Showing 27001 words to 30000 words out of 204120 words

Chapter 10 - Gurbin Ido Book One Complete Hausa Novel

shigo baquwa a rugar nan,wadda hatta da kyanta ya banbanta da irin namu,babu tausayi ko tsoron Allah furera ta maida shatu da maimunatu tamkar bayi da basu da 'yanci,shatu bauta maimunatu bauta,Allah ya zubawa shatun wani irin haquri juriya da kuma kau da kai wanda cikin irin nata ta sanwa maimunatu,don babu lallai tayi yakai irin nata,a haka dai suke rayuwar. Abinda ya faru ya kuma janyo shatu da maimunatu suka zama abun qyama shine......a al'darmu ta fulani,baka ganin nagge ko sauran dabbobi ka nuna su tankasu,komai kyau da burgewar da suka baka,cikin irin haka,cikin rashin sani shatu taga wasu nagge na bappa labaran,yana gab da fita dasu kudu,ranar an fiddasu kiwo ta nuna wata babbar nagge a cikinsu tace a haka kamar lafiyayya me kyau da ita,amma kuma bata da lpy,suka yita fada dame kiwon,aka mata ca,ta bada haquri,saboda mantawa da tayi ta aikata hakan,kuma tace tana musu tsoron asara ne,magani ya koma a maidata gida a bata,koda suka dawo gida baice bata da lafiya ba yadda shatu ta fada,ba'a wayi gari da naggen ba ta rasu,rigima sosai daada taso a tayar,amma bapp ya hana,abinda basu sani ba ni da kaina bayan asuba na fita zan dora sanwar safe,na lura da naggen bata da kuxari yadda ya kamata,ni da kaina nasan tabbas bata da lpy,to amma dana fada qaryatani daada tayi,tace kawai dai don tana zuwa wajena ne yasa nakeson kareta,anyi wannan rigimar ta mutu,shatu da tsohon cikinta taje diban ruwa matan gidan barau daya daga cikinsu ta takaleta da fada yadda suka saba mata,tunda muke da shatu bata taba gayamin ko kawomin qarar kowa ba,amma inajin labarin yadda wasu cikin rugar suka matsanta mata,a ranar taso dauke kai amma yau da gobe,ga yanayin tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe,talatu bata duba wannan ba ta dinga ja mata riga shatu na gocewa,daga qarshe dai da talatu taga ba zata kulata ba sai ta tureta,wanda sauran kadan ta afka cikin rafin,Allah ne kawai yayi ruwan ba shine ajalinta ba,sosai ran shatu ya baci bayan tasha da qyar,cikin bacin rai idanuwanta cike da hawaye ta kalleta

"Na dauka ko banci darajar komai a wajenki ba zanci darajar cikin dake jikina,tunda kema macace,idan kinyi hakane don ki tozarta ni kije,Allah yana gani,kuma ina fatan kiga sakayya da gaggawa anan kusa" daga haka shatu bata qara ba bata rage ba,ta dauki ruwanta ta wuce,suka taru suka yita maida magana,tare da maido maganar nagge,a nan suka fara qulla wataqil mayya ce ita din,kwana biyu tsakani kuwa talatu taje diban ruwa ruwan yayi ciki da ita,ya kuma zama ajalinta,aka fara lugwigwita magana tare da fara yada jita jitar shatun mayyace,kafin kace me?,magana ta fantsama a gari,dangin talatu da sauran mutane 'yan bani na iya suka dauki sanduna sukayi gidan furera kan sai an fiddo shatu sun kasheta,ya tabbata mayyace ita,da qyar da sudin goshi qurar ta lafa,baiwar Allah shatu,ashe sanadin wannan tashin hankalin naquda ta tasammata,furera haushin abinda ya faru tayi banza da ita,daga ita sai maimunatu ne suka yita fama,daga qarshe tace maimunatun ta lallaba ta kirawo mata ni,har maimunatu takai bakin qofa ta qwala mata kira,saita tsaya,ta yafitota da hannu ta koma gaban shatun ta duqa

"Daada,akwai wani abun da kike so ne?" Murmushi ta sakar mata,ta daga hannayenta ta cirw dukka duwatsun jiki da maimunatu ta dade tana qulafucin tabar mata ta zura mata su,saidai yarinyar a sannan sam bataji farincikin da take ayyanawa zataji ba duk sanda daadar tata tabar mata dutsunan

"Daada kin barmin ne wai?" Kai ta gyada

"Na bar miki maimunatu......kiyi haquri kiyi haquri.....kiyi haquri kinji,ki fuskanci rayuwa duk yadda tazo miki,ki zama mai gaskiya da amana,karki yadda a kamaki kinci amanar wani,idan kinga saade,kice ina mata fatan alkhairi" sanda yarinyar ke gayan abinda uwar tace nayi mamakin yadda ta iya riqewa,hankalin maimunatu a sannan ya tashi sosai duk da qarancin shekarunta,ba kowa zai gane hakan ba sai wanda irin haka ya sameshi,cikin rudewa tace

"Daada" hannu ta daga mata

"Barci nake ji,yi sauri ki kiramin yuuma" maganar data sanya maimunatu tashi ta fita a dakin da gudu,fitar da ta zama silar rabuwarta da mahaifiyarta kenan rabuwa ta har abada,don koni sanda na shiga wajen shatu rai yayi halinsa,haka akayi mata sutura bata ko haife abinda yake cikinta ba,sanda na koma gida da daddare randa shatu ya rasu,tunda na tsaya na taya maimunatu da bata dame rarrashinta zama,mahaifiyarta ta rasu ta barta babu ko mutum daya da zata jingina dashi tayi kuka taji sauqi cikin ranta,Bappa da kansa ha sameni,ya shaida min ya yanke hulda da wata alaqata da duk abinda ya shafi shatu matuqar shike aure na,duk randa na kuskurewa hakan kuwa,zai dauki tsatstsauran mataki a kaina,bansan me aka gayawa bappan ba bayan fitata wajen shatu,amma dai na sani cewa akwai qullin daadar himu da kuma furera a ciki da suka sake tunzura komai,don kuwa bappan mutum ne mai sanin ya kamata,sannan ta yaya zaa rabani da maimunatu kuma abar mu'amalar dake tsakanin furera da daadar himu?,??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????bayan duka gida daya ne,abu daya ne?,duk da furera ta cikasu da labaran qarya na cewa babu abinda ya hadata da shatun illa aikin bauta data dauketa,mutuwar shatu sai furera ta sake sakankancewa,ta mallake dukka dabbobin shatu da maimunatu suka zama nata,maimunatu bata tashi a komai ba illa me aikin bauta,ta riqeta wani irin riqo na qunci da kuma wahala,dole inaji ina gani na dauke idanuna daga kan maimunatun,nayi kamar bansan tana raye ba,saidai ban fasa mata addu'a ba da nema mata sasauci"

"Yanzu 'yan wadan nan abubuwan sune suka zama hujja da kuma dalilin da ake qyamatar yarinyar bayan cikin abun babu wani abu guda daya data aikata?"

"Sune anni" kada kai kawai anni keyi,wani abu ya tsaye mata a zuciyarta me taba rai,tana kwatanta yuuma da maimunatu,inda an samu sakaci ko wani abu makamancin hakan haka zai iya faruwa da yuuma kenan sanda tana qarama,duk da ita tana gaban mahaifinta ne cikin soyayya da kulawa a sannan?.

"Wannan duka ba hujja bace,zallar jahilci ne da kuma son zuciya,kuma tabbas sai Allah ya yiwa yarinyar sakayya,zan dauke maimunatu daga wannan garin don bata cancanci zama a nan ba,maraya?,maraya wasa ne?,daka taba maraya hawayensa guda daya tak ya diga a qasa saboda kai,gwara ka rasa dukkan abinda ka mallaka ciki harda lafiyarka,kukan maraya masifa ne bare a sakashi a damuwa" yalwataccen murmushi ne ya bayyana fuskar yuuma

"Da nafi kowa jin dadin hakan anni,tabbas zanfi kowa murna"

"Kafin na wuce zan karba maimunatu zan wuce da ita,in sha Allah qarshen kukanta yazo,lallai mahaifiyarta macace mai nagarta,nagartar da nake jin yaqini da tabbcin akwaita tattare da maimunatu,tunda dukkan alamu sun bayyana"

"Amma anni wani hanzari ba gudu ba.....anya kinyi duba da tarin banbanci da tazarar dake tsakanin ja'afar da maimunatu kuwa?,shirinki me yuwuwa ne?" Tambayar dake rai da zuciyar laila kenan,labarin ya dauki hankalinta cike da mamaki da kuma al'ajabi,zuciyarta kuma ta narke matuqa da tausayin maimunatu

"Nasan ta inda zan bullowa lamarin,ki tayani da addu'a,kiyimin fatan dacewa" ajiyar zuciya mai qarfi yuuma ta sauke

"Allah to yasa a dace,yasa ta silarki marainiya maimunatu zata samu salaama a rayuwarta"

"Ameen ya hayyu ya qayyumu" anni ta fada tana lanqwasa yatsunta,tare da tunanin ta inda zata fara.


*_Arewabooks::huguma_*


d'
=?%?d'
=?%?d'
=?%?d'
=?%?d'
=?%?d'
=?%?d'
=?%?d'
=?%?d'
=?%?d'
=?%?d'
=?%?d'
=?%?

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

=??=??=??=??=??=??=??

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR CONTINUES PATRONAGE_*>?p?>?p?>?p?>?p?>?p?>?p?>?p?>?p?
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: *10*

"Assalamu alaikum" ta furta kamar yadda yake a al'adarta duk sanda zata amsa waya,daga daya sashen muryarsa ta bayyana,cikin sanyi daya sanya annin ta shanshano wani abu daga gareshi tun kafin yace wani abu

"Barka da dare"

"Dare?,a garinku kenan" daga can sashen da yake sai daya dafe goshinsa,ba zata taba yarda ta karba yadda ya bata ba sai tayi challenging dinsa

"To barka da safiya shikenan?"

"Yanzu naji magana.....barkanmu kadai" dorawa yayi da

"Kun tashi lafiya,ya jama'ar gidan?"

"Alhamdulillah,lafiya qalau,jama'ar gida mun barsu a gida,mu mun danyo balaguro nan cikin adamawa"

"da wannan qafar anni?" Ya fada murya a kwance cikin nuna kulawa

"Eh,to ya za'ayi,duk inda Allah ya tsaga sai ka taka saika taka din kafin lokacin da takun naka zai qare"

"Hakane....." Ya fada a taqaice

"Banji duriyar jafar ba" ta fada cikin zaquwa da son jin muryarsa,ajiyar zuciyar da taji jabir din ya sake sai da gabanta ya fadi

"Maganarshi na kira nayi miki anni" ya fada a sanyaye

"Menene kuma?" Ta tambayeshi gabanta yana faduwa

"Anni har yanzu dai.....har yanzun babu wani ci gaba anni,sai abubuwan sunyi kamar zasu gyaru sai su sake rikicewa"

"Kuma dai?" Ta fadi cikin tsantsar damuwa,kamar tana gabansa ya gyada kai

"Wallahi anni,yanzu haka tun jiya banga fuskarsa ba,nayi iya bakin qoqarina ma naga ya fito ko ruwan zafi ne ya sha idan ma bazaici abinci ba amma ko motsi yaqiyi bare ya bani alamar da zata gayamin yana raye lafiya lau"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" kalmar da taja hankalin yuuma,ta koma ta zauna daga shirin tashin da takeyi din,ta kuma kamawa daada sukakai salatin tare.

Sosai fuskar anni ta nuna alamun tashin hankali da kuma damuwa,wannan wata matsala ce data zama kusan jarrabawa cikin tata rayuwar,saidai a yadda Allah yayi mata komai a rayuwa,ya albarkaci zuri'arta,to ta dora hakan a matsayin jarrabawar da ubangiji kan yiwa kowanne bawa don ya gwada imaninsa

"Ka kira wayarsa?"

"Ya rufeta anni,yaqi bude wayar.....amma ki kwantar da hankalinki,koda bazaice komai zan sanar dashi daga bakin qofa,awa uku suka rage ya cika awa ashirin da hudu a dakin,idan har bai bude ba ya fito zan sanarma jami'an tsaro na qasar su shigo su balle qofar su dubamin shi,duk da jikina yana bani lafiya qalau yake,tunda fitilar dakinsa naga a kunne take tun jiyan kawo yau"

"Jabir.....duk yadda zakayi ka tabbata kayi ya fito haka a dakin nan,na gaji da zamanku a wannan qasar jabir,bana jin zan barku kuci gaba da zama kamar yadda kukeso"

"Kada ki damu anni"

"Ka kula dashi don Allah,duk abinda ake ciki ka shaidamin,kada ka yarda da maganar babanku kan kada a gayamin komai,ni hakan shine kwanciyar hankali na"

"In sha Allah,i will do my best anni"

Jikinta a matuqar sanyaye ta sauke wayar daga kunnenta ta ajjiyeta a gefanta,sai ta hade hannayenta waje guda

"Ya Allah.....mun tuba Allah,Allah ka kawo mana qarshen wannan matsalar,wannan damuwa Allah ka yanke mana ita gaba daya,ubangiji ka aiko mana da HASKE"

"Ameen......lafiya kuwa anni?" Yuuma ta tambayi annin cikin matuqar kulawa da kuma damuwa,saboda ta fuskanci koma wacce irin matsala ce lallai ba qarama bace a wajen annin

"Jafar ramatu,har yanzu jafar ya kasa komawa kamar kowanne irin mutum,jafar ba jahili bane....amma bansan me yasa ya kasa yarda da qaddararsa ba,gaba daya rayuwar jafar ba ita bace a yanzu,wani jafar ne na daban da dukka muke kallon an sauya mana shi,tsahon shekara uku amma komai ya kasa wucewa?"

"Jafar dai anni?" Yuuma ta tambaya tana dubanta,kai ta jinjina

"Shi.....tun daga shaheeda da amra suka rasu,bamu sake gane kan ja'afar ba,babu irin roqon Allahn da ba'ayi masa ba,ana kan yi masa ma,ba irin nasiha jan hankali da ban bakin da jafar bai samu ba,ba za'ace babu sauqi ba sam,saidai tashi danganar data zo sai tazo wani iri,duk da cewa dama miskili ne mara son magana me kuma bau dadden hali.....amma hakan baisa rayuwa ta naqasa tako ina ba,yana rayuwarsa kamar kowa,yana kuma yin dukkan wani abu daya dace da mutum kamarsa zaiyi,amma tun bayan nan jafar gaba daya ba shine tare damu ba,sai abun yayi kamar zai dai daita,sai ya sake dilmiya cikin damuwa me zurfi,na dauka zaman gidansa ke sake dagula masa lissafi......sai nasa ya tattaro ya dawo cikin gida,duk da haka babu wani canji,sai na sake tunanin kodai zaman kadaici ne?,tunda a baya shi din me aure ne?,na shiga nema masa yarinyar da zata dace dashi,ta kuma kula dashi......amma abun takaicin,wallahi ramatu yadda kikasan nayi busa a iska,baisan ma anayi ba,wannan yasa duka yaran suke kasa daurewa,saboda kowacce tana tsammanin samun kulawa da soyayya daga gareshi,to duka babu ko daya da suke samu,abinda yake sanyasu sarewa kenan,su kuma ce sun haqura......ba tare da sun duba cewa a yanzun shi din tamkar mara lafiya yake ba,zuciya da qwaqwalwarsa na buqatar magani ta hanyar mu'amalantarsa da dawowa dashi ya dawo ja'afar na asali......sannan koma meye sai ya biyo baya.....karo hudu kenan,amma dukkaninsu sun gaza daurewa zama dashi.......abinda ya bani mamaki da tsoro,yasa kuma na saare shine,wadda na nema masa a karo na shida 'yar uwarsa ce,a yadda abun ya dauko naji dadi.matuqa,saboda ina hangen haske da kuma waraka,don yadda yarinyar ta jajirce,ashe akwai mummunar manufa a ranta,dukiyarsa take hange,Allah ya toni asirinta,na gano na kuma watsa tafiyar,tunda dama shi wanda ake dominsa baima san inayi ba" shuru anni tayi tana maida numfashi,abun yana matuqar damunta da zuciya,a yanzu duk duniya zata iya cewa bata da matsala sama da wannan.

"Iyaka nazari da hangena,babu wata hanya da zamu samu yadda mukeso sai ja'afar ya haqura yayi aure,saboda jabir bazai taba dawwama tare dashi ba,shima mutum ne,aure zaiyi,don maganar da ake yanzun,watanni kadan suka rage akai masa kudi da sa rana,yau idan jabir ya tafi,shikenan haka zamu zuba idanu muna kallon rayuwar jafar ta dulmiya ta nutse a gaban idanuwanmu?" Kai yuuma ke girgizawa,tsahon wasu mintuna shuru ya baqunci dakin,kafin yuuma ta saki ajiyar zuciya

"Maganarki gaskiya ce anni,hanya daya ce tak ta fitar da ja'afar daga yanayin da yake ciki,hanyar kuwa itace,a sama masa mace mai tsananin sonsa,so fisabillahi saboda Allah,jajirtacciya da zata iya kasancewa koda yaushe tare dashi,mai juriya da zata iya daukan dawainiyarsa.....komai nisan zangon da zasu samu dashi kafin a cimma gaci...."

"Wannan shine abunda muka kasa samu har yanzu" anni ta katsi numfashin yuuma,gyara zama yuuman tayi

"A nawa tunanin kaf cikin matan da kuke nema masan,kuna sama masa ne irin matan can wajejenku,wadanda idanunsu ke a bude,suke ganin cewa 'yantattun mata ne su,wadanda zasu shiga gidan aure ne da dukka iko da isa irin wadda d'a namiji ke da ita,ba bautar aure zasuyi ba,zama ne na 'yanci da cin gashin kai" shuru ne ya sake ratsa dakin,sai hayaniya daga jama'ar dake karakainarsu daga waje jifa jifa tana ratsasu.

Sosai maganar yuuma ta ratsa anni,ta kuma sanyata zama ta dinga wareta daya bayan daya tana nazarinta,lallai yuuman tayi wani dogon nazari da kuma tsinkaye,wanda ita kanta bata yishi ba tsahon lokacin da aka dauka matsalolin suna faruwa.

Kusan rarrabuwa hankalin anni yayi kashi kashi,tana sauraren kira daga khalid,tana kuma ci gaba da nazarin maganar yuuma,tare da tunanin inda zata kamo bakin zaren,ta damu da ja'afar matuqa,tana kuma shiga damuwa ainun game da lamarinsa.


Sam hankalin anni bai kwanta ba har sai data samu tabbacin lafiya lau daga bakin jabir

"Ka bani shi jabir zamuyi magana" kai jabir din ya girgiza yana duban bakin qofar dakin da yake zaune a yanzu daura da ita,kamar wanda aka bawa gadin wajen

"Bai fito ba har yanzu anni,duk da munyi magana,amma ina da tabbacin nan da dan wani lokaci koda baiyi kiran kowa ba zaiyi kiranki" ya fada with full confidence,saboda yasan tsakaninsa da annin

"Shikenan,ka sake kula don Allah jabir"

"In sha Allah anni" ya fada shima zuciyarsa na karyewa,bayason wannan ja'afar din na yanzu,yafi qaunar ja'afar dinsa na asali,duk da dama tun asali azama da ja'afar din sai shi,duk da yadda mutane suke daukansa suke kuma kallonsa....amma zai iya cewa bai taba rayuwa da wani mutum me dadin zama irin ja'afar din ba,wasu abubuwa ne game tattare dashi da idan ka fahimcesu shikenan.

Wunin ranar gaba daya anni ta qarar dashi kan tunanin maganganun yuuma,ita kanta yuuma ta fuskanci yau din annin akwai damuwa fal tattare da zuciyarta,don ko abincin rana data kawo mata bata cishi ba sai kusan gefin la'asar,ta jima sosai tana waya da daya daga cikin yayanta.

Sanda rana ta kammala faduwa,wanda ya zamana lokaci ne na sallar magariba,annin na daya daga cikin mutanen da basa wasa da ibada,wannan ya sanya ubangiji ya bata kyakkyawan tsufa da kuna qwarin jiki,banda ciwon qafa babu abinda yake damunta,zaka zaci shekarunta basu kai yadda take fada ba.

Tana saman abun sallah tana lazumi,hannunta riqe da carbinta,ta tsakankanin labulen dakin tana hangen wulgawar mutanen gidan kowa na sabgar gabansa.

Waiwayawa tayi ga laila dake kwance tana latse latsen waya abinta sakamakon bata sallah ta watsa mata harara,ta shafa addu'arta tana shirin mata magana akayi sallama daga tsakar gidan.

Tsam anni tayi da ranta,saboda sautin muryar kamar tasan me ita,hakanan sai taji kamar ta saba jin muryar dama. Yuuma dake alwala tana wanke qafafuwanta ta waiwayo,sosai mamaki ya cikata,karon farko bayan wasu shekaru da suka shude rabon da taga maimunatu cikin gidan,don haka ta miqe cikin kulawa

"Lafiya maimunatu?" Tafukan hannuwanta dake a dunqule ta budewa yuuma,kyakkyawar sarqar wuya ta ainihin dutsen wuri da kuma murjani na asali ta bayyana

"Kun yada wannan ne a gidanmu dazu" zubawa sarqar idanu yuuma tayi,don tasan bata da ita,dutsene maj tsada wanda su kansu fulani sunsan dajarsa

"Anya kuwa?.....amma....qarasa rumfata ko anni ce,don nasan da laila ba zata saka wannan ba" kai ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login