Showing 3001 words to 6000 words out of 58720 words

Chapter 2 - Auren Shehu Book 1 Hausa Novel Complete

25 Jan 2025

600

,a gaban mu ya gabatar da kan shi wajan Dady, ya ce sunan shi Usman, ya na so ya zama daya daga cikin almajiran Dady in da hali, Amma sai dai be da kudin sadaka sai da a bashi aikin yi, Ammy I'm sure Dady ya fada mi ki sai dai kin manta tunda daliban na sa da yawa, ku tambayi Falmat ma ku ji zancen fa ba na yau ba ne an kwana biyu"

"Ahaaa kin ji ai Ammy, kawai out of blue mutum ya zo Dady ya karbe shi! Gashi nan dai magana za ta fito, Dan Boko haram......"

Ammy na mai kallan Zainab ta ce da Iya

"Iya dan je ki zan neme ki zuwa anjima kadan, bari dai na gama da yaran nan"
"Toh Hajiya"

Iya ta fita ba a san ran ta ba, dan kuwa ta na dan tsintar zancen da ake duk da Ammy ta sauya harshe.

Iya na fita Ammy ta mayar da hankalin ta ga yan matan na ta biyu, ta na mai nuna Zainab da dan yatsa ta ce

"Kin ga Yakura? Idan kalmar Boko haram din nan ba ta fita bakin ki ba Allah sai na sabar mi ki! Malam ne zai aje dan boko Haram gidan sa?"

"Bare ma ba dan Boko Haram ba ne, mutum ne kamili mai ilimi da zurfin tunani....."

Cewar Hallita ta na mai hango Usman cikin ranta.

"Halitta?????"

Ammy da Zainab su ka kira sunan ta a tare. Nan ta yi wuki wuki da idanu, gudun kar mahaifiyar ta da yar uwar ta su gano tuni ta kamu da san almajiri kuma daya daga cikin masu gadin gidan ne ya sanya ta tashi da sauri ta na mai aje ruwan da ya rage cikin fridge. Sai da ta rufe fridge din sannan ta juyo ga Ammy da Zainab wanda su ka tsura mata idanu su na jiran jin ba'asi.

"Ammy na gama bari na je na gyara daki na"

Ta fada in da ta yi hanyar fita. Kan ta kai koma Ammy ta katse ta, in da ta ce

" Halitta ya aka yi ki ka san mutumin da Yakura ke magana akai kamili ne? Mai ilimi da zurfin tunani....?"

Gaban ta na faduwa ta juyo su ka hada idanu, ta yi saurin mayar da kallan ta ga Zainab wacce ta daga mata gira cikin alamar tambaya.

"Dady na ji ya na fada Ammy, Kuma duk wanda Dady ya amince ya rabe shi ko shakka babu mutumin kirki ne"

Ta na gama fadin haka ta fice. Zainab kuwa dan tsalle ta yi tana dariyar mugunta har da tafa hannu ta ce

"Ammyyyy you see your child abi? Allah ya sa ba siriki za ki yi da Mai gadi ba"
Duka Ammy ta kai mata ta na fadin

"Bakin ki baya fadan alkhairi Yakura! Allah ya rufa mana asiri da wannan mugun fata, bakin ki ya sari danyan kashi"

"Toh ni kam sai dai na taimaka da amen, kin dai san halin diyar ki sarai ba hankali gare ta ba, bari na dena kiran sa Boko haram kar dai brother in-law ne, Ni kam na yi gaba"

Ta fice ta na jiyo Ammy na fad'in
"Yar butan uwa, za ki dawo ki same ni ne, oh ni Aleesha Allah ka raba ni da mugun ji da mugun gani!"

Ta na maganar ne tana girgiza kai.

***

Halitta dakin ta ta shige, har lokacin gaban ta bai dena faduwa ba, in da ta haye bisa kan gadon ta tana mai rufe idanu. Tun da ta ke babu mahalukin da ya taba shiga ran ta tamkar wannan bawan Allah da yar uwarta ke ikirarin dan Boka haram ne. Ba za ta taba mance ran da ta fara tuzali da shi ba.

Watanni bakwai da su ka wuce, sun dawo daga taron makarantar su Falmat su ka tadda shi bakin gate. Ka na ganin shi ka ga buzu ko bafulatani saboda yanda yayi nadin rawani da kuma yar riga yar shawara da ke jikin sa. Kasancewar shi bafulatani sam be yi karamin jiki irin na zubin fulani ba, dogo ne mai alamun karfi da faffadar kafada.

Kafin Mai gadi ya bude gate Malam da ke zaune a gidan gaba tare da direba ya sa aka sauke masa gilashin motar in da yayi masa Sallama. Ganin Malam ya taso da sauri, har kasa ya durkusa zai gaishe shi, Amma ya ce ah ah ya tashi su gaisa, Malam ya bashi hannu su ka gaisa.

Nan ya gabatar da kan sa a matsayin Usman, bafulatani dan cirani, ya zo ne gidan Malam domin neman ilimi kasancewar Malam na daya daga cikin Malaman da ya ke sauraran tafsirin su gidan rediyo, be da arzikin biyan Malam sadaka, Amma zai yi masa aiki har lokacin da zai gama samin ilimin a sallame shi.

Daga gidan baya Halitta da Falmat ke hango shi, ita kan ta Falmat ta yaba da kamalan sa, bare Halitta da ta saki baki da hanci ta na kallan sa.

Bayan Malam ya gama nazari kan sa na wasu mintina ya ce da shi ya bari ya dawo gobe da safe. Da haka su ka yi sallama ya tafi, inda su kuma su ka shige ciki. Bayan sun sauka daga motar ne Hallita ta dubi Malam ta ce

"Dady dan Allah ka duba lamarin bawan Allan can, kamar dai ya na da kamala, idan da yiyuwar taimaka masa a taimaka masa"

Malam na murmushin jin dadin yanda diyar ta shi ke da tausayi ya ce

"Toh in Sha Allah diyar albarka, dadi na da ke tausayi da jin kai, na mi ki alkawarin matukar na yi bincike na ga be da aibu zan dauke shi matsayin dalibi na, kin san rayuwar ce yanzu ba kamar da ba, mutane sun zama abin tsoro"

"Wallahi da gaskiyar ka Dady, muna zaman zaman mu kilu ta ja bau, ka yi binciken dai, rabi da wannan sarkin tausayin"

Falmat ta fada yayinda ta ja hannun yayar ta su ka yi hanyar ciki.

"Dady a duba dan Allah"

Cewar Hallita ta na mai sake waigowa. Kai Malam ya jinjina mata alamar ya ji ta.
Haka Halitta ta yi ta bibiyan lamarin har Allah ya taimaka bayan Malam yayi bincike, a iya binciken da aka yi ya gano Usman bafulatanin wata riga da ake kira rugar Shehu ne, Baban shi ne shugaban rugar, haka kuma Usman shi ne babban dan sa. Kasancewar bai ga wata bayyananniyar matsala daga gare shi ba ya sanya Malam karbar shi a matsayin daya daga cikin almajiran sa da ke daukar karatu a gida. Malam ya ce zai iya bashi ilimi ba tare da ya biya sadaka ba, Amma shi ya dage lalle a bashi aiki cikin gidan, idan har ya sami ilimi a arha ba lalle ya ga darajar sa yanda ya kamata ba. A wannan dalilin ne Malam ya bar shi ya na taya Mai gadin gidan gadi cikin dare.

Ajiyar zuciya ta saki ta na mai juyi bisa gado, ita kan ta tasan lamarin da zuciyar ta ke bijiro mata akan Mai gadin nan lamari ne mai girma a gaban iyayen ta. Ba ta ji shigowar ta ba, sai jin zaman ta tayi bisa gado. A hankali ta furta

"Halitta shin ba za ki dena sa kan ki cikin tunani ba? Sai kin sakawa kan ki cuta akan abin da ba zai taba yiyuwa ba!"

A hankali ta bude idanun ta tana mai duban kanwar tata Falmat. Falmat ta na da jiki sosai da kuwa gidan kaf babu wanda ya kai ta kiba. Kiban ta be sa ta yi muni ba dan kuwa irin matan nan ne Duma duma masu kyau na kayatarwa. Kamar Zainab ita ma Falmat baka ce, ta na da hanci har baka da manyan idanu. Duniyar nan kaf babu wanda ya san cikin ta kamar wannan kanwar ta ta, ita kan ta takan yi mamakin yanda ta ke bude mata cikin ta. Falmat sanye cikin kamfala mai ratsin shudi da ja, dinkin goguwar riga har kasa, kannan ya sha tauri da kallabi kai ka ce gidan biki za ta je.

"Falmat ya zan yi da jarabawar ubangiji? Kin san dazu na yi barin baki gaban Ammy da Yakura kuwa?"

Halitta ta fada cike da damuwa. Falmat na mai dafe kirji ta ce

"Kai Halitta! Wasa ki ke yi wayan ki ya fi gaban haka!"

Kai ta girgiza sannan ta ce
"Idan dai a kan abin da rai ke so, I'm full of disappointment Falmat, wallahilazim! Amma dai na gyara maganar, Allah ya sa dai kar su gane halin da na ke ciki"

Shiru ne ya biyu baya, kamin daga bisani Falmat ta ce

"Halitta?"

Halitta ta amsa mata da

"Uhm"

"Ina mai baki shawara da ki sassauta wannan lamarin, kin san ba abu ba ne mai yiyuwa ko da kowa wannan mutum ya kai matsayin haka, bare kuma bakauye, dadin dadawa Mai gadi a gidan mu....."

"Bakauye Mai gadi ba mutum ba ne? Ba Allah ne ya halicce shi kamayar yanda ya Halicce mu ni da ke da su Dady ba??"
Halitta ta katse, ba ta gushe ba ta kara da

" Saboda Allah ya dan san mana kankani daga ni'iman shi sai mu zamo ma su butulci ta hanyar kaskantar da bayin shi? Bari na fada mi ki magana daya Falmat! Ina san shi! Ina san Usman tsakani da Allah!"

Jikin Falmat sanyaye ta ce
"Allah ya ba ki hakuri, Allah ya kawo sauki cikin lamarin ki, dama na zo fada mi ki Dady ya tafi, kin ce ya na tafiya na fada mi ki"

Zumbur Halitta ta yi ta mi ke, da sauri ta nufi bandaki, ta na fadin

"Toh ina zuwa na wanke fuska ta, Allah ya taimake yau dai na kara ganin Usman Falmat"

Shiru Falmat ta mata ta na kallan ikon Allah. Bayan ta fito daga bandaki ga mamakin Falmat sai ga Halitta an tsaya gaban madubi ana goge fuska tare da shafa hoda. Dake Halitta irin matan nan ne jajur sam ba ta damu da shafa powder ba tsabagen farin ta, ita da Zainab kamar su daya, kalar fata ne ya bambamta su, in da Zainab ke baka, Halitta Fara ce sol, dan fari har wani jaja ta kan yi musammam idan ta sha wuya ko ta shiga rana.

"Wannan shafa powder na menene? Ina za ki wai?"

Ta na shafa man lebe ta ke duban Falmat ta cikin madubi, ta ce

"Ina dai za mu je, ai har da ke za mu fita yanda Ammy ba za ta zargi komai ba"
"Ina za mu toh"

Falmat ta tambaya cikin rashin fahimtar in da Halitta ta dosa. Sai da ta shirya tsaf cikin bakar doguwar riga, tare da nada bakin mayafi, kallo daya za ka mata ka san ko shakka babu Halitta jinin larabawa ce, dan kuwa ta fito a shuwar ta sak. Zuwa ta yi ta na mai ruko hannun Falmat ta ce

"I want to see him, please, na san dai ba zai yiyu cikin gidan nan ba, Amma duk yanda za mu yi na gan shi ko sau daya ne Falmat, ba sai mun yi magana ba, kawai na gan shi ya ganni Falmat....."

'wannan bawan Allah ko dai asiri ya yiwa Halitta'

Cewar Falmat cikin zuciyar ta, dan kuwa lamarin na Halitta ya fara bata tsoro, lalle lokacin da za ta shaidawa Ammy halin da take ciki yayi!


AUREN SHEHU

Biyu

***

Kamar ta san abin da ta ke ayyanawa cikin ran ta, ta na mai duban idanun ta ta ce

"Falmat na yarda da ke, Amma ki sani matukar na ji wannan maganar ta zaga wajan Ammy ke zan tuhama.."

Cike da nuna rashin gaskiya Falmat ta shiga girgiza kai tare da fadin

"Kin san dai ni mai rufa mi ki asiri ce Halitta, amma wannan abun da ki ke shirin yi ba daidai ba ne, ki tuna fa Dady ya ce ko saurayi bai yarda mu kula a waje ba ko mu kawo masa gida ba tare da yana da masaniya akai ba, Amma yanzu kin shirya dan baya nan ki ce mu yi karya ki ga namiji Halitta?"

Hannun Falmat ta saki, ta na mai dafe kai ta furta

"Ya Ilahi! Ya iIlahi! Ya Allah ga Falmat! Dalla wa ya ce ma ki zance zan yi da shi? Kawai fa yi za mu yi kamar za mu fita ne idan Allah ya sa yana waje sai na Wan gan shi..."

Cike da mamaki gami da tausayin halin da yar uwar ta ke ciki Falmat ta zura mata idanu. Ganin haka Halitta ta kara da

"Haba mana yar ?anwa ta, in ba ki taimaka min ba wazai taimake ni? Kin san dai Yakura is a snob, ji da kanta ba zai bari ma ta saurare ni ba balle ma taimaka min sai dai ma ta tona min asiri idan dai wannan ce, please Falmat! Zan baki wannan abayar tawa da ki ke so"

Jin batun abaya sai ga Falmat ta mike tsaye, ta ce

"Da ga yau shikenan gaskiya ba zan kara yin karya dan kawai ki ga Usman Mai gadi ba Halitta..."

"Usman! Sunan shi Usman ba Usman Mai gadi ba"

Halitta ta gyara mata cikin jaddadawa. Fita Falmat ta yi tana mitar kar Halitta ta takura mata wallahi sai ta fasa raka ta. Haka ta lallaba ta, bayan ta Wauko mayafin ta, su ka yiwa Ammy karyar za su je gidan wata kawar Falmat, dan kuwa cikin su Falmat ce kadai mai kawa a cikin unguwar. Sai da Ammy ta yi mitar dama jira su ke Malam ya tafi su sami kafar yawo, tare da kashedin kar su dade sannan su ka kama hanya.

Tun da su ka kama hanyar fita gaban Halitta ke faduwa, fatan ta Allah ya cika mata buri ya sa Usman na nan farfajiyar gidan. Ai kuwa su ka ci sa'a can kusa da gate ta hango shi tare da abokin gadin shi. Zaune su ke bisa teburi ga ledar dafaffiyar gyada gaban su, suna afawa a baki su na hirar duniya.

Tun da ya hangi fitowar su idanun sa ke kan su, kokari ya ke ko zai iya gano wacce ta diro daren jiya cikin su. Sam Halitta ba ta lura da yanda ya saka mu su Ido ba domin kuwa ta yi kasa da na ta idanun tun fitowar su, Falmat ce dai ta ke kokarin kare masa kallo tun daga nesa ta na mai mamakin yanda yayarta ta fada ma san dankauye irin shi. Ganin yanda ya tsura musu ido Falmat ta ja tsaki

"Mtsw ashe ma mayen kallo ne! Ji fa yanda ya tsura ma mutane idanu sai ka ce mujiya! Wallahi ya ci sa'ar ki da sai na tsawatar masa!"

"Kai Falmat ke da wani ido ki ka san ya na kallan ki? Bare kuma ai ban da burin da ya wuce ya lura da ni nima..........."

"Hajiyoyi za a fita ne?"

Cewar abokin gadin Usman yayin da ya tashi ya nufi gate din gidan domin bude musu kofa.

"Eh sannun ku da aiki"

Falmat ta furta ta na mai kai kallon ta ga Usman wanda fuskar sa ke Wauke da fara'a, haka ma Halitta wacce tunda ta sauke idanun ta bisa fuskarsa mai kwarjini da dumbun annuri gaban ta ya shiga faduwa.

"Toh Allah ya dawo da ku lafiya"

Ya fada sa'ad da ya bude kofar ya na jira su fita ya kulle. Ganin yanda Halitta ta yi kasake ta na duban shi ya sanya shi fadada fara'ar shi, cike da girmamawa ya sunkuyar da kai alamar gaisuwa, ba Halitta ba hatta Falmat sai da hakan ya burge ta, ganin Halitta na shirin ba da su ya sanya ta jan hannun ta su ka yi waje ta na fadin

"Amen Isa, godiya mu ke"

Isa na mayar da kofar gate ya koma wajan zaman shi ya zauna, tare da fadin

"Ina ruwan Falmat, 'ya'yan Malam ne ai, kila ba za ka san su sosai ba saboda ba sa fita, in za su fita kuma fuskarsu kullum a rufe, na yi mamaki ma yau ka ga ba su rufe ba"

Kai Usman ya gyada masa da ke mutum ne da be fiya magana ba, tunanin Falmat ya ke dan ko shakka babu ita ma ta yi kama da wacce ta diro daren jiya, sai dai kuma yanayin kibar Falmat ce ke karyata ita ce din. Duk da waccar hijabi ne jikin ta har kasa, Amma ba ya Jin ta kai Falmat kiba. Nisawa yayi kafin ya furta

"Isa ina da wata tambaya domin Allah"

"Ina jin ka"

Cewar Isa ya yayinda ya bare gyada ya afa a baki.

"Shin Malam ya na da 'ya'ya mata da yawa ne,?"

"'ya'yan sa uku ne, wannan biyun da ka gani, sai guda, ita ba ta fiye zama a gida ba, jami'ar kwana ta ke ai"

Isa ya amsa masa zuciya daya ba tare da ya kawo wani abu cikin ran sa ba. Shiru ne ya biyo baya, Isa bai fasa cin gyadar sa ba, shi kuwa Usman zaton shi ne ya tabbata, Zainab ita ce diyar Malam da ya gani jiya ta hauro kan katanga.

'ita ko wannan Bingel me zai sa ta haura katangar gidan su tsakar dare haka?'

Tambayar da yayiwa kan sa kenan, ji yayi duk duniya be da muradin da ya wuce ya san musabbabin wannan lamari na diyar Malam.

Halitta kuwa tun bayan fitar su take washe baki kamar wacce aka ma bushara da gidan aljanna. Ba ta bari sun dade gidan da su ka je ba ta ringa azalzalal Falmat su tafi gida, dan kawai su dawo ta kara ganin shi. Su ka yi rashin sa'a kafin su dawo Usman ya tashi sai Isa kawai su ka tadda. Haka ba yanda ta so ba su ka wuce ciki.

Dakin ta tayi kwance, bayan ta sallami Falmat da abayar da ta yi mata alkawari. Da kwanciyar ta ishe ta ne ta leka account din ta na Instagram, nan ta ci karo da hotunan Zainab na club, tun tana dauke kai har ta kai hotan da tayi tsakiyar maza ta na busa hayakin shisha, ka na gani ka san sababbiya ce a harkar. kasa zama ta yi, zuciya na zafi ta tashi ta nufi dakin ta.

Kai tsaye ta bude kofar dakin ta shiga batare da ta buga mata ba. Bisa gadon ta tarar da ita ta yi kwanciyar rub da ciki, sanye cikin wando "bump short", da yar riga wacce ko cibiya bai rufe mata ba. Ba komai ya dauki hankalin Halitta ba face wata yar zanen fulawa da ta gani kugun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login