Showing 195001 words to 198000 words out of 204120 words

Chapter 66 - Gurbin Ido Book One Complete Hausa Novel

Yadda take taunar abinda ke cikin plate din ya burgeshi,saboda yadda dan qaramin bakinta yake juyawa,tsigar jikinsa ta zuba,ya matsa kadan sannan a hankali ya riqe fuskarta ya hade bakinsu waje daya.

Sai daya tsotse dukka labban nata da sauran maiqon dake kai,tuni plate din hannunta ya yafi yayi nasa waje,abinda yake ciki ya watse,dauke kansa yayi a hankali yana maida numfashi,shi da ita suna kallon farantin dake watse a qasa,tabe baki tayi kamar zata saki kuka tana duban yadda dan waken yayi d'ai d'ai,dubansa ya maida kanta

"Meye wannan?"

"Dan wake nane fa?,kaga abinda kayimin" ta fadi a mugun narke,da alama qiris take jira ta saki kuka,murmushi ya saki yana dan take yatsunta da nashi

"Yanzu tsakani da Allah ni na zubar miki?,ba ke kika zubar da kayanki ba?, mene abun dadi a nan ma fulawa ne ko da menen?,kaman bama" baisan hakan daya fada tunzurata yayi ba,kawai saita sake masa kuka

"Ragowarshi kenan fa,Allah saika sakemin wani" ta fada tana hawaye daya na bin daya

"Bari na kira baaba tab....."

"A'ah" ta fada da sauri tana maqale kafada

"Ni kaine zaka yimin" hannu ya dora saman kansa yana dubanta,sai kuma dariya ta kubce masa

"Bansan ta yadda akeyi ba" kafin ta amsa baaba tabawa tayi sallama ta shigo ajjiye flask din abincin ta

"Subhanallah me ya faru?" Ta tambaya,tana kuka tana gaya mata ja'afar ne ya zubda mata dan wake,kuma tace ya sake mata wani yace zai kirata

"Ikon Allah.....sai haquri manya,yanayin nata cikin kenan,yanzu kiyi haquri na sake miki wani"

"Shi zaimin Allah,shi ya barar min"

"Jeki baaba zanyi" ya fada yana tattare hannuwan rigarsa

"An shiga uku toh....." Baba tabawa ta fada taba riqe baki tare da dafe kai,wannan rigimar bata taba ganinta wajen maimunatu ba sai yau,itakam ba zata iya kallon babban mutum mai matsayi da kima kamar ja'afar ya gwaggwafe yana dan wake ba,sai ta fice daga kitchen din tana cewa

"Allah ya sawwaqa".

Cikin lokaci qalilan ya fuskanci dan waken nan fa bazai yiwu ba,ga maimunatu ta kasa ta tsare,asalima hira ta koma tana masa ko a jikinta,jira take ya.kammala taci,shuru yayi sai kuma ya kashe gas din,kafin tace komai juyo ya dauketa cak,sai ta dubeshi

"Baka gama ba fa"

"Babban son of beans zan baki,zo muje kiji" ya fada dukka jikinsa yana amsawa,gaba daya ta canza masa,cikin ba qaramin qara mata daraja da martabar da mace ke samu a auratayya yayi ba,duk da dama maimunatun yayi imani da ta dabance,sosai madarar shanu ta ratsata tun tana qaramarta.

Ko acan babbar bedroom din shagwabe masa tayi,tanata qwallar shagwaba shi kuma yana biye mata,a sannan kaga yadda lallabarta kamar qwai sam ba zaka ce shine wannan Captain J din ba,matuqin jirgin sama,kuma babban dan kasuwa,maabocin izza miskilanci shan qamshi da jin kai ba,gaba daya ya sukurkuce maimunatu,wani lokaci har tsoro yake bata.

Tare sukayi wanka kamar yadda ya saba mata,yakan gaya mata sunnah ne mai qarfi yin wanka tare da iyali,saita koma jikin kujera ta takure kamar wata 'yar mage,don tun dazun tace masa tana jin sanyi.

Binsa take da kallo sanda yake taho wa wajenta dauke da wasu fararen socks masu taushi,yayi mata kyau sosai,kayan daya sanya din sun amsheshi ba kadan ba,ko yaushe sake fresh yake da kyau,ko ba'a gaya maka ba hankalinsa a kwance yake.

A hankali ya duqa gabanta idanunsa cikin nata,farare sol din qafafunta ya kama ya soma zura mata safar,har ya gama tana kallonsa,sai yasa hannu yaja kumatun ta

"Wai duk yunwar dan waken ce?,kada ki cinyeni angel" murmushin ta saki tana lumshe idanu,tuni ya bata abinda yafi dan wake,a hankali tace

"Idan na cinyeka kuma wa zan kama?,kawai ka yimin kyau ne,so nake na haifo baby me kama da kai" dan fuska ya bata cikin salon tsokana

"Baby ko babies?,biyu ko uku nakeso,kuma masu kama dake ni nakeso" kafada ta maqale tana murmushi

"Ban yarda ba,nafison me kama dakai gsky" ido ya zaro

"Angel......kina kallon kanki da kyau kuwa,kinsan yadda Allah ya tsara halittarki?,duk sanda na kalleki saina yima daada addu'a da fatan dawwama a aljanna data haifomin ke" murmushi tayi tana sake lumshe idanunta,farincikin samun miji d'aya da d'aya kamar ja'afar na sake kamata,bata da abinda zatace da anni itakam a rayuwa,ta gama mata komai data hadata da d'an jikan nan nata,wanda ya hada komai na rayuwa,ko a aljanna shine zabinta

"Ko baki qoshi bane naga kina wani kallona qasa qasa?" Ya fada cikin sigar tsokana yana kai hannuwansa saman qirjinta daya soma cika sosai saboda yanayin ciki,hannuwansa ta ture tana bata fuska hadi da turo baki

"Nifa yunwa nake ji Allah,a bani abinci ko kuma na cinyekan" tattausan murmushi ya saki yana dora kansa saman cinyarta ta tadda zai iya ganin fuskarta sosai

"Bana gajiya dake angel,bana gajiya da kasancewa tare dake,you are my world angel" a hankali ta dora tattausan lips dinta akan nasa,ta bashi wani hot kiss,sai ya lumshe ido yana fadin

"Wash Allah amma,zata kasheni" dariya ya bata sosai har tana qyalqyalawa,gami da sanya hannunta ta rufe fuskarta.

Babban hijab ya dauko mata yace suje taci abincin a wani wajen,daga nan tadan tattaka ta miqe qafart,hakan yayi mata,taji dadi sosai,don tunda ta kwanta ciwon bata fita ba.

Leqawa tayi ta gayawa baaba tabawa zasu fita,tayi musu adawo lafiya tana binsu da kallo,murmushi kwance akan fuskarta tana mamaki.lallai mata suna da wata babbar baiwa da daraja,mutum kamar ja'afar amma yarinya kamar maimunatu ta sukurkutashi,inda wani na waje aka baiwa wannan labarin zai qaryata,captain ja'afar a kitchen yana sakun dan wake(>?#?>?#?kadan daga aikin mata,munfi gaban haka,talaka ko mai kudi ko malami dukka a tafin hannun mata suke,Allah dai ya qara mana albarka da juriyar haquri da mazanmu,ya qara mana qauna da fahimtar juna a tsakaninmu,ameen)

A hanya yake gaya mata ya sama mata malama da zata dinga zuwa kullum,qarfe sha daya na safe zuwa biyu kullum suna karatu,muhimman subjects da take buqatar samu a waec neco da jamb dinta,in sha Allah karatunta bazaya tsaya ba.

Qwararriya ce sosai matar,hasalima hausa kadan kadan takeji,sunanta miss serah,sosai taji dadi, hankalinta kuma ya sake kwanciya,don yanzu babban burinta a yanzu shine ta zama full house wife,ta kyautata masa matuqa kamar yadda taga daadarta tanayi sanda take raye,gata da soyayyar da ja'afar ke nuna mata babu wani abu da zata saka masa dashi face nuna masa zallar soyayya da kulawa.

Wannan eatery din mai tsada daya saba zuwa ya kaita,yace yau sai ya qureta,ta zaba duk abinda takeso a kawo mata

"Zan baka mamaki"

"Haka nakeso" ya fada yana zube mata idanun nan nasa,ta kuwa zaba abinci kamar hauka, waitress din ta kalleshi

"Sir,total din fa da yawa" fuskarsa a dan daure kamar yadda ya saba zama boss dinsa duk sanda ya fito ya kalleta

"Kiyi aikinki kawai,ba ruwanki da abinda za'a charger"

"Ok sir" ta fada tana juyawa a ladabce,cikin zuciyarta tana jin inama ace itace maimunatu,tunda suka shigo idanunta yana kansu,wata irin madarar soyayya take gani suna zubarwa zallarta(haka dan adam yake,a duk sanda kaga wani ya zama wani,ko ya taka wani muqami,burinka kawai dama kaine shi?,shin kasan irin qayoyin daya taka ya wuce a hanya kafin ya iso bigiren da yake kai?,so duk wanda ya zama wani akwai qalubale taf daya haura kafin yakai tudun nasara,jajircewa haquri da juriya gaskiya da amana suke kai dan adam duk wani mataki a arayuwa,kamar yadda amanar maimunatu ta sake baiwa anni sha'awa wajen hada iri da ita).

Tun tana ci cikin marmari yana tsokanarta har ta fara zare idanu,dariya irin wadda ya jima baiyi ba ya dinga mata,har sai daya sanya hannayensa dukka biyu ya rufe fuskanshi,Allah yasa babu kowa a kusa dasu.

Sautin kukanta kawai yaji,ya daga kai da sauri yaga tana hawaye

"Ya salam,me kuma akayi miki?"

"Ba kaine ba kakemin dariya saboda ban cinye ba?" Lallai shagwaba ta sake gaba,haka don dole ya danne dariyarsa ya dinga rarrashinta,ya lallaba kayarsa suka biya bill suka wuce.

Yanason cika umarnin abbi,don haka ya biya gidan umma sa'adah ya ajjiye maimunatu yace zaije ya dawo,ta gaida umman,cikin murna da zumudi ta shige cikin gidan yaja motar kai tsaye zuwa gidansu unaisa.

Yana shiga gidan guard din suka fara rige rigen gaidashi,kafin a shiga cikin gida a gayawa haj Aayah zuwansa,babban parlor din da ake sauke baqi na musamman a gidan tasa aka kaishi,ta dubi unaisa wadda tunda taji ance captain ja'afar ya iso ta miqe ta zauna daram,zuciyarta gaba daya tana gareshi,ta gaji da dakon zuwansa,ta kira wayarsa har sau babu adadi bai daga ba,shi yasa ya samu daddynta da maganar,shi kuma ya gayawa abbi wanda da farko baisan me ake ciki ba.

Cikin shigar alfarma haj Aayan koda yaushe take,macace mai izza taqama da fadin rai,duban unaisa tayi,tana jin haushinta yana cikata yadda taga ta rikice daga cewa yazo,tana jin bacin ran yaron a ranta,diyarta kamar unaisa ta zauna wannan auren jeka nayi kan,ga yaran qawayenta 'ya'yan wasu wadanda takeso ta aura mata su amma fir yarinyar taqi sa taimakawar qanwarta anty talatu,yau zata kawo qarshen komai

"Ki zauna,ni zanje na ganshi" kai unaisan ta daga badon taso ba,haka kawai taji ita hankalinta bai kwanta da ita ba,amma sai ta koma ta zauna kawai.

Ko zama baiyi ba,yana tsaye a falon ya baiwa qofa baya yana duba wata calendar dake dauke da hotuna da bayanan shugabannin da suka mulki nigeria yaji sallamar haj Aayah maimakon unaisa.

A nutse ya juyo suka hada ido ita dashi,ta zuba masa idanu tana karanto abubuwa da yawa da suka janye hankalin diyarta a kanshi,bata taba masa kallon tsaf ba sai yau,tabbas ya cika namiji,inda unaisa zata samu yadda takeso a game dashi babu abinda zaisa ta shiga lamarinsu,yayin da shi kuma kallon farko ya karanci akwai abinda ta shigo dashi,sai ya sake dai daita kansa,ya tattara dukka wani izza da kwarjininsa waje guda
[11/25, 4:47 PM] Safiyyatulkiram: 86


*BAYAN WASU SHEKARU*


Babban dakin taro ne wanda ya cika maqil da zallar mata,manya mata masu ji da aji da kuma jin sun kai wani matsayi sun kuma taka mataki na rayuwa.

Daga can step inda mai gabatarwa take,ta qarashe bayaninta da fadin

"We will call our star that we have gathered here to honor her......maimoon abubakar muhammad" ta qarashe kiran da madaukakin sauti.

Shuru dakin taron ya dauka,kowa ya tattara hankalinsa gami da zuba idanuwansa yana jiran ganin bullowarta,wasu sun santa,amma kuma ako da yaushe basu gajiya da ganinta,ita din ta dabance,tun daga yanayin halitta zuwa suttura da kuma yadda tasan mutuncin dressing,idan akace dressing to dressing mai nuna zallar kamala da kuma aji a rayuwa,dai dai da qamshinta na musamman ne,baa maganar sauran abubuwa,wadanda kuma basu santa din ba,zumudi suke suyi tozali da kyakkyawar fuskar da labarinta ya cika kunnuwansu kafin zuwan wannan rana,fuskar data zama ta alkhairi kuma jirgin fito ga duk wani mabuqaci mai neman taimako,fuskar data hadu da qalubale da gagwarmayar rayuwa iri daban daban,amma tayi hobbosa ta tabbatar bata koma baya ba.

Cikin nutsuwa sautun takalman qafarta dake da tsinin dunduniya maras tsaho suka ratsowa ta cikin mutane,sai ta dauki hankulan mutane da dama nima na juya don ganin tahowar tata.

Kyakkyawar farar bafulatanar usul,mai wani irin haske daya cakude da surkin jaja jaja,tamkar jini zai diga a jikinta saman lallausar fatarta mai santsi da sheqi,wadda ke nuni da zallar hutu wadata da kuma jin dadi,ma'abociyar wani irin kyau mai fusgar hankali da wani irin kwarjini daya cakude da zallar kirki da son jama'a dake saya mata soyayyar mutane duk inda ta tsoma qafarta.

Sanye take da dark blue din wani yadi na mata,wanda aka yiwa ado da light blue da kuma yarfin gold din zare,kalar data sake fitar da kyanta,wani lafiyayyen mayafi ne a jikinta da bashi da shara shara ko kadan mahadin lafiyayyan takalmin qafarta mai madauri,hannayenta kana iya hangen warwaraye masu fashion masu tsadar gaske,wanda zaka tsammaci gold ne,amma ba shi bane,kasancewar sam bata da sha'awar amfani da gold din.

Ci gaba tayi da takowa har ta iso wajen,ta karba abun maganar tana duban fuskar mc din,tata fuskarta dauke da murmushi,sanna ta maida dubanta ga matan dake gabanta,gyara zaman fararen eye glasses din data sanya don qawata adonta tayi,sannan tayi bismillah ta fara magana cikin tataccen turancinta daya cakuda da zazzaqa kuma lallausar muryarta.

Duk wata hayaniya tsaiwa tayi,muryarta tacu gaba da tashi har ta gama ta koma yarenta na fillanci,a nutse ta waiwaya tana miqawa mc din loud speaker din tana dan kare fuskarta da hannunta da yasha jan lalle saboda hasken flashes na kyamarori,karban abun maganar tayi tana kiran sunayen wasu matan manya da sukayi fice wajen bada taimako,suka qaraso wajen suka miqa mata dukka kyaututtukan da aka tanada saboda ita.

Fuskarta dauke da murmushi da kuma hawayen farinciki ta sake karbar abun magana

"Inama mijina yana kusa!" Maganar da taja hankalin kowa a wajen,sai suka maida dubansu gareta,dan qaramin murmushi ta saki

"Eh haka nace,inama mai gidana yana kusa,shi yafi cancanta da ya karba dukka wadan nan karramawar....kunsan dalili?" Kusan hada baki sukayi wajen fadin

"A'ah"

"Saboda da bazarsa nake rawa,hakanan shine tsanin dana taka har na zama abinda na zama a yau,da shawarwarinsa taimakonsa da kuma gudunmawarsa nake dukka wasu abubuwan yabawa da kuke gani a yanzu,ina fata a duk inda yake Allah ya karemin shi da kariyarsa ya dawomin dashi gida lafiya don sirrin hasbunallahu wani'imal wakil" kabbara duka matan suka saki,dai dai da sanda ja'afar ya lumshe idanunsa yana lafewa a bayan mota,live yake kallon yadda taron ke gudana,da taimakon d'ansa as'ad dake dauko masa komai ta wayar hannu video call ta watsapp.

Sai yaji.kamar lokaci yaqi gudu,awa hudun da zaiyi kafin jirgi ya saukeshi a nigeria saita koma masa kamar shekaru hudu,wani kewar matar tasa ta dinga ninkuwa cikin ransa,shikam da dan adam yana kyautar aljanna a duniya,tabbas da ya yiwa maimunatu kyautarta tun a nan halak malak,baisan wanne irin so take gwada masa ba sa kullum qara gaba yake.maimakon yayi baya,baisan wacce irin kulawa bace wannan tamkar jariri sabon haihuwa.

Duk yadda mutane suka kai ga tsareta suna son gaisawa da ita,wasu suna daukan hoto da ita hankalinta yana kan lokaci,duk bayan mintuna sai ta duba agogo,yau rana ce mai.muhimmanci a wajenta,kuma lokacinta mai tsada ne a yau din,saboda ja'afar zai dawo daga tafiyar da yayi,bayan ya kwashe wata guda baya nan,normally koda office yaje ya dawo bata wasa da bashi kulawa,koda kuwa tare da waye take,zata katse komai ta bashi hankalinta tunaninta jikinta dama lokacinta,takan ce shine kadai dan abinda zata iya masa,tunda ta fuskanci a duniya abinda yafiso kenan,ya jita ko yaushe a kusa dashi,koda zama tayi masa hira ne ya wadatar.

PA dinta taja gefe ta kuma yi mata bayanin uzurin da take dashi,da qyar ta samu ta sulale ta qofar baya ta samu ta fice inda driver yake kiranta,sauke wayar dake hannunsa as'ad yayi yana duban fuskar mahaifinsa ta cikin screen din wayar yana murmushi

"Abyy.....ummu ta gudu fa" murmushi ne ya subucewa masa yana gyada kai,yasan ta gudu ne saboda shi,a duk sanda yace mata gashi a hanya zuwa gida.....kome takeyi hankalinta yabar kansa ya koma gidan,har sai ta tabbatar ta samar masa da duk abinda zai iya nema ko buqata

"Kace ina mata sannu tare da ban gajiya kafin na iso"

"Zataji abby....amma abyy,pls saqona fa?,baka manta ba?" Kai ya gyada

"Ina sane ranka ya dade
'
"Thank you aby" ya fada yana dariya gami da kashe wayar,ya kuma fella yana bin bayan mahaifiyarsa da sauri.

Daga nesan farfajiyar wajen take iya hangensu,gajee ce goye da nasma tana riqe da hannun nasim tana musu 'yar tsere,fuskarta dauke da dariya sosai,dukkan alamu sun nuna tana jin dadin kasancewa da yaran.

Daga gefe kuma saman kujerun da aka tanada a farfajiyar dai,sa'ad ne zaune riqe da tab dinsa shi daya yana faman dannawa,kamar mahaifinsa,shi ko da yaushe ba mai hayaniya bane,hakanan ba mai son damu bane,yafi ganewa zaman shuru,rashin son hayaniyarsa ya sanyashi baro hall din,ya gwammace surutai da maganganunsu nasim akan qarar amsa kuwwar hall din.

Daga gefe asim ne yake musu tafi yana biye da waqar da gajee keyi musu,shikam kusan halinsu daya da as'ad din,ba ruwansa,dan wasa ne,ya dauko kawunsa uncle JB kamar yadda suke ce masa.

Idanuwanta ta maida kan gajee,gaba daya ta canza shekaru biyar kenan da suka shude,tun bayan mutuwar inna furera wadda ta rasu saboda lalacewar qodarta guda daya data tabu,dayar kuma an yanke an dauke,bayan ta rasun gajee data auri saurayin ta bayan ta gama zuba rashin kunya da diban albarka kan shi takeso,wata biyu kacal ya ajjiye mata saki cikin dare suka kada shanunsu suka qara gaba,haka ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login