Showing 189001 words to 192000 words out of 204120 words

Chapter 64 - Gurbin Ido Book One Complete Hausa Novel

itama ta koma ce masa abbuu,ya samu cikakkiyar lafiya ya kuma koma kan ayyukansa kamar daa,ya murmure fes dashi kamar babu wata jarrabawa data taba samunsa,a yanzun abu daya ya ragewa hajja shine ya qara aure,shi kuwa gani yake bazai samu mace kamar hauwa'u da shatunsa ba.

Ko yaya maimunatu ta motsa sai a kawo mata caffa,tako.ina gata da kulawa take samu,hatta su laila kaman zaayi musu haihuwar jikan fari,kusan ranaku d'ai d'aikune basa zuwan mata a yini ana hira,haka afrah itama fashin kwana daya ko biyu take,ba abinda maimunatu keyi saidai taci abinda ranta keso tasha abinda ranta keso,duk da cikin yazo mata da laulayi sosai,amma tana samun sauqi saboda akwai masu debe mata kewa.

Saidai fa duk yadda gidan yakai ga mutane,da zarar oga captain ja'afar ya dawo zai dauke abarsa ya wuce sassansa da ita,hidimarta kuma ta koma wuyansa,ita kanta maimunatu qorafi take masa ya dinga hutawa yaji da aikin office kawai amma yakance

"Da da hali zan ajjiye komai ne,nayita rainon cikin nan har sai randa kika haihu zan sake fita na barki" idan kun sake ganin maimunatu yana cikin gidan saidai idan wata muhimmiyar fita ce ta kamashi.

Tako ta ina babu abinda zata cewa rayuwa sai godiyar Allah,cikin dare daya Allah Almusawwiru ya canza mata rayuwarta gaba daya,bata da wani sauran qunci ko kuma damuwa kwata kwata,saidai lokaci lokaci takanyi tunanin inna furera,ko yaya take ciki?,me takeyi a halin yanzu,da gaske bata sonta don bata taba waiwayar inda take ba.

Abinda bata sani ba shine,inna fureran ta hadu da ibtila'i,bata da lafiya ta fita wani private asibiti da aka bude jikin rugarsu,bayan ta gama fadi tashin neman adreshin maimunatu har gembu amma kowa ya hanata,daga bisani kuma ta samu adress din,saidai har garin gombe ta shigo amma ta bace,tayita yawon neman gidan bata samu ba,qarshe ta hadu da 'yan damfara suka karbe sauran 'yan kudadenta,sai bara tayi ta hado kudin motar dawowa gida.bayan taje asibitin an gama dubata likitan yace

"Akwai wani aiki da mukeson bawa.mutane,aiki ne da yanzu yanzu zaki zama.shahararriyar attajira idan kinso" a yanzu ba abinda inna furera keso kamar wannan kalmar ta zata zama me kudi, kowacce hanyace tana jin zata iya binta,don haka tace

"Ko meye likita zanyi,zanyi wlh"

"Ba wani abu bane mai wahala,jini zamu diba leda biyu,zamu biyaki naira miliyan talatin" jin yawan kudin ya sanyata zamowa qasa,sai gata dabas zaune a qasa tana raba idanu,fillo yaji kudi sama ta ka ba tare daya siyar da kasanarsa ba=??=??=??

"Shin da gaske kake likkita?"

"Hajiya ba wasa a maganar nan,jinin muna kaiwa ana taimakawa marasa qarfi a cikin gari,saboda ku fulani kun fisu lafiya da yawan jini saboda yanayin abincinku da nasu ba daya bane"

"Aradu likkita ko yanzu ina iya kwanciya ka diba" ta fada jikinta na mazari,don har ta gama hango kudaden da abinda zatayi dasu idan sun samu,lallai magauta da maqiya ganin bayanta ba yanzu ba,ita din me sa'a ce,tayi musu shalll.....
[11/25, 12:59 PM] Safiyyatulkiram: 85


"Angel ya kika yimin haka?,kinajin naquda kika bari na tafi na barki?,bayan alqawari ne muka yiwa juna,dadi ko wuya zamu rabasu tare?" Kyakkyawan murmushi ta sauke masa duk da har yanzu da qwalla a idanuwanta

"Banason raba maka hankali ne ko na tashi hankalinka,kayimin dukka wani abu daya dace kayi din"

"Duk da haka angel,ki yafeni" ya fada yana sanyata cikin jikinsa yana kuma shafa bayanta a hankali.

Yadda taji zuciyarsa na bugawa ya alamta mata zuciyarsa ta motsu da soyayyarta,hanya mafi sauqi kenan da take gane hakan

"Ka cancanci dukka yabo da kuma jinjina" ta fada masa murya can qasa,sai kuma ta zare jikinta a hankali,da kallo ya bita

"Banyi wanka bafa,jikina duka warin asibiti yakeyi"

"Yafimin qamshin dukka turaren dake duniya" ya amsa mata yana narkar da idanunsa cikin nata,yana sake jin ta zama mallakinsa.

Motsawar da daya daga cikin yaran sukayi shi ya tuna musu da wanzuwar yaran a wajen,ya saki wani qawataccen murmushi yana juyawa zuwa inda suke,yasa hannu ya fara dauko wanda yafi kusa dashi ya dorashi saman cinyarta,sannan ya sake dauko dayan shima ya jerashi da dan uwansa,yasa hannu a hankali ya bude fuskokinsu da kyau.

Idanu ya zuba musu kamar yadda itama taketa kallonsu,cike da mamakin yanzun wadan nan yaranta ne?,mallakinta ne?,ita da ja'afar dinta?.

Gani yake kamar sun masa nesa duk da kusa dashi suke,kamar zasu kubcewa idanuwansa,kawai sai ya ranqwafo dab da fuskokinsu yana sake qare musu kallo,dai dai sanda dayan shima ya motsa ya tura hannunsa a baki ya fara tsotsa.

Dago kansa yayi sai suka hada ido,ta tabe baki gami da yamutse fuska

"Kaga kura da shan bugu ko?" Wata qawatacciyar dariya ce ta subuce masa

"Wonderful,na dauka idanuna kemin gizo,ashe da gaske ne photocopy na na baki, alhamdulillah,kinga tun yanzu suna alamta miki da daddynsu sukeyi ba dake ba" rigimar ganga ta saka masa shi kuma ya lalace wajen lallashi,kamar ba mutane ke jiransa a waje ba

"Kin manta yanzun kin girma ne?,maman twins ce ke fa?" Ya rada mata a kunne,saita sunne kanta a kafadarsa tana dariya

"Karki damu,next year photocopy dinki zamu ajjiye,kinga shikenan rigima ta qare" ido ta fidda tana dubansa

"Mutuwa kakeso nayi hubby?"

"Ba zaki mutu ba,saikin haifan kamar haka kamar haka sau shida,suma sun bani jikoki kamar hakan" ya qarasa maganar yana debesu ya maida su gadonsu dake kusa da nata,sannan ya dauko tea din da umma sa'adah ta ajjiye ya dawo kusa da ita ya zauna sosai cinyoyinsu na gogar na juna,har sannan binsa take da kallo,idan suka kebe ya sake mata kamar hakan nan saika rantse da Allah ba shine ja'afar marwan akko ba

"Haaa.... bude bakin ki karba" hankali kwance ya zauna yana bata tea din,tana sha yana mata tambayoyi game da haihuwar tata tana bashi amsa,gab da zata shanye dr noor ta turo dakin ta shigo,kanta tsaye bata wani koma da baya ba,don itama wayayyar 'yar boko ce,wannan din ba baqon abu bane a wajenta,sai suka gaisa tayi masa barka sannan ta wuce wajen yaran kai tsaye tana sake kallonsu,yaran sun bata sha'awa matuqa,bama itaba,duk wanda yaji labarin an haifa twins yaran captain ja'afar akko sai ya leqo ganinsu,ya kuma tafi da kyansu da girmansu a baki,wannan yasa tuntuni hajja ta tofesu da addu'o'in tsari

"Bakin dan adam bashi da kyau,wasu jariran da yawa tun a nan ake nakastasu,wasu suke rasa rayuwarsu,wani ma zai tanka abu baisan yana da kambun bakan ba,sai musiba ta fadawa abu yayita lalacewa a rasa dalili"(haka zancan hajja yake,don Allah komai zamu gani ya burgemu bama akan mutum kawai ba mu dinga shuru da bakinmu koda zuciyarmu ta yaba,idan ma ya zama dole sai.munyi magana mu hada da tubarkalla.ma sha Allah,wasunmu da yawa basusan suna da kambun baka ba,da yawa qila sun zama silar lalacewa ko mutuwar wasu amma basu sani ba,mu kula,kambun baka daban maita daban,a musulunci babu maita,amma akwai kambun baka,mu zama masu yawan fadin ma sha Allah,kome muka gani ya burgemu,ko uwa baason ki fiya yaba kyan danki ko wani abu nashi,zai iya yiwuwa kina da kambun bakan ke a karan kanki amma bakisan kina dashi ba,sannan mu iyaye mu dinga kula da yawaita yiwa yaranmu addu'a,musamamn idan zamu fita wani waje,musamman kuma idan Allah ya musu baiwar kyau ko wani abu,ga masu zuwa kasuwa su dinga haquri suna aje yaran a gida,mu rage yabon yaranmu da rage yawan fadin baiwarsu,kamar baiwar wayo ko basirar karatu,wani da ya tanka shikenan,sai kiga karatun yaro nata komawa baya a rasa daga inda matsalar take,karmu manta da addu'ar da annabi kewa jikokinsa sayyadina hassan da hussain,Allah ya kare mana su daga mugun ido da mugun baki ameen summa ameen).

"Allah ya raya su,ya albarkacesu captain, congratulations" ta fada tana duba maimunatu

"Thank you dr noor" ya fada shima yana jin dadin kulawar da take bawa familyn nashi.

"Yauwa komai lafiya lau,zaku iya tafiya nan da awa biyu,amma ya kamata su fara shan nono yanzu,saboda wannan yellow din nonon kada lokacin samuwarsa ya wuce,yana da amfani sosai a jikinsu".

Cikin awanni biyun suka gama shirya komai sai tafiya gida,a nan fa aka fara dambarwa,anni na cewa gidan dr zaa wuce da ita,hajja na cewa gidan wajenta zata je,yayin da umma sa'ada ma ke ganin ita yafi cancanta ta karbeta,saidai shi ogan ba wanda ya cewa komai,sai tsintarsu sukayi a sabon gida,ainihin gidan da shaheeda ta zauna,wanda aka sake gyarawa aka kuma sake canza masa fasali,tuni ya gama aikinsa an zuba komai,suturun sawar maimunatu kawai zaa dauko,don twins dakinsu ya dade da kammala,an sanya komai da yara zasu buqata,da gadajensu na kwanciya kowa nashi daban.

"Shikenan dan uwana ya raba magana" anty maama ta fada tana dariya,don ita kanta yadda yaran suka shiga ranta,inda zaa bata maimunatu karba zatayi da gudu,shuru tayi dai kawai ganin masu son karbar nasu nada yawa,kuma duka sun fita cancanta.

Cikin kwanaki shidan da suka biyo baya kusan kullum gidan cike yake da 'yan barka,masu wuni da masu zuwa su tafi,yaran sunzo da wani albarka da kuma farinjini na musamman,ba daga dangin maimunatu ba daga dangin ja'afar ba,ga 'yan uwan amma suma da baa barsu a baya ba,don wadan nan sune jikokin fari a wajenta.

Baaba tabawa ke zaune a gidan,sai wata mai aikin yasira da anty sa'adah ta kawo mata,gefe daya ga afrah da take wuni sai dare take tafiya,kullum akwai driver da zai daukota ya kuma dawo da ita permanent wannan umarnin captain ja'afar ne.

Tun afra na iya irga kayan barka da abinda maimunatu da yaranta suka samu har ta bacewa lissafi,saidai ta karba takai dakin yaran ta ajjiye kawai,ita kanta batasan adadin mutanen da sukazo mata ba suka mata alkhairi,bata taba sanin ja'afar mai mutane bane har haka sai data haifa 'yan biyu,tarin tururuwar mutane,wasunsu shi kansa bai sansu ba,duk da haka ba'a hana kowa shiga gidan, saboda anni tace albarka ce,kuma lokaci ne.

Hatta abbu da abbi baa barsu a baya ba,kowanne sai daya tako qafa da qafa yaga jikokinsa,kuma kowannensu sai daya ajjiye musu barka mai nauyi,bama kamar abbuun da yakejin su kamar 'ya'yansa,yana ji kamar shi aka yiwa haihuwar shi da yake da qarancin zuri'a.

Kayan lefen da aka ranta masa kudi aka masa aka sanyashi biya su ya maimaitawa maimunatu wannan karon,akwatina yayi mata sosai kamar yadda kowanne yaro a cikinsu aka masa nasa,duk da komai nasu iri daya ne,kasa cewa komai maimunatu tayi,saboda gatan da ja'afar din ke gwada mata har gani takeyi yayi yawa

"Kadan daga aikin manya,indai zuciyarsa naso....to babu algus a soyayyarsa,da dukka zuciya ruhi da gangar jikinsa yakeyi a aikace" baba tabawa ta fada,jinjina kai kawai maimunatu tayi,don ita din ganau ce ba jiyau ba.

Hankulan abbuu hajja da umma sa'adah ya kwanta sosai,iya soyayyar da ja'afar ke nuna mata da danginsa kadai ya tabbatar musu koda babu su maimunatu ba zata wulaqanta ba.

Ranar suna tun asuba abbi da abbu kowa yayi radin suna a masallacin unguwarsu,akayi rabon goro da alawa aka fadin sunan yaran,marwan abbinda abubakar saddiq abbu,a nan gida afrah ta zaba musu nickname da (sa'ad da as'ad).

Gidan dr kuwa suna sukayi sosai,yayin da gidan captain ja'afar sukayi nasu sunan,fadin irin kyan da maimunatun tayi bata baki ne,don kusan sau hudu ja'afar yana dawowa gidan ta boyayyar qofar baya,don kawai yazo ya sake ganinta ita da yaran nashi masu zubin diyan larabawa kamar yadda baaba tabawa kan fada idan ta gama musu wanka ta shiryasu tana dan musu rawa.

Dukka danginta sun amsa kira,abinka da mai dashi,tun daga gembu har adamawa,abun farincikin tron suna ya watse lafiya,gift data samu kuwa tattarasu tayi tace ba zata iya budasu ba sai ta huta sosai.

Kwanaki biyu rak gidan ya zamana iya na masu shi,sai baaba tabawa da kuma yasira,saidai duk da haka lokaci lokaci daga can gidan abbunta ko gidan dr marwan suna shigowa dubata tare da ganin yara.

Cikin wani irin gata da kuma kulawa ta shiga rainon yaranta,gefe daya kuma hajja tana tsumata da gyara na musamman,dukka wata kulawa ta buri ta dorawa jikokin nata biyu afrah da maimoon,kasancewar bikin afra ya matso,sai ya zamana duk wani gyara da za'a yi mata tare da maimunatun take hadawanata gyaran har yafi na maimunatun,sosai hajja ya bude tsohuwar ajiyarta na tsohuwar babarbariya,ta shiga gyaran jikarta da kyau,duk wani gata daya dace tayi mata lokacin biki da bata sameshi ba yanzun take zubeshi,daga ita har abbun,shi kansa garar da yayi mata mai uban yawa abar kallo ce,duk da ja'afar din yace baya buqatar komai amma kuma abbun yace ya sani yayi haquri,aladace,kuma alada mai kyau ce wadda musulunci baiyi suka ba.

Sosai itama ta hada hankalinta da kyau wajen kula da jikinta yaranta dama mijinta,a yanzun take jinta a matsayin cikakkiyar macen aure kamar kowacce diya mace,tayi kwance kwance tana debe tsaffin dabarun kama miji ba boka ba malam daga bakin hajja sa baaba tabawa,sannan tana samun sabbabi daga wajen afreen dinta da kuma fatiman jabir wadda tuni ta haife nata boy din don har ya fara wayo.

Kafin tayi arba'in gaba daya ja'afar din ya sukurkuce mata,kulawar da take bashi kamar wani fami da kuma qwalele take masa,tako ina ta cika sosai,ta qara kyau da haske,ga wasu fitinannun turaruka da take amfani dasu,randa ya ritsata a daki akaso yin aika aika Allah ya qwaceta da qyar,tun daga ranar take takatsantsan,don so take itama saita cika kwanakinta sannan ta rikeshi yadda zata ida rikitashi da kyau.

_sai muce Allah ya qara danqon qauna moon din captain>?p?=?
?=?
?,muje zuwa ga page din qarshe in sha Allah_
[11/25, 12:59 PM] Safiyyatulkiram: 84

Kallon kallo suka yiwa juna na wasu daqiqu kafin hajiya Aayah ta janye idanunta,ta sake tabbatar da izzar sa da kuma jin kan da akace yana dashi,ta sani,jinin gidan marwan akko ne,kuma jikoki ga maryam farouq kumo,ta wani fannin kuma shi din jinin sarautar wani yanki ne na qasar gombe daya gada daga kakansa mahaifin aishatu mahaifiyarsa,bai tsintsa a qasa ba

"Sai yau suka turo ka ka maidata kenan?......" Ta fada tana dubansa kai tsaye cike da burin nuna nasa martaba da darajae diyarta,daure masa kai maganar tayi,kafin yace wani abu duk da baida niyyar tofawar ta sake magantuwa

"Wato ga mara galihu wadda aka gaji da ita aka baka sadakarta,kq koromin diya gida babu abinda ta aikata maka,bayan ka jingineta cikin gidanka ba sid'i ba sad'ad'a.....lallai munubiya tayi gaskiya,duk sai yanzu zancanta ke bayyana sosai,na yarda nayi sake dana bar unaisa tabi zabin ranta......to wai shin ma kai ke aurenta ko wadan can tsofaffin da ka baro a gida?" Kai tsaye ya qanqance idanuwansa cikin nata yana dubanta,mai takeson fada?,martaba da muhibbar mahaifansa take shirin tabawa ko kuwa yaya

"To bari kaji,ina raye unaisa ba zatayi zaman boranci ba,yanda suka rayu ba wanda ya takura musu haka 'yata zata rayu,kaje ka gaya musu,indai sun shirya zama da diyata dole su martaba ta su kimantata su kuma daukaka darajar ta,don ita din me daraja ce,indai kanason zamanka da ita dole kasan darajar ta da kimarta"

"Idan kuma akaqi fa?" Ya fada yana jin wani abu na tsaye masa a wuya saboda taba masa ababen da duk duniya bashi da kamarsu,cikin mamaki take kallonsa

"Saika sawwaqe ma diyata,tunda dai aisha ko maryama ne suka haifamin ita ba" gam ya runtse idanunsa,tabbas da haduwar hanya sukayi da matar nan ba abbi bane sila sai ya nuna mata zallar kuskure da kuma wautar data tafka yau din.

Da gudu kuma cikin kuka unaisa data gaza gamsuwa da tahowa mommyn nata ita daya,ta biyo bayanta ta kuma labe tana sauraren abinda ke afkuwa ta afko dakin cikin kuka

"Haba mommy.......ya zakice haka?" Da mamaki take kallonta

"Ai biyoni kikayi?,to idan bance haka ba me zance,shashasha kin tsaya kamarki namiji na wahal dake kamar shine autan maza,to indai bazai sanyaki a gaban kowacce diya mace ba ciki harda uwarsa wallahi bazan bari kici gaba da zama dashi ba,don ke din mai daraja ce" idanu ya zubawa unaisan yana son hango darajar da hajiya Aayah ke magana akanta tattare da unaisa,hala bata da masaniyar komai,darajar daya tabbatar babu ita sam,amma zai basu assignment mai wahala,zai kuma bar musu tabo,ya zaro hannunsa dake dunqule a aljihunsa,wanda sai sannan yaji saman receipt din da aka basu a wancan eatery din ya dora,ya maida hannunsa ya zaro reciept din tare da ciro wani irin biro mai hade da pen perfume.

Yana dora hannunsa saman takardar unaisa ta saki mommyn ta taho da sassarfa tana isowa gareshi

"Don Allah kada ka aikata,zan zauna zan kuma zama duk yadda kakeson gani na,wallahi mommy laifina ne,nice nayi masa laifi,ni na jawo yacemin na taho" ta fada cikin kuka gami da dana sanin gayawa haj Aayah duka magangun da haj munubiya ta kitsa mata,hadi da janyo hajiyar tazo har gida ta sake tsarawa mommyn tata zance,duk tayi hakane don a sake azawa ja'afar rashin gaskiya,a kuma yi masa kaca kaca

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login