Showing 15001 words to 18000 words out of 58720 words

Chapter 6 - Auren Shehu Book 1 Hausa Novel Complete

25 Jan 2025

462

bacci"
Ta na mai jawo bargo ta dada rufe ta. Sai da ta karanta mata adduar bacci ta shefa jikin ta sannan ta juya ta fita.

Ta na fita Zainab ta yi zumbur ta mike, dan kuwa ta san babu mahalukin da zai sake shigo mata daki tunda har Ammy ta ga ta yi bacci, bari ma kuwa idan akwai wacce za ta iya shigo mata munafunci Halitta ce, ita kuma sun yi fada toh ta tabbatar hakan ta ya cimma ruwa.

Wankan ta tayi ta fito tsaf cikin wondan ta pencil Jean blue tare da yar karamar riga ja, ta faka gashin nan tsakiyar ka kai ka ce ba diyar musulmai ba ce. Ba ta damu da yin make up, dan irin su Zainab ake yiwa kirari da "black beauty better than gold always shining". Tsadaddiyar powder mai sanya fuska sheki ta shafa, turaruka kuwa 212 sexy, escada magnetism, tare da Indian night Jasmine sai da su ka koka.
Gaban madubi ta tsaya ta na mai karkada kugu ta ke yiwa kan ta kirari

"Zeee oh Zeee the slay mama, the club mama, kuma salihar Dadyn ta"

Sai da ta yi mai isar ta, ganin sha biyu ta kusa ta sanya hijabi har kasa, bayan ta gama gyara gado, ta saita fululluka kai kace mutum ne kwance ta sa bargo ta rufa mu su, takalmin ta mai tsinin gaske a hannun ta na mai sanda ta fito. Ganin wutan falon a kashe ta san kowa ya kwanta, sadaf sadaf ta zaga ta baya ta fice.

Isa kuwa da Jauro masu gadin gidan nan gaban gate su ke kwance bacci ya sace su dan yau ko karnukan gidan ba su sake ba. Kallo Waya Zainab ta mu su ta ja tsaki tare da fadin

" Ji be su kwance kamar mushe! Idan ma sace gidan za a yi wato a yi tunda Dady bayanan, Allah ya kai mu gobe za ku yiwa Ammy bayani!"

Ba ta kara tsorata ba sai da ta ga gate din bude, wato ko sakata ma ba su sa ba! Har ta juya a fusace za ta tada su, sai ta tuna tana tayar da su shikenan asirin ta ya tonu, ta na mai adduar Allah ya kare su Ammy ta sa kafa ta fita, hakan yayi daidai da dalle ta da tocilit da aka yi, yanda hasken ya dalle idanun ta ya sanya runtse idanun ta na mai fadin

"Oh my God"

Tsaye ya ke ya na duban ta, suna hira da su Isa bacci ya kwashe su, dan haka ya dan fita waje mike kafa. Kusan mitunan shi ishirin waje gaban gate, dake unguwar ba mai hayaniya bace sosai kafar mutane ya dan dauke, jin wani ni'imataccen kamshi ya sanya shi dan waige waige tare da tunanin ko dai aljana mai turare ce ta bakunce yau, wanda fitowar ta ya gasgata masa da haka, dan kuwa dai da ya haske ta ganin ta ya ke tamkar aljanar ce tsaye gaban shi.

Ganin ba a da niyar daina haska ta ya sanya ta kare fuskar ta da tafin hannun ta, cike da nuna bacin rai ta ce

"Dalla Bobo dena haska ni kafin ka sa a kama mu! Kai fa iskancin ka yawa gare shi!"

Jin haka ya sanya shi kashe tocilan ba tare da ya iya furta komai ba, dan kuwa harshen sa ya sarke kamar wanda aka daure harshen cikin bakin sa. Bude idanun ta tayi tare da fadin

"Bobo....."
Ganin wanda ke tsaye gaban ta sai da ta dan ja da baya, shi din nan dai Usman, sanye da rigar saka da rawani irin na buzaye, hannun sa na dama rike da sandar gora, dayan hannun kuma tocilan ne. Ta na shirin juyawa ta koma sai ga motar Bobo, ai kuwa kafin Usman ya ankare da gudun ta ta nufi motar, ganin haka Bobo ya tsaya ta shige ta na fadin

"Kai let's get the hell out of here, ina tsoran Allah ina tsoran wannan dan boko haram din can!"

*Khadija Sidi*AUREN SHEHU

4.



Jin kalmar "Boko Haram" jiki na rawa Bobo ya figi motar ya na mai tayar da kura, fadi ya ke

"How? Ya aka yi ki ka san dan Boko Haram ne?"

Karar yanda Bobo ya figi motar ne ya sanya su Isa da Jauro fitowa a guje suna fadin

"Su waye nan! A tare! A tare!"
Ina sai sahun tayar motor Bobo su ka gani, idan shi kan shi Usman da ke tsaye kamar mutum mutumi Jauro ya ce

"Yo kai Wan cirani kana nan tsaye ashe, me ke faruwa ne?"

Isa ya kara da
"Wacce mota ce ta tashi a guje yanzu? Su waye?"

Maimakon ya ba su amsa, sai ya juya abin sa yayi ciki, suna tafe bayan sa, su ka koma ciki, daki yayi wucewar sa ba tare da ya tanka mu su ba.

Isa da Jauro su ka tsaya jugum jugum suna duban juna, Jauro ne ya gyara tsayuwa ya ce

"Ina Isa? Ni fa Allah na gani ban yarda da wancan dan ciranin ba! Ga fa karar tashin motar da mu ka ji! Mu ka tashi mu ka ga gidan nan bude, shi kuma mu ka taras waje tsaye kamar gunki, Anya kuwa Isa?"

Isa wanda kamar Jauro ya shiga ransa, ya dan yi ta maza ya dake, ya na mai yamutsa fuska ya ce

"Anya kuwa me?"

"Anya kuwa lafiyayyan mutum ne?"

Jauro ya fada cike da damuwa.

"Ka gan shi da wata rashin lafiya ne?"

Cewar Isa cikin dakiya dan ya san in da Jauro ya dosa. Jauro na mai girgiza kai ya sake cewa

"Ka san abin da na ke nufi Isa, dan kuwa na san kai ma zuciyar ka ta yi rawa akan lamarin Usman....."

"Na raba ka Jauro, na raba ka! Kar ka manta Malam ya karantar da mu akan zato, ya ce zato zunubi ne ko da kowa ya kasance gaskiya, Ni ka ga tafiya ta kunto karnukan nan, da bacci be dauke mu ba ai duk da ba haka ba!"

Isa ya tafi ya na mita, Amma cikin ransa tunanin da Jauro ya ke shi ma din shi ya addabi zuciyar sa.

Usman kuwa can lambu ya shige in da ya saba raba dare, wata yar doguwar kujera ta hutawa ya samu yayi kwance idanun sa na kallan sararin samaniya. Kamanin Zainab ke masa gizo, haka kuma kan sa ya dada kullewa akan lamarin ta,

"Shin ita wannan diyar Malam din ina za ta je da tsohon daren nan? Shin mahaifiyarta ta san da fitar ta? Shi wannan da ya Wauke ta a bakar mota mai bakin gilashi wanene shi?'

Tambayoyin da ya ke yi cikin ran sa ke, wanda ya kagu ya samu amsar su.

Ita kuwa Zainab tun da su ka tafi Bobo ke tambayar ta ya aka yi ta san mutumin nan dan boko haram ne? Wanene shi? Sai da ta nutsu sannan ta iya amsa masa da

"Daya daga cikin daliban Dady ne, kuma ya na mana gadi, haka kawai jinina be hadu da shi ba wallahi, ka ga jiya ma shi ya kama ni, gashi yau ma an kuma! Allah dai ya tushe bakin sa...."

"Wa ya ce mi ki dan boko haram ne?"
Bobo ya sake tambaya cike da damuwa.

"Haaaaa'a! Are you even listening?"

Zainab ta fada cike da tsiwa, ba ta gushe ba ta kara da

"Dallah waye zai yarda dan boko haram ya zauna gidan su? Na ce da kai dalibin Dady ne!"

"Toh Zeeee ke ce na ji kin kira shi da boko haram....."

"Saboda ya na min kama da su ba! Ba wai ina nufin shi din ba ne, ko da ya ke it's possible shi din ne tunda ba wai kwakkwarar bincike aka yi ba...."

Ta fada ta na kallan Bobo wanda ya fara hada zufa. Dariya ne ya kwace mata, ta ce

"Sai shegen tsora, dallah wasa na ke ma"
Bobo na mai goge zufa da hankaci ya ce

"Ai dai mutanan ne abun tsoro, Allah ya mana tsari da su, mugu be da kama Zee"

Cikin faduwar gaba yayin da kamannin Usman su ka bayyana a zuciyar ta, ya fito mata sak a kamannin mugu, ta na mai saurin kawar da tunanin ta ce

"Amen, Allah ya min tsari da shi!"

"Wa fa?"

"Dan Boko haram mana, Maigadin gidan mu!"

Ta fada kai tsaye.
"Ki ka ce ba dan boko haram ba ne?"

Bobo ya sake tambaya cike da damuwa.
"Aaaarrrrghhhh Bobo don't spoil my mood!"

Ta fada cikin tsawa. Hannun ya daka tare da fadin

"Allah ya baki hakuri Zeee Mama!"

"Ba Allah ya ba ni hakuri ba, you better take me to a nice club!"

"I got you, kafin nan bari na baki sauti mai dadi"
Cewar Bobo yayinda kunna waka ya na mai kure karar.

Ranar club yayi ma Zainab dadi, ta hadu da sabon saurayi wanda tare su ka cashe a daren ranar har ta shagala da lokaci, dan kuwa dai ba ita ta ankara ba sai da shida ta wuce. A kidime ta azalzali Bobo wanda ta janyo shi tsakiyar kedaru su na cashewa. Sabon saurayin da ya Kira kan sa Mike ne ya nuna dacewar ya aje ta gida, hakan ba karamin dadi yayiwa Bobo ba, amma Zainab ta hana, ta dai ce ya bari sa yi magana daga baya. Haka su ka yi sallama Bobo na mitar ta katse masa shagali su ka dauki hanyar gida.

Dab da za su shiga unguwar ya kalle ta ya ce

"Babe kin katse min runs wallahi"

"Mtswww"

Ta ja tsaki ba tare da tanka ma sa ba, gaba daya hankalin ta ba ya tare da ita, shikenan yau kam asirinta ya tono, tun da take zuwa club ba ta taba kaiwa haka a waje ba, har a idar da sallar asuba ba ta koma gida ba? shin me za ta ce da Ammy idan har ta shiga dakin ta tashin ta sallar asuba ta ga ba ta dakin? Ya ma za ta yi ta shiga gida gari waye haka babu daman ta haura? Kuma ta san su Isa da Jauro ba lalle sun bude gidan ba in ba dai dan boko haram din nan ya kwana nan in da ta barshi tsaye ba ne, wanda ko jikin ta kunne ne ta san ba abu ba ne mai yiyuwa ba, kila ma ya riga ya fadawa Ammy fitar ta.....

Tsigar jikin ta ne ya tashi yayinda gaban ta yayi mummunar faduwa, a zahiri kuma fadi ta ke

"Ya Ilahi....."

"Kai Zeeena ashe kin iya ambaton Allah!"
Cewar Bobo cike da zolaye. Harara ta watsa masa, tare da fadin

"Dadi na da kai Bobo rashin sanin ciwon kai! Ba ka ga halin da na ke ciki ba ne wai?"

Dariya ya ke yayin da ya sami waje ya faka, suna hango gidan Malam ya ce

"Come na, stop panicking! Kwantar da hankalin ki babe, calm down, ki fita ki je gate din gidan ku, idan bude ya ke ki shigewar ki kai tsaye, ba kya bin masu gadin ku bashin bayani, idan rufe ya ke ki buga mu su su bude mi ki, gidan uban ki ne, idan Momcy ta gan ki tell her kin fita exercises ne, shikenan!"

"Yen yen yen yen! Ni na rasa yanda aka yi na ke mu'amala da kai Bobo! Duk randa na fita da kai sai ka jawo min matsala!"

Ta na gama fadin haka ta fice a fusace tare da buga masa murfin mota. Zuciyar ta na bugu ko wani taku ta yi, wayar Halitta ta shiga kira, ta yi ringing ta gama ba ta daga ba, hannu na rawa ta kira Falmat, ita ma din ba ta daga ba, isar ta gate din ta dan tura ta ji a rufe, sai da ta dan yi jim sannan ta yi karfin halin bugawa. Har ta fitar da rai da bude gate din, ta na shirin juyawa sai ta ga an bude hujun da aka yi jikin gate din domin ganin na waje.

Idanun ta ta tsinta cikin na sa, tuni ta tsinci kanta cikin mummunar faduwar gaba, yayin da bugun zuciyar ta ya karu, sai da yayi sakanni ya na kallan ta, ta na mai cuna kumatu cike da tsiwa ta ke mayar masa da martanin kallan, dan kuwa tsoro baya hana Zainab rashin kunya..

"Malam dalla ka bude min gate! Ka zuba min na mujiya ba ka taba ganina ba ne?"

Ga mamakin ta sai kuwa ya bude, shigar nan dai da ta gan shi da ita jiya da daddare, shi ne jikin sa, Goran nan dai be aje ba, ta na rike hannun sa na hagu, hannun sa na dama kuma ruke da rediyo ya na jin labarai.

Ko kallan sa ba ta kara yarda ta yi ba, bare su hada idanu kai tsaye ta wuce ciki kamar dai yanda Bobo ya ce ta yi, addua ta ke Allah ya rufa mata asiri kar ta hadu da Isa ko Jauro, sa'ar da ta yi da an idar da sallar asubahi su ke komawa su yi baccin su tun zuwa Usman gidan, shi kadai su ke bari da gadin safe, karnuka kuwa ana kiran sallar farko ake daure su, saboda kar su dami masu sallah masallacin gidan da haushi, duk da dai ta waje masallacin ya ke.

Sai da ta kurewa ganin sa, zuciyar sa cike da tunani kalala wanda duk yanda ya so ya cire daga zuciyar sa ya gagara, ya mayar da gate ya rufe.

"Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun! Babu shakka Allah ya jarabci Malam da diya kamar yanda ya ke jarafta salihan bayin sa cikin ikon sa! Ya Allah ka kare Malam daga sharrin wannan Bingel!"

Cewar shi a zahiri, yayinda ya koma mazaunin shi bisa benci, ya kishingida ya na mai cigaba da sauraron labaran shi a tashar BBC hausa.

Cikin sanda takalman ta a hannu ta ke tafiya, ta kitchen ta bi ta shiga falon, dab da zata karasa dakin ta muryar Halitta ya daki kunnan ta

"Yakura daga ina ki ke?"

Jiki na rawa ta saki takalman su ka zubi kasa, Kallan Halitta ta ke ta na mai waige waige ta ga ko ita kaidai ce. Ita kadai din ce sanye cikin hijab har kasa, hannun ta ruke ta carbi dan Halitta ba ta komawa bacci bayan sallar asuba, zama ta ke ta yi zikiri da adduo'i har gari ya waye rana ta fito, sannan ta shiga kitchen ta taya iya abin karin kumallo. Ta fito za ta kitchen din kenan su ka yi kacibus da Zainab ta na sanda za ta shige dakin ta.


*khadija sidi*
AUREN SHEHU

5.



Wani irin sassanyar ajiyar zuciya ta saki, ta na mai duban Halitta murya kasa kasa ta ce

"daga ina na ke kuwa? Dage exercise mana!"

"Exercise din tun karfe 4:45 na dare Yakura? Ki ji tsoran Allah! Ammy ta turo ni tashin ki sallah Yakura, na san ba gidan nan ki ka kwana ba, daga ina ki ke?"

Halitta ta kara tambaya ta na mai tsare ta da idanu.

"Daga yawon ta zubar na ke ko da yanda za ki iya ne? Ki na da abin yi ne? Kuma Allah ya mana katangar karfe da saidawa!"

Kafin Halitta ta bata amsa ta yi saurin kwasar takalman ta, ta yi wuf ta shige dakin ta. Jim ta yi ta na maimaita kalaman Zainab cikin ran ta

"Daga yawon ta zubar na ke......"

Ta kara maimaita.

"Shin anya kuwa shirun nan da na ke akan abin da Yakura ta ke yi Allah ba zai tambaye ni ba? Ko dai Ammy zan fadawa? Ko da ya ke in har na fadawa Ammy kamar na fadawa Dady ne, Allah kadai ya san halin da Dady zai shiga muddin ya sani, Allah ka ga zuciya ta, Allah ka mana magani"

Kitchen ta wuce, ganin Iya har lokacin ba ta fito ba sai ta wuce dakin Iya domin ta ga ko lafiya.

Zainab kuwa ta na shiga bandaki ta shige ta yi wanka, fitowar ta daga wanka ta tarar Ammy tsaye tsakar dakin, abin ku da mara gaskiya sai da zuciyar ta ta dan yi rawa. Ta na kame kame ta ce

"Ammy, aw ashe ke ce"

"Ni ce jiki yayi sauki kenan, ai na turo Halitta ta tashe ki sallah da asuba...."

"Eh mun hadu ai"

Ta yi saurin katse ta. Kallon ta Ammy ta ke kamar mai nazari, kafin daga bisani ta ce

"Me ki ke cewa ne? Kamar yaya kun hadu?"

Zainab na mai sosa kyeya ta ce

"Ah ah ina nufin na gan ta, da ta zo tashi na, eh ta tashe ni din"

"Oh toh, Ni ce min ta yi ba ta gan ki ba, ta na tunanin kin tashi tuni har kin shiga toilet"

"Eh ai ina toilet din na jiyo shigowar ta, haka na ke nufi Ammy"

Kai Ammy ta gyada, sa'annan ta kara da

"Ya ciwon kai?"

"Ciwon kai? Aw Alhamdulillah na sami sauki, Ina kwana Ammy?"

Cewar Zainab yayin da ta zauna bakin gado, Allah Allah ta ke Ammy ta fita ko ta samu gaban ta ya bar faduwa.

"Lafiya lau Alhamdulillah, ashe ba mu gaisa ba, Allah ya kara sauki, sai ki yi maza ki fito mu karya ko?

"Wallahi Ammy ba zan iya cin abinci yanzu ba, wani irin bacci na ke ji, rabona da bacci tun jiya da safe, kin san bacci ba a cin bashin sa "

Ta na mai duban ta cikin nazari ta ce

"Wannan baccin na ki kuwa anya Yakura? Me ya hana ki bacci? Nan fa na shigo na tarar ki na ta bacci?"

"Ah ah, wai ina nufin ban yi ishasshe ba, ina yi ina tashi saboda ciwan kai"

"Toh Allah ya sauke, ki daure dai ki ci wani abu kafin ki kwanta"

Zainab ta amsa mata da toh, dan dai kuwa ba ta da buri da ya wuce Ammy ta fita ta samu ta ji hakarkarin ta bisa katifa. Illai kuwa ta na fita ko mai ba ta iya shafawa, ta dauko wata yar riga iya gwiwa ta sanya, ba batun sallar asubahi ta bi lafiyan gado abin ta. Nan da nan bacci ya dauke ta.

***

Haka rayuwa ta cigaba da gudana. Zainab ta kasa hakura da club ta bari sai ta koma makaranta kamar yanda ta saba, saboda sabon saurayin ta Mike, shi ne ke zuwa daukar ta ya dawo da ita.

Ba komai ne ya bata lasisin wannan shagalin na ta ba face shawarar Mike da ta bi na siye daya daga cikin masu gadin gidan. Cikin masu gadin uku ta san Isa da tsattsauran ra'ayi ko da wasa ba zai amince da ita ba, Usman kuwa shi tsoran sa ma ta ke ji, dan haka sai ta kama Jauro ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login