Showing 90001 words to 93000 words out of 204120 words

Chapter 31 - Gurbin Ido Book One Complete Hausa Novel

ta sani,babu kuma abinda take ganewa,idan ma yace mata boarding school ba lallai ta fahimceshi ba.

A ba zata albishir din yazo mata,don ko a mafarki bata taba kawo hakan ba,bata taba tsammanin haka ba,tunda a society din data tashi bata ga ana hakan ba,cikin ruhinta ta dinga jin wani farinciki da bashi da misali yana kutsawa,ashe dai tana da rabo,ashe dai burinta zai cika?,tana shirin buda baki tayi masa godiya ya fice abinsa,yana fitar ta miqe cikin farinciki,tayi wani dan tsalle,ta qanqame jikinta waje guda tana fadin

"Alhamdulillahi,miyatti Allah" cikin walwala karsashi da kuma kuzari taci gaba da aikin nata,Allah Allah take ta gama ta shirya,batason yaa hisham din yazonya jirayeta,tunda bai gaya mata qarfe nawa zaizo din ba.

Sanda ta kammala girkin unaisa ta shigo,kamar ko yaushe cikin takun taqama isa da jin cewa NA FIKI FA,ta qarasa inda maimunatu ta adana warmers din,tasa hannu tana budewa,kafin ta zaqulo faranti cikin nata kayan kitchen din tasa serving spoon ta fara diba ba tare data ce da maimunatun kanzil ba.

Bata daga kai maimunatun ta kalleta b,don kusan ta saba da hakan,ita ke girkin safe da kuma na dare amma unaisan tana rigata ci,da farko iya cikinta take,ganin unaisan tana diba ya tabbatar mata itama tana buqata,duk da bata taba budar baki ta gaya mata hakan ba,shi yasa idan ta tashi yi takeyi harda ita

"Ina kwana?" Ta gaidata kamar yadda kowanne lokaci take mata,ganin cewa ya girme mata,ita kuma tana mata kallon yaya ne a wajenta,tunda shekaru da tazarar dake tsakaninsu tana da yawa.

Bata amsa mata ba,saima dawowa da tayi ta dubeta

"Daga yau idan kin gama girki,a cikin warmers dina nakeso a dinga xubashi,banason amfani da kayan kowa" ta fadi tamkar me magana dame aikinta.

Maimunatun bata kawo komai cikin ranta ba,hakanan ranta bai wani baci ba,cikin girmamawa ta amsa mata da to,sai tasa kai cikin izza tana fita daga kitchen din.

A kan lokaci maimunatun ta gama komai,ta gyara wajen ta wuce dakinta,daga nan toilet ta fada ta soma wanka.

Yana gaban madubi yana amsa wayar muzaffar, cousin dinsa,kuma daya daga cikin ma'aikatansa dake aiki companynsa na lagos,gyara tie din suit dinsa yake,yana dai daita wuyanta yadda ba zata dameshi ba,ya gama ya dauki comb yana sake gyara qawatacciyar sumar kansa wadda take fidda sassanyan qamshi tare da wani sheqi na musamman da takeyi.

"Okay,zan kiraka idan na iso,ka zama ready,banason jira" ya fada yana jefa comb din inda ya daukoshi tare da gyara hannun suit din nasa wanda aka yiwa wani ratsi daya sake qawata ta tare da nuna ainihin tsadar da take dashi,jikinsa sai fidda qamshin turaren bad boy yake na kamfanin carolina Herrera yakeyi,nan gaban madubin ya zauna,ya janyo sock dinsa ya sanya,sannan ya dauko takalminsa qirar qasar Italy dake daura da inda yake ya saka,sai ya miqe daga durquson da yayi yana furzar da iska cakude da ajiyar zuciya daga bakinsa,hadi da lumshe idanunsa yana tuna shaheeda,baisan dukka irin wadan nan wahalhalun ba muddin suna tare,komawa yake dan lelenta,bata barinsa yayi komai.

Karar da yaji cikin wayarsa ya sanyashi hanzarin duba fuskar wayar,sai ya miqe yana daukan wayarsa,ya kuma janyo trolly dinsa zuwa qofar dakin,yana dora handle dinsa a bakin qofar unaisa tana turowa itama.

Da kallo kadan ya bita dashi bayan ya janye mata baya,tana sanye da wata doguwar riga mai budadden hannu silk material butter color,tayi ado sosai wanda ya bayyanar da zallar hutu da jin dadin data samu tun daga gidan mahaifanta,saboda yadda farar fatarta take a kwance very smooth,bakinta sai qyallin lip gloss yake,tana tauna chewing gum a hankali.

"Gud morning dear" ta furta tana murmushi tare da sake takowa gabansa,sai ya dan goce kadan yana amsa mata can qasan maqoshinsa

"Morning" idanunta ta sauke kan akwatin hannunsa,da alama tafiya zaiyi,wanda ko alama itakam batasan da zamanta ba,tadan bishi da kallo sanda ya sanya hannu ya bude aljihun gaban trolly dinsa,kudade ya ciro,ya matso daura da ita kadan ya ajjiye yana cewa

"am going to travel somewhere,zaku iya kiran number dake jikin nan whenever you need something" binsa tayi da kallo sanda ya gama jawabinsa,ya kuma taka cikin cikakkiyar nutsuwarsa ya soma barin falon

"Ba wannan nake buqata,ba kudi nake so ba,ba kuma shine ya kawoni ba" cak ya tsaya daga tafiyar da yake,hannunsa daya na soke a aljihun wandon suit dinsa yana kal???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?lon qofa ba tare daya juyo ba,kamar kuma bazai juyo din ba,kamar yadda kuma yanayinsa ya nuna baida niyyan yin magana,saidai kuma faaida trolley din yayi,ya waiwayo ya kuma fara dawowa,cikin wani irin yanayinsa dake saurin sanya karaya da karyar da duk wata zarra jin kai da jin isa na 'ya mace ya aza mata idanunsa,a gabanta ya tsaya yana dubanta,ya sake sakaya daya.hannun nasa dake waje cikin aljihun wandon nasa,yadan raba qafafunsa kadan
??

"Me kike da buqata?" Ya furta with husky voice,wadda bata sauka ko ina ba sai tsakiyar zuciyarta,ta kuma nada ajiyar wani yanayi mai tsauri ga zukata.

Nata idanun ta daga da niyyar gaya masa abinda yake ranta quru quru,saidai inaaa,zarrar ba daya bace,don kuwa kasa qarasar da kallonta tayi izuwa fuskarsa,saita zube idanunsa a qirjinta,wanda iya nata tsahon kenan

"Iya abinda zaki samu shi nake baki,indai wannan jikin kikeso,to a shawarce ki koma gida,don abune da bazai taba samuwa ba wajen wata har abada....." Daga haka ya juya abinda hankali kwance,ya riqe trolley dinsa ya fara turata waje,sai a sannan yace mata

"Idan kin gama abinda zakiyi kina iya ki rufemin dakina" sai ya qarasa tura akwatinsa ya fice.

Wani wawan kuka ga saki sannan ta sulale a waje ta zauna,ya Allah,itakam wanne irin abune J yakeso tayi?,wanne abu zatayi taja hankalin ja'afar,saita kifa kanta saman kujerarsa tana sheshsheqa.

A shirye tsaf cikin Egyptian hijab ta fito ruwan golden yellow,tayi matuqar kyau qwarai,kyakkyawan fuskartan nan me dauke da wani lafiyayye kuma boyayyen kyau tayi fayau tsakiyar fuskar hijabin.

Yana zaune cikin motar w farfajiyar gidan,don bai shiga ciki ba tunda yasa daya daga cikin masu gyaran farfajiyar yayi mata sallama,wayarsa na a hannunsa yana chart,ya bude qofar mazaunun gaba dake daura dashi,takun tafiya ya sanyashi daga kansa,ya sauke su ga madubin dake gefan murfin motar,fes ta fito a ciki,tana takawa cikin nutsuwa inda yake tsimayinta din.

Gabansa yadan fadi,ya lumshe idanunsa yana sauke ajiyar zuciya,kana ya kauda dubansa daga gareta,kasancewar yasan haramcin aikata hakan a yanzu,har yau yana jinta a ransa,kuma har yau yana jin zafin rasata,tun daga randa zai shiga dakin anni yaji tana masa tayin auren yayan nasa yakejin wani abu ya tsaye masa a wuya,saboda tabbacin rasatan da yayi,amma yayi namijin qoqarin ganij ya fidda komai daga ransa,tunda yana da tabbacin ya rasata rashi na har abada.

Baisan me yahau kan yayanshi ba daya kasa gane baiwar da Allah yayi masa,ya kuma yi masa musaya na abinda ya rasa,duk da baisan gaibu ba,amma yana da yaqinin idan maimunatu batafi marigayiya quality ba,to tabbas marigayiya ba zata fita ba,ko yanzun driver yaji yana zancan ya kaits makarantar,sai yaga rashin dacewar hakan yace zaije.

Sauke qafafunsa yayi ya gyara zamansa gami da ajjiye wayar sanda ta iso dab da motar,ya sanya hannu yana laluba maqullin tare da amsa sallamarta sanda take yunqurin shigowa cikin motar cikin nutsuwa da kamewa

"Ina kwana ya hisham?" Murmushi ya sakar mata

"Haba anty moon,ai kya bari na fara gaidaki dai ko?,matar babban wa yayace itama" kunya ce sosai ta kamata,tayi qasa da kanta tana yaba karamci da kirkinsa,shi kam halinsa yasha banban dana dan uwansa,tasan hakan tun ba yau ba,tun tana gidan dr.

Motar ya kunna suka fito daga unguwar gaba daya suka hau main titi da zai kaisu pen resources,rashin sabo ya haifar da shuru a tsakaninsu,duk da yaso yadan jata da hira ko zata sake amma sai ya fasa,sabon album na wani waqar hausa ya sanya musu,duka sai sukayi shuru kowa yana saurare,musamman maimunatu da batasan waqoqin ko kuma mawaqin ba,ta dinga bin duka baitukan cikin zuciyarta tana nazartarsu,sai taji waqoqin sun mata,suna kuma motsa mata wani da wani abu ckin zuciyarta,duka baituka ne da suka shafi soyayya da qauna,masu taba zuciyar duk wanda yake cikin soyayya.

Sanda suka isa makarantar ayi mata dukka abinda ya dace,an kuma ce next week ne zasu fara daukan sabbin dalibai kamar yadda ja'afar ya gaya mata,sosai farincikinta ya nuna,har hisham yana tsokanarta,ya zaci hukuncin da yayan nasa ya yanke bazai mata dadi ba,sai kuma yaga akasin hakan,tabbacin mutum ce ita mai tsananin son karatu.

Kasancewar batasan hanya ba yasa bata gane inda ya nufa da ita ba sai da suka je,gidan anty maama,abinda ya yiwa maimunatu dadi qwarai,ko babu komai zata miqe qafarta ba zata koma waccan kurkukun da wuri ba,karon farko data soma zuwa,qawataccen gida mai bala'in daukan hankali da nuna gayu da kuma dukiya,cikin tafkeken falonta na alfarma ta saukesu,farinciki fal zuciyarta,ta rasa wacce irin sauka zatayi musu,take tasa masu aikinta suka cika musu gabansu da kayan ciye ciye har babu adadi

"Amma dai ba daga gida kuke ba,don nasan J bazai barku ba" anty maama ta tambayi jabir sanda maimunatu ta shiga toilet don tayi futsari ta kuma hado da alwalar sallar azahar,saboda mukhtarinta ya shiga,yana bare ayaba mutuniyar tasa ya amsa mata

"Daga makaranta,na kaita sun mata interview"

"Makaranta?,wacce?"
"Pen resources boarding"

"What?" Anty maama ta fada cikin mamaki tana kallon hisham,kai kace shine ja'afar din

"Bama day din ba?" Ta sake tambaya

"Yadda dai kikaji haka ne" ya amsa mata yana tauna ayabar,don shima bashi data cewa akan al'amarin J din

"Meye hakan yayi kenan?,mtseew lemme call him,wannan sam bai dace ba,yana son yayi avoiding nata ne akwai a fakaice,ya Allah.....wanne irin mutum ne J din?,kuma anni ta sani ta barshi?"

"To ya zata masa,badai matarsa bace?" Wayarta ta janyo ta fara laluban layin jaafar din,wanda a dai dai lokacin yana kwanye bayan lafiyayyar motar company dinsa datazo daukansa,a nutse ya daga wayar yana duba me kiran,sai ya daga ya kara a kunnensa.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 39

*************Karfe biyar da rabi ne na yammacin ranar lahadi,cikin dakin kwanan dalibai na makarantar,maimunatu ce zaune saman gadon afrah,ta baje litattafai kai kace duka litattafan data mallaka ne a gadon.

Sanye take da chiffon fabric,material ne da aka yiwa dinkin simple gown brown color da ratsin coffe,sai milk color da akayi adon flower din jiki,dinkin dogon hannu ne,amma daga tsintsiyar hannun an sanya masa roba,abinda ya rage fadin hannun kenan ya zama tattara,abinda ya zama kamar wani ado na musamman,saman kanta wani silk v-shape vail ne data yafashi ta kuma daureshi qasan habarta,fuskarta da labbanta sai glowing suke tamkar ta shafa musu wani abun,saidai kuma ba abinda ta shafa din,nutsuwa da hutu data samu ne koda yaushe yake qara bayyana sirrin kyanta.

Tsaki taja ta ajjiye pen din hannunta tana lanqwasa yatsunta,karatun exams take,saboda rana ita yau zasu zana jarabawar da daga ita sai ss two,ta riga taci alwashin wannan karon sai ta kawo first position da izinin ubangiji,tunda jarabawar farko tazo ta sha biyar,ta second term tazo ta uku,wannan karon ta daya take buqata.

Kanta tadan daga sama kadan,inda afrah tun dazun ta haye gadonta tana waya,abinda yasa sukayi exchanging gado kenan,a boye take wayar,saboda duk lokaci irin wannan ana karbar wayoyinsu ne sai sun kammala jarabawa kuma.

Har ta bude baki zatayi magana afran kamar ta sani sai gata ta motsa tana saukowa,harara maimunatu ta bita da ita,sai ta bushe da dariya tana fadin

"Am sorry moon,afwan,bazan iya skipping amsa wayar nan bane"

"Bansan me yake damunku ba afrah,exam around the corner amma ta waya kike?"

"Ke kuwa kinsan dadin soyayya?" Tambayar ta tuna mata da himunta,sai kuma tayi hanzarin yin ta'awizi

"Ban sani ba" ta amsa mata kai tsaye saidai cikin gatse,tana kuma miqewa tare da zura slippers dinta,dariya afrah ta saki,duk da ta fahimci gatsen ne

"Naga alama ai,tunda duka tarin English novels din dana baki wancan hutun haka kika dawomin dasu,banga alamar kin karanta kowanne a ciki ba"

"Kanki akeji,don na karanta kuma sai nazo na zauna ina baki labarin abinda na tabbatar kema kin sanshi" ta qarashe maganar tana shigewa toilet dinsu,saidai a zuciyarta afran ta motsa mata tasirin da labaran sukayi mata,kuma har yau idan ta tuna sai taji shauqin,saidai kuma bata son abinda zai shiga karatunta,shi yasa bata sake neman wani ba,tana jiyo afran tana mata shaqiyanci

"To ban taba jin sunan kowa a bakinki ba idan ba ya hisham ba,ga waya kina da ita amma kinja kin aje,ke bakya zancan kowa fa a rayuwarki,dole nace bakisan dadinta ba" koda a dakin take ma ba zata tanka mata ba bare tana bandaki,don tana da attitude na qyaliya sometimes,ita afra ta saba da wannan,tace ta saba zama miskilai irinta,haka sister dinta take,da itace zamansu zai bada kala sosai.

Har ta gama fitsarin data shiga yi ta dauro alwala bata sake jin afra tace komai ba,don haka ta bada a ranta ta fita ne a dakin,don indai ta fara dauko yi mata shaqiyanci irin wannan.....duk da itama gwanar miskilanci ce idan taso,amma bata shuru da wuri,wani lokaci har sai su fatima sun shiga maganar take barta ta sarara.

Ga mamakinta sanda ta fito afran na dakin,tana zaune inda maimunatun ta tashi,wani littafi ne a hannunta,amma kuma ba shi take karantawa ba,wata takarda ce riqe a daya hannun hagun nata,ta tattara hankalinta kacokam a kanta,kamar zata koma cikinta,yadda taga afran ta nutsu yaja hankalin maimunatun,sai ta fara takowa a hankali itama tana duban hannun afran.

Tana sake matsowa tana kuma sake fahimtar meye a hannun afran,invitation ne,invitation din kuma bana kowa ba face nata,na daurin aurenta,gabanta ya fadi sosai,tsoro kuma ya tsarga mata,ya akayi IV din ya shigo cikin kayanta?,litattafanta na karatu?,bayan kusan gaba daya a gembu tabarsu tun randa kawu sama'ila ya bata ta danqawa inna saratu bata taho dasu ba.

Cikin matuqar dakiya maimunatu ta miqa hannu zata karba IV din tana cewa

"Ba wannan aka ce ki karanta ba,litattafan makaranta zaki duba" gocewa tayi da katin yadda maimunatu ta gaza kamashi,sannan ta watsa mata harara

"Anqi ayi karatun,sai aukin cewa mutum yayi karatu amma ashe bada zuciya daya kika daukeni ba moon?" Afra ta fada kamar idanunta zasu fado

"Me kuma ya faru?" Tayi tambayar kamar batasan komai ba

"Indai masu irin dabi'arki ne ai zasuyi fiye da hakan,wannan katin daurin auren waye?" Tambayace takai tsaye,wadda babu hanyar da zata kauce mata,suna dai gashinan ya fito baro baro a jiki full name nata,tace sunan waye kenan?.

"Yanzu har a miki aure cikin hutun nan amma koni ki kasa gayamin moon?,ashe yadda na daukeki daban yadda kika daukeni daban,na gode,na gode sosai" ta fadi tana miqewa daga gadon bayan ta ajjiye mata katinta.

Da hanzari ta kamota tana dubanta

"Ni ba cikin hutun aka dauramin aure ba,da aurena na shigo school din nan" amsar tata ta bawa afra mamaki matuqa,ta kuma taimaka wajen sauke fushinta,mamaki ya maye gurbin hakan.

Janta tayi suka zauna tare,sannan ta dubi afran

"Sai da nayi watanni da aure sannan na fara zuwa nan" a nutse ta warware ma afrah komai,babu wani abu data boye mata,don itama tana jinta da gasken gaske har cikin zuciyarta,asali ita bamai yawan magana da dogon surutu bane,kuma tun zamansu tare suka fuskanci ba kasafai hirar samari data aure take burgeta ba yasa basu fiya irin wannan hirar ba muddin tana cikinsu,hakan yasa babu wani abu da ya tado maganar bare su sani.

"Captain ja'afar marwan akko?,shi na gani a rubuce,da gaske shine mijinki?" Afra ta fada wani murmushi na fita saman fuskarta,kai maimunatu ta jinjina mata

"Dama ance yayi aure,mata biyu,ashe harda aminiyata ta gobe a ciki, congratulations.....congratulations once again sister,kin ciri tuta,ke dashi kun tsinci dami a kala" ta qarashe maganar tana duban idanun maimunatu,fuskarta fal da murmushi,maganar ta bawa maimunatun mamaki,ta waro idanu tana duba afrah ba tare da tace komai ba,ita kuwa batayi qasa a gwiwa ba ta dora da

"Duk yadda zan fasalta miki kyanki haduwarki da kuma nutsuwarki ba zaki fahimta ba maimunatu,tunda a kanki ake magana,kina da dukkan wani qualities da nake da tabbacin babu namijin da zaisan kina dasu ya iya dauke kansa a gareki ki wucess,infact.......ba namiji ba,koni macen na gama yiwa brother na kamu,ashe J ya riga dsya qwamshe wannan rabon" takai qarshen maganar murmushinta na sake yawa zuwa dariya dariya,dole kuma ta dora murmushi kan fuskar maimunatun,tasan halin afrah sarai,duk da cews ba wai yaune ranar farko da ta fara ko suka fara kodata ba ita dasu ayman

"Well......abinda yasa nace ke kuma kin tsinci dami a kala?.....hmmmm..... captain ja'afar.......matashin da yake sanya razani da yawa a zukatan 'yammata,matashin da ya sanya idanuwan 'yammata da yawa zubda qwalla,matashin da ya sanya zukata da yawa cikin bege da qauna mai tarin yawa,ciki harda cousins dina su biyu,wanda har yau basu debe tsammani a kansa ba" ta qarashe tana sakin dariya,tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login