa gami da kashe fitilar gaba daya ya sake nufar bedroom din.

Sai daya shiga toilet ya daura alwala yayi bursh sannan ya dawo ya kashe qwayayen dakin ya nufa gadon,addu'ar bacci yayi yaja duvet yana rintse idanunsa gami da addu'ar Allah ya kawo masa bacci da wurwuri,saidai inaa,addu'arsa bata ciba,don gaba daya qamshin ta daya maqalewa pillow din data kwanta jiya akai shi kuma yau ya daukeshi yayi amfani dashi shi ya maqale masa a hanci,ya shiga tuna masa da ita gamida tada masa hankali.

Dogon tsaki yaja kamar zai cire harshensa,dukka anni ce taja masa,ta yaya za'ayi mutum da matarsa amaisheshi gauro?,don ya kaita boarding school a baya....ai ya aikata hakanne a sanda baisan daraja da kimarta ba,a yanzun kuwa duk duniya yafi kowa sanin martabarta,da wannan tunanin da kuma kewar ya dinga fama har ya samu baccin ya daukeshi.

????????sati guda kacal amma gaba dayansu kowa ya jikkata a jiki da zuciyarsa,tuni ya sallama cewa soyayyarta ce tayi masa mummunan kamu,irin kamun da yakejin labarinsa a labarai yake kuma qaryatawa,ashe da gaske haka ne?,komai yakeyi tana cikin tunani da zuciyarsa,sai ya fara samun cikas a ayyukansa na office,wasu abubuwan sai yayita mistake,sai jabir ya ankarar dashi,mamaki yanata shigan jabir,lallai gigitaccciyar soyayya ce ta kama ja'afar din

"Kaga masu abu da abunsu,malaman soyayya" ya fada a ransa yana sakin qaramin murmushi.

Yayin da bangaren maimunatu kuma taketa dojewa kan gajiyar tafiya ce ke luguiguitata sanda afra suke mata tsiyan ta faye zama cikin tunani,sannan bata baccin kirki cikin dare,ko tana kewan captain ne?.

Tun tana qaryatasu tare da basu uzurorinta har ta soma sallamawa itama,a hankali ta sake zama so silent,duk da bata yiwa su afrah miskilanci amma a yanzu kamar ta sauya musu su dinma,tafi kebewa ita kadai ta zauna shuru,wanda ba komai take ba illa tunani.

?????????Karfe tara na safiya ne,yana kwance bayan motarsa qiran ferrari,daga gidansa na government house road zuwa gidansa dake zuwa gidansa dake daya baro tun randa ya dauko maimunatun,bai sake komawa ba,koda ta koma makaranta ma a nan gidan yaci gaba da zama,a yanzun ya samu qwarin gwiwar zama a ciki tunda aka kwashe kayan shaheeda daga ciki,akwai takardun da yakeson debowa daga can gidan kafin ya wuce office.

Gaisawa sukayi da masu gadin gidan nasa,sannan ya wuce ciki da dan gaggawarsa yana gayawa driver din nasa kada ya kashe motar yana fitowa.

Bai jima ba ya dauko abinda zai dauko din ya fito,yana saukowa daga stairs din yana sake duba file din don tabbatar da cewa ya dauko komai a ciki da yake buqata.

"Ka kulamin da jaka karka karcemin ita fa" muryar da yaji kenan data samyashi dago kansa,ido hudu sukayi da unaisa,wadda ke takowa cikin gidan,sanye da wata irin mini gown da straight leg trouser,kusan rabin fuskarta mamaye da sun glasses,tana tauna chewing gum.

Cikin tsawa ya bawa mai gadin umarni

"Ina zaka da wannan jakar?"

"Ah....hajiya ce tace a kawo mata ciki"

"Kana qara taku daya da ita a bakin aikinka,koma da ita inda ka daukota" cikin rawar jiki da kuma matuqar tsoron rasa aikinsa ya janye akwatin zuwa baya,bai kuma sake bi takan maganar unaisa dake cewa karya fitar mata da kaya ya qaraso mata da ita ciki.

Wani kallo me cike da qasqanci da kuma qyama ya jefeta dashi,zallar kwarjinin da yake dashi ya daketa,gaba daya sai tayi collapse,har ya qaraso bakin sassan nata da ta zura key da nufin budewa,ya sanya hannunsa ya zare key din ya jefa a aljihunsa ya kewayeta ya fice abinsa ba tare daya ce mata uffan ba.

Sai daya kira dukka ma'aikatan gidan yaja kunnen kowannensu kan kada wani a cikinsu ya kuskura ta sashi abu yayi mata,koda ja mata luggage dinta ne,yaja musu kunne da kakkausar murya kam duk wanda yayi hakan a bakin aikinsa,cikin bin umarni kowa ya amsa mishi,tare da tabbatarwa kansu ba zasuyi wannan gangancin ba,a yanzun samun gidan aiki me cike da kyautatawa da bayan salary dinsu harda allowance ake basu abu ne mai matuqar wahala,bai tsaya sauraren rantse rantse da ban haqurinsu ba ya shige mota ya bawa drivern umarni su fice a gidan.

Ranshi ya baci sosai,amma tun kafin yakai office ya tattara damuwarta ya watsar,abu daya ne ya sani cewa ko sama da qasa zata hadu bazai taba iya zama da ita ba,bazai furta mata komai ba,amma dole takai kanta gida ta kuma gaya musu daga inda take,ta bakinta komai zai fita yana nan yana zuba idanu.

A bakin office dinsa ya tarar da jabir yana jiransa,gaba yayi yana qoqarin shiga tare da fadin

"I come late,am sorry" ya dauki uzuri,sabida ba dabi'arsa bace saba alqawari da lokacin zuwa aiki,binsa da kallo jabir yayi yana qoqarin karantar yanayinsa,gaba daya ja'afar din ya wani sukurkuce a 'yan kwanakin,duk da yadda yake nuna qarfin hali,anya zai jure?,bazai tayashi baiwa anni haquri ba ta sauka daga kujerar naqin data hau ba?.

Koda ya sameshi a office din bashi lokaci yayi,sai da yaga ya dan nutsu sannan suka gaisa,ya miqa masa takardun ya koma ya jingina da makarin kujerar da yake kai yana kallon ja'afar din duba na kai tsaye.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 72

Tambayar da annin tayi mata gaba daya sai taji ta daburce,daga ita har ja'afar din sun zuba mata idanu,kowa yanason ta dauki zabinsa,bai taba tsintar kansa cikin fargabar jiran fitar amsa daga wani waje ba irin yau,koda aiki da kasuwancinsa da yake daukansa da muhimmanci bai fiya damuwa da rashin samuwar wani abu ba,idan yayi duk abinda ya dace yana ci gaba da harkokinsa ne ya barwa Allah zabinsa.

Ita kuwa anni fatanta daya maimunatun kar ta amince da tsarinsa,wannan din wata hanya ce da zata sake samar mata da kima da daraja a idanunsa,ya dandana yaji idan tana da muhimmanci cikin rayuwarsa,musamman yanzun da ya fara sanin ainihin ita din wacece.

Maimunatu kuwa zahirin gaskiya tana son makarantarta,saboda ta saba da ita,gasu afra da takejin kamar ba zata rabuwa dasu ba,kada ma afra taji labari,ko don ita kadai batajin zataso canjin makaranta

"Nafison wadda nakeyin yanzu" kamar an sauke masa guduma a kansa haka yaji

"Subhanallah" ya fada can qasan ransa,yana dauke idanuwansa daga kanta

"To kaji,saboda haka kada ka wuce gobe baka maidata ba,tun gabanin na hadaka da marwanu ya cimin qaniyarka,don ni din yanzu na fuskanci wani sabon raini kayimin" cak ya miqe daga zaman yana cusa hannunsa a aljihun wandonsa,wani bacin rai yaji yana ratsashi,bai taba tunanin zata iya zabar maganar anni akan tasa ba,baice komai ba ya fara takawa zai fice a falon

"Yauwa dakata.....iyayen marigayiya sunyi magana jiya akan debe kayan yarinyarsu za'ayi sadakarsu,na riga nace musu su sauraremu zuwa yau......ya kamata a fiddasu haka ayi mata sadaka Allah yakai mata ladan k...." Tun bata qarasa ba ya tari numfashinta

"Nan da one hour su sameni cikin gidan su dauki dukka abinda zasu dauka" ya taka yana barin falon,umma tabawa da anty maama suna binsa da kallon tausayi,sunsan anni,da biyu tayi hakan.

Umma tabawa ce ta sauke ajiyar zuciya

"Banda abin maimunatu,ke da zaki goyawa mijinki baya,saiki biyewa anni ku kware masa baya?"

"Har yaban tausayi,don Allah a sassautawa dan qanina" anty maama ta fada tana murmushi,su duka suna kallon maimunatu,kunya da nauyinsu ya sake cikata,maganar anni ta tsaida su

"Kunga,ke maryamu bakisan dawar garin ba,keko tabawa da kika sani bai kamata kice komai ba,ku bamu guri ni da ita" ta buqata daga garesu,sai suka miqe anty maama tana cewa suje kitchen baaba tabawan ta sake nuna mata kwabin alkubus irin na rannan,duk sadda tayi nata da qyar takesha,sai ya kusa cabe mata yayi nauyi.

"Maimunatu"anni ta kira sunanta a tausashe

"Na'am" ta amsa mata kanta har yanzu a qasa

"Allah yayi miki albarka,ya jiqan mahaifiyarki,ya bayyana mahaifinki,babu abinda zamu ce dake sai Allah ya kyauta qarshenki,bamu zaci dawowar ja'afar da sauri haka ba,sai gashi cikin tafiyar nan taku jabiru yana shaidan canjin da ya gani na tunkarar rayuwar ja'afar din ta sanadinki,ni kaina shaida ce,yana shigowa naga haka akan fuskarsa,banda wannan maganar dana masa wadda baiso nasan a yau din zamu jima dashi,xan kuma ga ainihin ja'afarunmu,amma babu komai,mun saba irin haka dashi,kema kada ki damu don ki goyi bayan hukuncina,dama haka naso,saboda ta hakane zaki gane girma da martabarki a ransa,karki damu da dukka fushinsa,ki bishi a hankali,zai sauko da kansa,bashi da riqo sosai musamman akan abinda yake so" kalmar abinda yake so din ta sanya maimunatu daga kai tana kallon anni,sai ta sake mata murmushin su na manya

"Eh,a yadda naga yanayin ja'afar,na tabbatar indai ba mutuwa ba babu abinda ya isa a yanzu ya rabashi dake,naji dadi hakan da ya zaman kece kika samu wannan gurbin,dama abinda naketa taraddadi,kada waccan ta qwace matsayin da naketa miki fatan samunsa,abu daya kawai nake gudu, wahalar da abokiyar zamanki zataci,ja'afaru ba irin mazan dake iya zama da mace biyu bane,saboda idan suka fara son abu suna fara sonshi da gaske ne,suna kuma miqa masa dukkan yarda soyayyarsu da kuma amannarsu,shi yasa tun farko naso marwanu ya qyale batunta,amma bazaiyiwu na tursasashi ba,dukkansu suna min biyayya akan dukka maganata,to ya kamata a qalla suma na dinga basu dama cikin rayuwarsa,ba fata nake ba,ba kuma baki nake ba,amma tabbas dole akwai abinda zai biyo baya,kedai kawai abinda zance dake,ki koma makaranta abinki,karki waiwayeshi ko sau daya" kai ta gyada tana jin gamsuwa da maganar anni,hawayen farinciki yana sauko mata,ta rasa da wanne irin harshe zata yiwa anni godiya,batasan girman soyayyarta gareta ba.

Ko awa daya cikakkiya ba'a rufa ba ya aiko khadim ta fito zasu tafi,sai ta narke fuska,bata zaci zaice yanzu yanzu ba daga zuwansu,wuni ta dauka zatayi a nan din,gashi ta fara jin dadin hira dasu laila.

Murmushi anni tayi,a qufule yake kenan da alama,abun yana mata dadi ita kuma sosai cikin ranta,hakan na sake nuna darajar maimunatu a wajensa,sai ta dubi maimunatu

"Tashi ki bishi ku tafi,zaki zo wataran ki wuni,karki damu" haka ta tashi jiki a sabule tana goge qananun qwalla,su fa'iza zasuyi mata rakiya anni ta hana kowa zuwa wajen,tace su barta ta fita ita daya.

Tunda ta shiga motar baice komai da ita ba,saidai tana jin yadda yake sauke numfashi da kuma ajiyar zuciya lokaci bayan lokaci hadi da fidda wata iska daga bakinsa,da alama ransa a bacen yake,duk sai taji babu dadi cikin ranta,amma kuma sai ta kama kanta,tunda dai me zata ce masa?,tun farko shi ya zaba matan kamar yadda anni tace,yanzun kuma ita kanta bataga kamatar biye ma tsarinsa haka kai tsaye ba ba tare da an dan latsashi ba,amma can qasan ranta sai takeji babu dadi sam,abinda ya dauke walwalarta itama gaba daya,amma sai ta maida dubanta ga titi tana kallon yadda suke wuce hanya.

Duk da ba sanin garin tayi sosai ba,amma ta fahimci kamar ba hanyar gida suka nufa ba,saidai bata tanka ba,tana dai kallon hanyar ne kawai.

Sau kusan uku yana satar kallonta,ya zaci zata nuna damuwa ko wani abu da yayi kama da haka,amma sai yaga kamar ma batasan me ya faru ba,abinda ya sake qular dashi,ya dinga hadiyar zuciya shi daya yana lumshe idanunsa hadi da budesu,matsa mai kyau yakeson mata amma kuma driver ke jan motar ba shi ba,wannan yasa ya qagu su isa gidan.

Da yake ba wata tazara tsakanin gidan nasu da government house road,nan da nan suka isa ainihin gidan nasa dake can,wanda a nan ya fara rayuwarsa da shaheeda.

Tun daga tsarin ginin katangar zaka san cewa ba qaramin gida bane,ba kuma ginin wasa aka yi masa ba,shi kansa yana kimanta gidan saboda ya qunshi abubuwan tarihi masu yawan gaske da suka shafi rayuwarsa a ciki,uwa uba da kudin aikin da yake mutuwar so a rayuwarsa ya ginashi,wato sanda yake a matsayin cikakken captain ja'afar marwan akko dinsa.

Tun a gate security suka fara miqa gaisuwa,yana amsa musu da hannu,saboda ba'a cikin yanayinsa yake ba,motar tasu ta sulala zuwa cikin katafariyar harabar gidan,sannan suka tsaya a parking lot.

Yana gaba tana biye dashi,idanuwanta suna kallon tsarin gidan,ginin turai zam,komai kuma yana nan a tsaftace a muhallinsa tamkar dan adam yana rayuwa a ciki.

Bata fahimci inda sukazo ba har sai da suka qaraso ainihin falon gidan,idanuwanta suka ci karo da hotunan shaheeda dana amna da amra,tamkar tana raye,sai taji zuciyarta na karyewa a hankali,tausayin amna yana tsirga mata,jikinta yayi sanyi sosai,dan adam ba'a bakin komai yake ba,kamar zaka kirata ta amsa,kamar zata tashi taci gaba da rayuwa a gidanta.

Wani sashe na daban suka bulla,kallo daya tayi ma sashen tasan bangaren mai gida ne,falo biyu suka ratsa sannan suka isa ga makeken bedroom dinsa.

Aljannar duniya shi yafi dacewa a kirasa,komai yana nan a muhallinsa fes dashi,hatta da ac din dakin a kunne take tana aikinta,ana kula da gidan sosai,don akwai amintattunsa da yake sanyawa duk bayan kwana biyu su shiga su gyara har bedroom din

"Ki zauna ina zuwa" ya fada yana wani shan qamshi,sannan ya fice yana jan qofar dakin.

Sai data gama qarewa dakin kallo tsaf sannan ta taka zuwa saman sofa bed din ta zauna,idanuwanta suna qarewa dakin kallo,very neat and clean,idanunta suka sauka kan tarin takardun sake saman gadon gefe guda,tayi mamaki don dakin fes yake,su kadai ne a wajen,batasan ya akayi ba ta miqa hannu ta debosu ta fara dubawa.

Hotunan shaheeda 'yan biyunta da kuma ja'afar dinne,sunyi masifar kyau,ahali me kyau da daukan hankali,tana kalla tana sake jin wani abu yana tabata a zuciyarta game dashi,yadda ta ganshi cikin hoton ya gaya mata he's nice and friendly to his family,daga hoto na qarshe sai wani dan littafi dake dauke da sunan my dairy.

A hankali ta soma buda shafin farko,a nan ta gane na shaheeda ne,sai taci gaba da budewa tana karantawa,tun batayi nisa ba ta fuskanci duka akan ja'afar tayi littafin sanda tana raye,da farko ya zame mata kamar novel,ta dinga karantawa yana debe mata kewa da kuma sakata murmushi,halayensa abinda yafiso da wanda bayaso,yadda fushinsa da walwalarsa take

"He's arrogant and very annoyed person sometimes,but hes the best husband i know in the planet" murmushi ya kubcewa maimunatu,sai taji kamar gata ga shaheeda take gaya mata hakan,girarta ta dage

"Na shaida hakan" ta fada a fili,sannan taci gaba da bin rubutun tana fahimtar kowanne zance da yake ciki,daga bisani kuma labarin ya fara tabata,har zuwa sanda tayi rubutun ta na qarshe,wanda akan amna da amra tayi.

Kasa riqe kanta tayi,kuka ya subuce mata sosai,ba abinda take tunawa sai daadarta da kuma abbanta,tausayin amna kuma na sake sarqafar zuciyarta,qaunar yarinyar na sake shiga zuciyarta.

Sai da kukan ya lafa mata,duk da hawayen baibar sauka ba sannan ta daga kanta tana maido da littafin shafin da shaheedan ke bayyana halaye da dabi'un ja'afar din,ta dora hannunta a kai tana sake maimaita wajen.

Ko kusa bataji motsi ko alamun shigowar sa ba,har sai da taji ya sauke wata ajiyar zuciya mai qarfi,ta daga kanta da sauri tana dubansa,shima ita yake kalla,idanuwansa sun kada sun canza kala,da alama wani abu ya taba zuciyarsa sosai.

A hankali tayi yinqurin hade littafin ta rufe,bakinta yana fadin

"Am sorry,kayi haquri" tausasan hannayensa yasa ya riqe hannunta ya dakatar dasu daga qoqarin rufewar da takeyi,sannan ya zare littafin yana duba saqonni wajen da yaga tana karantawa,sake daga kansa yayi ya kalleta,sai ya zame shima ya zauna kusa da ita sosai har jikkunansu na gogar na juna,ya kuma sanya littafin atsakiyan su,kamar masu bitar karatun jarabawa,yatsansa tabi da kallo zuwa wajen da ya dorasu

_bana jin a duniya za'a sake samun wata macen da zata soshi ta kula dashi kamar yadda nake sonshi_ abinda paragraph din ta qunsa kenan,tana kaiwa nan ta tada kanta tana kallonsa,shima sai ya sanya qwayar idanunsa a tata,suka shiga kallon kallo,a hankali ya maida littafin ya rufe,ya aje a gefansa,sannan ya kama fuskarta ya saka a tafin hannunsa,ya hade fuskokinsu waje daya,suka fara musayar numfashi.

Shuru ya ratsa a tsakaninsu,ba komai dakin sai qarar ac dake kadawa da kuma qananun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login