Showing 138001 words to 141000 words out of 204120 words

Chapter 47 - Gurbin Ido Book One Complete Hausa Novel

ta aje gefe,tana dariyan maganan amna,tunda dai yau ta tayata yanka veggies ta damu kowa da zancan ita tayi girki,sai ta miqe ta shiga kitchen din,ta hada komai a basket din ta riqowa amnan,har zuwa dab da inda motarsa ke kunne yana jiran amnan.

Tana hangoshi yadda yake duba agogon dake daure ga tsintsiyar hannunsa,sai ta gyara tsaiwarta sosai,ta kuma tsaya a wajen data tabbatar bazai ganta ba,so take ta qare masa kallo irin wanda bata taba ba tsahon saninta dashi,tanason ta gano dame yafi sauran maza da yake da kwarjini izza da kuma qasaita har haka?,saidai tun batayi nisa da bin qwaqwafin nata ba ta fara ganewa cewa tabbas da bambanci,sai ta lumshe idanunta tana sauraren sautin bugun zuciyarta,ta cikin idanuwanta kuma tana hango wancan lokacin da ya sanya yatsunsa biyar saman fuskarta,ta bude idanunta da hanzari kamar a lokacin abun ya faru,ta saukesu a kansa sanda ya saki wani qasaitaccen miskilin murmushi yana jan kumatun amna bayan ya karba kwandon hannunta.

Qaramin tsaki taja tana kauda kanta daga dubansa,haushinsa yana saukar mata,sai ta juya a nutse tana barin wajen,ta tsani duk mutumin dake busa hayaqi qwarai,har batason hada muhalli dashi,batasan ya akayi take manta wannan a kansa ba.

Koda ta koma sabgarta taci gaba dayi cikin gidan ita da amna,bata tashi tunawa da wayar ba sai da azahar bayan ta idar da sallah amna tayi bacci, fiddota tayi daga kwalinta ta budeta,sabuwa ce dal,sannan daga gani ba qaramar waya bace,mamaki ya kamata,me ya sami tata wayar?,bata sani ba,iya abinda zata iya tunawa kawai shine sanda wayar ta sulale ta fadi daga hannunta sanda ya tareta ya sanyata a wata iriyar koma.

Baki ta tabe ta miqe ta jonata a charge,sannan ta dawo ta kwanta saman kujerar ta buda daya daga cikin novels din afra dake wajenta,wanda batasan ta hado dashi cikin kayanta na makaranta ba,sai yanzu data qarasa zazzage akwatin,don baifi kwanaki goma sha hudu suka rage musu komawa makaranta ba.

Guraren qarfe uku da rabi taji ana knocking sassan unaisa,sai ta gyara kwanciyarta bayan ta duna lokaci,taci gaba da karatunta,sosai littafin yake daukar hankalinta,batasan ya akayi ta qulla alaqa me qarfi da films na soyayya da litattafansu ba,zama da madaukin kanwa,afra ta koya mata qarfi da yaji.
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 57

A hankali ta sake dawowa saman gadonta tana runtse idanu tare da sake cije lebanta ta kwanta a hankali kamar wadda ke da gyambo a jikinta,karo na uku kenan tana shiga bandaki tana canza pant dinta tare da sake tsarki,sai a sannan ta tuna da maganin dazun da tasha na wajen anty maama,ta tuna yadda ta tankwabe gorar daga hannun laila dake niyyar sha,filo taja ta dora kanta tana sake tuna abinda anty maama tace da laila

"Baki da hankali ne laila?,baki gane me nake nufi ba kenan?,to kika sake kika sha wannan yau saidai abbi ya bada sadakar aurenki ko babu sadaki" tana kaiwa nan wasu hawaye masu dumi suka silmiyo mata zuwa saman filon,batasan wannan aikin zai mata ba,batasan abinda zai sanyata ji ba kenan,mugun feelings kamar zata fashe haka takeji,inda ta sani ta kuma fahimci maganar anty maama koda wasa ba zata shashi ba,sai ta sake takurewa waje daya tana cusa fuskarta cikin pillow,tana jin yadda mararta ke sake daurewa,ta dafeta sosai tana fidda hawaye,dai dai lokacin ya dora hannunsa akan handle na qofar,ya kuma turo qofar dakin sannu a hankali,cikin wasi wasi,don ko daya baiso ya samu bata falon ba bare ya bata amna ya koma ba.

Tattausan qamshin dake gauraye da sanyin ac madaidaici wanda baiyi yawa ba,kana baiyi kadan ba yaa doki hancinsa,cikin qamshin ya iya tantance qamshin turarenta da take amfani dashi,take wata kasala ta saukar masa,ya soma takawa a hankali qafafunsa na nutsewa cikin tattausan carfet dinta daya dauki sanyi sanyi.

Yana iya hangen direction da gadon yake,don haka bashi da buqatar haske,ya qarasa a hankali ya tsugunna a gaban gadon ya kwantar da amna,ya dora hannunsa saman kanta idanunsa suka sauka a kanta.

Yana iya hangenta saboda fararen kayan bacci dake jikinta,wanda a ido kawai zakasan suna da wani sulbi,silk ne masu asalin santsi da daj taushi taushi,milk duvet dinta ya tsaya iya qugunta,sassalka baqa kuma yalwatacciyar sumarta ta baje saman filon,baka iya ganin ainihin fuskarta saboda nutsata da tayi cikin filo.

Idanunsa ya kauda daga kanta ya lumshe su yana jin wani iri cikin jikinsa,gaba daya weather din dakin ya fara canza masa yanayi,ya kammala mata addu'ar ya tofeta da ita,sai ya laluba babu pillow kusa da ita.

Can ya hangi filon dab da gwiwarta,yana jin cewa tayi bacci,don tunda ya shigo baiga ta motsa ba,don haka ya haura saman gadon a hankali,ya sanya hannu yadan xame filon

"Wayyo Allah na" ta fada cikin wata iriyar wahalalliyar murya tana kai hannu da niyyar damqe filon,duk da batasan waye ya shigo na,saidai cikin rashin sani ta kama hannunsa gam ta riqe cikin tattausan tafin hannunta dake da wani irin dumi,motsa filon tamkar ya motsa mararta ne,don ta jingina qafarta ne dashi wai ko zata zamu relief.

Hannunsa dake cikin nata ya kalla kafin ya maida dubansa gareta,sai a sannan ya lura da yanayin kwanciyarta,yakai hannunsa a hankali saman kafadarta yana yunqurin juyota,saidai sam taqi yarda da hakan ya faru,don ya zuwa yanzu lallausan night scent dinsa ya gaya mata waye cikin dakin,ba zata so kuma yaga yanayin da take ciki ba,duk kuwa da cewa ita kadai tasan meke faruwa da ita.

Hankalinsa yaji yadan tashi,kada dai ace yarinyar bata da lafiya?,take zaune a daki zata kashe kanta,wannan tunanin yasa ya qara qarfinsa kadan,sai gata ya birkitota gaba daya, tashin farko kuma ta afka jikinsa gaba daya,ta samu kyakkyawan masauki a faffadan qirjinsa dake cike da lallausan gashin dake bada wani ni'imtaccen qamshi na musamman,gashin da duka gaza boyuwa ta tsajiyar maballan pyjama dinsa masu salki,gashin kanta kuma ya baje masa saman fuska,daddadan qamshin hair mist dinta ya ratsa hancinsa zuwa qwaqwalwarsa,take kuma ya aika da wani muhimmin saqo,ya sake nutsa fuskarsa zuwa tskaiyar kanta ba tare daya damu da yadda gashin ke shige masa baki da hanci ba.

"What's wrong with you?" Ya mata tambayar da wata irin kwantacciyar murya,wadda shi kansa baisan yana da ita ba,maimakon ta amsa masa saita sake qanqame hannunsa dake cikin nata har yanzu,wata sabuwar qwalla na zarto mata daga idanunta,dumin qwallar da ya sanyashi jin hankalinsa ya tashi,ya hada dukka qarfinsa waje guda ya dagata da niyyar sake tambayarta,saidai a wannan karon ma sake shigewa tayi cikin jikinsa da kyau,don bata qaunar hada idanu dashi ko kadan,gani take idan ya kalleta zai iya karanto ko meye ke damunta,idan kuwa har ya fahimta batasan wanne irin abun kunya ta barwa kanta ba,samun gurbinta cikin jikinsa yasa haduwar wasu sassa na jikinsu waje daya,take kuma suka aika da saqo xuwa ga kowanne sashe na jikinsa shima,kowanne sashe kuma ya amsa

"Tell me what's going on?" Ya sake qarfin halin tambaya,don so yake ya fara sanin matsalarta kafin yasan maganin da zai bata ko yasa a rubuta mata.

Hannunsa kawai takai saman mararta ba tare data shirya ba,tunaninsa take ya rabu gida biyu,yanayinta yana alamta wani abu,amma kuma tunaninsa yafi karkata ga cewa ko period ne,saidai kuma yadda mood dinta ya canza fa?,period na sanyasu haka?.

Da qyar ya samu ya gyara zamansa ya fidda wayarsa,ya kuma turawa hisham tex bayan ya riqeta sosai cikin jikinsa,duk da yadda yakejin wani abu na taso masa,kowacce jijiya a jikinsa na harba jini da sauri tana kuma aike masa da saqonni.

Saqon na shiga ya samu reply,ya duba ya miqe zai kwantar da ita,saidai taqi sakinsa, kitchen yakeso ya shiga ya dauko abinda hisham yace dashi amma taqi sakinsa,tausayinta ya saukar masa saboda gumin da yaga tana hadawa,duk da sanyin ac mai dadi dake zarya a dakin,dole ya koma ya zauna,ta kuwa kifa fuskarta akan cinyarsa da kyau,abinda yasa numfashinsa ya kusa daukewa,sai ya sanya hannunsa ya dauketa,ya maidata saman pillow din yana gyara mata kwanciya.

Ko kusa ranso baiso,amma dole bashi da wani zabi da ya wuce yayi mata uterus massage,ya matso dab da ita,ya sanya hannunsa yana dauke rigarta daga saman shaffen cikinta,wanda kwata kwata baiyi kama da cikin dake cin abinci ba.

Lallausan tafin hannunsa ya dora saman marar tata,daga ita har shi sai da suka qwaci numfashinsu da qyar,ta runtse idanunta sabbin hawaye na kunya suna fita,ya motsa hannun nasa a hankali ya fara shafa marar

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ya furta jin yana niyyar loosing control dinsa,sai ya runtse idanunsa yana aro jarumta,tare da tunawa kansa wasu abubuwa da suka taimaka wajen riqeshi da riqe kansa.

Lokaci mai tsaho suna a haka,sannu a hankali yaji jikinta ya saki gaba daya,yanayin fitar numfashinta ya canza,sai ya bude idanunsa a hankali akan fuskarta,bacci ne ya dauketa,duk da bata bar fuskarta a saitinsa ba,ta kauda fuskarta daya bangaren ne,ta yadda ba zasu iya ganin juna ba saidai idan leqawa zaiyi.

Wata iriyar qatuwar ajiyar zuciya ta kubce masa,yanajin yadda ko ina a jikinsa ke motsawa yana qin yarda da ban haqurinsa,a hankali ya dauke hannunsa daga saman mararta yana dan duban wajen,red pant dinta ya fito ta qasan wandon rigar baccinta ya haska fara sol din fatarta,da baya da baya ya fara zame jikinsa yana sauka daga saman gadon,bayan ya sauka gaba daya sai yaja duvet din ya rufesu su duka,ya dauki remote na acn ya sake dai daita musu temperature din,sannan ya aje remote din yayi hanyar fita yana hada hanya.

Da zafi zafi ya dinga hada steps din bibbiyu yana haurawa samansa,yana shiga dakin ya fidda dukka kayan jikinsa,ya rage daga shi sai pant na maza daya sanya kafin ya fita,gaba daya zufa ke karyo masa sosai,bugun zuciyarsa na canzawa,tun ba yau ba yasan kanshi sarai,ta wannan fannin ba kasafai yake da dauriya ba,dabi'arsa kuma ta banbanta data sauran maza,wannan ya sanya ya riga kowa aure a cikin sa'anninsa.

Zama yakeson yi amma ya gaza zaman,sai ya matsa ya diba remote na dukka acn dake falo da kuma bedroom dinsa ya qure temperature dinsu,ya watsar dasu a gefe guda.

Dai dai lokacin da unaisa ke takowa zuwa saman nasa,duk taku daya tana yinsa ne da manufar practical na yadda zata tunkareshi,tana ji a ranta yau komai zai qare tsakaninta dashi,itama zata kai wani bigire da tsohuwar matarsa takai,zata tsallake shingen da take da tabbacin tsallakewarta zuwa nan wajen ne kawai zai bata soyayya da martabar da takeso daga wajensa.

Knocking ta fara yi,abinda yaja hankalinsa ya kuma bashi mamaki kenan,ya zubawa qofar idanu qwaqwalwarsa nason tuno masa waye yayi saura a gidan da xai doshi sashensa a wannan lokaci?,unaisa ya bawa kansa da kansa amsa,sai ya maida wandon pajama dinsa ya nufi qofar kawai kai tsaye,ya mance cewa babu riga a jikinsa.

Mutuwar tsaye tayi sanda sukayi arba dashi,idanunta qur bisa fuskarsa zuwa qirjinsa,wani abu ya soma zagaya jikinta,lallai kaman dai tazo da sa'arta kenan?,batayi qasa a gwiwa ba ta sakar masa murmushi,sannan cikin dabara ta turo qirjinta zuwa gaba tana karkacewa cikin kwarkwasa.

Koda bata ce komai ba shi din ba yaro bane qarami,dai dai gwargwado yasan mata ciki da bai,ya kuma karanci mabanbantan hali da dabi'a irin tasu,uw uba ma ya taba yin aure,don haka daga uya sleeping dress da ta saka a jikinta take tsaye kuma a gabansa ya isa ya gaya masa me take nufi?

"Zanyi maganinki" ya ayyana hakan a ransa yana mata duban baki da wayo,yayin da ita kuma ke masa duban so da kuma sha'awa........
[11/24, 10:10 PM] Safiyyatulkiram: 60

Cikin mamaki ta sauke idanunta daga fuskar laulo zuwa kan kwanon da laulon yake ajjiyewa a gabanta

"Gashi inji innarmu,tana gaisheki,wai kuma tana hanya" maganar laulo ta sake jefata a wani mamakin bayan wanda take ciki,duk da haka yuuma batayi qasa a gwiwa ba ta girgiza kai da dan guntun murmushi saman fuskarta

"Haii laulo,yau kuma tuwo ne a idanunka ka mance da dakin daada ka kawo aiken nan?" Kansa ya girgiza

"Nan inna tace na kawo,dakinki yuuma" mamakinta sake ninkuwa yayi fiye da dazu

"Ni kuma laulo?" Kai ya gyada

"Eh ke", kafin ta sake samun damar cewa wani abu yaron ya juya ya five abinsa.

Har sai daya baceea ganinta sannan ta dawo da dubanta ga kwanon,lafiyayyen dambu ne daya wadata da kayan zogala da gyada,maida murfin tayi ta rufe kana ta matsar da kwanon gefe cikin tantama,zuciyarta na bata za'aje a dawo.

Tasan babu wani abu da ya hadata da innar da har zata nanngo abinci irin wannan ta kawo mata,tabbas laulo shirme yayi,zaya kuma dawo,da wannan tunanin ta tashi ta shiga sabgarta na kula da sanwar abincin daren data dora.

Dai dai sanda ta sallame sallar la'asar inna fureran ta kwada sallama a tsakar gidan nasu,gaba gadi ta kuma tako sassan dakin yuuma,ba tar data waiwaya ta kalli sashen daada ba.

Sauraren isowarta yuuma tayi,fuskar inna fureran fal fara'a tayi sallama ta danno kai

"Anata sallah hajiya yuuma?" Cike da qarin wani mamakin tace

"Eh la'asariya ce na idar,maraba furera" ta fada tana ware mata babbar lallausar daddumar dake gefanta,wadda duk cikin siyayyan da anni ke mata ne.

Zama inna fureran tayi tana qarewa dakin kallo a fakaice,wannan shine kusan karon farko data shigo dakin a lokaci irin wannan kuma a nutse tayi zaman dirshan, komai na dakin yuuma me kyau ne,batajin kaf rugar tasu za'a samu daki ya nata,babu ko shakka maimunatu nacan a muhallin daya kere wannan din,lallai ko zata samu kudi babu ko tantama a wajenta

"Barkanmu da almuru" yuuma ta fada ganin irin kallon da takema dakinta,sai tayi caraf ta amshe

"Barka kade yuuma,ina wuninmu?" Gaisawa sukayi,itadai yuuman nata saurare,saboda ta tabbatar ruwa baya tsami banza.

Shuru ne ya biyo bayan gaisuwar tasu,sai da yuuma tace

"Saiga laulo da dambu yayo batan kai dashi ya kawo dakin nan" bakinta har qeya tace

"Kai haba,ba batan kai bane wallahi,dai dai yayo,ke nace ya kawowa" cikin mamaki ta jinjina kai

"Ni kuma?,harda wahala haka furera?na tsammaci na daadar himu ne"

"Babu komai fa,banda abun yuuma ai mun xama daya,daada?,ai wata kusan tafi kusa,ai yanzu munfi kusanci da ita akan ke"

"Gaskiya ne,gashi kuma naga ta fita"

"Dama.ba wajenta nazo ba,wajenki nazo mu sada zumunta,tunda jininki ya auri jinina kuma ai yanzu dangi muke ni dake yuuma" inna furera ta fada tana ta gyara zama kamar wadda ke zaune akan qaya

"Gaskiya kam" yuuma ta amsa mamaki yana kasheta,kafin ta fita a wannan mamakin kuma sai taji inna furera ta fashe da kuka,cike da wani zallar mamakin da kuma tsoron kada ta qulla mata wani sharrin take kallonta

"Toooo.....subhanallahi, meye haka furera?, lafiya?"

"Dole nayi kuka yuuma,dole nayi kuka,kusakuren dana tafka wa yarinyar nan maimunatu,kiga yadda ta gujeni,aka dauketa daga wajena aka aurar da ita a wani waje daban,har yanzu bata waiwayeni ba,ni kuma bansan muhallinta ba bare naje na nemi yafiyarta" sai ta kama habar zaninta tahau fece majina.

Dariya hade da mamakin furera suka kama yuuma,saidai ta danne kawai taci gaba da kallonta tana cewa

"Allah sarki,ai sai a godema Allah da yasa aka gane kuskuren da akayi,alhamdulillahi,Allah ya yafe mana"

"Ameena....ameena" ta shiga amsawa tana sharce hawaye,wanda kusan hawayennata dukka akan naggenta da suka dinga mutuwa ne,asarar data tafka.

Sai data gama dukka koke kokenta ta miqe zata tafi sannan tace

"Umm....nace ba,ai sai a bani kwatancen gidan nata,can inda take a gomben ko?,sai a leqa aga dakin nata,a kuma nemi yafiya,bai kamata a matsayina na uwar riqonta ba kuma ya zamana bansan inda mazauninta yake ba"

"Tooo....anzo wajen" yuuma ta fada,ta shafa addu'ar da takeyi sannan tace

"Yanzu kam bana ce miki ga inda muhallin maimunatu yake ba,tunda ba zuwa nayi ba ko sanda ake bikin,ban samu na leqa ba" gaban inna furera ya fadi,har yanayin fuskarta yadan sauya

"To,ikon Allah,to kuma su can gidan surukan nata fa?" Kai yuuma ta sake girgizawa

"Shima bana ce ba,tunda nafi shekara rabona da garin gombe,sannan koda can ma kinsan ba ni nake kai kaina ba,yafendo ke aikomin da mota ta daukeni daga nan qofar gidan zuwan wancan" shuru furera tayi,ga qoshi ga kuma kwanan yunwa,yanzu ya kenan?.

"To ai inaga ta zo da sauqi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login