Showing 129001 words to 132000 words out of 204120 words

Chapter 44 - Gurbin Ido Book One Complete Hausa Novel

samu number da take kira ba,tilas ta shiga motar gidan driver ya maidata gida,don ta qagu ta isa gidan suyi magana da anty talatu,sannan kuma ta fara tsare tsare da shirye shiryenta.

*_ADAMAWA_*
_RIGAR UMMARU_


A matuqar rude zaninta a hannu,tana tafe tana qoqarin maida zanin nata ta daurashi dai dai yana sake qwace mata,duk da hakan bata saurara da uban saurin da take zambadawa ba zuwa makwantar sabbin,inda take jiyo muryar laulo yana qwala mata kira babu qaqqautawa,ta kuma tabbatar ba lafiya ba,don dama duka kwanakin musiba da jarrabawa take.

Daga nesa ta tsaya cak tana bin dabbobinta da kallo,wanda da kadan da kadan sun zaizaye sun rame,dukka wannan cikar tasu kyau da kuma qoshin lafiya babu ita a tare dasu,kamar wadanda ake suda,ko kuma annoba ta fadawa.

Gabanta dukan uku uku yahau,ganin nagge guda hudu manya runtuma runtuma aqas babu alamun rai tattare dasu,tun kafin ta qaraso wajen ta dora hannayenta aka idanunta suka tara ruwan hawaye

"Yauwa inna,gasunan,nidai bansan me ya faru ba,ba zagaya zan kama ruwa,dana dawo na tarar babu gajee a wajen,dana duba da kyau kuma sai na samu wannan naggen guda biyar a zube a bakin ruwa,to guda daya ce me sauran rai,na ruga na kira na lami ya yankata ya siya,yace zai aiko miki da kudinki" sulalewa kawai tayi a wajen,tahau taba naggen daya bayan daya,batayi aune ba qwalla ta qwace mata,ta soma sharbar hawaye

"Wadan nan ne sukayi dakon jawosu,tunda kinsan anyi doka an hana yarwa,yana taba amfanin gonar manoma,saiki biyasu" daga haka laulo yayi gaba abinsa ba tare daya tsaya bi takan inna furera ba.

Kamar zata fadi haka don baqinciki,haka ta nufi shiyyar dakunanta ta dauko.musu kudin,qarta qartan samarin fulani ne majiya qarfi sun zuba mata idanu,banda haka bataga abinda zai sanyata biyan wadannan kudaden ba bayan asarar data tafka goma da ashirin.

Da qyar tayi sallar magariba ta hadeta da isha'i,tana zaune a wajen,ita ba addu'a ba ita bata bar wajen ba,sai qiyasta girman asarar da take tafkawa takeyi,tunda maimunatu tabar hannunta komai ya sake tabarbare mata,tun bayan tafiyarta take qunzuge kudaden da anni ke aiko mata,taqi daukan mai mata kiwon,ta tilasta gajee fita kiwo ita da laulo,da sunan gajeen takewa tanadin kudin daki dama na biki gaba daya,don tace bata ga abinda ubanta yake dashi ba da zai kai mata gidan aure.

To gajen dai ba'a son ranta ya fara fita kiwon ba,don dama gaba daya bata saba ba,a sangarce ta tashi,uwa uba kuma ita aure kawai takeso da himu,wannan yasa gaba daya ita da dabbobin suka shiga wahala,babu kulawa me kyau,a hankali suka fara lalure lalure,sai kuma haka siddan suka fara mutuwa,yau wannan gobe waccan,kudaden da taketa tarun su ta dunga diba tana musu maganu tare da karbo taimako na kambun baka da maita,waiko mayu ke kadar mata da garke,ita kuwa gaje ba abinda ya shalleta,idan suka fita kiwon sai tayi batan dabo,shi dai laulo baisan ina take zuwa ba,amma dai bata dawowa yawanci sai gab da zasu koma gida,tun inna furera bata gane meke faruwa ba,har ta gane,qaura wambai ta fadi ina take zuwa amma ta qeqashe qasa taqi fada,har inna ta haqura ta zubawa sarautar Allah ido.

A hankali ta bayyana wani baqon bafullatani take bi su fice daga shiyyar abinsu,haruna kyakkyawan bafulatanine wanda yake ruwa biyu,wani irin kyau ne dashi don hatta qwayar idanunsa launinta daban yake,idanun haruna a bude suke,sabida sunyi yawon kiwo gari gari qasa qasa,don haka babu wuya ya yaudari yarinya ta fada soyayya dashi,da wannan kyan nashi yake amfani,ya yaudari 'yammatan dashi kansa baisan iya yawan adadinsu ba,da haka ya yaudari gaje ta fada soyayyarshi da sunan aurenta zaiyi,tana da son abu me kyau,don soyayyar himu fiye da rabinta kyansa ne yake janta,sai gashi ta samu wanda ya fishi.

Hankalin inna furera ya tashi qwarai,ta tashi haiqan don rabasu amma a banza,da sun fita kiwo suke jonewa,kuma gashi ta gaza hanata fita kiwon,saboda bata dame fidda mata dabbobin,daga qarshe ta yanke shawarar bari kawai ta samu daadar himu da maganar aurensu,gwara ayi a daura,duk tsiya idan tasan da igiyar wani a kanta kome zai yanke,shima harunan bazai bita ba.

Sai data gama maganarta tsaf sannan daadar himu ta watsa mata wani kallon banza

"An gaya miki shashasha nike?,ko ba'a cikin garin nan nake ba ai nasan kome ke faruwa,da farko kinso kai diyarki birni ki hana dana,saboda kina ganin acanne zata samu me arziqi,da hakan bai yiwu ba sai kika haqura,yanzun kuma diyarki ta gama lalacewa....ta gama bidar maza shine kikeso ki joganawa dana?,bazai yiwu ba,nima na fasa hadin,dana fita zaiyi duniya ya nemi arziqi kamar kowanne namiji,ko nima zan kere sa'a cikin rugar nan" sosai ran innafurera ya baci,ta dinga zage zage tana cewa daadar himu ta yiwa diyarta sharri,daga abun arziqi sai ya zama na tsiya?,idan himu bazai auri gaje ba ai basai ta hada da sharri ba.

To itama daadar ba baya bace,sai ta tasowa inna furera,suka fito har tsakar gida suna yi,yuuma na jinsu bata ce musu ta tafas ku sauke ba,sosai daadar himu ta tasar mata,har ta fara bankada sirrin inna fureran,da roqarta da tayi kan ta rufa mata asiri,shine silar alqawarin da ta yiwa daadar himu na bawa himu gaje don su samu suci dukiyar a tare asiri a rufe

"Barni yuuma,rabu dani na nunawa matar nan nima ba kanwar lasa bace" daada tace da yuuma sanda ta taso tana shirin kashe rigimar,saboda yadda suka fara tonawa junansu asiri,da qyar ta samu ta raba,bayan mutane 'yan gulma sun fara marmatsowa,kowa yana son jin abinda ya shiga tsakanin tsaffin aminan,tun daga sannan sukayi baram baram,aka rabu dutse a hannun riga(dama duka tarayyar da babu Allah a ciki,to tabbas qarshenta kenan koma fiye da wannan).

Ajiyar zuciya inna furera ta saki,sai ta miqe tana zura takalmanta,ta kuma nufi turken dabbobin,tsaiwa tayi tana qare musu kallo,baqinciki na sake sudarta,wai me yasa komai yake shirin tabarbare mata ne?,watsewar wadan nan dabbobin dai dai yake da watsewar dukka farincikinta da kuma kima da daraja data samu a baya cikin qauyen ta dalilinsu,kuma hanya ce da zata bawa maqiyanta kamar su daadar himu damar yi mata dariya gami da zundenta,kai ta girgiza da sauri,ba zata taba barin hakan ta faru ba,ko ta yaya sai ta dawo da garkenta kamar yadda yake ada,amma kuma ta yaya?,ina taga kudin da zata sake siyan wasu dabbobin ta cakuda da nata?.

"Maimunatu" shine sunan daya fado mata,tabbas!,wannan itace amsa,tun daga kan kayan lefe sadaki da irin mutanen da suka je daurin auren yarinyar ta tabbatar ta taka wani babban shinge,kuma koda bata gani ba,jikan tsohuwa anni ai ba wasa bane,tunda tasan anni,sani na daga ni sai ke ba sanin shanu ba,ko daga motocin dake shigowa da ita garin da irin rabon da take zakasan ba qananun mutane bane.

Murmushin samun mafita ne ya subuce mata,ta saki ajiyar zuciya,hankalinta kuma taji ya kwanta sosai,dole ta nemo gidan maimunatu,tana da tabbacin zata samu dukkan kudaden data yanka mata,ai dai komai lalacewarta ita taci gaba da riqonta bayan bacewar ubanta da kuma gushewar uwarta daga doron duniya,idan ta kama ma sai ayi lissafin din abincin data dinga ci da ita har zuwa sanda aka aurar da ita,da wannan tunanin ta juya zuwa cikin gida,saidai abu daya da take ganin zai kawo mata tarnaqi shine,ina zata samu kwatancen gidan maimunatu,daga nan har garin gombe?.
"Yuuma mana" tsukakkiyar kwanyarta ta bata amsa,take kuma ta gamsu,don haka ta dage katifar ciyawa dake dakinta tana laluben sauran kudaden data adana,ta lissafa taga nawa suka rage mata?,tunda tun bayan auren maimunatun anni tace yuuma ta shaida mata,kudin aikatau an gama biyansu,tunda a yanzu tana gidabta tana zaman aure bautar Allah bata mutum ba,a ranta take qiyasta adadin kudin zasu kaita gwambe?,don bata tunanin kudin dawowa,tasan ko a jirgi tace tanaso a dawo da ita za'a kawo ta.

Barazanar daukewa numfashinta yake daga qirjinta sanda ta daga wajen ta kuma kakkabe katifar taga wayam

"Hukumullahu min zalika" ta fadi kalmar da ita kanta batasan cikakkiyar ma'anarta ba,yadai fadane kurum,gumi ne ya fara tsargo mata,ina kudadenta suka shiga?,cikin lokaci qalilan tayi gumi kashirban,ta koma bakin itacen gadon ta zauna tana sauke numfashi kuka kamar zai qwace mata,ta xurfafa tunaninta kan waye yabi dare yabi rana ya dauke mata kudinta?.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 55

Yana daga tsaye ya dauki yaron anty maama yana dan jan kumatunsa suna gaisawa da ita,tana dan dubansa yadda yake sake zama fresh cikar hankali zati da kuma kamala na sake bayyanar masa,wanda sau da yawa cewa akeyi captain J yayanta ne,itama ba musawa take ba,cewa takeyi eh,don ba kowane zai yarda kan qaninta bane

"Sun wuce gida ne?" Ya aza shanyyun idanunsa dake nuna zallar gajiya kan fuskar anni yana tura mata tambayar

"Maimunatu?....tana ciki" baba tabawa dake fitowa dauke da plate data yayyanka fruit ta amsa masa saboda tayi tsammanin da ita yake.

"Da kin barshi ai tabawa,dan kusun uwa,mutum sai shegen izza?,sunan iyalinka ba xaka iya fada ba,so nayi naga qarshen iya shege" anni ta bishi da mita sanda yake takawa da kansa zuwa cikin gidan,baiso ma ya tsaya bata lokaci wajen,don yasan yau a ciki suke da juna shi da anni

"Haba anni,kaara dai yake miki,sunan ne na zamani dai,ba'a fadi dai a gabanki ba" anty maama dake dariya a ciki ciki ta fada qasa qasa yadda bazai jiyota ba

"Shidai ya sani,wallahi gwara yayi ta kansa tun wuri bai qure masa ba" annin ta fada taba miqe qafarta sosai yadda zata fi jin dadin zama sosai, anty maama dai nata tsokanarta,don batasan me ake ciki ba game da gidan ja'afar din ba,daga annin har baba tabawa sun sirranta abin,suna fatan komai zai dai daita a kurkusa.

Ba zato ba tsammani sukaga an dauke labulen falon,kamar saukar ruwa da daukewarsa kowa yayi tsit,idanunsu suka sarqafe guri daya lokacij data daga kai don ganin wanda ya shigo din,da qyar ta qwaci kallonta daga kansa,ya jing????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  ina da bakin qofar hannayensa shoke a aljihunsa yana ci gaba da kallonta.

Dan kwalinta ya zame ya koma rabin kanta saboda santsi,hakanan babu lafayar jikinta ta cireta ganin cewa su kadai ne,santala santalan fararen qafafunta sun fito sosai har qaurinta saboda miqe qafar datayi ta dora amna akai,sai ya lumshe idanunsa yana jin zuciyarsa nadan bugawa kamar alamu na fara jin bacin ransa, imagining yake a ransa khalid ko hisham.....wani a cikinsu ya shigo ya sameta a haka?,tunanin da yasa ya gaza bude idanunsa,yana jin sautin muryar qannensa dake wucewa ta gefansa sumi sumi daya bayan daya suna gaidashi,ba wadda ya amsawa,haka suka wuce don idan da sabo sun saba,idan ta motsa masa hakan yake musu.

Sautin muryar amna data taho da sauri tana kiran

"Welcome dad" ya sanyashi bude idanun nasa,kana ya bude mata hannayensa gaba daya ta taho da sauri,tashin amna daga saman qafafunta ya bata damar miqewa itama,haushi yadan kamata na yadda duka suka sulale suka barta ita kadai,sai ta gyara dankwalinta sosai,tayi masa sannu da zuwa,sannu da zuwan da yayi kaman bai jita ba,ta duqa a hankali ta dauki wayarta,sannan itama tayi hanyar fita.

Yana sane da ita,amma ya basar kamar baiga tahowarta ba,sai data ratso ta shiga tsakiya,sannan ya juyo,da wani irin zafi da zafin nama yana fuskantarta,fuskokinsu suka hadu waje guda,sai ta tsorata da yanayin da taga fuskarsa,duqawa yayi a hankali ya sauke amna qasa

"Jeki cema maama ta goge miki baki da tissue,am coming"

"Zan bika dad?" Ba tare da ya gama tantance me ta fada ba ya daga mata kai,sai ta cilla tayi gida cikin tsananin murna.

Tazarar dake tsakaninsu ya sake ragewa,abinda ya sabbaba musu fara musayar numfashi,ya kafeta da dukka idanunsa yana kallon matsoraciyar fuskarta,wadda har ta runtse idanunta,zuciyarta na wani irin bugawa fiye da kima,a hankali kuma tsigar jikinta ta fara tashi,jikinta ya fara saukar mata da wani feeling saboda dumin numfashinsa dake gauraye da lallausan qamshinsa wanda ke sauka saman fuskarta,yar yar jikinta ya fara yi tako ina,wani baqon yanayi da tunda take bata taba jinsa a tattare da ita ba.

"Me yasa kika zauna haka?,kin manta ke matar aure ce?" Maganar da sam ba ita yaso yi ba ta subuce ta fita daga bakinsa da husky voice dinsa wadda ta cika kunnuwan maimunatu.

Jikinta ne gaba daya ya dauki rawa,wayar hannunta ta sulale a take ta fadi a qasa,qarar faduwar tata ya sanya idanuwansu shida ita kaiwa kan wayar,suka kuma dauke a tare suna kallon juna,sai ya tsaya kawai yana kallon kyawawan idanuwanta da suka sakeyin kyau kamar kullum a lokaci irinn wannan,idanuwan da suka dan sauya launi,suka kuma cika da qwalla,ya sanya hankalinsa sosai ga qwayar idanun nata yanason karantarta

A hankali ya zame idanuwansa daga cikin nata,ya maida qwayar idanun nasa ga jikinta yana kallonta har zuwa saman tafin qafarta,sai yaja baya ganin yadda jikinta ke dan rawa,mamaki na darsuwa a ransa,baiga wata magana da yayi da zata sanyata shiga wannan mood din ba,amma sai ya sassauta kafin fushinsa wanda baisan me yake sake hasalashi ba

"Ki dauko mayafinki ki sakemi a mota" yayi maganar yana bata hanya,tuni ta tsallake,ko takan wayar tata bata bi ba ta wuce da sauri sauri,ya bita da kallo,sai data bace ya maido dubansa ga wayar,sai ya duqa a hankali ya daukota,ya dannan gurin power ta kawo haske.

Face dinta dake cike da cuteness ce ta cuka screen na wayar,cikin uniform dinta na makaranta,lafiyayyen murmushi ne kwance akan fuskar tata daya qara mata wani kyau na musamman,duk da screen din wayar ya fashe amma hakan bai hana bayyanuwar kyan hoton ba,samun kanshi yayi da kallon hoton na wasu sakanni,sannan ya kashe hasken wayar,ya sanyata a aljihunsa yana miqewa,a kasalance yabi ta qofar baya ba tare da ya koma ta cikin gidan ba ya fice parking lot na gidan.

Toilet ta fara shigewa ta maida qofan ta rufe,numfashi take ajewa gami da cure hannayenta waje daya,tanason ta gama tantance abinda ke damunta tukunna,tsahon minti biyu kafin bugun zuciyarta ya dai daita,hawayenta kuma suka tsaya,saidai abinda takeji cikin jikinta bai sauya ba,famfo ta kunna,ta tara hannayenta ta wanke fuskarta da kyau ta gyarata sannan ta fito,tana takawa a hankali cikin sake daidaita nutsuwarta don kada yanayinta ya nuna wani abu.

Ranta fal haushinsa,me tayi haka da zai sanyata a kwana yana mata irin wannan tambayar?,ya kuma rutsata da idanuwansan nan data tsani ya kalleta dasu,tana cewa dukkansu a haka suke zaune kamar ita?,meye tayi wanda ba dai dai ba?,ko wani tafi a cikinsu?,don kawai tana da aurensa?.

Laila fa'iza rahama da sahla 'yar anty maama ne sukayo mata rakiya,sai amna dake riqe da hannun maimunatu wadda ta kafe kai da fata yau fa a wajen anty moon zata kwana.

Daga dan baya kadan dukka suka tsaya,saboda kowannensu shakkarsa yake,ta qarasa ta sanya hannu ta bude qofar,tana addu'ar Allah yasa ba'a bayan yake ba,gaba daya batason haduwar sabgarta da tashi sam,saidai yana zaune a owners corner,hannunsa dauke da ragowar ruwan daya dauko a hanyan kitchen kafin ya fito.

Tana shiga amna ta shigo tana fadin

"Daddy.....tare zamu tafiko?" Ta wuce kai tsaye kusa dashi,duban maimunatu yayi,bata yarda sun hada ido ba,sai kuma ya maida kallonsa ga amnan

"Ban miki bayani ba?,ba yau zamu tafi ba,I have prepared something for you soon" kafada ta maqale,idanunta na hada ruwan hawaye

"Nooo daddy....,nafison na bika yanzu" yadda ta narke din sai ta bashi tausayi matuqa,tana yawan son ta bishi,amma kuma sai yake ganin kamar ba zata samu kulawa irin tasu amma ba.

"Let's go"
"Yeeyy..... that's my dad" dolensa tasa murmushi kubce masa,sai yasa hannu ya lakaci kumatunta

"That's my baby" shima ya mayar mata.murmushin da bata shirya ba mai dan sauti ya kubce mata,fitar sautin sa ya sanyashi waiwayowa ya dubeta,sai kuma ta maze,kamar ba ita ba,ta maida idanunta da hankalinta sosai ga titi.

Bata sake tabbatar da surutu da kuma wayon amna ba sai da suka dauki hanya,hakanan ya daure ya dinga biye mata a wasu maganganun nata,itakam farinciki ya cikata,yau zata kwana a wajen daddynta.

Shuru maimunatu tayi tana saurarensu,a hankali taji kewa sosai na cikata,kewa ta mahaifi,tana iya tuna wasu abubuwa da suka faru tsakaninta dashi,gata da soyayyar da yake gwada mata a wancan lokacin,bata manta wasu ba duk da shekaru sun fara nisa,gefe guda kuma tana bin yadda jikinta keta motsawa, mood dinta yana dan canzawa kadan kadan,wanda ita kanta batasan dalili ba,wannan yasa motsinta ya dauke kwata kwata daga cikin motar,har sai da amna tace

"Anty moon,zaki dafamin pepper chicken?" Murmushi ta sauke tana duban fuskarta,har cikin ranta take jin tausayin yarinyar data

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login