Showing 117001 words to 120000 words out of 204120 words

Chapter 40 - Gurbin Ido Book One Complete Hausa Novel

saman kujera

"Wash" ta furta ba tare da tunanin komai ba,ta fadi kalmar ne saboda yadda taji kamar an bubbuge mata gabbanta,uwa uba kuma gudun zuciyarta daya qaru wanda sai a yanzu take qoqarin sai saita kanta.

Hijabinta ta zare ba tare data lura da kallon da baba tabawa ke binta dashi ba,ta isa ga fridge ta bude,ta fidda ruwa me sanyi saboda yadda takejin maqoshinta ya bushe sosai,bata buqaci cup ba ta balle murfin ta fara sha a hankali,idanunta na hango mata shi cikin falon nasa da bai fiya haske ba,cikin wata abaya ta maza

"A haka he's very calm and quiet,amma macijin sari ka noqe ne" ta fadawa kanta da kanta tana cire robar daga bakinta,ta dora ragowar saman fridge din sannan ta juyo.

Sai a sannan ta lura da kallon da babab take mata,ta kuma tsargu,amma kafin ta tambaya ita ta rigata

"Har me?,wai har kin dawo?" Kai ta gyada mata tana neman wajen zama,hannu tasa ta kama baki,sai kuma ta kada kai

"Nidai nasan ba'a ajewa miji abinci a taho a barshi dashi"

"Aiki yake baba,kuma waya ma yake amsawa,so yana buqatar space,may be wayar ta sirrice" ta fada har zuciyarta,saidai ita baba tabawan ta kalli hakanne da sunan bawa kai kariya kawai

"To Allah ya kyauta" yadda baban tayi sai duk maimunatu taji bata ji dadi ba,saboda itama baban kamar bataji dadin yadda tayin ba,to amma kuma ta yaya zata iya zama dashi a muhalli guda?,ko abincin data kai din kawai tasan karambani tayi da kuma bin umarni,tana da yaqinin zaiyi wuya yacu,ta fahimci kamar yana da jin kansa,izza da kuma qasaita,bai taba neman wani abu daga garesu ba cikin gidan dai dai da ruwan sha kuwa,sai taja wayarta kawai ta kunna data tahau sabon Whatsapp dinta,ta kuma fara da yiwa qawayen nata guda uku sallama.

Taci sa'a kuwa ta samu afrah a online,cikin mamaki take tambayar da gaske itace,sai suka zarme da hira,wadda ta daukesu lokaci mai tsaho,daga bisani sukayi sallama bayan ta bata labarin latest Korean dramas masu zafi da suka fito.

Kai tsaye ta wuce Vidmate ta saukesu masu yawan gaske,saidai tana tunanin yadda zata kallesu a nutse ba tare da sun hanata bitar karatuttukanta na makaranta ba.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 49

A kasalance yabar sashen nata zuwa nasa,gaba daya ta sakarwa jikinsa wata irin kasala,ya rasa dalilin da ya sanya duk sanda incident irin haka zai faru tsakaninsu sai haka ta kasance.

Sam bai kula da wanzuwar mutum a wajen ba,har ya kama stairs zai hau yaji an kirayi sunansa a tausashe,sai ya tsaya cak,ya kuma waiwaya a hankali.

Unaisa ce tsaye,sanye da wata fatar gown,kanta babu dankwali sai qaramin vail data yafa a kanta me shara shara,idanunta a kansa,tana dubansa cikin wani irin kallo wanda ya nuna yadda tayi laushi har cikin idanunta,qasan ranta tana jin wani irin qaunarsa tana fusgarta,zuwa yanzu takai maqura,hakanam tana jin haqurinta yana neman gazawa,tayi iya matuqar qoqari a irin yadda ta saba rayuwarta,sai ta sake sassauta fuskarta tana fatan ya duneta da idanun tausayi,bata taba kawowa cewa izzarsa miskilancinsa da kuma jin kansa sunkai har haka ba,tayi tunanin a kurkusa zata tagi da imaninsa kamar yadda yake tafiya da imanin duk wani da namiji,fara takowa tayi a hankali,yana biye da ita da idanu,har zuwa sanda yaga tana shirin wuce iyakar da yakega ya kamata ta tsaya

"Stop there" ya fada da muryarnan tasa dake dauke d wani irin amo,ba zato babu kuma tsammani sai jinta yayi ta fada jikinsa gaba daya,ta kuma sanaya hannunta ta qanqameshi da kyau idanunta yana tara qwalla.

"Meye haka?, what's this?" Ya fada yana yunqurin tureta daga jikinsa,saidai hakan bai samu ba saboda yadda ta sake cukuikuyeshi tana fadin

"Na gaji.....na gaji,am going to kill my self indai ba zaka saurareni ba" furucin nata yayi masa banbarakwai sosai atsakiyan kansa,diyar musulmi ke zance aikata ta'addanci a karan kanta?,bawai don ya damu ko kima ya tsorata da furucinta ba yace

"Okay,okay......sakeni tukunna" kamar ba zata sakeshin ba sai kuma ta sakeshi,ta kuma ja da baya tana dauke qananun qwallar fuskarta,hannyensa ya shiga yarfewa kamar wanda wani abun qi ya tabawa fata,fuskarsa ya sake hadewa ya tsare gida sosai yana dubanta

"Am all ears" ya fada yana goye hannuwansa a qirji,idanunta tadan watsa bangaren sasan maimunatu,ta yaya zatayi irin wannan maganar dashi a waje.irin wannan,by mistake yarinyar tazo guftawa ta jisu?,ta tabbatar idan haka ta faru ajinta ya gaba zubewa a idanunta har abada

"Am not comfortable here......i need privacy" kamar bazai amsata ba,sai kuma ya juya ya soma takawa zuwa saman a nutse cikin takunsan nan na daban,ta bishi da kallo tana jin wani abu yana tsarga mata,kafin daga bisani ta soma bin bayansa,tana qiyasta irin kalmomin da zatayi amfani dasu wajen ganin tasha kansa.

Suna isa tsakar falon idanuwanta na sake sauka ga hotunan shaheeda,yadda ta tsani mutuwarta haka ta tsani bude idanu taga wadan nan hotunan,asalima tana kishinsu fiye da yadda take jin kishin maimunatu,tunda a yanzun maimunatu bata tsare mata komai ba,bata ma.kallonta a matsayin matsala gareta,saidai tana jin haushin amsa sunan matar mijinta da tayi,harara ta jefi hoton dashi,wanda ja'afar dake qoqarin ganin ya saurareta idanunsa suka shaida masa hakan,wani abu me kama da mamaki ya saukar masa

"Harara?,for what?" Maida idanunsa yayi ga sassan da hoton shaheeda ke maqale,dai dai sanda ya dauke dubansa zuwa ga unaisa,itama dai dai sannan ya dauke idanunta zuwa kansa,sai suka hada idanu,kamar an zare wani abu daga zuciyarta taji,bataso ya ganta ba,amma ita ba wannan ne damuwarta ba,damuwarta ta fidda wadda ke cikin hoton daga zuciyarsa gaba daya,kamar yadda ta five a filin duniya,ita kuma ta maye gurbinta

"Uhmm.....go on" takowa ta soma yi tana sake nufoshi,ta dora dukkan wani yanayi da zai baka tausayi a kan fuskarta,saidai tana zuwa gab dashi ya sake dakatar da ita

"Don't do it" ya fada calmly gami da yi mata nuni da hannu kan yana saurarenta,bata da wani zabi illa fashewa da kuka harda sheshsheqa,abinda ya bashi mamaki ganin cewa shi din bai aikata mata komai ba,fuska ya hade sosai yana dubanta,sai kuma ya kau da kai yana jan tsaki can qasan ransa

"Bansan meye laifi na,ban kuma san me na aikata maka ba,don kawai nace ina sonka ja'afar?,ta yaya da hakkina a kanka tsahon shekara kusan guda ka takemin kamar bakasan da wannan ba"

"Anzo wajen" ya fada a ransa yana jin tana sake ficewa daga ransa,ta yaya yarinya mai cikakkiyar kunya da nutsuwa zata iya duban idanun da namiji.....duk da kasancewarsa mijinta,amma a matsayin budurwa ta gaya masa hakan?,well.....batayi laifi ba,tunda hakkinta ne kamar yadda ta fada din,amma bayajin koda danneshi akayi zai iya aikatawa,hes not in the mood gaba daya,bayajin wani feelings a yanzu a kanta ko dis.

Kujerar dake daura dashi ya qarasa ya zauna a hannun kujerar,yaci gaba da dubanta hankali kwance sanda taketa kukanta tana sake qara ma kukan salo a fatan da take na samun nasara a kansa,can qasan zuciyarsa yake qissima ta yadda zai raba kansa da wannan matsalar.....eh.....matsala mana,zuwa yanzun yana jin unaisan ta zame masa matsala,babu abinda take haifar masa banda kwasarwa kansa zunubi,bayan yana da tabbacin abune mai wahala ya iya karbarta cikin rayuwarsa,zuciyarsa wata irin zuciya ce mai wahalar sha'ani


"I already told you,zamanmu abu ne mai wahala da ban hango yiwuwarsa,ni am ready to dismissed you,the choice is yours.....karki sake tara ta da irin wannan shirmen" daga haka ya miqe ya nufi bedroom dinsa,ta yunqura zata bishi,saidai ko kafin ta isa ya maida qofansa ya rufe,ta daga hannu kamar zatayi knocking sai ta sauke,ta fahimci wasu daga cikin halaye da kuma dabi'unsa,idan ta sake tayi knocking masa qofa,batasan me zai biyo baya ba,sai ta juya da gudu gudu tana sauka daga stairs din kuka yana kufce mata,ta gaji gaskiya,ta kuma kai maqura,tana jin ta iso geji,batason kuma ta bata dukkan wani tanadi da tayi masa,zata dauki mataki na gaba itama da takeji har cikin ranta da zuciyarta shine dai dai.


???????Ta tabbatar idan har ta zauna a wajen baba tabawa babu abinda zai hanata cewa taje takai masa abincin dare,wannan shine worst abu da zata sanyata,bata jin zata iya hada idanu ko muhalli dashi,gaba daya ya ajema ranta da zuciyarta wani abu,wani irin nauyi da kwarjininsa daya qaru cikin idanunta,gefe guda wani abu me kama da haushinsa da take ji,gaba daya halayyarsa batayi mata ba,hisham ya fishi sauqin kai kirki fara'a da iya mu'amala da mutane,komai nasa cikin tsumewa da tsare gida?.

Leqawa kawai tayi ta duba baba tabawan don tasan ta tashi kuma lafiya take,don ko ita tayi mamakin jimawar da tayi tana bacci

"Zan koma na kwanta baba,jikins yau banajin qwarinsa"

"Ashsha.....amma dai ba ciwon bane ko?,yana shirin dawowa ina shirin tattara komatsaina na koma inda nafi wayo?" Dubanta da kyau maimunatu tayi,gabanta ya fadi,sai taji an cire dukka sauran walwala daga zuciyarta,komawa tayi ta zauna a maimakon tashi da tayi dazun

"Tafiya kuma baba?" Kai ta gyada

"Eh,ai gwara na koma gida hakanan,tunda naga jikin naki ai yayi kyau,banda tsautsayin da ya faru yau ma ai da yau din a gida zan kwana" gaba daya jikinta ya gama mutuwa,batason tafiyar baban,saboda tasan ba komai bane zai faru sai zaman kadaici kara dadi,wanda a yanzun ta fara sabawa da rayuwa da mutane,daya daga cikin dalilan da ya sanya ko hutun makaranta bata fiya son ayi ba,banda tanason tazo taga anni wasu lokutan.

"Don Allah baba ki bari sai zuwa wani lokaci,ko kuma idan zan koma hutu,saura kwana ashirin gaba daya mu koma" kai ta girgiza

"Banda abinki maimunatu ta yaya zan zo cikin yara gotai gotai dani na zauna banda ma lalura ta rashin lafiyar?,ai gwara na tafi,kema kyafi sakewa kiyi bautar aurenki yadda ya kamata" daga qarshe ta shagwuba mata magana,wadda ta sanya bata sake cewa komai ba,sai tayi qas da kanta.

Bata sani ba ko kewar baban ta fara, yadda ta tsara guduwa daki batayi hakan ba,sai ta zauna suna fira sama sama,yayin da baban tayi amfani da wannan damar tana sake jan hankalin maimuntu a fakaice akan rayuwar auren nata.

Washegari gaba daya bata fito a daki da wuri ba,tana qiyasta lokacin da zai shigo gaida baba tabawa,ta kuwa qiyasta dai dai,don kuwa ya shigo gaida ita din,saidai a gurguje,don yana sauri zashi gida karbar kudin auren salma hafsa da kuma nadiya,harma da laila,sosai baba tabawa taji dadin labarin,bayan kuma maimunatu ta fito ta shaida mata.

Tun a waya ta kira laila tayi mata murna,saboda tasan yadda take son auren,don babu wanda ya zaci ma za'a karba harda nata,ta kuma dan tsokaneta,baba tabawa na zaune tana jinsu tana dariya,ko bayan ta gama wayar ma hirar familyn dr marwan din suka shiga,wanda duka baba tabawan ce ke bata labarin yawan zuri'ar khalidu akko,da kuma karamcin mutan gidan dr marwan din,wanda ita kanta maimunatu shaida ce,bata taba zaton a duniya akwai mutane irinsu ba,sun samu dukkan wata dama ta rayuwa,amma hakan baisanya sun wulaqanta kowa ba,ko kuma sun dauki kansu a wani abu ba.

***********Washegari tun safe maimunatu tana dakin baba tabawa,gaba daya yau din ranta babu dadi,tare sukayi abincin safe,baba tabawan ta dora na dare da wuri,saboda da yamma sukayi da driver zaizo ya dauketa,ko mai maimunatun takeyi cikin kasala da rashin dadin rai takeyinsa,tana jin inama ace zata iya hana baban tafiya,inama zata yarda suyi zamansu tare,saidai tasan hakan ba mai yiwuwa bane.

Suna gama girkin ta wuce dakinta,tayi wanka,sannan ta shirya cikin wata chiffon gown da aka fidda mata desin me kyau,ta bude sosai daga qasa,ta gyara kanta,ssnnan tayi rolling vail din da tazo dashi shima na plain chiffon mara ado a jiki,jikinta na fidda sassanyan qamshin turaren burberry london,bata saka komai a fuskarta banda powder da lip balm,saidai fuskar tata koda yaushe fresh take,saboda hutu data samu sosai,uwa uba fatarta me kyau ce,babu wani qurji ko pimples ko daya,yan makarantarsu da yawa suna zaton tana shafa wani.mai ne na musamman,saidai ko kadan,haka fatarta yake naturally,ta dauki wayarta,ta sake fitowa wajen baban.

Zuwa la'asar din baba tabawan ta kammala komai,ta kuma dauko jakarta zuwa falon maimunatun,yayin da take biye da baban dauke da wata leda data cika mata ita da kayayyakin da tasan zataji dadinsu,fuskarta gaba daya a narke take,tana riqe da ledar har zuwa sanda suka fito babban falon gidan,sai baba tabawan taja ta tsaya

"Af....niko nace bai kamata na tafi bamu gaisa da abokiyar zamanki ba,tunda nazo banga fuskarta ba"

"Gaskiya kam" maiminatu ta fada tana dan kallon sassan nata,bata manta when last data shiga sassan nata ba,tun daga ranar itama bata sake sanyata a idanunta ba,sau daya tak dai ta hangota a parking lot na gidan zata fita cikin motarta,saita amsa jakar baba tabawa ta riqe mata,don batajin xata iya shiga sassan matar.

Ko minti uku cikakke baba tabawa batayi ba ta fito,fuskarta babu yabo babu fallasa,bata dai ce da maimunatu komai ba suka wuce inda mota take jiranta.

Maimunatu bata bar gaban motar ba sai da taga fitarsu daga gidan,ta sauke ajiyar zuciya tana jin jiki da zuciyarta babu dadi,ta juyo a hankali ta soma takawa zuwa cikin gidan,tana wassafa zaman kadaicin da zatayi na kwanaki ashirin,har zuwa sanda zata koma makaranta.

Tun kafin maimunatun ta qaraso ita ta ganta,ta zuba mata idanu sosai tana kallonta, yadda ta fahimci ita bata ganta ba ya bata damar kallonta yadda taso,suna sake kusantar juna wata irin fargaba ba ratsa zuciyar unaisan,wanne irin kyau da canzawa yarinyar takeyi?,ba haka tasan fuska da jikinta ba,lokaci guda taga kamanninta na juyewa,tana tashi daga maimunatu 'yar ruga zuwa wata balarabiya daga yankin qasashen larabawa,brown mayafin data yane kanta dashi ya sake taimakawa wajen fidda haske da kuma kyanta,wani dunqulallen abu me tauri ya daki zuciyar unaisa,tayi qoqari qwarai wajen ganin ta dauke idanunta sanda suke gab da juna,ko don gudun kada maimunatun ta ganta amma kuma ta kasa,matsowar nata kusa da itanne ma ya sake haifar mata da wani ciwon a zuciya,kyanta ya sake fitowa fes ga idanunta,lallausan qamshi me aji dake fita daga jikinta,sai taja wani tsaki mai qarfi sanda taga yarinyar ta wuceta ba tare data ko nuna ta gane?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 ta ba bare tayi yunqurin gaidata.

Wani abu ne yazo ya tsaya mata a wuya,me yarinyar ke nufi?,tana nufin wuyanta yayi kauri kenan?,ko tana nufin zata goga da ita ne?,zata amsa sunan kishiyarta?,anya kuwa babu wani abu daya taba ratsa gsakaninta da ja'afar wanda ya sanya faduwar darajarta a idanun yarinyar da har zata iya gotawa bata gaidata yadda ta saba ba?,idanunta ta kulle da qarfi tana girgiza kai,bata fatan ya santa kafin yasan yarinyar,wannan shine abu mafi muni a gareta,indai hakan ta kasance ta tabbatar akwai gagarumar matsala,dole ta samawa kanta mafita da kuma 'yanci,don haka sanda ta bude lafiyayyar motar tata ta shiga,sai ta zaro wayarta tahau kira,a maimakon ta kunnata ta fice kamar yadda tayi niyya da farko.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 50



Itako maimunatu ko daya ta manta da sha'anin unaisa,tunda ta wuceta ta isa sashenta,sai ta kulle falonta abinta,da farko ta rasa me zatayi,don babu wani aiki da zai debe mata kewa,daga bisani ta tashi ta debo litattafanta na makaranta ta soma dubawa,don tunda ta dawo rashin lafiyar da tayin bata barta wannan karon tayi karatun kirki ba.



Bata bar kan litattafan ba sai da aka kira sallar magrib,bayan tayi sallar ta kuma ci abinci sai ta jawo wayarta tahau watsapp,shaf tama manta dashi,kasancewar bata wani saba ba,ya kuwa debe mata kewa sosai,don bata sauka ba sai da aka kira isha'i,tayi isha'in,ta kashe dukka wutar dake falo ta wuce dakinta,kayan bacci ta canza,ta haye gado,sannan ta duba last episode data tsaya a drama dinta ta kunna abarta ta dora daga inda ta tsaya.



Karfe tara harda mintuna ya shigo gidan,ya jima sosai yau a office fiye da yadda ya saba,duk da cewa dama lokaci irin wannan da suke soma shirye shiryen lissafin shekara da kuma tafiya hutun qarshen shekarar yana dan samu jimawa a office din fiye da ko yaushe.



Daga yanda yake takowa kadai zakasan ya gaji tubus,ya tura qofar falon ya shige kansa tsaye,don yasan babu wanda zai samu a falon,sannan ya soma haura samansa kai tsaye,yadan dubi sashen da qofar falon sassanta yake,yadan sasssuta saurinsa kadan kamar xai tsaya,sai kuma yaci gaba da tafiyarsa zuwa saman da dan sasssarfa.



Fridge ya fara isa ya ciro ruwa mai madaidaicin sanyi,sannan ya dawo saman daya daga cikin qawatttun turkish chairs din da suka qawata falon ya zauna,ya bude murfin gorar ruwan ya kafa bakinsa,yanajin yadda sanyinsa da baiyi yawa ba yana ratsa hanjinsa,rabi kawai yasha ya dire robar,ya sunkuya yana sabule takalmi da socks na qafarshi hadi da janyesu gefe,sannan ya miqe yana dauke briefcase dinsa,daya hannun nasa kuma yana sassauta tie din wuyansa,don burinsa shine kawai yayi wanka a yanzun,ko qafafunsa da hannayensa da suka sage zasu samu sassuci



"Oh shit" ya furta a hankali sanda wayarsa ta dauki daddadan sautin ringtone,ya murda handle na bedroom din nasa ya tura ya shiga gefe guda kuma yana qoqarin ciro wayar ya duba me kiran.



"Anni kuma?" Ya fada da dan mamaki a ransa,don yasan ko dazun sai daya biya ta gida,jakar ya wulla saman gado

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login