Showing 93001 words to 96000 words out of 204120 words

Chapter 32 - Gurbin Ido Book One Complete Hausa Novel

da tuna irin dambarwar da suka sha,tana cikin masu yi musu dariya kafin ta fahimci girman jarrabawar da suka fada,kafin ta fahimci waje ja'afar data fara yin hankali ta fara tausaya musu.

Dubanta maimunatu takeyi kwanyarta na tafiya cikin nazari da tunani afran ta dora,saidai wannan karon cikin seriousness take maganar

"Qawa,kada kiyi wasa da damarki.....kada kuma ku tsaya kallon ruwa kwado yayi miki qafa,kina da dukkan komai da zakiyi wining a kansa da zuciyarsa,karki barwa kishiyarki waje ko fili ko kadan,kada kuma ki sake wadan nan alamomin rainin daga wajenta suci gaba da fitowa a kanki,ta yaya zaki sakar mata rayuwarki tayi yadda taga dama?,mijinki rayuwarki ne ko yaya kika gai ga qinsa,wannan zaiyi amfani ne kafin ki amsa sunan matarsa,duniya ta fara kallonki da sunan,amma bayan kin amsa din kuwa,baki da wani zabi daya wuce ki gyara komai,indai bakiyi hakan ba....baki kyautawa anni ba,sannan bata cancanci wannan tukuicin daga gareki ba" maganganun afra sun ma maimunatu nauyi a ka,ta saqa abubuwa masu yawa a zuciyar maimunatu wanda suka dinga yi mata kai kawo aka,saidai tana duba abin,tana duba yadda lamarin zai kasance,ba zasu fahimta bane cewa yadda suke kallon lamarin dashi kansa mutumin ba haka abun yake ba?.

To sai da tayi mugun da gaske sannan ta yakice tunani me qarfi da ya kamata daga ranta,ta koma karatunta ka'in da na'in,itama afrah bata sake ce mata komai ba,saidai a fakaice take mata karatun yadda soyayya take,sau tari a gabanta take wayoyinta yanzu,ta daina kebewa kamar yadda takeyi a baya,wani lokaci saidai ta tashi ta bata waje,idan taga dama ta qyaleta,idan kuma bata so ba ta biyota nan ma ta addabeta.

*************Tsararriyan books shelve,wadda ke dauke da tarin litattafai a jere cikin tsari da tsafta da kuma sanin makamar aiki,tsaye yake a gabanta,daya daga cikin qofofinta a bude,da alama wani littafi yake nema,hannunsa daya dauke da wani littafi daya nutsu qwarai yana dubashi shafi bayan shafi,yayin da daya hannun nasa kuma ke riqe da cup dauke da matsatsen ruwan tuffa da inibi,sanye yake da wasuSlim fit suit Korean design royal blue color,shigar da a duk sanda ya yita take masifan karbarsa,kamar dama anyi suits da blazers saboda shi ne,kallo daya zaka yiwa kwantacciyar fatarsa kasan cewa hutu da jin dadi sun ratsashi,duk da cewa babu cikakken hutun ba ma'ana a ruhinsa,saboda uban tulin tarin ayyuka da kullum yake jibgama kansa,duk don yayi keeping kansa busy,ya raba kansa kuma da dukka wani tunani da kuma damuwa.

Fuskarsa nan mai cika da haiba da kwarjini tana nan a yadda take,babu faraa ko walwala sam kamar bashi daya bane a cikin qawataccen office din nasa ba,sumar kansa zuwa ta fuskarsa nata sheqi tare da fidda qamshin hair mist mai kwanatar da zuciya.

Taku daya yayi zuwa baya kadan da qafafunsa dake sanye cikin wasu lafiyayyun baqaqen takalma,wanda zaka rantse da Allah ba'a fita waje dasu saboda yadda suke sheqi,babu alamun saukar qura a kansu,ya dan jingina da teburinsa yana furzar da iska daga bakinsa bayan yakai shafin qarshe,yana tuna sanda shaheeda ta bashi gift na littafin,sai ya dan rufe littafin kadan yana kulle idanuwansa na wasu sakanni,kullum kwanan duniya yana jin cewa ya rasa babban bango kuma majingina a rayuwarsa,tunda ya rasata kullunm rayuwarsa sake jigata takeyi,babu wani sassauci tako ina.

Idanunsa ya buda a hankali sanda akayi yaji ana scanning key din office din nasa,qofar kuma ta bada qara alamun an budeta kenan,bai wani motsa ko kuma ya damu ba,saboda yasan duk duniya mutum daya ya bawa wannan damar wato jabir,shi dinne kuwa,ya sako kai cikin office din bakinsa dauke da sallama,hannunsa dauke da file yayin da idanunsa suke kan fuskar ja'afar,yayi kyau shima cikin tashi suit din da take kamanceceniya data ja'afar,ya qara haske da kuma qiba yayi fresh,alamun duk yadda yakeso haka take samuwa a gareshi.

Bakinsa ya motsa yana amsa sallamar tasa,kana ya miqe tsaye sosai saman qafafunsa,ya sanya hannu a nutse ya maida littafin inda ya daukoshi,ya rufe sannan yafara takawa zuwa kujerarsa,jabir din na biye dashi da idanuwa,yana kuma karantarsa,ransa da zuciyarsa na masa rashin dadi,don ko kowa baice komai dashi ba,yasan akwai abinda ya motsa zuciyar ja'afar din.

Sai da ya zauna sosai sannan ya tura file din gaban

"An gama hada komai,na gama nawa signing din,saura naka,zaka duba inda yake da gyara sai kayi,ka saka hannu mu miqa musu takardun, withing one to two weeks ya kamata a gama" ya qarshe maganar yana maida dubansa ga wayarsa daya zarota daga aljihu,saboda qarar shigowar text,murmushi ya subuce masa ya buda text din yana dubawa,yayin da hankalinsa kacokam ya koma kan wayar tasa,abinda yaja hankalin ja'afar,ya tsaya ya zuba masa ido,kana yadan bugi table din dake tsakaninsu.

Daga kai jabir din yayi yana dubansa,har yanzu murmushi bai bar kan fuskarsa ba

"Ina jinka"

"Baka tare dani" ya amsa masa kai tsaye da tsayayyar muryar nan tasa

"Yes.....gaskiya ne,hankalina bai wajen magana ta gaskiya,yanzu me ya rage?,inason naje gida lunch ana jirana" zube masa idanunsa yayi sosai kafin ya janyesu,kana yace masa

"Kana iya tafiya" da wani irin low tune da ya sanya tausayinsa sauka a zuciyar jabir,yafi kowa sanin yadda shaheeda tayi tattalinsa a lokacin rayuwarsa harma fiye da haka,amma a yanzu duka yayi loosing wannan caring din,dole abubuwan su dinga tabashi,duk da cewa shi yaqi bada wannan damar,yana da hope akan maimunatu shima kamar yadda yaji anni tana fada,ya sake samun gamsuwa akan yarinyar tun ranar da suka zauna sukayi magana ne tsaho a kanta da anni amma ya tattarata ya kaita makarantar kwana,annin kuma ta hana kowa masa magana,tace su xuba masa idanu suga iya nasa gudun ruwan.

A dan shurun da ya ratsa ta tsakaninsu ne tex ya shigo tasa wayar shima,sai ya jawota yana dubawa,qaramin tsaki yaja

"this is nonsense" furucin ya fita can qasan maqoshinsa,idan ba kunne kasa sosai ba ba zaka ji me yake fada ba,kira yayi ya aje wayar saman table bayan ya sakata a loud speaker,bugu biyu ya daga

"Me kake cewa ne?,ace duk gidan a rasa me daukota?" Yace da hisham kai tsaye,lumshe idanunsa hisham yayi daga wancan bangaren kafin ya amsa shi

"Babu yaaya,drivers din duka sun fita tare da abba,yana da baqin da suke zirga zirga dasu,ni kuma nan da minti goma akwai wanda zanwa surgery,kuma emergency ne har mutum biyu,kafin na gama kuma an ja lokaci" katse kiran kawai yayi,ya fara laluban number anty maama.

Itama bugu biyu ta daga suka gaisa

"Driver dinki yana kusa ki bani aronshi?"

"Wai.....ai kuwa yau tun sassafe ya debi yara abbansu yasa ya kaisu qauye"

"Ok" yace a gaggauce

"Akwai wani abu ne?"

"No,ki gaida yaran, thanks "

"Okay" itama ta bishi dashi,tasan halin kayanta fes,bama fadar zaiyi ba

"Waye ya bawa drivers na gidan nan hutu ne gaba dayansu?" Ya jefawa jabir dake nanuqe da wayarsa yana maidawa fatimansa reply na dinta tambayar,sai a sannan ya daga kai ya dubeshi,duk nema neman drivers da yakeyi yana jinsa,ya kuma san dalilin hakan,don kusan da goyon bayansa anni tayi wannan hukuncin

"Hey man,kai ne mana?,ka manta kenan ka zauna ka sani a gaba zaka fara tuhuma?" Tsaki ya sake ja yana tattare files din da suke gabansa

"Bari na fito maka a mutum,duk wannan goce gocen da kake bazai maka bafa,ka tashi kaje dauko yarinyar mutane kawai,three months bata nan amma don zaka bata just thirty to fourty minutes ka daukota a school sai ya gagara saboda adalci irin naka?" Wani kallo ya masa,tunda yaji amsar daya bayar yasan da issue din kenan,sai ya dakata daga hada takardun

"Idan kaji haushi me zai hana kaje kai" dariya ya sake sosai

"Ba dole na bace,ga dole na can tana jirana,kuma inda itace da tuni na tsufa a school din,don bazan bari Allah ya kamani da laifin rashin sauke haqqin dake wuyana ba" yana gama sai ya miqe yana 'yar dariyarsa zai fice daga office din,har ya kusa qofa sai ya tsaya

"Da zaka zo sai mu wuce gida tare ka fara yin lunch kafin ka tafi" ya fada with full caring in his voice,saidai kallo dayan da ja'afar yayi masa ya bashi amsarsa,sai ya kada kai kawai ya fice a office din yana murmushi,ya gode Allah daya bashi juriya da hikimar zama da ja'afar din,mutumin da yake jinsa tamkar cikin mahaifa guda suka kwanta dashi.

Riqe da suit dinsa a hannu ya fito,kana ya sauko kai tsaye zuwa floor din qarshe ya kuma wuce parking lot na ma'aikatar,key dinsa already yana hannunsa,tunda ya sallami driver dinsa,don yau din ya tsara lokacin tashinsa,zai iya kaiwa dare,don haka ya bashi umarnin tafiya idan akai azahar,sai gashi kuma wani abun da babu shi cikin schedule dinsa na yau ya taso masa.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: *GURBIN IDO*
37

*AREWABOOKS:HUGUMA*
https://arewabooks.com/chapter?id=6364b8542730d61e0981706d
______________

Sanda sukai jarabawar first semester ta goma sha biyar tazo cikin su arba'in,ko kadan hakan bai mata dadi ba,saboda ta saba,har ta gama rayuwar primary dinta bata wuce ta biyar,bata nunama kowa ba sai aminanta kuma roommates dinta,afra ce tace

"Naga qoqarinki ma maimoon(sunan da suka koma ce mata kenan),a wata uku kacal kin doke mutum ashirin da biyar?" Kai ya girgiza sanda take hada kayanta,don a gobe kowa zai wuce gida hutu

"Ina qoqari a nan afreen(sunan da ita dinma take kiranta dashi),bazan iya nunawa kowa result dina ba"

"Zaki iya maimoon,i trust you,duk wanda ya iya arabic,boko bazai bashi wahala ba sam sam sam,boko minor abune akan arabic"

"Next time I will try my best in sha Allah" ta amsa mata tana sakar mata murmushi,tare da jin dadin irin qwarin gwiwar da ko yaushe afra take bata.

Washegari tana ta zuba idanun ganin wanda zayazo daukarta saiga yaa hisham,ya fito suka gaisa dasu afra,ya kuma gabatar musu da kansa da kansa a matsayin yayan maimunatu,sosai abun ya mata dadi,ya girmamasu ya kuma mutuntasu a mazauninsu na aminanta,su kansu sun nuna jin dadin hakan,afra taso su gaisa da 'yan gidansu,suga kuma sabuwar aminiyarta,to amma ya hisham din ya bada uzurin yana da patient da zai gani,dole sukayi sallama suka shiga mota.

Yana qoqarin tada motar ya lura da envelope din hannunta,wadda ke dauke da tambarin makarantar,sai ya miqa hannu

"Duk da ba'ayimin tayin ganin result din ba,nayi shishshigi,a bani na gani" idanu tadan zaro,ta yima kanta alqawarin babu wanda zai gani,har sai tayi abun arziqi,amma tana jin nauyin hisham din

"Ya hisham,don Allah.....ka bari sai next term saina hada maka da wannan din duka ka gani gaba daya" ta fada tana marairaice masa,wanda har ga Allah ita din batasan tayi ba,kamar yadda batasan mugun kyan da hakan ya qara mata ba,har sai daya janye idanunsa da sauri daga fuskarta yana fadin

"Subhanallah" cikin ransa ya furtata a hankali

"Ba matsala,Allah ya nuna mana" yadda taga yayi maganar yana tada motar ba tare da ya sake waiwayowa ba yasa taji babu dadi cikin ranta,sai taji kamar bata kyauta masa ba,don haka ta zaro ta miqa masa,sannan tayi qas da kanta tana jiran jin maganar da zai fada mata

"Kinyi qoqari sosai,ma sha Allah,wannan ne karonki na farko fa?" Ya fada cikin nuna qwarin gwiwa da kuma qarfafata,maganar tazo mata a ba zata,ta kuma bata mamaki,sannan kuma taji dadi gaki da sake samun qwarin gwiwa.

Ta zaci gidan abbi zai kaita,sai taga ya wuce da ita gidanta,bata tambayi dalili ba,bayan ya aje ta tayi masa godiya,ta kuma bashi saqon gaisuwa wajensu anni,tare da roqonsa a kawo mata amna.

Gyare gyare ta shiga yi,irin na mutumin da ya kwan biyu baya waje,sai data gama komai sannan ta sake wanka,ta kuma wuce kitchen ganin azahar har ta gota don ta samawa kanta abinda zataci.

Har zata shiga ta tuna da unaisa,sai taga bai dace tana cikin gida ba amma batasan da dawowarta ba,ko banza ta girme meta a shekaru,wannan tunanin yasa ta karkata akalarta zuwa sashen unaisan.

Knocking biyu aka tambayi waye,kai tsaye ta amsa da itace maimunatu,sai da aka dauki mintuna sannan ta bata izinin shigowa.

Zaune take saman doguwar kujerar falon nata,ta miqe qafafunta akai tana shan lemon fata,da alama tun dazun a hakan take a zaune,kawai dai batayi niyyar bata izinin shigowar bane,kallo daya tayi mata ta canza fuska ta kuma kau da kanta taci gaba da kallonta ga tv.

Koda ta gaisheta sama sama ta amsa

"Na dawo,nace bari na shigo na sanar miki" wata dariya ce ta zowa unaisa,ya tabbata ja'afar din mugun dan rainin hankali ne,hakazalika da biyu ya dauki yarinyar ya kaita makarantar kwana saboda ya raina ajinta da kwanyarta,to amma hakan yayi mata ita din,tunda ko banza kawo yanzun tana dan samun wasu sauye sauyen,duk da cewa ko sau daya bau taba hada dakin kwana da ita ba

"To yayi" tace mata kawai taci gaba da shan lemonta tana kada qafa gami da ci gaba da kallonta,ganin babu wani magana data sake hadasu sai maimunatun ta miqe zata fita

"Agwai" ta kirayeta da sunan da maimunatun tafita sanin me sunan yake nufi,sunan yadan sosa ranta,amma bata nuna ba ta waiwayo tana dubanta

"Am please idan kin tashi girkinki,ki dinga yi iya cikinki,wanda naci a baya ma shahada nayi,don ba abinci kowanne irin mutum nake ci ba,so ina da masu aiki,zasu dinga yin komai" kai ta gyada sannan tayo gaba tana bar mata dakinta.

Ga mamakinta sai taji maganganun unaisa sun dan sosa ranta kadan,abinda tun tasowarta da irin cin zarafin data gamu dashi a rayuwa bata taba jinsa akan kowa ba,ko hakan yana da nasaba da zama dasu afra?,hakan na nufin ta fara sanin kanta da kuma sanin mene ne rayuwa?. Muje zuwa dai.

Tunda ta dawo gidan bataga koda gilmawar J ba,abinda ko sau daya bai WaWata da ?asa ba,sau tari mancewa take dashi kwata kwata cikin rayuwarta,tasa litattafanta a gaba tana ta haddar hadisan data daukarwa malamin islamiyyarsu alqawarin zata kawo masa su kafin a koma hutu,da kuma izifin data diba shima zata daw da haddarsa,don hatta haddar qur'aninta bata bari ta tsaya ba,tana ganin wannan damar ta roqa alfarma,yake mata qari kuma tana kawo masa.

Ta fannin boko ma litattafan da zasu sake inganta mata koyo da gane turancinta ta karba aro masu yawa daga library din makaranta ta taho dasu,wadan nan abubuwa sune abokan hirarta,kewar da tayi fama da ita zamanta na baya a gidan yanzu duka babu,mantawa ma take da inda take,wani lokaci ma idan tayi breakfast bata sake neman abinci saina dare,batajin yunwa sam idan ta duqufa karatunta,bare kuma ba wani motsi zatayi me yawa ba bare ya zazzage mata cikinta ya jawo mata yunwar ba,tana daki kwance,saman gado idan ta gaji ta dawo falo saman kujera,ba kasafai take shiga kitchen din ba,dalilin da yasa har zuwa sannan batasan ma kalar 'yan aikin da unaisa ke maganar ta kawo ba,don sanda zata shiga da safe basu soma nasu aikin ba,lokacin da zata sake komawa kuma dare yayi sun gama nasu aikin sun bar kitchen din.

To da wannan damar data samu yasa tayi karatu me yawan gaske,wanda ita kanta batasan ta yishi ba,hutun da akazo gida don yinsa nata hutun kadanne.



Randa tayi sati a gidan,tana daga bakin window dinta ne taji cewa ja'afar din tafiya yayi ashe,ta bakin unaisan sanda tayi baqi take rakasu zuwa parking lot na gidan xasu shiga motarsu,saita janye zuwa ciki,ta bude shafin gaba na littafinta taci gaba da karatunta.

Sai da tayi kwana takwas da dawowa sannan su fa'iza suka zo mata,harda amnanta,ranar kamar sallah haka ta jita,sun sameta anata sana'ar wato karatu,amna na jikinta ta dauketa zuwa kitchen don ta sama musu abun sha,kafin tayi tunanin me zata girka musu.

Sanda suka shiga amnan nata mata tambayoyi da zuba mata surutu,tabbacin yarinyar tayi kewarta matuqa,bata lura da unaisa dake tsaye riqe da cup da yoghurt a hannunta ba har sai data kirayi sunan yarinyar,tare suka waiwaya zuwa gareta ita da maimunatun,maimunatun ta dubi yarinyar data zubawa unaisa idanu tana kallonta,duba na rashin sani da kuma rashin sabo

"come-on baby,new mom dinki ce" unaisa ta fada tana murmushi gami da miqawa yarinyar hannu,karon farko da yaro ya burgeta,kasancewarta ba ma'abociyar son yara ba,tsantsar kamanninta da silly mahaifinta din nan ya bayyana,tana fatan batayo miskilanci irin nasa ba.

Kamar kuwa yarinyar tasan me take rayawa a zuciyarta,sai ta noqe kafada tana ci gaba da kallonta

"Zo mu gaisa mana,haba amna,nace miki new mon dinki ce" ta sake maimaitawa dai,sai ta sake maqale mata kafada,wannan karon kallon fuskar maimunatu dake duba lemon da zata dauko musu tayi

"Wannan ce new mom dina,ke ban sanki ba" ba unaisa da yarinyar ta fadawa maganar ba,ita kanta maimunatu taji mamakin maganar,ta dago kanta tana duban fuskarta,waye ya gaya mata itace new mom dinta?,ya akayi ta fahimci haka?,duk da dai yarinyar nada wata muguwar kwanya da kaifin basira,wanda maimunatu tafi tsammanin daga wajen mahaifinta ta gajeta.

Sauke amnan tayi qasa tana dubanta

"Itama new momma ce,kije ki gaisheta kinji" saita gyada kai,duk da bata sake jikinta ba amma haka ta nufi unaisan,abun ya yuma unaisan ciwo sosai,yarinyar ma ba zata zo wajenta ba sai wannan agwai din ta yarje

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login