Showing 6001 words to 9000 words out of 58720 words

Chapter 3 - Auren Shehu Book 1 Hausa Novel Complete

25 Jan 2025

455

Zainab, dab da mazaunan ta, ta na mai tafa hannu ta furta

"Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun Mai Zan gani jikin ki Yakura kamar Tattoo?"

Jin maganar kamar daga sama ya sanya ta sakin wayar hannun ta ta tashi zaune da sauri ta na duban Halitta.

"Haba Halitta! Ya za ki shigo min daki haka ba sallama! In aka yi magana you claimed Ustaziya ke diyar Dady! Yes Tattoo ne jiki na so what?"

"Tattoo fa Yakura? Ki na diyar musulmai ki yi tattoo? Ba ki ji tsoran tsinuwar Allah? Yanzu dan Allah idan Dady ya gani ya ki ke tunani zai ji....?"

"It's not meant for Daddy's view shi ya sa na yi shi kusa da ass dina ok?"

Cewar Zainab ta na mai sake nunawa Halitta inda zanen tattoo din ya ke. Halitta kamar za ta yi kuka dan takaici. Zainab kuwa ko a jikin ta, sai ma ta kara mata da yi da

"Toh dan ma na yi tattoo na kafirta ne? Tsinuwar Allah kuma ai tsakani na da Allah na ne, bare ke da ki ke claiming ki na tsoran tsinuwar Allah na ga ai kina make up once in a while, kuma in za a zana mi ki gira sai an aske...."

"Auzubillallah! Allah ya tsare ni da aske gira, ban taba ba, kuma ba zan taba ba in Sha Allah"

Halitta ta katse ta. Kom??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????awa ta yi, ta yi irin wannan kwanciyar ta rigingine, ta na duban Halitta ta ce

"An yi rashin sa'a ban sami wanda su ka iya permanent one ba ne, wannan iyakan sa shekara daya, Amma ya na gogewa zan fita US a yi min permanent, after all jiki na ne ba naki ba, oya me ma ya kawo ki daki na?"

Shanye bakin cikin da ya taso mata cikin ranta ta yi, wayyar ta ta daga mata, nan hotan nan ya bayyana a idanun Zainab, Halitta ta ce

"Wannan wani irin shiga ne Yakura? Yanzu har kya iya zama cikin maza da wannan shigar ta ki? Har ki dauka ki sa a social media? Kuma ki na busa hayaki Yakura! You smoke? You are smoking in the picture! Me mutane za su yi tunani akan Dady muddun su ka san ke diyar shi ce?"

Zainab na kallan ta irin kallan nan na hadarin kaji ta ce

"Wai ke Haliita ba za ki fita harka ta ba? It's my life, my personal life! Ko kin ga na sa sunan Dady jikin sunana? Ina ruwan Dady da rayuwa ta a waje? Cikin gida na ke diyar sa, ina shiga irin wanda ya ke so a cikin gida in da ya ke gani na, ina masa ladabi da biyayya and he is satisfied! a school da social media I'm the person I chose to be, I don't use his name! mahaifina kenan bare ke da kike kanwa ta! Dan Allah ki fita harka ta Halitta!!"

Ta dan tsagaita ta na mai jan wayar ta, Instagram ta shiga ta dubo sunan Halitta, ta ce

"Alright ga shi nan na yi unfollowing din ki, I expect you to do the same in dai ke ba mayya ba ce! Wannan masifar har ina!"

Ran Halitta idan yayi dubu ya baci, cikin zafin rai take kallan Zainab, ta ce

"Ki tuba Yakura! Ko dan darajar mahaifin mu ki tuba, kuma ki sani idan babu mutuwa akwai tsufa, ke mace ce, Rayuwar diya mace kalilan ce, Me za ki ce da 'ya'ya duk randa su ka wayi gari aka yi musu nuni da wannan hoto aka ce ke mahaifiyar su ce? Da wani ido za ki kalle su?......"

"Get out of my room! Ba na bukatar wa'azin ki, ki bari sai Dady ya hau mambari ki ja masa baki! Nonsense!"

Ta katse ta cike da masifa. Jiki sanyaye Halitta ta juya, ko da ta kai kofa sai ta sake juyowa ta da dubi Zainab da ke kallan ta kamar zakanya, ta ce

"Ba zan fasa mi ki wa'azi ba Yakura, ba zan fasa mi ki addua ba, Allah ya shirye ki"

"Mtswww"

Amsar Zainab kenan, yayin da ta tashi ta rufe kofarta da key bayan fitar Halitta. Idan ran ta yayi dubu ya baci dan kuwa a rayuwar ta ta tsani sa ido, gani ta ke duk duniya babu wanda ya sa mata ido kamar Halitta, shi ya sa ma sam ba sa shiri.


AUREN SHEHU

3

Ta na zama bisa gado ta Wau wayarta ta kira abokin zuwa club din ta da ta ke kira Bobo, bugu daya ya daga tare da faWin

"Zeee oh Zeee the slay mama the club mama, diyar Malam ta ki halin Malam! Ai ni na san baki fushi Zeeena....."

"Eh en fa Bobo!"
Ta katse shi, ba ta gushe ba ta kara da

" Kar ka wani dame ni da dadin baki! Da ka san masifar da ka kusa jawo min jiya da ka ji tsoran Waga waya ta!"

"Toh yanzu dai Allah ya baki hakuri, ko da ya ke tun da ki ka kira ni ma na san kin huce, wetin dey sup? Malam don commot?"

Cewar Bobo cikin muryar zolaya.
"Ehen na, him don go Maid, toh ya za a yi? Any happening tonight? Amma dan Allah kar ka kai ni club din talakawa, ka san I can't stand them!"

Ta fada ta na mai yamutsa fuska. Dariyar kyeta ya saki, fadi ya ke

"Heheheheh Zeeena na daWe ban ga wanda ya ke kyamkyamin talauci kamar ki ba, babe don't worry I got you, ki shirya 12 daidai ta yi mi ki gaban gate din ku, na san dai yau ba batun haurawa tunda Malam baya nan"

"Ba ka da matsala, su Isa ne ai wa'inan, in su ka sa shayi gaba har na wuce ma ba lalle su sani ba, sai ka zo"

Ta na maganar ne yayinda Usman ya fado mata rai, ta na mai adduar Allah ya mata katangar karfe da shi, su ka yi sallama da Bobo ta aje wayar.

***

Kamar yanda ta saba duk sanda ta san ta kulla harkallar ta, ana isha'i ta fara kukan ciwon kai, daga Ammy har Falmat babu wanda ya kawo wani abu cikin ran su, sai ma tararraya ta da su ka din ga yi, musammam ma Ammy. Halitta kuwa ko kallan in da take ba ta yi, dan cike fal ta ke da Zainab. Ammy ce ta bata magani ta sha, ta ce lalle ta je ta kwanta, amma Zainab ta ce ah ah, gwara ta zauna jikin su za ta fi jin dadi.

Sai da ta bari goma da rabi yayi sannan ta ce ciwan ya ci karfin ta, bari ta kwanta dan Allah kada wanda ya shigo ya tada ita, dan idan aka tada ita ba lallai ta iya komawa bacci ba, gashi kuma dama ciwon kai ta ke. Ana bin ta da sannu haka ta mu su sallama, ta koma daki ta yi kwanciyar ta har da kashe wuta.

Da ya ke uwa uwa ce wajen sha daya Ammy ta kasa hakuri, sai ga ta a dakin, ganin wutan a kashe ya sanya ta yin sanda zuwa ga gadon Zainab, wacce jin shigowar uwar ta saki jiki ta yi lum kamar mai bacci. Hannun ta dora bisa goshin Zainab ta na mai hamadala, fadi ta ke

"Alhamdulillah ta sami bacci"
Ta na mai jawo bargo ta dada rufe ta. Sai da ta karanta mata adduar bacci ta shefa jikin ta sannan ta juya ta fita.

Ta na fita Zainab ta yi zumbur ta mike, dan kuwa ta san babu mahalukin da zai sake shigo mata daki tunda har Ammy ta ga ta yi bacci, bari ma kuwa idan akwai wacce za ta iya shigo mata munafunci Halitta ce, ita kuma sun yi fada toh ta tabbatar hakan ta ya cimma ruwa.

Wankan ta tayi ta fito tsaf cikin wondan ta pencil Jean blue tare da yar karamar riga ja, ta faka gashin nan tsakiyar ka kai ka ce ba diyar musulmai ba ce. Ba ta damu da yin make up, dan irin su Zainab ake yiwa kirari da "black beauty better than gold always shining". Tsadaddiyar powder mai sanya fuska sheki ta shafa, turaruka kuwa 212 sexy, escada magnetism, tare da Indian night Jasmine sai da su ka koka.
Gaban madubi ta tsaya ta na mai karkada kugu ta ke yiwa kan ta kirari

"Zeee oh Zeee the slay mama, the club mama, kuma salihar Dadyn ta"

Sai da ta yi mai isar ta, ganin sha biyu ta kusa ta sanya hijabi har kasa, bayan ta gama gyara gado, ta saita fululluka kai kace mutum ne kwance ta sa bargo ta rufa mu su, takalmin ta mai tsinin gaske a hannun ta na mai sanda ta fito. Ganin wutan falon a kashe ta san kowa ya kwanta, sadaf sadaf ta zaga ta baya ta fice.

Isa kuwa da Jauro masu gadin gidan nan gaban gate su ke kwance bacci ya sace su dan yau ko karnukan gidan ba su sake ba. Kallo Waya Zainab ta mu su ta ja tsaki tare da fadin

" Ji be su kwance kamar mushe! Idan ma sace gidan za a yi wato a yi tunda Dady bayanan, Allah ya kai mu gobe za ku yiwa Ammy bayani!"

Ba ta kara tsorata ba sai da ta ga gate din bude, wato ko sakata ma ba su sa ba! Har ta juya a fusace za ta tada su, sai ta tuna tana tayar da su shikenan asirin ta ya tonu, ta na mai adduar Allah ya kare su Ammy ta sa kafa ta fita, hakan yayi daidai da dalle ta da tocilit da aka yi, yanda hasken ya dalle idanun ta ya sanya runtse idanun ta na mai fadin

"Oh my God"

Tsaye ya ke ya na duban ta, suna hira da su Isa bacci ya kwashe su, dan haka ya dan fita waje mike kafa. Kusan mitunan shi ishirin waje gaban gate, dake unguwar ba mai hayaniya bace sosai kafar mutane ya dan dauke, jin wani ni'imataccen kamshi ya sanya shi dan waige waige tare da tunanin ko dai aljana mai turare ce ta bakunce yau, wanda fitowar ta ya gasgata masa da haka, dan kuwa dai da ya haske ta ganin ta ya ke tamkar aljanar ce tsaye gaban shi.

Ganin ba a da niyar daina haska ta ya sanya ta kare fuskar ta da tafin hannun ta, cike da nuna bacin rai ta ce

"Dalla Bobo dena haska ni kafin ka sa a kama mu! Kai fa iskancin ka yawa gare shi!"

Jin haka ya sanya shi kashe tocilan ba tare da ya iya furta komai ba, dan kuwa harshen sa ya sarke kamar wanda aka daure harshen cikin bakin sa. Bude idanun ta tayi tare da fadin

"Bobo....."
Ganin wanda ke tsaye gaban ta sai da ta dan ja da baya, shi din nan dai Usman, sanye da rigar saka da rawani irin na buzaye, hannun sa na dama rike da sandar gora, dayan hannun kuma tocilan ne. Ta na shirin juyawa ta koma sai ga motar Bobo, ai kuwa kafin Usman ya ankare da gudun ta ta nufi motar, ganin haka Bobo ya tsaya ta shige ta na fadin

"Kai let's get the hell out of here, ina tsoran Allah ina tsoran wannan dan boko haram din can!"

AUREN SHEHU

4.



Jin kalmar "Boko Haram" jiki na rawa Bobo ya figi motar ya na mai tayar da kura, fadi ya ke

"How? Ya aka yi ki ka san dan Boko Haram ne?"

Karar yanda Bobo ya figi motar ne ya sanya su Isa da Jauro fitowa a guje suna fadin

"Su waye nan! A tare! A tare!"
Ina sai sahun tayar motor Bobo su ka gani, idan shi kan shi Usman da ke tsaye kamar mutum mutumi Jauro ya ce

"Yo kai Wan cirani kana nan tsaye ashe, me ke faruwa ne?"

Isa ya kara da
"Wacce mota ce ta tashi a guje yanzu? Su waye?"

Maimakon ya ba su amsa, sai ya juya abin sa yayi ciki, suna tafe bayan sa, su ka koma ciki, daki yayi wucewar sa ba tare da ya tanka mu su ba.

Isa da Jauro su ka tsaya jugum jugum suna duban juna, Jauro ne ya gyara tsayuwa ya ce

"Ina Isa? Ni fa Allah na gani ban yarda da wancan dan ciranin ba! Ga fa karar tashin motar da mu ka ji! Mu ka tashi mu ka ga gidan nan bude, shi kuma mu ka taras waje tsaye kamar gunki, Anya kuwa Isa?"

Isa wanda kamar Jauro ya shiga ransa, ya dan yi ta maza ya dake, ya na mai yamutsa fuska ya ce

"Anya kuwa me?"

"Anya kuwa lafiyayyan mutum ne?"

Jauro ya fada cike da damuwa.

"Ka gan shi da wata rashin lafiya ne?"

Cewar Isa cikin dakiya dan ya san in da Jauro ya dosa. Jauro na mai girgiza kai ya sake cewa

"Ka san abin da na ke nufi Isa, dan kuwa na san kai ma zuciyar ka ta yi rawa akan lamarin Usman....."

"Na raba ka Jauro, na raba ka! Kar ka manta Malam ya karantar da mu akan zato, ya ce zato zunubi ne ko da kowa ya kasance gaskiya, Ni ka ga tafiya ta kunto karnukan nan, da bacci be dauke mu ba ai duk da ba haka ba!"

Isa ya tafi ya na mita, Amma cikin ransa tunanin da Jauro ya ke shi ma din shi ya addabi zuciyar sa.

Usman kuwa can lambu ya shige in da ya saba raba dare, wata yar doguwar kujera ta hutawa ya samu yayi kwance idanun sa na kallan sararin samaniya. Kamanin Zainab ke masa gizo, haka kuma kan sa ya dada kullewa akan lamarin ta,

"Shin ita wannan diyar Malam din ina za ta je da tsohon daren nan? Shin mahaifiyarta ta san da fitar ta? Shi wannan da ya Wauke ta a bakar mota mai bakin gilashi wanene shi?'

Tambayoyin da ya ke yi cikin ran sa ke, wanda ya kagu ya samu amsar su.

Ita kuwa Zainab tun da su ka tafi Bobo ke tambayar ta ya aka yi ta san mutumin nan dan boko haram ne? Wanene shi? Sai da ta nutsu sannan ta iya amsa masa da

"Daya daga cikin daliban Dady ne, kuma ya na mana gadi, haka kawai jinina be hadu da shi ba wallahi, ka ga jiya ma shi ya kama ni, gashi yau ma an kuma! Allah dai ya tushe bakin sa...."

"Wa ya ce mi ki dan boko haram ne?"
Bobo ya sake tambaya cike da damuwa.

"Haaaaa'a! Are you even listening?"

Zainab ta fada cike da tsiwa, ba ta gushe ba ta kara da

"Dallah waye zai yarda dan boko haram ya zauna gidan su? Na ce da kai dalibin Dady ne!"

"Toh Zeeee ke ce na ji kin kira shi da boko haram....."

"Saboda ya na min kama da su ba! Ba wai ina nufin shi din ba ne, ko da ya ke it's possible shi din ne tunda ba wai kwakkwarar bincike aka yi ba...."

Ta fada ta na kallan Bobo wanda ya fara hada zufa. Dariya ne ya kwace mata, ta ce

"Sai shegen tsora, dallah wasa na ke ma"
Bobo na mai goge zufa da hankaci ya ce

"Ai dai mutanan ne abun tsoro, Allah ya mana tsari da su, mugu be da kama Zee"

Cikin faduwar gaba yayin da kamannin Usman su ka bayyana a zuciyar ta, ya fito mata sak a kamannin mugu, ta na mai saurin kawar da tunanin ta ce

"Amen, Allah ya min tsari da shi!"

"Wa fa?"

"Dan Boko haram mana, Maigadin gidan mu!"

Ta fada kai tsaye.
"Ki ka ce ba dan boko haram ba ne?"

Bobo ya sake tambaya cike da damuwa.
"Aaaarrrrghhhh Bobo don't spoil my mood!"

Ta fada cikin tsawa. Hannun ya daka tare da fadin

"Allah ya baki hakuri Zeee Mama!"

"Ba Allah ya ba ni hakuri ba, you better take me to a nice club!"

"I got you, kafin nan bari na baki sauti mai dadi"
Cewar Bobo yayinda kunna waka ya na mai kure karar.

Ranar club yayi ma Zainab dadi, ta hadu da sabon saurayi wanda tare su ka cashe a daren ranar har ta shagala da lokaci, dan kuwa dai ba ita ta ankara ba sai da shida ta wuce. A kidime ta azalzali Bobo wanda ta janyo shi tsakiyar kedaru su na cashewa. Sabon saurayin da ya Kira kan sa Mike ne ya nuna dacewar ya aje ta gida, hakan ba karamin dadi yayiwa Bobo ba, amma Zainab ta hana, ta dai ce ya bari sa yi magana daga baya. Haka su ka yi sallama Bobo na mitar ta katse masa shagali su ka dauki hanyar gida.

Dab da za su shiga unguwar ya kalle ta ya ce

"Babe kin katse min runs wallahi"

"Mtswww"

Ta ja tsaki ba tare da tanka ma sa ba, gaba daya hankalin ta ba ya tare da ita, shikenan yau kam asirinta ya tono, tun da take zuwa club ba ta taba kaiwa haka a waje ba, har a idar da sallar asuba ba ta koma gida ba? shin me za ta ce da Ammy idan har ta shiga dakin ta tashin ta sallar asuba ta ga ba ta dakin? Ya ma za ta yi ta shiga gida gari waye haka babu daman ta haura? Kuma ta san su Isa da Jauro ba lalle sun bude gidan ba in ba dai dan boko haram din nan ya kwana nan in da ta barshi tsaye ba ne, wanda ko jikin ta kunne ne ta san ba abu ba ne mai yiyuwa ba, kila ma ya riga ya fadawa Ammy fitar ta.....

Tsigar jikin ta ne ya tashi yayinda gaban ta yayi mummunar faduwa, a zahiri kuma fadi ta ke

"Ya Ilahi....."

"Kai Zeeena ashe kin iya ambaton Allah!"
Cewar Bobo cike da zolaye. Harara ta watsa masa, tare da fadin

"Dadi na da kai Bobo rashin sanin ciwon kai! Ba ka ga halin da na ke ciki ba ne wai?"

Dariya ya ke yayin da ya sami waje ya faka, suna hango gidan Malam ya ce

"Come na, stop panicking! Kwantar da hankalin ki babe, calm down, ki fita ki je gate din gidan ku, idan bude ya ke ki shigewar ki kai tsaye, ba kya bin masu gadin ku bashin bayani, idan rufe ya ke ki buga mu su su bude mi ki, gidan uban ki ne, idan Momcy ta gan ki tell her kin fita exercises ne, shikenan!"

"Yen yen yen yen! Ni na rasa yanda aka yi na ke mu'amala da kai Bobo! Duk randa na fita da kai sai ka jawo min matsala!"

Ta na gama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login