Showing 1 words to 3000 words out of 58720 words

Chapter 1 - Auren Shehu Book 1 Hausa Novel Complete

25 Jan 2025

452

??ࡱ?>??  ????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Root Entry???????? ?F?WordDocument????12 0Table????????Data
???????????????????? P?z KSKS?12 ?}???????rr



O
c
? ??
??????????$O ?*r

??



?+?c
+?c
?+c
??
c
 ?^`????^Normal d??,CJmH sH nHtH_HOJPJQJ^JaJTA`????TDefault Paragraph FontOJPJQJ^Jfi`????f Table Normal :V ?4?
l4?a? OJPJQJ^J(k`????(No List ?}?%234Dnepv????ܯ?????j?????!?7<@BM^T?e?z??ԏh???8?????N??FIKRA WRITER'S ASSOCIATION

AUREN SHEHU

'

Kwance ya ke a rigingine kan ciyayi irin wannan ciyayin da ake kira "carpet grass" Hannayen sa biyu tallabe da ?o?on kansa, cikin nazari yake duban taurarin da ke jere reras suna she?i bisa sararin samaniya. Babban lambu ne mai Wauke da Sangare biyu, Sangaren bishiyoyin 'ya'yan itatuwa, bishiyar mangoro, gwaiba, yazawa (cashew) da dai sauran su, sai kuma Sangaren da ke Wauke da kujerun hutawa. In ka Wauke kukan tsuntsaya babu sautin da ake ji kasancewar dare ya fara tsalawa, kusan ?arfe biyu ne.

Sanye yake cikin rigar sa?a irin na fulani, kan sa Wauke da rawanin da ya zaga har kewayen fuskar sa hakan ya sa fiye da rabin fuskar shi Suya. Kasancewar shi na daya daga cikin masu gadin daddare na gidan, kusan kullum ya kan kai biyu a nan cikin lambun, yayi kwanciyar sa ya na mai nazari, hakan ba ?aramin nishaWi ya ke saka shi ba.

Gefan sa ?atuwar sanda ce wacce ake kira da gora, ta korar shanun sa ce duk da kuwa rabon shi da rugar su wacce ake kira "Rugar Shehu" ya kusa shekara.

Jin dirar mutum tare da haushin karnukan gidan lokaci Waya ya sanya shi yin zumbur ya tashi zauna ya na mai duban in da ya ke kyautata zaton mutum ne ya diro cikin gida. Jin shiru babu wani motsi sai na haushin karnuka ya sanya ya tashi tare da jan sandar gorar shi kai tsaye bakin bishiyar da ke kusa da katangar lambun ya nufa, idan ya ke kyautata zaton koma menene ya diro nan ne hanyar shi.

Tun dirowar ta take ?o?arin janye ni?abin ta da ya ma?ale jikin reshen bishiyar da ya mata tsani. ?o?ari ta ke iya ?arfinta don ta ga ta ciro amma ina, gashi ta san mutukar ba ta samu ta shige ciki ba lalle masu gadi za su kama ta yau, don kuwa haushin karnukan yau ya fi na kullum. Jin ta ku a bayan ta ya sanya ta juyawa da sauri, ganin ya Waga sanda ya na shirin runtsuma ma ta aka, ta runtse idanu ta na mai faWin

"Wayyo ni Dady!!!!!"

Cak ya tsaya, hannun shi na rawa tsabar firgici na ganin kyawun halittar Allah, tabbas kyau dai babu irin wanda bai gani ba a Rugar su, amma sam bai taSa ganin wacce ta firgita shi ba kamar wannan halittar da ke gaban sa.

Fuskar ta ya bi da kallo, wanda rashin ni?ab ya ba shi wannan damar, domin kuwa jikin ta rufe ya ke da hijabi tun daga sama har ?asa. Kamar yanda ya ke nazartar taurari haka ya tsinci kan sa cikin nishaWi yayin da ya shiga nazari akan fuskar ta.

Baka ce, irin wannan bakin mai shek'i kamar jikin tarwaWa. Tsayuwar hancin ta da ya zo dab da ?aramin bakin ta ba ?aramin ?arawa doguwar fuskar ta kyau yayi ba......

Jin shiru ba ta ji saukar gora kan ta ba ya sanya ya ta buWe manyan idanun ta, hakan ba ?aramin sake rikita shi ta yi ba ganin fararen idanun ta bisa kan shi har sai da ya Wan ja da baya ya na mai tasbihi ga ubangijin sa, domin ya tabbatar wannan halittar da ke gaban shi ba mutum ba ce.

Ta na mai duban shi cike da tsoro musammam ganin mutum mai faWi da tsayin da tun da ta zo duniya ba ta taSa ganin irin shi ba, daWin daWawa gashi yanayin shigar shiri irin na waWannan mutanen da suka saka Nijeriya a gaba ko kuma Fulani masu garkuwa da mutane, wannan tunanin tare da jin taku da haushin karnukan da ya ?aru, wanda hakan ya tabbatar ma ta masu gadin sun kusa shigowa lambun ya sa ta sakin ni?ab din ta na mai Wage hijabin ta yanda za ta sami damar sauri, ta yi amfani da damar gushewar tunanin mutumin da yayi kasake ya na duban ta, ta bi hanyar da zai sada ta da kitchen da sauri, hannu na rawa ta ke ?o?arin fidda Wan mukulli da ta Soye cikin dan wando da ke sanye jikin ta.

Har tuntuSe ta ke garin waige domin tabbatarwa ba ya biye da ita.
Allah ya taimake ta ?ofar ya buWu, kasancewar ta sababbiya a harkar, cikin sanWa da lalube ta ke tafiya domin wutan lantarkin kitchen din a kashe ya ke, sai dai hasken farin wata da yake ratsowa ta taga. Ba ta tsorata ba sai da ta jiyo muryar masu gadi daga cikin garden, ta na mai ro?on Allah ya sa ba asirin ta ba ne ke shirin tonuwa ba, ta bi ta falo ta shige Wakin ta cikin rawar jiki. Dan tun da take fitar dare ba ta taSa shiga tsaka mai wuya kamar na yau ba.

Hijabin jikin ta ta cire, ta na mai ajiyar zuciya ta zube bisa gadon ta.
Hasken da ya gauraye Wakin sanadiyyar wutan lantarkin da aka kunna ya sanya ta yi zumbur ta tashi zaune a tsoro ce. Ganin wacce ke jingine jikin bango ya sanya ta fiddo ido tare da faWin

"Wai ke Halitta ba za ki fita harka ta ba? Wannan masifar har ina haka?"

A hankali Halitta ke ?are ma ta kallo, tun daga dan ?aramin matsattsan wandan da ke jikin ta (bumshort) zuwa matsatsiyar jar riga wacce ta tsaya ma ta iya cibiya, ga kan nan ya sha kitson attachment da aka yi da gashin doki mai tsada da ake kira (Brazilian hair). Ta na mai girgiza kai ta furta

"Yakura......."

"please Halitta, ba yanzu ba, na gaji da yawa!!"

Ta katse ta tana Waga mata hannu. Ganin an murWa ?ofar Wakin ya sanya ta saurin janyo bargo domin Soye shigar da ke jikin ta. Mahaifiyar su wacce su ke kira Ammy ce ta shigo, ta na hamma tsabagen baccin da ke idanun ta, ta ke duban su cike da damuwa ta ce

" dama na san dole kuma kun tashi, hayaniyar su Audu da haushin karnuku ne ya tada ku ko?"

"eh wallahi Ammy....."

Su ka faWa a tare wanda hakan ya sanya Halitta sakin baki cike da mamaki ta ke kallan yayar ta ta, ita kuwa ko aji kin ta ta ce

"na kasa gane menene matsalar su da za su na sakar mana karnuka su na mana hayaniya, ya kamata a hana su shiga garden ma kawai...."

"ke da ki ke Waki ya aka yi kika san garden su ke?"

Halitta ta na sane ta jefa mata wannan tambayar, domin kuwa duk wani rashin ji da 'yar uwar ta ta ke yi babu wanda ba ta sani ba.

Jin haka ta san in da ta dosa dan haka sai ta yi burus tare da faWin

"Ammy dan Allah daga ina hayaniyar nan ke tashi?"

"eh toh ni ma na fi tunanin garden din ne, ai Malam shi ma ya fita ya mu su magana...."

Ras! gaban ta ya faWi

"Allah ka rufa min asiri ba dan hali na ba ba dan aiki na ba"

Adduar da ta shiga jerowa cikin ran ta kenan. Ita kuwa Halitta dariyar mugunta ta saki, sannan ta furta

"Allah ya sa Dady ya gano dalilin wannan hayaniyar ta su ya mana magani, ni dai sai da safen ku"

Ta na murmushin mugunta ta dubi yayar ta wacce ke watsa ma ta harara, ta ?ara da

"a juri kai zuga gabas wata rana ya zo da ruwa, ko ya ki ka ce Yakura"

"uhum"

Cewar ta dan tsoro ta kasa magana, gani ta ke burin Halitta ta biye ma ta su yi hayaniya dan ta sami damar tona mata asiri. Halitta na fita Ammy ta bi bayan ta na faWin

"bari na bi bayan ki Halitta, babu mamaki Falmata na nan Wakin ta tsoro ya hana ta motsawa"

Suna fita ta fidda wayar ta da ya dame ta ta da ?ugi, ganin wanda ke kiran ta ta ja tsaki, Wagawa ta yi tare da karawa bisa kunnan ta, cikin nuna fushi ta ke magana

"Bobo wai menene? Na faWa ma ka zuwa na club in dai na dawo hutu gidan nan abu ne mai hatsari, ka bari mu koma school ka ce ah ah, ga shi kai ba za ka iya bari mu dawo da asuba ba sobada jarabar bacci irin na ka, ai gashi yau saura kiris Dady ya kama ni!"

Shiru ta yi na wani Wan lokaci ta na sauraran shi, kafin daga bisani ta kashe wayar ba tare da ta sake tankawa ba. Nan ta kwanta ta na jiran tsammani, jin shiru babu wanda ya dawo ta san asirin ta bai tonu ba tukunna, dan haka ta tashi, kai tsaye toilet ta nufa ta yi wanka tare da Wauro alwala domin rama salloli uku da ke kan ta, la'asar, magariba da isha'i.

***
Allah yayi dare gari ya waye. Babban Waki ne irin na ?a?an manya, komai na Wakin an yi masa ado da kala biyu, wato shuWi da fari. Ba wani tarkace ba ne a Wakin, face ?atan gado na alfarma tare da setin madubi da dirowa.

Kamar kullum yau ma sai da rana ta take, bayan ladanin masallacin da ke cikin gidan su ya ?ira sallar azahar sannan ta iya motsawa, wayar ta ta jawo, ta shiga Instagram in da ta saka hotan da ta yi daren jiya a club. Nan da nan hotan ya sami karbuwa in da samari da wasu yan mata su ka shiga danna mata "like" tare da "comments" kamar yanda aka saba. Sai da ta gamsu sannan ta aje wayar ta tashi da kyar ta yi wanka tare da Wauro alwala.

Maimakon da ta fito ta yi azama wajen rama sallolin da ake bin ta, wato Asuba da Azahar, sai ma tsayawa ta yi gaban madubi Waure da tawul da ya tsaya iya gwiwa, cikin jin daWi da alfaharin baiwar dirin da Allah ya mata, da ke masha Allah ita kan ta ta san Allah ya mata mata dire. Hakan ya s koda yaushe ta na kan social media cikin saka hotunan ta wanda ta yi da matsattsun kaya, dan kuwa ta na cikin Waya daga cikin sannanun matan nan da ake kira "Slay Queen" a Instagram.

Sai da ta Sata lokaci wajen shafe shafe da kwalliya, ta fito fes cikin Winkin atamfa riga da siket, sannan ta Wauko hijabi wanda ya ke kai mata har ?asa ta sanya. Murmushi ta ke ganin yanda ta fito saliha sak, ita da kan ta ta shiga yiwa kan ta kirari

"woo ni Zeee the slay mama, the club mama, kuma salihar Daddyn ta"

Nan ta gama juye juye gaban madubi, sannan ta shimfiWi sallalaya aka shiga jera sallar asuba da azahar.


***


Malam Abubakar Birma sananne kuma hamsha?in Malami ne wanda ya yi suna a Nijeriya, musamman Kano da Maiduguri. Babarbare ne Wan asalin garin Maiduguri. Matan shi biyu, Hajja Kulu ita ce matar shi ta farko, wacce ta ke ?abilar Barebari, ta na zaune ne gidan Malam da ke birnin Maiduguri. Yaran ta da shida, maza huWu da mata biyu. Sai kuma Hajja Aleesha, wacce ta ke ?abilar Shuwa Arab. Ita ce ke zaune Kano, ?a?a uku gare ta, kuma duka mata, sun haWa da Wiyar ta ta farko Zainab mai kimanin shekara ishirin da biyu, wacce ake kira Yakura, sai mai bi mata, Halitta mai shekara ishirin, sai auta Falmata, wacce ta ke da shekaru goma sha takwas a duniya.

Cikin ?a'yan Malam, Allah ya jarrabe shi da fitinanniyar Wiya, wacce babu wanda zai ga Wabi'un ta ya danganta ta da Malam. Ba kowa ba ce fyace Wiyar Hajja Aleesha ta farko, wato Zainab. Club ne daga na cikin gida Nigeria kudu da Arewa har zuwa ?asashen ?etare babu wanda ba ta zaga ba, sai dai wanda ba ta sami dama ba, haka kuwa buWe ido babu wanda Zainab ba ta yi ba kasancewar ta na yawan harka da gurSattun yaran masu kuWi, yawanci ta haWu da su ne ta cuWanyar makarantun boko da su ka yi tare.

Social media kuwa ta yi ?auran suna, mabiyan ta bila adadin haka, haka kuma masoyan ta da masu hure mata kunne domin kuwa abu biyu ne ya haWar mata, ga kyau ga naira, babu shakka Allah ya bata duniya.

Duk wannan hali da Zainab ke ciki Malam bai sani ba, shi a na shi ganin cikin ?a?an shi babu mai kamala da nutsuwa da ya kai ta, domin kuwa kullum a haka ta ke zuwa ma sa a nutse. Ga shi shi ba ma'abocin social media bane bare ya san wainar da ta ke toyawa, haka zalika shi ba mazauni ba, yau ya na Maiduguri, gobe ya na Misira, gata ya na saudiya. Sanda ya ke gari kuma ita kuma Zainab ta na makaranta, nan American University of Nigeria da ke yola, dama nan ta fi she?a ayar ta, dan idan ka ga irin rayuwar da ta ke yi ba za ka taSa cewa Wiyar Malam ba ce, Wiyar Malam ta?i halin Malam.

***

Jin a ranar Malam zai tafi Maiduguri ya sanya Zainab kafewa a lalle ita za ta kai ma sa kayan shayin da ya nema a kai ma sa falon shi na baki, saboda ta na so ta ga Malam akan bu?atar ta na sake wayar ta ?irar Samsung da ko wata huWu ba ta yi da siya ba, a cewar ta cemeran ba ta da kyau sam, ta na bu?utar latest IPhone da gaggawa.

Da shigar nan na ta cikin hijab har ?asa, ta tura ?ofar falon a hankali, zuciyar ta Waya da sallamar ta da Shigan ta falon lokaci guda ta yi, cak ta tsaya yayinda idanun ta su sauka kan fuskar nan da ke Suye cikin rawani, kamar yanda ta yi arba da shi jiya da daddare. Tuni gaban ta ya fara faWuwa, babu shiri ta juya da niyar komawa, muryar Malam ne ya dakatar da ita, ya na mai faWin

"Yakura shigo mana, wannan da ki ke gani Walibai na ne, da kuma driver da masu gadi, kasancewar kullum kuna killece cikin gida shiyasa ba za ki gane su ba, muna tattaunawa ne akan zargin wasu Sata garin da su ke yun?urin hauro mana gida cikin dare......."

Duk da mazan da ke zaune falon sun kai su goma, babu wanda ta ke iya gani sai wannan mai rawani, hankalin ta bai ?ara ta shi ba sai da ta ji kalaman da Malam ya furta, ba ta san sanda ta kara kai kallon ta ga mutumin ba, shi ma Win kallan ta ya ke ya na mai gasgata abun da zuciyar shi ke raya masa

"wannan ita ce Singel din da na yi gamo jiya, ashe ba aljanah ba ce, to menene dangantakar ta da Malam? "

Abin da ya yake rayawa cikin ransa kenan, kamar kuwa Malam ya sani, sai ji yayi ya furta

"Wiya ta ce, wannan ita ce Zainab, Wiyar mai Waki na ta biyu, mahaddaciya kuma kamila a cikin ?a?ana"

Jin haka ya daWa kallon ta, a hankali ya maimaita sunan

"Zainab.."

To idan dai lafazin Malam haka ne, to babu shakka ba ita ya gani ba. Hukuncin da ya yanke kenan yayinda ya sake ?ura mata ido domin neman bambamcin tsakanin wannan kamilar Wiyar Malam da kuma waccar da ya gani a daren jiya.
Aje tiren abincin ta yi gaban Malam, kai a sunkuye ta gaishe shi, ya na amsawa ta tashi da sauri ta fice daga falon dan kuwa ita kan ta tana jin idanun wannan bawan Allah a kan ta. Sai da ta kusa isa kitchen sannan ta dan tsaya ta nutsu gudun kar su Ammy da Halitta su gane halin da ta ke ciki.


Katon kitchen ne wanda mutum goma za su iya aiki ciki ba tare da an takura ba. Ya tsaru sosai dan kuwa cike ya ke bam da duk wani kayan amfanin kitchen. hatta fridge biyu ne cikin kitchen din, na kayan miya da nama daban, sai kuma na ruwa da lemoku da kuma kayan marmari. Ta tarar da Halitta na jera lemo da ruwa cikin fridge, gefe kuma Ammy ce ta ke yiwa Iya mai aikin su bayanin abincin da ta ke so a dafa da rana.

"Ammy anya kuwa cikin masu aikin gidan nan ko daliban Dady babu yan Boko Haram ko masu garkuwa da mutane?"
Cewar ta yayinda ta dauki daya daga cikin ruwan da Halitta ke jerawa a fridge.

"Auzubillallah!"

Ammy da Iya su ka furta tare, ita kuwa Halitta tsayawa ta yi ta na duban yar uwar tata, da ko a jikin ta, kofi ta ja ta zuba ruwa ta jika makoshin ta. Sannan ta kara da

"Ya ki ke kallo na haka kamar wata gaula? Wallahi I'm very serious about this one"

Tsakanin ta da Allah ta ke bayani yayinda ta mayar da hankalin ta ga Ammy, ta ce

"Ammy kin dai san yan boko haram din nan dai malamai su ke hari, ki tuna fa shugaban su Yusuf wanda aka kashe lokacin shugaban kasa yar aduwa an ce ya taba neman ilimi gun shiek Jafa'ar Allah ya ji kan rai, kin ga dole Dady yayi takatsantsan dan wallahi ina kyautata zatan wanda na gani gun Dady dan boko haram ne.....!"

"Kul kar na sake ji!"

Ammy ta katse ta, cikin tsawatarwa ta juya harshe zuwa yaren ta na shuwa, fadi ta ke

"Idan ki ka kuskura Malam ya ji wannan maganar wallahi sai ran ki ya baci, ke fa dadi na da ke danyan kai! Kina maganar Boko haram gaban iya kalan ta fita ta yada cewa Malam na aje yan boko haram gidan sa ko? Oh ni wannan rashin hankalin na ki Yakura ina za ki da shi?"

"Toh bare ma ni gidan nan kaf ban ga wanda ke kama da Boko haram ba......laaaa ko dai Usman ta ke magana ne?"

Cewar Hallita, yanda ta ambato sunan Usman Win cike da farin ciki, in da idanun ta har wani sheki su ke ya sanya Ammy da Zainab kura mata idanu. Ita ma din sai a sannan. Ta ankare ta yi saurin faWin

"Daya daga cikin almajiran Dady ne fa, ina ranar da mu ka je taron makarantar su Falmat? Ranar mu ka tarar da shi bakin gate ya na jiran Dady

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login