Showing 63001 words to 66000 words out of 204120 words

Chapter 22 - Gurbin Ido Book One Complete Hausa Novel

da hafsat da kuma laila,don haka annin tace a barshi zuwa sanda zasu gama din watanni shida nan gaba masu zuwa.

********Dai dai lokacin da suke shigowa farfajiyar gidan sanye da hijabansu na makaranta suna taba hira,motar dake fake a parking lot na gidan ta tsaya,mamallakiyar motar ta budeta ta fito.

Zabgegeyar farar bafulatana,fara tas,wadda kamanninta da haj aishatu ta nuna qwarai,sanye take da wani danyan lace daya kwanta a fatarta,komai na jikinta matching ne,jikinta ba abinda yake sai fidda wani tatausan qamshi,tana rungume da baby boy wanda duka duka bazai wuce shekara daya da watanni biyar ba.

"Auty maama" 'yammatan suka kusa hada baki wajen kiran sunanta,tana rufe motan da key ta waiwayo tana dubansu,fuskarta ta wadatu da fara'a sosai,macace m'abociyar fara'a da kuma kirki,bata debo a qasa ba,ta debo kyawawan halayen mahaifiyarta haj aishatu umar sanda da kuma dr marwan akko

"Yammatan gidan baaba dr" ta fada sanda suka qaraso gaba dayansu,murmushinsuka sako,don dukkansu sunji dadin zuwan nata,saboda akwai shirye shiryen da suke akan bikin gidan,wanda sun tabbatar bazaiyi armashi yadda suka tsara ba saita ce wani abu,a matsayinta na babbar yayarsu,wasu na shirin amsar yaron hannunta,yayin da khadija ta amshi hand bag dinta,suka soma rankayawa ciki bayan sun gaisheta hira ta balle.

"Ina kuka baro maimunatun kuma yau?" Anty maama ta tambaya sanda suke gab da shiga ainihin ginin gidan,inda zao sadaka da qofar kowanne sashe dake cikin gidan,sai a sannan suka laluba suka ga ba maimunatun,da alama guduwa tayi saboda anty maaman

"Tare muke guduwa tayi halan,kinsan halinta,halim fulani ne har yanzu a jikinta,bada kowa yanzu take iya haduwa cikin gidan nan ba,hatta amma wasan buya sukeyi" murmushi ya kufcema anty maama,kunyar yarinyar da kamun kanta yana matuqar burgeta,duk da a cikinsu take amma bata yada dabi'ar kunya ba,har yanzu yarinyar batasan hanyar gidanta ba,da hirar maimunatun suka rakata ta gaida ammi sannan ta isa sassan mahaifiyarta amma,bayan ta aikawa anni da saqon gaisuwa gami da sanarwar ta iso zata shigo.

"Ina duka yaran?" Amma ta tambayi anty maama

"Suna islamiyya,amma for now nasan ma sun taso,nace ma iliyasu driver ya wuce dasu wajen haj,idan na dawo zan biya na debosu"

"Yayi kyau,Allah ya taimaka" amma ta fada,don ba wani dogon hira suke da ita can can ba,kasancewarta diyar fari a wajenta

"Wai maimunatu nita gani ta gudu amma?" Anty maama ta fada tana dariya,sai amman tayi murmushi

"Kyagaji da gani indai maimunatu ce,yanzu ko sassan nan bata zuwa" kai anty maama ta gyada,kamar ba zata ce wani abu ba sai kuma ta magantu

"Allah dai ya tabbatar da alkhairinsa,ubangiji yasa ta zame ma rayuwar ja'afar haske,nafi sanya hope a kanta amma akan samiha gsky,duk da ba'asan maci tuwo ba sai miya ta qare,Allah yasa dai manya ya riqesu da kyau" ajiyar zuciya amma ta sake,don abinda taketa tsoro da fargaba kenan,musamman da yadda kwanaki suketa matsowa,amma bataji.batun dawowarsa ba,koda kuma sunyi waya baya ce mata komai kan dawowar tasa ita kuma bata taba tambaya ba saboda.kara da kuma alkunya,amma dai duk sanda tayi sujjada tana gayawa Allah,wannnan shike bata nutsuwa.

Bata jima sosai ba tace bari taje wajen anni ta fita a sashen.

Bayan gama gaisuwa da 'yar tsokana da wani lokacin take kwasan annin da ita,sai anni ta kirayi sunanta

"Inaso kiyimin total na kayan jere dana kitchen,babanku ya buqata,zai siyawa maimunatu"

"A ina anni"
"Oho,wani kamfani ne yace anan da suke kawo kaya daga turkey,da so yayi aje can direct,to kuma lokacin ya qurace,danginta daga can gembu sun nema ya barsu suyi kayan,yace ai diyarsa ce,duk da haka saida suka aiko da kudin kayan,to nace gwara a siya wani abun me daraja da kudin a bata,tunda shi yayi niyyar yin kayan"

"Ma sha Allah,abbi ya kyauta,kuma hakan yayi,ko gold ne sai a siya mata,ba matsala anni" ta amsa mata tana fiddo wayarta daga jaka

"Yauwa,sannan kuma,bashi nakeso ki bani" kai ta daga tana duban anni tana 'yar qaramar dariya

"Me zakiyi da bashi kuma tsohuwa,bayan duka lalitar familyn farouq kumo na hannunki"

"Ke banson iya shege,kiyi ta kanki,magana nake miki ta gaske,aron kudi zaki bayar,amma ni ba kawomin zakiyi ba,lefe nakeso ki hada na maimunatu dana samiha,banason sanya kudina nazo na kasa tambayar jafar,idan nakine sai nafi maida kai ya maida miki kudinki akan kari,so nake komai yayi da kudinsa saboda sai yafi jin auren a jikinsa" dariya anni ta bawa anty maama,ta wani fannin kuma jikin anty maaman yayi sanyi

"Wai har yanzu baice komai ba?,baya cewa komai?" Kai anni ta jin jina

"Eh,amma ki barni dashi,idan yasan wata ai baisan wata ba,kallonsa kawai nakeyi,zai shigo hannuna ne,baisan wace maryam kumo ba har yanzu" ajiyar zuciya anty maama ta saki

"To Allah ya kyauta,ya kuma shiga lamarin"

"Ameen ya hayyu ya qayyumu,jabiru ya turo nasa kudin ta hannun hisham,duk da naji yace akwai wasu kayayyakin daya siya musu shida jafar din,daso yayi ya biya harda na jaafar din na hanashi"

"Eh gwara da bai biya din ba,gaskiyarki anni,gatan sai yayi masa yawa ya gaza riqe abun da muhimmanci"

"Shina gani ai" anni ta fada da qwarin gwiwa,shi yasa takeson anty maama din,saboda tana da matuqar hankali da nutsuwa

"Ba damuwa,naga wasu akwatuna sabbin design masu goma goma,zan siyawa jabir a matsayin gudu mawata,shi kuma zan siya masa set daya,set daya kuma zan saka cikin lissafinsa"

"Yayi dai dai,Allah ha saka miki da alkhairinsa kema,ya qara muku zumunci,Allah ya qara hadamin kanku" anni ta fada cikin jin dadi

"Ameen summa ameen" daga nan suka shiga tsara yadda komai zai kasance daga kan kayan lefen zuwa sauran hidimomi na bikin,harda yadda za'a gyara maimunatu duka anni ta dora saman wuyan anty maama.

Bayan ta gama da anni kuma ta koma bangaren qannenta,a sannan su salma sun shigo,nan suka zauna suka tsara komai bisa tsari da kuma burgewa,saidai har suka ci suka cinye hirarsu babu giccin maimunatu.

Can cikin garden na gidan ta boye kanta,batajin komai a kan auren tunda batasan meye gundarin abinda ya qunsa ba,bata gama wayewa da sanin meye shi ba,bata saba da zabin abubuwa a rayuwarta ba bare tace wannan zabin bai mata ba,kota damu,kawai dai tana jin kunya da kuma nauyin mutan gidan,tunda tasan meye surukuta,ta gefe guda kuma wani lokacin zuciyarta nayin rawa da kuma d'ar d'ar,tunda ta sani cewa kowacce mace tana auren namijin daya ganta yace yana sonta,itama ta maida masa martanin tana sonshi,amma ita nata angon batasan wanne kala bane,daga wacce duniya zaizo?,yaya kuma zai karbeta?,wadan nan sune kawai abubuwan sa takan nanatawa kanta lokaci zuwa lokaci,saidai yadda taga kowa ya daukaki abun a gidan yana bata mamaki,sannan yadda su laila ke sanyata a gaba,suyita gaya mata abubuwa game da angon nata sai ta yita mamaki,don ita bataga alfanun hakan ba,kiyi kaza kiyi kaza,kullum maganarsu kenan,sun canza mata abubuwa masu yawa,kama daga manta turarenta sa sauransu,itakam duka bataga wannan takurar da tsare tsaren na meye ba,badai a daura aure bane kawai a kaita can gidan ba shikenan dai?,amma magana daya biyu sai suce kina da kishiya,saikinyi kaza kinyi kaza,itakam bataga wani abun damuwa da damun kai ba.

********Cikin tsari ilimi da kuma gogewa anty maama ta hada lefe na alfarma,kowacce amarya ta rabauta da akwati goma goma,rana daya aka kai na samiha dana amaryar jabir Aaliya,said kuma kumbo da ammi abokiyar zaman amma ta qarawa kowacce amarya guda hurhudu,shima kowanne shaqe yake da kayan al'adun aure dana zamani,abun dai ya qayatar ya kuma bada sha'awa sosai.

Tarbar girma suka samu daga kowanne bangare na gidajen amaren,suka dawo gida suna yabon tarbar da suka samu,suna kuma tattauna yadda suka fuskanci dangin hajiya Aayah dama ita kanta haj aayah din keji da samiha,kasancewarta diyar fari a wajenta da zata fara aurarwa,su uku kuma kacal Allah ya bata.

Gembu aka yanke za'a kai lefan maimunatu,za'a kuma tafi ne har da ita,daa sunce abar kayan basai an kawo ba saboda gudun wahala da kuma zirga zirga,amma anni tace sam,aure za'ayi mata na gata da kuma 'yanci cikin danginta kamar kowacce diya,za'a kai mata kayan kamar yadda aka kaiwa kowa,kuma za'a daukota daga gaban danginta a kawo musu ita.

Wannan abun da anni tayi yayi matuqar qara mata kima da daraja a idanun dangin maimunatu,ya kuma qara musu qaimin fidda maimunatu kunya,tare da nuna ita din jininsu ce,duba da abunda bare tayi mata?,ina ga su da suke jininta?.

Kamar yadda annin ta tsara kuwa haka akayi,bikin saura sati biyu suka daga gembu da maimunatu da kayan aurenta.

Gidan kawu sule suka sauka,qani ne ga mahaifin shatu mahaifiyar maimunatu,mutum ne mai zumunci ba laifi,qaddarar abubuwan da suka farun zasu faru yasa ya barwa fulera riqon shatu dama maimunatu,uwa uba kuma da yadda ta nuna tsananin tausayawar tata ga 'yar uwarta,abinda yaja kawu sule kenan,ya dinga tunanin ko wannan abun ya kawo jituwa da gyaruwar alaqa tsakanin su shatun da yaran inno,yayi tunanin ya barta ko Allah zai sake dai daita al'amarin,kuma har yanzun nan baisan rayuwar da shatu da diyarta maimunatu suka fuskanta ba,yayita yabawa fuleran ma,ya tsammaci aiki tayi da hankali tace a kawo auren nan wajensu sabida girmamawa,baisan ko labari bata dashi ba,sai bayan da yuuma ta tabbatar sun sauka a gembu sannan ta aikaqa fulera da saqon ankai kayan,abinda ya dugunzumata,ya kuma bata mata rai,kamar yadda suke da maimunatu amma ace sai daga wajen baare zata samu labarin aurenta?,ta kuwa ci alwashin tafiya gembu cikin satin ko satin gaba,lallai sai ran kowa ya baci,idan sunsan wata ai basusan wata ba.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 26


Kulawa me kyau maimunatu ta dinga samu daga wajen yadikko matar kawu suleman,itace matarsa ta biyu,kuma tafi daada saratu quruciya,don haka ta zage da bawa maimunatu duk wasu kaye kaye irin nasu daya kamata ace amarya tayi amfani dashi,sannan ta zage ta dinga karantar da maimunatun mene ne aure?,waye miji da sauransu,abubuwan da suka sake fadada tunanin maimunatu,ta wani fannin kuma suka sake haifar mata da wani tunanin na daban

"Wannan shine aure?,irin zaman da zanyi kenan da mutumin da bansan waye shi ba?,shima baisan wacece ni ba?" Abinda ta yita juyawa kenan cikin ranta.


***********Zaune yake gaban laptop dinsa,ya baje takardu yanata shigar da wasu bayanai cikin system din,gaba daya hankalinsa kacokam yana kan aikin,wanda ya share kwanaki uku yana yinsa,burinsa ya kammale komai waje daya ya kuma gama da wannan aikin.

Wuninn ranar ko abincin kirki baici ba,sai uban coffee da yaketa danqara,lokaci lokaci kuma ya hada da cake,ko a yanzunma mug din daya sake tsiyaya coffee din na gefansa,ya dauka a hankali yakai bakinsa ya kurba ya maida ya ajjiye,dai dai sanda jabir ke qarasowa wajen,hankalinsa akan ja'afar,hannunsa kuma riqe da wasu rantstsun invitation cards,mamaki fal randa da zuciyarsa na yadda baiji ja'afar din yace komai ba kan yadda IV din nasu keta trending yana yawo tsakanin family and friends,duk da ya lura aiki yakeyi wurjanjan a kwanaki ukun nan.

Yaji isowarsa amma bai juya ba sakamakon shigowar wasu emails har kusan hudu a jejjere,sai yayi minimizing abinda yakeyi ya tafi kai tsaye ga email din,don dama yana jiran wasu bayanai daga secretary dinsa,yace masa a daren ya kammla su ya turo masa.

Maimakon secretary dinsa sai yaga saqon daga wajen hamza BBY yake,daya daga cikin abokansu tun na makaranta ake kuma tare har yanzu,budewa yayi gajeran rubutune da kuma hoto daga qasa sa bai budu ba

_Allah ya sanya alkhairi manya,da ba'a gaya mana ba JB ya gaya mana,Allah ya nuna mana lokacin big boos,i salute you>???,biyu ka b'aro ashe_

Danna hoton yayi, within seconds ya bude, invitation ne dake dauke da sunansa,da sunan samiha da maimunatu,mutuwan zaune yayi,wani bacin rai yana ratsashi,ya dunqule hannunsa waje daya yana furzar da wata iska daga bakinsa,da gaske suke kenan,ba zasu fasa ba?.

Dai dai lokacin da jabir ya zagayo gabansa,yaja wata kujerar ya zauna yana zube masa IVs din a gabansa

"Ga hard copies" wani kallo ya watsama jabir din,wanda banda ya saba da irinsa ba shakka sai ya razana

"Are you in your sense?, what did you do?,su suna nasu kenan kai kana naka?,to sai kasan ya zakayi da mutanen daka gayyato da labarin qanzon kuregenka,don banga abinda zai kaini nigeria a yanzu ba bare na fuskanci abinda yake shirin faruwa" sai ya miqe ya fara tattara abubuwansa masu muhimmanci,huci kawai yake kamar wani maciji

"Da kaje da kada kaje babu abinda zai canza,so gwara ma ka nutsu ka karba abun hannu biyu,ka kuma fuskanci abinda ke gabanka dude" baiko daga kai ba bare ya bashi amsa,ya gama kwashewa ya wuce yabar masa wajen.

Dariya jabir ya saki yana kada kai,duk duniya su qalilan ne suka iya zama da ja'afar,cikinsu shi da shaheeda sun shiga ciki,shi yasa kowa yake jinjina mata har yau da bata raye,yana da murdadden hali da kuma wuyar sha'ani qwarai.

Sanda ya shiga dakin kasa ci gaba da aikin yayi,ji yake kamar yaci kansa,wani irin bacin rai ya dinga taso masa,yakai ya kawo yana jin wani huci na fita saman fuskarsa,idanunsa suka kai kan dan qaramin frame dake dauke da hoton shaheeda,sai ya qarasa wajen ya duqa

"Why did you go and leave me?" Ya furta a hankali yana kai hannunsa saman fuskarta dake qunshe da faffadan murmushin nan nata me sanyi,sai ya miqe da sauri da nufin yiwa zuciya da harshensa linzami,ya kuma ja da baya yana fadin

"Astagfirullah wa'atubu ilaika" yaqi yake da kansa ba tare da sanin kowa ba,bayason maida hannun agogo baya,bayason wannan mode din da yake zama out of sense,yanaso yayi nisa dashi,sai kawai ya fidda wayarsa ya duba cave mafi kusa dasu ya kirasu suzo su fiddashi,kayan jikinsa ya fidda ya sauya wasu ya jefa wayarsa a aljihu ya fito,jabir na zaune anan yana ta duba tarin saqonnin mutanensu,baice masa komai ba yadai bishi da kallo gami da tabe baki har ya fita.

Cikin mota kwanyarsa ta cake sosai,neman dukka hanyoyin da zai kaucema wannan auren yake,ana tsaka da wannan kiran wayar dr marwan abbi ya shigo wayarsa.

Sai daya sauke gauron numfashi sannan ya daga wayar,sallamarsa kawai dr ya amsa ya hau balbaleshi da fada,ta inda yake shiga ba ta na yake fita ba,maganarsa ta qarshe itace

"Duk abinda kakeyi ka barshi,kada ka sake jabiru ya baro turkey ba tare da kai ba,ka biyoshi ku dawo gida" daga haka dr ya kashe wayar.

Hannunsa guda daya ya sanya yana yamutsa sumar sa gami da kallon yadda suke wuce titi bayan ya sulalar da wayar gefansa,jin abun yake kamar mafarki,duk inda bacin rai yake ransa yakai nan wajen baci,zuciyarsa ta gaya masa jabir ne ya shaidawa abbi abinda yace

"I will deal with you jabir,definitely" ya fada cikin huci kamar jabir din yana kusa dashi.

********Kwanansa uku cur bai dawo gidan ba tun ranar daya fita,jabir yayi kiran yayi kiran har ya gaji,gashi dai kiran yana shiga,amma sai ja'afar din yayi rejecting,daga bisani jabir ya daina baiwa kansa wahala ya dakata da kiran nasa,don yasan tabbas a yanzun bazai daga ba,bazai kuma saurareshi ba.

A rana ta hudu ya iso gidan,tunda yayi knocking sau uku ya tabbatar jabir din baya nan,sai ya sanya key dinsa samfurin katin cirar kudi na atm ya bude qofar ya shiga.

Sai daya kunna qwai haske ya gauraye falon sannan ya wuce dakin baccinsa,yana tura qofar idanunsa suka sauka kan hoton shaheeda,sai yaji kamar ya jima bai kalli hoton nata ba,don haka ya qarasa a hankali,ya zauna gefan gadon nasa,sannan ya dauki frame din hoton.

Yadan dauki wasu sakanni yana kallon fuskarta,kafin ya ajjiye frame din bayan yayi kissing hoton,ya kuma karanta mata addu'a cikin ranta kamar yadda ya saba.

System dinsa ya dauko hade da charger dinta ya fito daga dakin,don dama kusan itace ummul'aba'isin dawowarsa gidan,sai kuma ya koma da baya,saboda tunawa da yayi da maganar da sukayi da abbi,ya buda wardrobe dinsa ya ciro passport dinsa ya sanya a aljihunsa ya dawo falon,ya jona caji a system din ya kunnata sannan ya wuce kitchen, fridge ya bude yana laluben abun sha,duk ya gama bulayin sa daga sama zuwa qasan fridge din amma baiga drink din da yayi masa ba.

Wani mix fruit ya dauka,saidai yana gama karanta rubutun jiki yaja tsaki ya maidashi,a qa'ida shan abun sha na kwalba gwangwani ko roba basu dameshi ba,yafison abun sha irin namu da gargajiya da za'a hada a gida,kamar kunun aya zobo da sauransu,daga qarshe ya dauki wani matstsen ruwan lemon zaqi hade da cup ya dawo falon.

Bai jima da fara aikin ba jabir ya iso,daga sallamar sa daya amsa bai sake bi ta kansa ba,shima jabirun sai ya shareshi,saboda ha fuskanci abun sai 'yar tursasawa kadan ta shigo ciki,dole sai an ma ja'afar haka idan anaso rayuwarsa ta dai daita nan kusa,don haka shima sai ya wuce daki abinsa.

Sai da yayo wanka ya canza kaya sannan ya dawo falon,saman hannun kujerar dake daura da ja'afar din ya zauna yana fadin

"Ka gama yajin kenan kayo bikon kanka da kanka" maimakon ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login