Showing 18001 words to 21000 words out of 58720 words

Chapter 7 - Auren Shehu Book 1 Hausa Novel Complete

25 Jan 2025

459

rike gam. A kulli yaumin ta kan tabbatar ta masa alkhari na safe daban na yamma da daban, ta haka ta samo hanyar shawo kan sa. Ta masa karyar cewa akwai kungiyar bitan karatu da su ka hada ne ita da yan makarantar su da ke zaune Kano, kafin su koma makaranta, Amma da daddare ake yi, ta na tsoran kar ta fadawa su Ammy ne su hana ta gabadaya, shi ya sa ta yanke hukuncin ta na bi ta bayan kasa, har su koma makaranta.

Duk da Jauro ya san maganar Zainab yashesshen zance ne, da ke ido a kabo ne da ta bashi sai ya sa hannu ya karfe, idan dare yayi sai ya tabbatar Usman da Isa ba sa kusa sai ya bude mata kofa, haka idan ta dawo shi ne ke bude mata.

Duk wannan hidimar da ya ke yi akan idanun Usman, tun ya na Wauke kai har ya gaji wata ranar Juma'a da yamma, ana saura sati daya Malam ya dawo Usman ya sami Jauro kishingide karkashin bishiya ya na shan rake, dan kuwa tunda Zainab ta fara bashi kudi kullum cikin kudi ya ke.

Sallama ya masa tare da zama kusa da shi. Tayin rake Jauro ya masa bayan ya amsa sallamar. Usman na mai godiya, cikin maganar sa mai cike da nutsuwa, yanayin yanda ya ke fito da kalmomin hausa daga bakin sa ne ki kara jaddada kasancewar sa na kabilar fulani, ya ce

"Alhamdulillah, na gode Jauro ka sha raken ka, dama akwai yar magana da na ke so mu yi da kai"

"Toh Madallah dan cirani, da me ka zo"
Cewar Jauro bai fasa shan raken sa ba. Shiru ne ya biyo baya, kafin daga bisani Usman ya ce

"Ka yi hakuri zan ma ka shisshigi, wala'alla za ka fahimce ni"

Jauro na mai fuzar da totuwar rake daga bakin sa ya ce

"Uhum, ina sauraron ka.

"Zancen fitar dare da Bingel din nan ke yi, diyar wajan Malam"

Cikin halin ko in kula Jauro ya ce

"Uhum? Menene na ka a ciki?"

"Akwai, Malam ya ba mu gadin gidan sa bisa amana, ni da na ke gani ina dauke kai ba tare da fadawa mahaifan ta ba, ina da alhaki, bare kai kuma da ka ke ba da gudunmawa Jauro!"

Jauro na mai tashi zaune ya ce

"oho! Ashe dai ka na gani, kuma ka san ka na da alhaki! Tun da ka ke gani ba ka san ka na da alhaki ba sai yanzu da ka ga ina dan samu ko fillo? Ni za ka yiwa halin na ku na fulanin daji ko? Dan bakin ciki!"

Usman na mai dafe kai ya ce

"Ya ilahi! Ba ka fahimce ni ba Jauro! Ba dan komai ya sa ban iya fuskantar Malam akan wannan batun ba sai dai dan kunya da nauyin sa da na ke ji! Da wani ido ko baki zan iya kallan Malam na ce masa diyar sa na haura katanga? Ko kuma duk dare ana zuwa ana daukar ta? A dawo da ita da safe?"

"Dan sa ido! Da Idon da bakin da ka zo ka tinkare ni yanzu mana! Yarinya na fita bitar digiri(Degree) din da ta ke yi a jami'a, ko da yake kai fa ko zo na kashe ka da turanci ba ka sani ba bare ka san kalmar Degree! Kai Allah dai ya raba mu da jahilci!"

Duk zuciya irin na Usman sai ya tsinci kan sa ya na mai murmusawa, ka na ya ce

"Ban da cin fuska mana Malam Jauro, na zaci za mu iya samin fahimtar juna shi ya sa ma na tunkare ka da maganar, amma tun da abin haka ne, Allah ya ba ka hakuri!"

"Ni kuma na taimaka da Aameen! Eh amen, kuma Allah ya raba mu da munafukai da yan bakin ciki"

Usman na murmushi ya amsa da amen, tashi yayi tare da yiwa Jauro sallama duk da dai be ji dadin yanda Jauro ya kasa fahimtar ta shi, sam be ruke shi a rai ba, shi dai fatan sa Allah ya bashi ikon kawo karshen wannan masifar da ke faruwa gidan Malam, duk da kamar yanda Jauro ya fada be san "digiri" ba, Amma koma menene wannan digirin in dai haka ake yin sa toh lalle ba alkhairi ba ne.

***

In da Usman ke kokarin neman mafita akan iftilakin da ke faruwa gidan Malam, ita kuma Halita soyayyar Usman ce ta sami wajan zama cikin zuciyar ta. Zaune su ke a falo, sun gama cin abinci kenan su ka zauna zaman hira. Falmat sanye da atamfa koriya dinkin doguwar riga, Halita kuwa kananan kaya ne cikin ta, riga da sikit jajaye, kanta daure da jan mayafi.

"Ni kuwa Halitta ina mamakin yanda ki ke kaunar Usman din nan, dan kuwa dai sai dai na kira shi kauna dan ya fi karfin so"

Cewar Falmat yayinda yanayin fuskar ta ke gasgata lafazan ta. Sanyayyar ajiyar zuciya Halitta ta saki kafin ta ce

"Daga Allah ne Falmat, Ni dai kawai ki taya ni addua"

"Toh zan taya ki, Amma duk randa Ammy ta san Usman ki ke so Halitta, I mean not just Usman o, but Maigadin gidan nan wallahi akwai kura...."

"Shhhhh"

Halitta ta katse ta, ta na mai kasa da murya ta ce

"Ke fa matsala ta da ke Falmat handsfree! Ki rufa min asiri kar Yakura ta ji....."

"Ji kuma na nawa?"

Da sauri su ka juya su na kallon ta, ba wanda ya san da shigowar ta bare ya san adadin mintunan da ta yi tsaye ta na sauraran su. Sanye ta ke cikin bakin material, doguwar riga ta yi daurin nan da ake Kira tura ka tsiya. Idanun ta kan Halitta wacce har ga Allah ba ta so maganar ya je kunnan ta ba ta ce

"Yanzu ke Halitta ki rasa wanda za ki so sai wannan Maigadin? Yo to menene abin so a wannan kazamin bafulatanin hammata fal gashi?"

In da Halitta ta fusata, ita kuwa Falmat mamakin yanda aka yi Zainab ta ga hammatar, ba ta san sanda dariya ta kwace mata ba, wanda hakan ba karamin tunzura Halitta yayi ba. Yakura ba ta gushe ba ta kara

"Ke anya kuwa bakin wannan ya san brush? As in kafin na so mutum I first imagine things people do when they're in love, as in can you imagine yourself with him? Like imagine kissing wannan dagageggen bakin na shi?"

"Wayyo Allah Ammy!"

Falmat ce ta saka ihu ta na mai dariyar mugunta, ita kuwa Halitta iya kulewa ta kule. A fusace ta ce

"Malama ina ruwan ki? Kin manta ba kiss ba! Abin da ya fi kiss! Idan ma auren shi na ce zan yi ina ruwan ki!"

Ta na mai daga hannu sama yayinda ta zagaya ta shigo falon sosai, kujerar da ke kusa da Falmat ta zauna, sannan ta ce

"Babu fa, babu ruwa na ko kadan, aw kin san abin da ya fi kiss ashe, yo ai na zaci uztazanci ya hana ki sani, Sha it's your life, Bari na ja baki na!"

"Alhamdulillah tunda kin san haka, da fatan za ki yi aiki da shi...."

"Ke fa ba kunya gare ki ba Halitta!"

Zainab ta katse ta cikin tsawa, ta kara da

"Kar ki ga kin yi tsayin kafa wallahi ina iya doke ki, mara kunya fitsararriya"

"Toh sarkin tsiwa! Tun daga daki na ke jiyo hayanoyar ku! Anya kuwa Yakura??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? Ke da waye kuma?"

Ammy ce wacce ihun Falmat ya sanya ta fito da sauri ta ke tambaya.

"Babu komai Ammy"
Halitta ta fada gudun kar Yakura ta mata tunan asiri, ilekuwa sai cewa ta yi

"Da komai fa Ammy, ai dai gaban ki yarinyar nan ta gama azazzabi da rawan jiki wajan jaddada bayani akan wannan dan bokon haram din, toh dai ruwa ba ya tsami banza, ga shi nan na ji tana managanar son shi ya kamata..."

Ta karasa maganar ta na yar dariya tare da girgiza kai. Daga Falmat har Halitta mutuwar zaune su ka yi, sun san Zainab da barin zance amma ba su taba zatan za ta tonawa Halitta asiri hakan nan kara zube ba.

Ammy na dariyar yake ta ce
"Ke kuwa Yakura ba dai zolaya ba, ina Halitta ina kula wani da namiji? Har kuma ki ce Maigadi? No wonder na jiyo ku tun daga daki, ah ah ni ma ban goyi bayan wannan wasan ba!"

"Atoh Ammy ke dai kya fada"

Cewar Falmat ta na mai fatan rufe asirin Halitta. Zainab kuwa ba ta damu da irin sakon da Halitta ke aika mata ta ido ba, sake cewa ta yi

"Wallahi Ammy ba wasa na ke ba, Halitta soyayya ta ke da Maigadin gidan nan"

"Lailaha ilallahu Muhammad a rasulillahi!"

Cewar Ammy ta na mai tafa hannu cikin tashin hankali ta ke duban Halitta wacce ita ma din kallo daya za ka mata ka tabbatar da damuwan da ta shiga.

"Halitta me na ke ji haka? Wannan wani irin mummunar labari na ke ji Halitta? Duka tarbiya, kulawa da soyayyar da mu ke baki abin da za ki saka mana da shi kenan Halitta?"

Tuni hawaye ya shiga fita daga idanun Halitta, ta na girgiza kai ta ke fadin

"Ah ah Ammy, wallahi ba haka ba ne Ammy...."

Cikin bambami Ammy ta ce

"Ba haka ba ne uban ki ne? Yi min shiru! Wallahi kin ba ni kunya kin yi asara Halitta! Yanzu idan Malam ya ji wannan tozarcin da cin amana ya ki ke tunanin zai ji. Dama aka ce tsintacciyar mage ba ta mage! Hakan nan mutum daga sama ya zo gidan ka ka karbe shi har da bashi wajan kwana, gashi nan zai masa sakayya ta hanyar hure ma diyar sa kunne ai! Toh kuwa zaman shi a gidan nan ya zo karshe"

Jin Ammy na batun zai bar gidan wani dadi ne ya mamaye Zainab, dan kuwa burin ta ke nan.

"Atoh ai tun da na fara ganin sa na san ba za a wanye lafiya ba, na yi magana a ce na fiya kyaman yan kauye, ga dai irin ta nan!"

Cewar Zainab ta na mai daga kafada tare da saukewa. Falmat ce ta saka baki ta ce

"Ammy ba ki fahimta ba, wallahi ba haka ba ne, shi wannan bawan Allah sam be ma san da Halitta ba, bare ma ya hure mata kunne, ba soyayya su ke ba, kawai dai Halitta na yawan maganar sa ne ya sa ke tsokanar ta da shi, Amma babu komai tsakanin su Ammy!"

"Ki ji wani yashesahen zance idan babu rami me ya kawo rami?"

Ammy ta tambaya a fusace, in da Zainab ta taya ta da atoh. Halitta kuwa ta ma kasa magana sai hawayen takaici da ge gangarowa daga idanun ta.

"Allah Ammy gaskiya na ke fada mi ki, in kuma ya kama a kira shi ne ki tambaye shi ki kira shi Ammy"

Shiru ne ya biyo baya na dan sakanni, Zainab sai adduar Allah ya sa kar Ammy ta yarda da zancen Falmat ta ke cikin zuciyar ta. Jin abin da Ammy ke fadi ne ya sanya ran Zainab yin baki. Tana mai ajiyar zuci ta ke fadin

"Toh ni fa in ce, jinina ba za ta taba san Maigadi mara asali ba, haba har na dan ji sanyi cikin rai na, toh wallahi kar na sake jin maganar nan ko da wasa!"

Ta na mai duban Halitta ta kara da

"Ke kuma Halitta na kara jin maganar Maigadin nan bakin ki sai na sabar mi ki"


Kai Halitta ta gyada kafin ta tashi ta fice da ga falon, dan kuwa gani ta ke muddin ta cigaba da zama zafin rai zai sa ta iya tonawa Zainab asiri akan yawan daren da ta ke, ita kuwa ba ta so ta biye mata garin ramuwar gayya su jawa mahaifiyar su matsalar hawan jini.

Ta na jiyo Zainab na cigaba da sukar zaman Usaman a gidan. Ita kuwa Falmat mamakin yanda Zainab ta hakikance ta na bata Usman da karya da gaskiya wajan Ammy, har ta kai ga ta na tunanin shin me ya taba hada su ta ke masa wannan tsana haka?

Duk yanda ta so a kori Usman a gidan, ranar ha?on ta ya kasa cimma ruwa, duk da dai ta ci nasarar tusawa Ammy kiyayyar sa cikin zuciyar ta, ko ba komai yau da gobe in dai Ammy ta tsane shi tabbas sai zaman gidan ya gagare shi. Ta sha alwashin sai ta san yanda za ta yi ta sa Malam ya kori Usman daga gidan.

****

Ana sauran kwana biyu Malam ya dawo Kano, haka kuma wata daya ya rage a fara azumin watan ramadan, bayan sun idar da sallar isha'i gidan Malam da ke Maiduguri, Malam ya karbi bakwancin aminin shi, Shiek Ahmad Suraj.
Kamar yanda Malam ya ke babban Malami haka ma Shiek Ahmad ya ke sananne a cikin garin Maiduguri, ba dan malamtakan sa kadai ba, har dama tarin dukiya da Allah ya ba shi. Duk da dai shi asalin sa dan Chad ne. Ba karamin farin ciki masa tarba na ban girma kamar yanda ya saba masa duk sanda ya zo.

Babban Falon Malam su ke zaune, falo ne ya kayatu kwaran gaske. Bayan sun gaisa tare da hirar bayan saduwa, Shiek Ahmad ya ce

"Ya Shiek dan wajan ka Sudais fa ya hada karatu, mu na sa ran dawowar shi gida Nigeria farkon shauwal da an kammala azumi"

Malam na mai washe baki ya furta

"Toh Alhamdulillah, ka ce Sudais ya zama cikakken likita, kuma mahaddaci wannan labari abin alfahari ne, Allah ya masa albarka, ya albarkaci ilimin da aka samu, ya sa a yi aiki da shi, ya kawo abokiyar rayuwa ta gari"

"Allahumma amen, abokiyar zaman kuwa Ya Shiek gidan ka na ke so a samu, dan kuwa sami 'ya'ya masu tarbiya irin 'ya'yan ka mata sai an duba akaramallah"

Cewar Shiek Ahmad wanda ke maganar har cikin ran sa da zuciya daya. Hakan ya sanya farin ciki bayyana a fuskar Malam, idanun sa har sheki su ke, ya na mai ruko hannun Shiek Ahmad ya ce

"Jazakallahu khair, jazakallahu khair, jazakallahu bi jannah da wannan sheda ta ka Shiek, Ni kuwa na maka alkawarin bawa Sudais diya ta mafi soyuwa a rai na, cikin su tafi kuwa nutsuwa, ga ladabi da biyayya, ga rukon addini, ga kunya, ga...ga...ga....sai Zainab! Ta na aji uku a matakin karatun jami'a, in da take karantar Microbiology anan American university of nigeria da ke Yola"

Cikin gamsuwa da jin dadi Shiek Ahmad ya ce

"Madallah da wannan diya da ta sami shaida mafi daraja daga wajan mahaifin ta, muna so"

Malam na mai murmushi ya ce

"An ba ku"

Hannun Malam Shiek ya rike cikin musabaha ya ce

"Mun karba, mun gode, Allah ya saka da alkhairi, in Sha Allah da yaron nan ya dawo sai a turo a sa ranar daurin auren ko?"

"Su waye za su saka rana da ya wuce mu? Ai kawai tsaya ka gani ya Shiek"

Malam ya dauko calendar ya na dubawa, ranar Juma'a ya zagaye wanda ya kama shabiyu ga watan juli Malam ya ce

"Ga rana nan duba ka ga, idan har ya maka, sai mu yi fatan Allah ya kai mu da rai da lafiya"

Shiek Ahmad na duba calendar da Malam ya nuna masa ya ce

"Hamdan ya yi Ya Shiek, Allah ya nuna mana da rai da lafiya"

Malam ya amsa da Allahumma amen.


*khadija sidi*
AUREN SHEHU

Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun, mu na mika ta'aziyar mu ga Sis Aysha, Allah ya mata rahama, Allah ya gafarta mana, Allah ya sa ta huta, ya albarkaci bayan ta. Allahumma amen

7.


Majalisar tasu wacce ta ke kusa da gidan Malam ya isa, Ya tarar ta cika yanda ya so, Dan haka zuciyar sa wasai ya ce

"Na zo da labari da Wumi Wumi, wannan jaridar sabuwa ce kal!"

Cikin kaguwa su ji labarin daga me cewa

"Siyar mana"

Sai wanda ya ce

"Ba mu mu sha"

Sai da ya sami waje ya zauna, cikin nuna gwaninta ya ce

"Yau da ido na na ga mace ta hauro daga gidan Malam........."

"Ahab! Toh wannan sabon abu ne? Har wani labari da dumi dumi? Toh ai idan wanan ne na sha gani malam!"

Daya daga cikin samarin ya katse shi. Uku da ga cikin su da sam ba su taba ji bare su gani ba kuwa baki su ka ruke, cike da mamaki guda ya ce

"Kai Uzairu ka ji tsoran Allah! Da kai ma Khalifa! Gidan Malam fa ka ce! Wannan ya tashi daga karya sai dai a kira shi kazafi!"

"Mtsw kai ne a gun ka sabo, kai Uzairu fada mana sabon abu ba wannan ba Alhaji"

Cewar daya daga cikin samarin da shi dama ya taba gani shi ma. Shi kuwa Uzairu da ya kawo gulma gwiwar sa ce ta yi sanyi, dan kuwa sun sace masa gwiwa, cikin so ya burge ya ce

"Ba nan kawai abin ya tsaya ba, wani namiji ne ya ruko kugun ta, gaban ido na su ke ta badala, tun suna daga waje har su ka shige mota, Allah ya kadai ya san me su ke aikatawa ciki dan kuwa gilashin baki ne wuluk...."

"Kai auzubillallah ko ma wacece wannan ba ta da ala'aka da Malam! Ba jinin Malam ba ce!"

"Eh toh ko ma wacece dai daga gidan Malam ta ke, dan kuwa a kulli yaumin in za ka gan ta fuskata rufe ta ke da wannan abun da su ke rufe fuska da shi tsabagen munafunci! Kai ni har da asuba na sha gani ana dawowa da ita!"

Cewar Uzairu ba tare da ya kula da tashin hankali da sauran samari da su ke masoya Malam su ka shiga ba. Daya daga cikin su wanda har lokacin ya kasa yarda da abin da ya ke ji ne ya ce

"Kai Uzairu, tsakani da Allah ban ji dadin wannan magana ta ka ba, Bai kamata ba, shin yanzu ina amfanin wannan kazafi haka?"

"Oh toh kazafi ne ma?"

Uzairu ya tambaya cikin nuna bacin rai.
"Eh kazafi mana, yanzu idan mun je za mu ga abin da ka fada zahiri?"

Uzairu na susa kyeya ya ce
"Ai sun bar wajan......"

"Ai dama ba nan za su zauna ba, amma da za ku zauna waccar rumfar ta kusa da gidan Malam har dare ya raba ko ma asubar fari kila ku ga an zo an sauke ta"

Cewar Khalifa wanda ya ke maganar ko shakka babu. Daya daga cikin su wanda dama dan adawar Malam ne sakamakon rashin jituwa da ke tsakanin mahaifin shi da Malam ya ce

"Allah dai ya biya, ka ce yau za mu yi kwanan waje, dan kuwa sai mun ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login