Showing 114001 words to 117000 words out of 204120 words

Chapter 39 - Gurbin Ido Book One Complete Hausa Novel

da take dauraye kwanukan da suka gama amfani dasu,ta goge jikin towel na kitchen din,sannan ta fito da niyyar budewa ba tare da tunanin komai ba.

A hankali ta kama handle din ta bude,abu na farko daya fara marabtarta qamshin jikinsa ne,wanda acn da aka balbalawa babban falon ke tunkudo qamshin da gaske zuwa nata falon.

Saman kanta idanunsa suka fara sauka,wanda dankwalin kanta ya zame xuwa rabin kanta,abinda ya bawa gashinta damar bayyana sosai,sai ya zame idanun nasa ya janyesu gefe,tasa dukka hannayenta biyu tana dafe dankwalin dake shirin faduwa daga kanta gaba daya,ta kuma janye qafafunta da taji suna sarqewa zuwa gefe ta bashi hanyar shigowa,a sace idanunta na binsa da kallo,cike da mamakin shigarsa ta yau ta zallar bahaushe,cikin wani lallausan farin yadi me shara shara,wanda hatta fara qal din singlet din dake jikinsa sai data bayyana,ya giftata ya bar mata qamshinsa wanda batasan me yasa take samun wata nutsuwa ta musamman ba duk sanda zata shaqeshi.

Kamar wata mara gaskiya ta rabe a bayansa

"Ina kwana?" Ta fadi a matuqar ta kure,nadamar yadda ta fito haka gaba gadi ba tare da tambaya ko sanin waye ba tana shigarta.

Gaba daya ya waiwayo zuwa inda take tsayen,hannayensa dunqule cikin aljihun rigarsa,ya zube idanunta da sukayi wani irin laushi saman qirjinta dake bayyana shatin baqar brazier dinta,yadda yake qoqarin janye idanunsa daga wajen haka zuciya da idanunsa ke ingizashi zuwa ga ci gaba da kallonta,yana jin kamar wani mayen qarfe aka dasa ma idanun nasa a wajen,yayin da wani abu me kama da tsarguwa ya saukarwa maimunatu jin shuru bai amsa ba,cike da jarumta da son tsira da mutunci ya raba idanunsa daga wajen yana lumshesu

"Karki sake irin wannan gangancin,kinsan waye da kk bude qofa batare da kin tambaya ba?" Yayi maganar yana sake qarewa shigarta kallo,hatta sambala sambalan qafafunta sun fito sosai saboda rashin tsahon wandon,yana kallonta 'yar qarama a gabansa,yanayin da ya tuna masa da zamanin amarcinsa da shaheeda, she's always like this......under eighteen,sannan taci gaba da zama da dabi'antuwa kamar yadda yakeso ta kasance masa,ta ina ta kuma yaya zai maida GURBINTA?.

"kayi haquri" kalaman suka sauka a kunnensa dai dai da irin yadda shaheeda take fada masa,bata kuma taba canza kalamanta da haka ba,koda shi ya bata mata,yakance

"Uhnnnn.....u are killing me shaheeda,ko yaushe kayi haquri?kayi haquri,You don't want to make excuses for yourself?" Daga kai maimunatu da sauri tayi ta dubeshi jin abinda ya fada,sai shima ya maida idanunsa kanta ganin yadda take kallonsa,sai a sannan ya karanci ashe a sarari yayi maganar,saidai can qasan maqoshinsa ne,janye idanuwansa yayi yana dan tsuke fuska kadan,ya akayi maganar ta fito fili?

"Shaheeda" takira sunan a ranta tana son tuno inda tasan sunan,ummin amna?,kwanyarta ta bata.....kafin ta gama tantancewa muryar baba tabawa ta yiwa falon tsinke.

Sai a sannan ya dauke kansa da shanyayyun idanunsa gaba daya daga dubanta ya maida ga baba tabawa,wadda har tayi niyyar juyawa a yanayin data gansu a tsaye,cikin sakanni ta karanci wasu qananun abubuwa a fuskar kowannensu

"Manya,har an fito?" Kai ya jinjina ya kuma ranqwafa yana gaidata,ta amsa cike da kulawa,ya sanya hannunsa a aljihu ya fiddo kudi ya ajjiye mata

"Ah.....ai an kammala karin safe,ka jira a gabatar maka" bata saurari amsarsa ba ta juya ga maimunatu

"Suna kitchen fa" ta fadi mata,kamar wadda ke jiran umarnin barin wajen tayi gaba tana qara hanzari,gaba daya kamar tayi layar zana haka take ji,da so samu ne dakinta ya kamata ta biya ta fafa dauko hijabi,to amma kuma baba tabawan fa?,hakan zai zama kamar wani rashin girmamawa ne a gareta,dole ta wuce zuwa kitchen din.

Sanda ta dawo falon a tsaye ta sameshi yana saita agogon hannunsa,qarin tashin hankalin baba tabawan bata nan a falon,sau daya tak ya daga kai ya kalleta ya maida ga abinda yakeyi,saita wuce dining ta jera komai,kafin tayi magana taga yana takowa zuwa wajen,yaja kujera daya ya zauna a kai,har yanzun bai kuma dubanta ba.

"Me za'a zuba maka?" Tayi tambayar tanason riqe rawar da muryarta keyi,don gaba daya ta gama rudewa,Allah Allah take ta gama serving nasa tabar wajen

"Anything" ya amsata a taqaice,warmers din ta fara qoqarin budewa,saidai duk wadda takama zata bude saita kasa,saboda santsi da kuma yadda jikinta yayi weak,tako ina a jikinta takejin idanunsa na mata wayo,tayi Allah wadaran shigar da kuma yadda ta zauna haka yau din babu ko dan baby hijab din da take amfani dashi ko da yaushe,a nutse yake karantarta,kafin ya kauda idanunsa yana latsa wayarsa,ata qarshe ne ya daga hannu da niyyar karba y bude ganin ta kasa,incidentally hannunsa ya sauka saman nata hannun,abinda ya haifar masa da wani irin shock a jikinsa,yayin da ita kuma tashin farko jikinta ya dauki rawa,ta kuma zame hannun nata da sauri taja baya kadan,yi yayi kamar baisan abinda ya faru ba,a nutse ya dauki bowl da serving spoon ya fara diban farfesun kayan cikin dake cikin warmer din.

Tsoronta gaba daya ta dunqule ta kuma hadiye,saboda tuna warning nata daya taba yi,ta matso a kasalance,ta jawo flask na tea data hada da kanta da wasu hadin kayan shayi na musamman data shekaran jiya tana cikin browsing ta fara zuba masa,wani irin qamshi me dadi ya gauraye wajen,har sai da yaja iskar data kwaso qamshin har cikin hunhunsa,deep inside kuma yawunsa ya fara tsinkewa,ta dauko kwalin suger ta dauki one cube ta saka,ta sake debowa zata qara sanyawa kenan yace

"Enough,ya isa" gaba daya kwalin sugar din ya subuce daga hannunta don dama a tsorace take,suka fara rige rigen afkawa cikin kofin tea din,abinda ya bawa ruwan zafin damar yin fallatsi,ya dawo mata hannayenta,taja baya da sauri tana jin zafin saukar ruwan zafin na ratsata sosai har kwanyarta.

Spoon din hannunsa daya fara diban farfesun ya ajjiye,ya hade yatsunsa waje guda yana kallonta,ta hada gumi tana yarfar da hannun,da alama ruwan ya tabata sosai,har ya dauki spoon din xaici gaba da cin abincinsa sai kuma ya kasa,komai tayi shige yake masa da silly attitude na shaheeda data sha yi masa farkon aurensu

"seat here" yayi maganar yana jan kujerar dake daura dashi,idanunta da suka tara hawaye ta daga ta dubeshi dasu,kamar wadda ke shirin sakin kuka,sai ta tako a hankali kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki,ta zauna a darare saman kujerar tana dubansa

"Let me see" ya fada yana miqa mata hannunsa,idanunsa cikin nata yana kallon yadda ta narke gaba daya,gumi kuma ya tsatstsafo saman goshinta.

Sai data maida dubanta ga lallausan tafin hannunsa kamar me tsoron wani abu,sannan ta miqa masa hannun nata a hankali,ya miqa nasa ya riqe yatsun nata.

Qaramar qara ta saki da siririyar muryarta me zaqi wadda ta ratsa dodon kunnensa da kyau,idanuwansa ya rintse sosai sannan ya budesu ya zubesu saman fuskarta wadda tuni hawaye sun fara mata zarya,ya dinke fuskarsa tsaf yana ci gaba da tsare gida

"What is that?,zaki kashemin kunne ne?" Kai ta girgiza,gaba daya hawaye ya wanke mata fuska,ta wani narke cikin wani yanayi daya darsa tausayinta cikin ransa,sai ya janye idanunsa yana qoqarin kawar da wannan ya mayar kan hannun nata.

Da sauri ya janye yatsunsa daga inda ya riqe din,saboda yadda wajen yayi jaa,da alama a wajen ta qone din,kafin yayi wani abu baba tabawa ta iso

"Lafiya dai ko maimunatu?" Tayi tambayar tana dubanta

"Subhanallahi" baba tabawan ta fada sanda taga hannun nata

"Garin yaya?" Ta jefa mata tambayar,rashin sanin amsar da zata bata yasa ta maida dubanta ga ja'afar,dauke kansa yayi kamar baya wajen,kamar bashi take kallo ba,kujerarsa ya sake jawowa gaba kadan,ya zamana dab da ita sosai

"Silly girl" ya fada qasa qasa,sake mele baki tayi zata sake sakin kukan,kamar yasan da haka ya kuma daga shanyayyun idanunta acikin nata,sai tayi hanzarin kulle nata idanun,ita kadai tasan me yake haifar mata idan ya mata irin wannan kallon,yana qara mata razani a kansa da kuma wani irin kwarjini da takeji kamar zai sata narkewa a wajen.

Sannu baba tabawa ta matso tana mata sanda ta duqufa yana mata tofi a hannun nata,ya kwashi kusan minti talatin yana mata tofin babu tsayawa,sannan ya zare hannunsa daga cikin nata

"Sannu maimunatu" baba tabawa ta fada fuskarta na nuna alhini,idanunta akan hannun nata da yayi jaa abinka da farar fata,kanta ta gyada

"Ko za'a kaita asibiti?"
"no need,bazai komai ba....in sha Allah,zanma hisham magana,zai prescribing mata pain killer,sai a kawo,she will be okay"

"To Allah yasa"baba tabawa ta amsashi,duk da bata gane komai da komai da yake fada ba

"Ki cire hijabin kisha iska" baba tabawa tace da ita,sai ta noqe taqi motsawa,ta yaya zata fidda hijabin data saka saboda yiwa jikinta shamaki,ya fuskanci sarai saboda shi din taqi motsawa,sai ya miqe kawai yana kwashe wayoyinsa ya xuba a aljihunsa

"Manya....ai ba abinda kaci" kai ya gyada

"Am okay,thanks" daga haka ya juya yana barin falon,yana kuma sanya hannunsa a aljihunsa yana laluben key din motarsa,don yau a masallacin wuro bokki yakeson yin ssallar juma'a,yanason kuma samun gaba gaba,ya tabbatar abbi ma yana ciki yanzu haka.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 46


Tunda ya dawo gidan baba tabawa tasan ya shigo,ta kuma gayawa maimunatu a fakaice indirectly cewan ya dawo din,ta yita zuba ido taga ta fita yi masa sannu da zuwa ko wani abu makamancin hakan amma bata gani ba,tunda tasan unaisa bata nan,dazun da ta zaga baya tana tsinkar musu lemon tsami taga fitarta,babu kuma alamun ta dawo.

Abun nata cin ran baba tabawa,har zuwa lokacin da suka zauna cin abincin dare,ta dubi maimunatu

"Waiku kam.....haka akewa miji?,ya fita ya wuni fafutukar nema muku abinci,ya dawo amma ko arziqin sannu da zuwa a gaya masa bai samu ba?,sa'annan ace abincin da zaici ma a gidansa ya gagaresa a kasa sammasa?,anya kuwa maimunatu?,ta yaya zaki bata dukka yardar da anni ta baki?,ta dora duk wani fatanta da burinta akanki amma kina neman bata kunya?" Qasa tayi da kanta,tana jin kunya da nauyin suna kamata tun gabanin xancan ma yaje kunnen annin,tabbas tayi kuskure da gaske,to amma kuma shi dinne.....ba irin sauran mutane bane,batasan ta yadda zata fuskanci bahagon mutum irinsa ba,yau inda ace shi din kamar hisham yake to da da sauqi sauqi,amma.....he's totally different from what they are seeing about him,ba abu bane mai sauqi tunkararsa

"Kiyi haquri baba,baice yana buqata ba"

"Kin taba nuna damuwa ko gwada kaiwar bare ki Fatima hakan?,bari na fito miki a mutum maimunatu" baba tabawa ta fada tana gyara zamanta,abinda ya sanya maimunatu tattara hankalinta waje daya

"Gaba daya na fuskanci inda zaman aurenki ua dosa,bansan na abokiyar zamanki ya yake ba,a gajarce zan gaya miki,ba'a yankewa mutum hukunci ba tare da ka ma'amalanceshi ba,ki sauya,ki zama kamar kowacce mace a gidanta,ki sauke naki hakkin da nauyin,ko meye zai taso a gaba....ko meye zai biyo baya zaki fita a ciki,kiyimin alqawari daga yau zaki canza,inason ganinki kamar kowacce macen auren maimunatu,ina miki sha'awar hakan,na san ja'afar,yana da zuciya me kyau wani abune daban ya canzashi,kuma ina kyautata zaton duk wanda ya aro wani hali da ba nashi ba,rabashi dashi abune me sauqin gaske,zaki canza maimunatu?" Kai ta gyadawa baba tabawa a hankali,tana sake jin nauyi,saboda tana ji a ranta da gasken butulci take son tayi,tana qasan inuwar alfarmarsu,ta samu rayuwa me kyau me cike da gata,sannan ta kasa ciyar da dansu abincin da shine ya siyo shi?,bayan duka duka bata zaman wata biyu ma cikin gidan?.

Da kanta baba tabawa ta shirya abincin cikin wasu sababbin warmers masu kyau

"Dauka maza kikai masa,daga yau babu ruwanki da abokiyar zamanki,duk sanda kika fuskanci yana da buqatar abinci kuma bata nan,bata kuma bashi ba,koda ba ranar girkinki bane dauka ki bashi,ke Allah zai bawa ladan".

Daki ta koma,ta zabo hijab cikin hijabs dinta ta sanya,ba abinda hijab din keyi sai qamsin turaren wuta na kaya,ya kuma amshi fatarta qwarai,kalar blue black,da kallo baba tabawa ta bita sanda ta fito,kamar tace mata ta canza mayafi a maimakon hijab din,amma sai kuma ta canza shawara ta qyaleta.

A hankali ya sauke ajiyar zuciya,sannan ya tura hannunsa cikin sumarsa yana yamutsata,hakanan yaji kawai komai baya maaa dadi,sai yakai hannunsa guda daya ya rufe system din dake gabansa ba tare daya damu da yayi shutting down dinta ba,duk da muhimmancin hakan,sai ya koma a hankali ya jingina bayansa da kujerar da yake zaune,ya kuma hade yatsunsa waje daya yana lumshe idanuwansa.

Wani irin bugu zuciyarta take sanda takai step din qarshe na benan,tana ji kamar ta koma,amma kuma idan tayi hakan bata kyauta ba,kamar ta wofantar da maganar baba tabawa ne,ci gaba tayi da takawa cikin tsoro da fargaba,tana tafiya kamar ba zata kai qofar da zata sadata da ainihin falon ba.

Sanda ta isa qofar sai taja ta tsaya cak,ta runtse idanunta da qarfi,a karo na farko zata fara taka sassansa,batasan da wacce fuska zata kalleshi ba,tsoronsa yana nan fal cikin zuciyarta,tanason baiwa kanta qwarin gwiwa,ta dora hannunta saman handle din,ta runtse idanunta gami da dauke numfashinta sannan ta tura ta sanya kanta.

Daga inda yake zaune miqe da qafafunsa saman table din gabansa idanunsa a rufe yaji an motsa qofar,saidai duk da haka hakan bai sanyashi motsawa ko bude idanunsa ba,a zatonsa unaisa ce,wadda ta gaza haqurin zuwa wajensa da ziyartarsa lokaci lokaci,bayan ya riga daya tabbatar mata gaskiyar abinda ke ranshi gami da bata zabi.

A hankali sassanyan qamshin da ya hanashi sukuni wunin yau,ya kuma wuni dashi cikin jikinsa ya fara cika masa hanci,ya kuma gauraye da sallamarta cikin siririyar muryarta din nan mai dauke da wani amo na musamman,ba tare daya shiryama faruwar hakan ba ya soma bude idanunsa da suka sauya launi saboda mintunan da suka dauka a kulle.

Fes ya sauke idanunsa a kanta,cikin shigar da yawanci shaheedansa ke yinta,shigar da yakan tsokaneta da ita zamanin da suna raye

"I want to see my wife gani na haqiqa..... please madam, remove it" murmushi take jifansa dashi,sannan ta zare din tana fadin

"Am all yours,and belongs to you".

Haka kawai ya samu kansa da gaza dauke idanunsa daga kanta,wani abu na masa yawo tsakiyan kai kamar ana yamutsa kwanyarsa,duk da cikin hijab take amma hoton dazu ke masa yawo cikin idanunsa,ya qureta da kallon dashi kansa yasan idan da ace ita din ba halaliyarsa bace ya kauceea koyarwar addini,baisan me ya sanya masa qulafucin kallonta haka ba.

cikin matuqar juriya da kuma dauriya take bawa kanta confidence,abun dazunke tabata,tana jin kakar qasa ta tsage mata ta shige,ko kuma tayi fiffike ta fice a dakin,ta iso gab dashi kana ta sulale a gabansa ta tsugunna,abinda ya bawa turarenta damar isa gareshi da kyau

"Barka da dare" tayi maganar da wani irin tune,sai ya tashi ya zauna sosai yana sauke sambala sambalan qafafunsa daga saman table din zuwa qasa

"Barka" ya amsata a taqaice,bata tsaya jiran cewarsa ko wani abu ba ta fara fidda warmers din,ya bude baki kaman zaiyi magana kiran jabir ya shigo wayarsa,sai ya maida hankalinsa ga amda wayar,inda ita kuma hakan ya rage mata wani mugun nauyi da takeji an aza mata tun farkon shigowarta falon,rawar da hannayenta keyi suka ragu,ta fidda koma ta kuma yi serving dinsa ta jera komai cikin nutsuwa,sai ta miqe ta fara takawa zata bar falon,cikin ranta cike da fata da addu'ar kada wani abu ya tsaidata.

Dan binta yayi da kallo kadan yana karantar tafiyartata duk da amsa wayar da yakeyi,tamkar wata me tafiya saman rairayi ko yashi mai laushi,duk da bai iys ganin qafafunta saboda hijabin da ya saukar mata,amma kuma yanayin tafiyarta kawai zai gaya maka qafafunta akan tsari suke,janye idanunsa yayi yana jan dan qaramin tsaki,tsakin da ya bayyanarwa jabir ta cikin wayar

"Lafiya?" Ya tambayeshi a taqaice

"No... it's not a matter,ina jinka" yayi maganar yana sauke dubansa ga abincin,wanda tuni yaja ra'ayinsa,bai kuma iya gama wayar ba ya zamo a hankali daga saman kujerar,ya sanya spoon din data ajjiye masa ya diba ya fara ci.

Har cikin ransa yaji nutsuwa da abincin dari bisa dari,dama baba tabawa zabinsa ce akan abinci,don haka duk wani tsohon cinsa ya tashi,yaci abincin sosai fiye da kima,ya kuma kwantar da tsohuwar yunwarsa,haka nan ya dinga jin wata nutsuwa na saukar masa,ba shakka samun abinci gamsashe ma rahama ne,duk wata gajiya da kasala da yake ji fiye da rabinta ta kama gabanta,sai ya samu kuzarin yin aikinsa fiye da dazun,ya sake kunna system dinsa,yaci gaba da nazarin meeting dinsu na dazu wanda tuni PA dinsa yayi documenting komai ya aiko masa,ya dinga cire kusakuran da yayi a dazun,lokaci lokaci yana dan jan tsaki,baisan ya akayi gaba daya dan qanqanin abu irin wannan ya dagula masa lissafi ba,saidai duk da hakan a yanxun ma idan ya tuna sai yaji tsigar jikinsa tadan zuba,yakan dan lumshe idanunsa kadan kana ya bude ya ture komai yaci gaba da aikinsa.

Binta da kallo baba tabawa tayi lokacin da tayi sallama take shigowa falon,sai taci gaba da kallonta baki bude,har ta iso tana zubewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login