Showing 36001 words to 39000 words out of 58720 words

Chapter 13 - Auren Shehu Book 1 Hausa Novel Complete

25 Jan 2025

615

waye? Haba Malam ya ka na Malami kana da sani ka ke ta ke sanin haka?"

Shiru ne ya biyu baya na dan wani lokaci, sannan Alhaji Sidi ya ce

"Na sani Malam, it's not easy, shi ya sa na ce ma ka kada ka yanke hukunci cikin fushi, Dan kuwa matukar yarinyar nan akwai istibiraqi kan ta auren nan sai an warware shi....."

"Idan kuma babu wallahilazim sai ta zauna da mijin ta matukar ba shi da bakin sa ya sake ta ba"

Ajiyar zuciya Alhaji Sidi ya saki, kana ya ce

"Idan har auren be sabawa addinin musulunci ba, be saba shari'a ba ai aure kam ka daura shi Malam"

Kai Malam ya jinjina cikin gamsuwa, Amma har ga Allah ba ya fatan wargatsewar auren Zainab da Usman, har lokacin be yi dana sani ba, ba kuma zai yi dana sani ba, da wannan kudirin su ka yi sallama da Alhaji Sidi. Maimakon ya kira Zainab kamar yanda yayiwa Alhaji Sidi alkawari, sai ya kiran kiran su Jauro yayi ya ba su umarnin su taya Usman a kwashe kayan BQ gaba daya a gyarawa Zainab da Usman dan kuwa a ranar za ta tare dakin mijin ta.

Ganin yanda su Isa su ke kai kawo hauka ne kawai Zainab ba ta yi ba. Hatta wayar ta da ta addabe ta da kara ganin Mike ne ke damun ta ba ta san sanda ta doka shi kasa ba, screen ya fashe. Halitta kuwa tun da su ka baro wajan Malam ta shige dakin ta ta kulle, kuka ta yi sosai kamar ran ta zai fita, duk da ba ta taba tunanin samin Usman a matsayin miji ba, Amma kasancewar shi mijin yar uwar ta abu ne mai ciwo a gare ta. Sam Ammy ba ta damu da halin da Halitta ta ke ciki ba, a tunanin ta halin abin da ya faru da Zainab ne ya sanya ta halin da ta ke ciki. Yan uwan Malam na jiki da kuma na ta yan uwan da su ke ta kira ta saka mu su kuka, cewar ta su kawo mu su doki Malam ya bayar da auren Yakura ga Maigadi, auren ma na sadaka ba tare da sadaki ba. Haka su ka ringa kiran Malam ya na gani ya ki dauka, karshe ma kashe wayan yayi gaba daya. Haka kuma ya ki sauraran ta bare su yi magana, tun ta na kuka har ta koma fada fada, ta na cewa Malam ya tsane ta ya tsani yayan ta shi ya sa ya mata wannan wulakancin.

Kafin azahar ta yi su Usman su ka gama gyaran BQ tas, dama kanana dakuna ne guda biyu, sai dan karamin kitchen da bandaki. Tun da su ka fara aiki Jauro ke jifan Usman da Habaici, bini bini ka ji ya ce

"Dan cirani an zama dan masu gida, an bar daji an zo birne ana mana surkulle"

Ko kuma ya ce

"Kai da na sani ni ma na yi kanzagi wajan neman suna da fa Malam ya dauran mata...."

Usaman na jin shi amma ya masa banza dan kuwa idan akwai abun da ya dami kwakwalwar sa ya bi bayan auren Zainab da aka daura masa, har ga Allah be da niyar kara aure saboda yanda auren shi da Cangwai ya kaya, bare kuma Malam ya aura masa mace wayayyiya, yar birni kuma yar boko kamar Zainab, shin ya rayuwar shi da Zainab zai kasance? Da wani idanu zai dubi Malam ya roke shi da ya sauwake masa wannan nauyi da ya dora masa?

Da wannan tunanin a ran sa ya wuni, dan kuwa ranar sam be sami kwanciyar hankali ba bare har ya samu ya kai lomar abinci bakin salati. Bayan la'asar Malam ya nemi ganin Usman a falon sa, Nan ma Jauro ya fara

"Dan masu gida sirikin Malam, an baka mata an baka wajen zama, maza je ka kila abin hawa kuma za a baka, kai ya kamata ka mu sirrin wannan surkullen na ka!"

Usman be kula shi ba ya wuce falon Malam. Sanye ya ke cikin rigar sakin shi fara, da bakin wando, fuskarsa rufe da farin rawani. Ganin takalma a waje ya sanya shi sallama tare da tsayawa daga waje. Malam ne ya amsa masa sallam sannan ya ba shi izinin shigowa.

Ganin ta zaune tare da Halitta sai da gaban shi fadi, badan komai ba sai dan yanda dukan su biyun su ka zuba masa idanun su da ya yi jajur kai ka ce mutuwa aka mu su, in da Halitta ke kallan sa cike da kewa, so da kauna, Zainab kuwa tsantsan tsana ne cikin na ta idanun, dan kuwa nan duniya idan akwai wanda ta tsana ya bi bayan Usman, wanda a yanzu haka shi ne mijin ta.

Da sauri ya kawar da kai gefe ya sami waje can baya ya na shirin zama Malam ya ce ya motso kusa da shi ya zauna. Cike da jin nauyi ya matsa gaban Malam wanda ke zaune kan doguwar kujera.

Malam na daga zaune ya ke kare mu su kallo, Halitta sanye cikin bakar abaya, kan ta nade da mayafin, Abin ku da farar mace har wani jaja fuskarta ta yi tsabagen kukan da ta sha. Shi kan shi Malam yayi mamakin damuwar da Halitta ta shiga sanadiyar hukuncin da ya yanke na auran yayar ta. Zainab kuwa Hijabin jikin ta har jirwaye yayi tsabagen hawaye da majinar da ya sha. Daci rai da bakin ciki ya sanya shi saurin dauke kai daga kallan Zainab yayinda ya furta

"Na yanke hukunci cikin gaggawa ba tare da na tambayi abu mai muhimmanci na game da shiri'ar musulunci ba sai da Alhaji Sidi ya nusar dani, ka sani Usman ko kadan ban yi danasanin daura ma ka diya ta da na yi...."

Jin haka wani sanyi ne ya ziyarci zuciyar Zainab, a tunanin ta Allah ya amsa adduar ta, Malam zai saka Usman ya sauwake mata igiya ukun da Malam daure ta da shi. Malam be gushe ba ya cigaba da fadin

" akwai tambaya mai muhimmanci da ya kamata na yi mata kafin na daura ma ka ita, kuma zan yi mata shi gaban ka tun da tsakanin mu da kai babu boye boye, amsar da za ta bani shi zai bani haske akan tarewar ka da ita ko kishiyar haka..."

Usman na mai dukar da kai cikin fatan Allah ya warware masa wannan nauyi da aka daura masa ya furta

"Na'am"

Zainab ba ta ankara ba sai ji ta yi Malam ya kira sunan ta da kakkausar murya ya na mai fadin

"Zainab ki duba girman Allah, tsakanin ki da Allah ki kin taba aikata zina? Yaushe ne ranar karshe da ki ka aikata?"

"Innalillahi wainnailaihi rajiun!"
Cewar Zainab hannun ta biyu ta sa ta toshe bakin ta tsananin kukan da ya ci karfin ta. Ita kan ta Halitta tambayar ta mata tsauri da bazata, shi kuwa Usman kan sa sunkuye ya na jiran amsar da zai iya zama mafita a rayuwar sa.

"Ke dallah rufa mana baki! Ki amsa min tambaya yanzu yanzu shasha kawai! Ba kya yawo ne? Idan ke kamila ce kamar yanda na yi tunani a da me zai sa na mi ki wannan tambayar? Ko za ki ce min ba ki taba kusantar zina ba idan har ma ba ki aikatawa ba!"

Malam ya fada a fusace, hakan ya sanya Zainab saurin fadin

"Wallahi dadi na rantse da Allah ban taba aikata zina ba Daddy, Daddy wallahi iyakaci na club, shi ma na maka alkawari ba zan kara zuwa ba Daddy...."

"Diya ta ni Birma a club!"

Malam ya katse ta cike da takaici. Zainab ta kara da

"Daddy idan har ka aurar da ni ga Sudais zan kasance mace ta gari a gare shi, Daddy ban taba zina ba Daddy, Daddy dan Allah ka sa ya sake ni, Daddy na tuba....."

Wani sanyi ne ya ziyarci zuciyar Malam, dan kuwa shi kan shi ya san da Zainab mazinaciya ce tabbas zai iya hadiyar zuciya ya mutu. Ya na mai godiya ga Allah da iya club din ya tsaya, ya ce

"Bakin alkalami ya bushe, Usman shi ne mijin ki, auren shi ya tabbata akan ki...."

Kukan Zainab be sa Malam ya tausaya mata ba, idanun sa kan Usman ya ce

"Usman ga ta nan halak din ka ce, ci, sha da suturar ta ya rataya hannun ka, dan Allah ka kasance mai adalci, Zainab amana ce gun ka, na ba ka ita amana ko bayan rai na, kamin alkawarin duk runtsi duk wuya ba za ka sake ta ba, dan Allah Usman....."

"Malam ba sai ka roke ni ba, Na daukar maka alkawari, Zan ruke ta amana, Na dau maka alkawari matukar ba a shiga hakkin Allah ba, ba zan taba sakin ta ba"
Jin alkawarin da Usman ya daukarwa Malam kamar wuka ya ke daba mata a kahon zuciyar, wasu zafafa hawaye ne ke zuba daga idaniyar ta tamkar wuta. Malam na duban Halitta wacce ita ma din hawaye ne ke kwaranya daga idanun ta jin alkawarin da Malam ya sa Usman ya dauka, Malam ya ce

"Halitta na yanke hukuncin ba da auren ki ga Sudais amadadin yar uwar ki, in Sha Allah kamar yanda mu ka tsara shabiyu ga wata juli zai kasance ranar daurin auren ki"

Da dashasshiyar muryar ta Halitta ta amsawa Malam da

"Toh Daddy, na yi biyayya"

"Allah ya mi ki albarka"

Halitta ta amsa da amin, kafin ya mayar da kallan sa ga Zainab wacce jin za a daurawa Halitta Sudais ba karamin bakin ciki ne ya kara taruwa cikin zuciyar ta ba. Gani ta ke Malam ya tsane ta cikin 'ya'yan sa ya aurar da ita ga Mai gadi, gashi zai aurar da Halitta ga dan abokin sa. Ba ta kara sarewa da Malam na sai da ta ji ya ce

"Usman sai matar ka ta hado na ta ya nata ku tare can BQ da na tanadar mu ku ko? Da ga yau kada ta sake kwanan min cikin gida, ki kwana dakin mijin ki, na sallame ki har abada"

Daga Usman har Zainab Malam su ke kallo, ganin babu alamar sassauci a fuskar sa ya sanya Usman kallan Zainab, kamar yanda yayi imani zai mutu haka ya tabbatar da tashin hankalin da ke tattare da Zainab.







*Khadija Sidi*Auren Shehu



12





Umarnin da Malam ya bawa Zainab na ta koma BQ ba karamin tashin hankali ya haddasa tsakanin Malam da Ammy ba, abin da bai taba shiga tsakanin Ammy da mijin ta ba ranar kuwa sun yi abin sam ba dadin gani bare ji. Shi kan shi Malam mamakin dama akwai ranar da Ammy za ta dubi tsabar idanunsa ta gasa masa maganganu haka ya ke. Ya na daga kwance ya ke kallonta, tun shigowar ta falon ta tsaya kan sa hannu rike da kugu in da ta ke shiga ba ta nan ta ke fita ba, sai da ta dan tsagaita Malam ya furta

"Alesha kin gama?"

"Ban gama ba Malam, idan ka ga na gama to ka raba wannan bakin aure mai cike da cuta da ka kulla tsakanin diyarka ta cikinka da Mai gadi wanda be da asali Malam! Ai ko addini cewa yayi mu zaba ma 'ya'yan mu mazaje na gari, haka kuma mu yi bincike akan mutum kafin mu ba su auren 'ya'yan mu, ban ga dalilin da zai sa ka lalatawa yarinya rayuwa ka aura mata maigadi wanda ba mu san komai game da shi ba! Ni jinin shuwa sulallan gwal ka biya sadaki na, Amma ka dauki diya ta, jini na ka bayar da ita sadaka!"

Ammy ta bashi amsa cikin tsiwa. Shiru Malam ya mata tamkar ba da shi ta ke magana ba. A hasale Ammy ta furta

"Malam ka na ji na fa!"

Dagowa yayi yana duban ta, ainihin so da kauna na hakika ya ke yiwa baiwar Allah nan, dan kuwa yanda ya ke san ta be so uwargidan sa Hajja Kulu ba, badan komai ba sai dan Ammy ita ce zabin ran sa, uwargidan sa kuwa zabin iyaye ce.

"Alesha duk yanda ki ke tunanin kaunar ki ga Zainab ya kai, ba ki fi ni san ta ba, Ni ne mahaifin Zainab dan haka ba zan cutar da Zainab ba, aure kuma na daura, babu abin da zai kashe auren nan sai Allah....."

"Karatun ta Malam? ka na nufin ka salwartar da karatun ta kenan? Yakura ta yi nisa a jami'a, wata daya ya rage su koma makaranta, aji uku Yakura ta ke, semester daya ya rage ta shiga aji hudu, yar jami'a ka daurawa ma Maigadi dan ruga Malam!"

Ammy ta katse shi ta na maganar ne kamar mai shirin fashewa da kuka. Cikin halin ko in kula Malam ya ba ta amsa da

"Wannan tsakanin ta da mijin ta ne, karatun na ta, idan ya ga zai iya barin ta ta karasa fabini'ima, idan ba zai bari ta karasa ba ma wannan zabin sa ne..."

"Toh kuwa sai ka zaba! Aure na da kai ko kuwa auren Zainab da Maigadi! Wannan zalinci ba zan iya jurar ganin shi ba!"

Gaban Malam ne yayi mummunar faduwa, da sauri ya tashi tsaye ya na mai duban Ammy ya ke fadin

"Alesha? Ni ki ke fadawa haka? Auren mu ko auren Zainab?"

"Kwarai Malam, ba zan iya zama gidan nan diya ta ta ciki na ta na auren Maigadi ta na kwana a BQ ba, ba zan iya zuba ido ina kallo ana tauye hakkin diya ta ba, ka zaba Malam"

Ta bashi amsa cikin dakiya, dan kuwa ta san yanda Malam ke kaunar ta ba zai taba zaban wani bayan ta ba duk da tsanar subda ta ke zargin ya yi. Ga mamakin ta sai ji ta yi Malam ya ce

"Na zabi auran Zainab da Usman, sai yaya? Me zai biyo baya?"

Zuciya tsinke dan kuwa sam ba ta yi zato ba Ammy ta ce

"Ka zabi ka sake ni kenan? Saki nawa ka min?"

Kai Malam ya girgiza yayinda ya koma ya zauna, fuskar sa dauke da murmushi ya kai hannun sa ga qur'anin da ke aje can gefe bisa dan teburi. Ya na kokarin budewa Ammy ta sake fadin

"Saki nawa ka min"

Ya na murmushi kaici ya ke girgiza kai, kana ya ce

"Alesha ashe dai har yanzu ba ki dena tunani irin na yara ba, saki? Ni Birma na saki mata ta? Ban taba sakin iyali na ba, ba zan fara akan ki ba Alesha, kin ce na zaba ko auren Zainab da Usman, ko aure na da ke, na zabi auren diya ta, ban yarda na mayar da diyata bazawara ba, haka kuma ban sake ki ba, ba zan kuma sake ki ba...!"

"Ni kuma ba zan zauna da azzalumin miji irin ka ba! Kai ne kullum cikin wa'azi Allah ya ce annabi ya ce! Amma ka kasa kare hakkin iyalin ka sai ma cutar da mu da ka ke kokarin yi! Allah ya saka mana! Ko ka sake ni ko ba ka sake ni ba zama na da kai ya kare!"

Baki bude Malam ke duban ta ya kasa magana tsabagen mamakin maganganun da Ammy ke fada masa. A fusace ta juya fuuuu ta fice ta na mai buga masa kofa ta wuce bangaran su.

Ganin yanda ta shigo a fusace ya sa Falmat bin bayan ta tana tambayar Ammy lafiya? Me ya faru? Ba ta bata amsa ba, sai ma hade kayan ta da ta shiga yi. Cikin kankanin lokaci ta hade kayan ta tsaf cikin yar akwati. Ganin haka Falmat ta kira Halitta da Zainab wanda duk abin nan da ake ko waccar su na dakin ta tana fama da kan ta.

A falo su ka tadda Ammy ta na jan akwatin ta niki niki za ta fita. Iya na tambayar lafiya Hajiya za ki yi bulaguro ne? da sauri Halitta ta karasa gaban ta, ta na mai taro akwatin ta ke fadin

"Innalillahi Ammy me za???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?n gani? Ina za ki je haka da yamma likis Ammy?"

"Gidan uban ku zan bari, aure na da shi ya kare, ya zabi auren Zainab akan aure na da shi!"

"Ammy ki rufa min asiri idan ki ka tafi ina zan sa kai na?"

Cewar Zainab ta na mai riko hannun Ammy.

"Uban ki ya dafa ki ya cinye!"

Ammy ta bata amsa a hasale. Cike da tashin hankali Falmat ta ke kuka, Zainab kuwa dama ta nemi kuka ta rasa sai dai na zuci, wani tsanar Usman ta kara ji, ta kuma kullaci Malam da har ya zabi rabuwa da mahaifiyar ta akan auren ta da Usman, wato ya tabbata Malam ya tsane ta ya kuma tsani mahaifiyar ta. Halitta na mai girgiza kai cikin rashin gasgata maganar Ammy ta ce

"Ammy ba haka ba ne, Daddy ba zai taba zabar rashin zama da ke ba Ammy, wannan masifa har ina, Innalillahi wainnailaihi rajiun! Ammy da kuruciya ba ki taba yin yaji ba, dan Allah kar ki yi da tsufan ku, Dan Allah Ammy....."

"Ke rufa min baki! Kuruciya ko tsufa namiji namiji ne! Uban ku ma namiji ne! Ba uba na ba ne, ba gidan uba na ba ne, wallahi ba zan zauna bakin ciki ya kashe ni ba, matsa min daga hanya!"

Ta na mai hambare Halitta ta tare da buge hannun Zainab ta ja akwatin ta ta yi waje. Iya kuwa wacce duk abin da ya faru ba ta gidan cike da al'ajabi ta ke bawa Ammy hakuri, Ganin dai Ammy ta ki ji Iya ta ce da Falmat ta yi maza ta shedawa Malam halin da ake ciki. Falmat ta fita da sauri ta nufi bangaran Malam, ta tarar da shi zaune in da Ammy ta barshi ya na karatun al'qur'ani, ganin Falmat da kuma abin da take fada masa hankali tashe be sa ya motsa ba, bare ya nuna mata wani damuwa. Kallan ta yayi cikin nazari kafin daga bisani ya bata amsa da

"Ammyn ku ta zabi ta tafi, ku bar ta ta tafi za ta dawo ne da kafafun ta, ku kasance masu hakuri Falmat"

"Daddy ba za ka tsayar da ita ba? Ba za ka hana ta tafiya ba Daddy?"

Kai ya gyada mata, sannan ya kara da

"Ki yi hakuri Falmat, babu yanda zan iya da hukuncin ubangiji dan kuwa auren Yakura ba mai rabuwa ba ne har illa mashaAllah"

Shiru ne ya biyu baya, jiki sanyaye Falmat ta juya ta fita. Malam ya bi bayan ta da kallo na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login