Showing 39001 words to 42000 words out of 58720 words

Chapter 14 - Auren Shehu Book 1 Hausa Novel Complete

25 Jan 2025

465

wasu dan mintina kafin ya mayar da hankalin sa ga karatun da yake.

Duk kokarin su na dakatar da Ammy a iska ya tashi, karshe ma cewa ta yi duk wanda ya biyo ta wajan gate sai ta tsine masa, su na ji suna gani ta ja akwatin ta ta fice, ko da ta zo giftawa ta bangaran Malam can kasan zuciyar ta ta so Malam ya fito yayi kokarin hana ta tafiya kamar yanda 'ya'yan ta su ka yi. Haka ta na share kwalla ta damkawa Jauro akwatin wanda ganin fitowar ta ya taso da sauri. Shi ya sanya mata cikin mota, ya na mata fatan Allah ya kiyaye hanya.

Ta na mai watsawa Usman harara ta shige mota. Shi kuwa gate ya bude, haka kuma be fasa mata a sauka lafiya ba yayinda mota ta fice daga cikin gidan.

*****

Kamar gidan makoki haka gidan Malam ya kasance. Duk yanda Iya ta yi kokarin sanin halin da ake ciki daga wajan su Falmat abin ya gagara. Sai da ta sami Jauro ya kwashe komai da karya da gaskiya ya fada mata. Ita kan ta sai da ta kullaci Malam da Usman.

Tsoran fushin Malam ya sa Zainab ta hade kayan ta tsaf kamar yanda ya umarce ta. Iya ta sa ta kai mata su BQ ta aje, Amma ta yi kwanciyar ta daki duk da dai ta na jiran tsammanin shigowar Malam matukar ya san ba ta bi umarnin shi na komawa BQ din ba. Malam shiru be shigo ba, haka kuma ba ta ji muryar shi sanda aka yi sallar Magariba da isha'i a masallaci ba kamar yanda su ka saba ji idan ya na jan sallah ba. Fushin da ta ke da shi be sa ta kasa shiga damuwa ba, Amma tashi ta je bangaran sa ta duba ko lafiya ne ba za ta iya ba gudun abin da hakan zai jawo mata.

Da wannan tunanin ta fito falo ta tarar da Halitta sanye da hijabi da alama shirin fita ta ke.

"Ina za ki je?"

Zainab ta tambaya a dake, maganar da ta fara shiga tsakanin ta da Halitta kenan tun faruwar masifar da Zainab ta jawo mu su.

"Daddy zan kai wa abinci"

Ta bata amsa a takaice kafin ta shige kitchen, jin batun abinci ya tunawa Zainab raban ta da abinci tun jiya da rana, dan haka ita ma kitchen din ta nufa.

Iya ta hade abincin Malam bisa wani dan kwando, Halitta ta dauka, ta na jiyo Zainab na tambayar Iya ko da kaza ta na so ta yi mata farfes Halitta ta fice, cikin ran ta tana fadin

'dole ki ci ferfesu hankalin ki kwance ya ke Yakura bayan kin dagula na kowa kin hana mu farin ciki'

A bakin kofar da zai sada ta da bangaran Malam ta hangi Usman tsaye, tuni gaban ta ya shiga faduwa hannun ta na rawa tsabagen yanda zuciyar ta ke harbawa, ta na shirin juyawa ta koma ya gan ta, cikin hanzari ya nufo ta da sauri ya na mai fadin

"Alhamdulillah, kada ki juya ina bukatar taimakon ki"

Yanda zuciyar ta ke bugawa kamar mai shirin fitowa ya sanya ta runtse idanun ta, ta na mai saurin bude idanun ta juyo ta na kallan shi yayinda ya karaso kusa da ita. Tsayin Usman ya sanya sai ta dan daga kai kadan take iya duban fuskarsa, dan kuwa in dai tsayi ne da fadi ka sami Usman an shafa fatiha.

"Yi hakuri na tsayar da ke, Malam be fito sallar Magarib ba haka ma Isha'i, a zato na wani uzuri ne ya hana shi, sai yanzu da lokacin karatu yayi Jauro ke sheda mana duk sanda ya shigo ya karaci sallamar shi Malam be amsa ba, kin ga abun da damuwa, yanzu ma na yi sallama na ji shiru"

Tun da ya fara magana ta saki baki da hanci ta na kallan sa, yanda muryar sa ta ke da girma be hana sa magana mai cike da kwanciyar hankali ba, Iyakar gaskiyar shi ya ke mata bayani duk da dai hausar ta shi ba ta fita sosai.

"Ko yaya ki gani? Ki taimaka ki duba mana domin Allah"

Halitta na mai gyara murya ta ce

"Toh toh, bari na shiga"

Ta yi saurin wuce shi ta na mai tasbihi ga Allah akan wannan masifa da ke dankare cikin zuciyar ta, wato masifar son Usman da ya ke miji ga yar uwar ta. Ba ta sami nutsuwa ba sai da ta shiga falon Malam ta na mai doka sallama, shirun da ta ji ne ya sanya ta karasawa har tsakar falon, ganin Malam ba ya ciki ya sa ta aje kwandon abinci, ta nufi dakin sa ta fara sallama, Nan ma shiru, a tsorace ta fara bugawa da karfi ta na sallama, jin shiru ta bude kofar dakin da sauri ta shiga, nan ma Malam ba ya ciki.

Ta na shirin juyawa ta fita ta jiyo kamar gurnanin numfashi na fita daga bandaki, a guje ta karasa ta bude bandakin, idanun ta yayi tozali da tashin hankali, Malam kwance a kasan bandaki hannun sa bisa kirjin sa, yanda ya ke gurnanin wajan fitar da numfashi ya sanya Halitta fasa ihu ta na fadin

"Daddy! Na shiga uku! Daddy Innalillahi wainnailaihi rajiun!!"

Jan shi ta fara yi tana kokarin tada shi, sai da ta sa iya karfin ta, Amma ta kasa sannan ta tuna da Usman da ke tsaye ya na jiran ta. A guje ta fita ta na fadin

"Usman Daddy na! Usman zo ka taimaki Daddy na!"

Tun kafin ta karaso ya juyo ihun ta, da sauri ya kutsa kai ciki kafin ta kai ga fitowa in da ya ke, tambayar ta ya ke

"Me ya faru? Me ya sami Mallam?"

Nuni ta ke masa da hannu izuwa dakin Malam, ta kasa magana tsabagen kuka da ya ci karfin ta. Cikin zafin nama Usman ya karasa dakin Malam, in da ya tarar da Malam kwance cikin halin da Halitta ta barshi.

"Allahumma ajirni fi masibati haza wakallifna minha! Innalillahi wainnailaihi rajiun"

Cewar Usman yayinda yake duba tufafin jikin Malam domin ya tabbatar da duka tsaraicin sa rufe ya ke. Ganin Malam na sanye da dogon wando kasan farar jallabiyar da ke jikin sa ya sanya Usman daukan Malam cak da ke Usman ba aboci karfi ne, cikin sassarfa ya yi waje da Malam Halitta na biye da shi. Kafin su kai ga farfajiyar gidan in da daliban Malam ke jira Usman ya dakatar da Halitta cikin bada umarni ya ce

"Ka da ki biyo mu, ki koma wajan yan uwan ki ku shedawa duk wanda ya kamata su sani, na mi ki alkawarin kula da shi, za mu tafi asibiti yanzu, wani asibiti ya ke zuwa?."

Halitta na shirin ma sa musu, Amma yanda ya juyo ya kalli idanun ta cike da tabbacin alkawarin da ya dauka mata ya sanya ta gyada kai tare da fadin

"Premier, a court road ya ke, Dan Allah kada ya rasa ran shi...."

"In Sha Allah......"
Cewar Usman yayinda ya juya da sauri, Halitta na kallan sa har ya kure ganin ta. Yanda ya fito dauke da Malam ya sanya hankali kowa tashi. Tuni daliban Malam su ka to kan sa, kowa na tamabayar lafiya, me ya sami Malam, me ya faru.


Auren Shehu

13


Da taimakon direban da ya kai Ammy Wanda dawowar sa kenan aka sa Malam cikin mota.

"Ba mu san me ya same shi ba, mun tarar da shi kwance a bandaki cikin wanan hali da ku ka gan shi yanzu, diyar sa ta fadi sunan asibitin da za a kai shi, wani turanci ne wallahi ya kwanta min"

Cewar Usman wanda shi ke zaune bayan mota, kan Malam kwance bisa kafarsa, ya na maganar ne cikin kokarin tuna asibitin da Halitta ta fada masa.

"Toh ai zaifi wata daga cikin iyalan na shi su fito a tafi asibitin da su, Hajiya ba ta nan ne?"

Daya daga cikin daliban Malam ne ya tambaya cike da damuwa.

"Eh haka zai fi, Hajiya ba ta nan, bari a kira daya daga cikin 'ya'yan na sa"

Usman ya fada ya na mai duban Jauro da Isa da niyar daya daga cikin su ya taimaka ya kira su Halitta. Ganin haka Jaura ya kada baki ya ce

"Dan cirani wannan kuma ai aikin ne kai da ka ke sirikin gidan, mu masu gadi ina mu ina shiga gida haka? Maza shiga ka kirawo matar ka a tafi"

Wani mugun kallo da Usman ya harbi Jauro da shi ya sanya shi saurin wucewa ciki ya na fadin

"Toh ni jan idan ka me zai min, dan ka zama surikin Malam ba zai ba ka lasisin aikan mutane kamar yaran ka ba, ka dai ci darajar masu daraja!"

Maganganun da Jauro ya ke ne ya dan ja hankalin wasu daka cikin daliban Malam har suna musayar kallan juna, dama suna da labarin abin da ya faru daren jiya. Idan Usman ya damu da lafazan jauro sam be nuna ba, kallan Malam ya ke ya na fadin

"Sannu Malam, Allah ya ba ka lafiya, Allah ya ma ka afuwa"

Jim kadan Jauro ya dawo Halitta biye da shi, hijabin da ta saka tare da nikabin da ta saka be boye hawayen da ke zuba daga idanun ta ba dan kuwa har ya dan jika nikabin.

"Matar ta ka ta ki fitowa sai kanwar ka"

Cewar Jauro ya na mai nuna halin ko in kula da kallan da Isa ya bi shi da shi. Cikin azama Halitta ta shiga gaban mota ta na mai rufo kofa, direba wanda dama shi ma tuni ya zauna a nashi guri ya sakawa mota key, Isa da sauran dalibai suna mai yiwa Malam addua aka rufowa Usman kofa. Tuni Jauro ya bude gate, direba na mai tashin mota cikin gaggawa su ka dauki hanyar asibiti.

Tun da su ka dauki hanyar asibiti Halitta ke gwada numbar Ammy duk sanda ta kira amsa daya nakurar ke bata, na
'numbar da ta kira a kashe ta ke, ta sake gwadawa anjima'

Har su ka kusa isa asibiti ba ta sami numbar Ammy ba, sai na kanwar Ammy wacce ita ma din Kano ta ke aure. Bayan Halitta ta sheda mata abin da ke faruwa na game da rashin lafiyar Malam ta tambaya ko Ammy ta je gidan ta? Cike da mamaki da damuwa ta ce ba ta je ba, a tambayi direban da ya tafi ina ya kai ta, sai a sannan wannan azancin ya zo wa Halitta. Bayan ta aje wayar ta ke tambayar direba ina ya aje Ammy? Direba ya ce shi dai tasha ya aje ta.

Isar su asibiti likitan da ke duti ya mu su karbar gaggawa ta hanyar sawa Malam robar shakar numfashi ta hanci da baki, sannan aka kwantar da Malam kan gadon da ke offishin sa. Halitta kadai ya amincewa zaman Office din sa'ilin da ya gama duba Malam ya ke tambayar ta ko ya shiga matsanincin damu ne? Allah ya takaita da ya fadi wani bangare na jikin sa be dena aiki ba, Halitta ta amsa da "uhum" kawai ba tare da ta iya ba shi cikakken amsa ba.

Sai da aka samu jikin Malam ya dan lafa sannan aka mayar da shi dakin kwantar da masu jinya, Amma har lokacin robar bada taimakon numfashi ne a bakin sa. Usman na mai duban Halitta ya furta

"Shin kin sanarwa Hajiya kuwa?"

Kai ta girgiza masa, murya dashe tsabagen kukan da ta sha ta amsa da

"Wayar ta ba ya shiga, kuma ban san in da ta je ba bare na kira su"

Shiru ne ya biyo baya na wani dan lokaci, daga bisani ya nisa tare da fadin

"Dare na yi, ina ga zai fi a mayar da ke gida ko? In ya so kya dawo da safe kila kafin nan an sami Hajiya...."

"Ni ah ah nan zan kwana gun Dady"

Halitta ta katse shi cikin nuna kafiya. Usman na kallan ta cike da tausayi ya sake fadin

"Ki yi hakuri ki tafi, jinyar namiji sai namiji, ba za ki iya....."

"Ba namiji ba ne, Dady na ne fa!"
Ta fada ta na mai fashewa da kuka. Shiru ya mata na wani dan lokaci, har ta yi kukan ta ta gama. Sai ji ta yi ya na kiran direba, cike da umarni ya ce da direba

"Maza ka mayar da ita gida...."

"Ni ba zan je ba ai na fada..."
"Shhhhh za ki je yanzu ma kuwa..."

Yanda yayi maganar ne cikin ba da umarni ya sa da ga Halitta har Direba tsayawa su na duban shi, ganin haka ya dan sassauta murya tare da fadin

"Malam ba zai ji dadi ba idan har ki ka zauna a nan, kuma kin ga ai farin ciki da samun lafiyar shi ki ke fata ko?"

Kai ta gyada masa kamar karamar yarinyar. Cikin rarrashi ya furta

"Yauwa diyar halak, Allah ya mi ki albarka. Yanzu sai ki tashi ku tafi ko?"

Ga mamakin Direba sai ga Halitta ta tashi, bayan ta sake duban Malam, ta kalli Usman ta ce

"Ka kulan min da shi, Zan dawo da safe"

"In Sha Allah"
Ya amsa mata a takaice. Hakan nan ba a san ran ta ba su ka bar asibitin. A hanya ta yanke hukuncin kiran yayar babbar Malam Hajja Dudu wacce dama ta san da auren Zainab da Maigadi da Malam ya daura. Nan ta fada mata halin da ake ciki na rashin lafiyar Malam, tare da tafiyar Ammy. Ta na mai salati da sallalmi ta yiwa Halitta alkawarin baro Maiduguri da asubar fari.

Da misalin karfe goma Halitta ta isa gida, ta tarar da Falmat zaune cikin zulumi, ganin ta taso da sauri ta na tambayar jikin Malam. Halitta ta amsa mata da sauki, ko ta sami Ammy a waya? Falmat ta ce ba ta same ta ba, Amma bari ta sake tambayar Zainab. Ta wuce dakin Zainab ganin ta yi dai dai ta na baccin ta cikin kwanciyar hankali da ke dama akwai bashin bacci kan ta ya sanya Falmat dawowa falo, Amma ta kasa fadawa Halitta Zainab din bacci ta ke, ta yi karya Zainab din ma ta ce ba ta same ta ba.

Iya ce ta shigo jin sun dawo, ita ma tun tafiyar su Halitta asibiti ta ke zaman jiran su. Bayan ta tambayi jikin Malam, tare da ko an sami Ammy ne ta yiwa Halitta tayin abinci, Halitta ta ce mata ta koshi sam bakin ta ba dandano. Da haka ta shige dakin ta, alwala ta yi ta yi sallar ishai tare da yiwa Malam addua, Allah ya kawo sauki cikin lamarin sa.

Washagari da sassafe Halitta da Falmat su ka nufi asibiti, Zainab kyememe ta ki bin su cewar ta ba ta so ta je ta ga wannan dan Boko haram din da Malam ya ce ya daura mata aure da shi. Sai da su ka isa sannan Usman ya tafi ya bar Malam tare da su Halitta da direba. Jikin Malam kam a iya cewa da sauki na bahaushe amma har lokacin ya na jin jiki, haka kuma be fara magana ba bare ma ya ci abincin da Halitta ta girka masa.


Kamar wasa Halitta ta gwada wayar Ammy sai gashi ta shiga, ta na kuka ta ke fadin

"Ammy kin tafi kin bar mu ga Dady nan kwance a asibiti rai a hannun mai duka...."

Salati Ammy ta ke yi daga dayan bangaran, cike da damuwa ta ke tambayar me ya faru? Me ya sami Malam? Nan Halitta ta kwashe komai ta fada mata, ta kare da

"Dan Allah Ammy ki tausaya mana ki dawo.."

Ammy wacce jikin ta ya gama sanyi ta yiwa Halitta alkawarin dawowa da sun isa Yobe, dan kuwa ta na hanyar Maiduguri amma sun kusa isa Yobe. Da wannan su ka yi sallama. Halitta ba ta jima da aje wayar Ammy ba sai ga Hajja Dudu, tare Uwargidan Malam Hajja Kilishi, sai kuma babban dan Malam wanda ake kira Gana. Tun asubar fari su ka dau hanyar Kano.

Ganin halin da Malam ya ke ciki tuni Hajja Kilishi ta fashe da kuka ta na mai tambayar musabbabin halin da Malam ke ciki. Daga Halitta har Falmat ba su so zuwan Hajja Kilishi ba, dan kuwa sun san ran Ammy ba karamin baci zai yi ba muddin ta zo ta tarar da ita.

Haka su ka wuni a asibiti, an samu Malam ya fara magana sama sama haka kuma ya dan ci abinci. Da yamma Usman ya dawo, ganin dakin Malam cike, ciki har da Zainab wacce tun ta hango sa ta ke watsa masa harara ya sa yayi jim kamar zai koma. Halitta ce ta masa iso ta hanyar fadin
"Usman shigo mana, ya za ka koma"

Cike da yar kunya ya shigo, ya tsugunna har kasa ya gaishe da Hajja Kilishi da Hajja Dudu. Su ka amsa ba yabo ba fallasa, Gana ya bashi hannun su ka gaisa. Hajja Dudu ce ta tambayi Halitta ko wanene Usman. Kafin Halitta ta ba da amsa Zainab ta yi carab ta ce

"Maigadin mu ne"

Gudun kar Halitta ta fadi dangantakar auratayya da Malam ya kulla tsakanin su, Nan kuwa ba ta san labari ya riga ya iske mu su. Maganar da Hajja Kilishi ta yi ne ya tabbatar mu su da hakan na cewa

"Ko shi ne sirikin namu mijin Zainab?"

Ras! Gaban Zainab ya fada, ta na mai dauke kai ta hadiyi yawun bakin ciki.

"Eh shi ne"

Cewar Halitta wacce amsar da ta bawa Hajja Kilishi ya mata nauyi matuka a baki, ta na mai danne kishin da ya taso mata ta kara da

"Shi ne ma ya kwana da Dady jiya"

Dukan su kallan Usman su ke, kan sa ke sunkuye. Jin amsar da Halitta ta ba su ya sanya ya dan dago kai ya na mai duban Zainab ta wutsiyar idanu. Ganin haka ya sanya Zainab watsa masa harara cike da tarin tsana.

"Allah sarki, sannu Allah ya ma ka albarka, ba a banza Malam ya ba ka auren diyar sa ba, ka cika dan halas, yanda ka rufa mana asiri Allah ya rufa na ka duniya da lahira"

Cewar Hajja Dudu wacce tun shigowar Usman ta yaba da hankali sa. Zainab kuwa ji ta ke kamar ta tashi ta fita a guje tsabagen tsanar Usman da ta yi. Jin Usman ya mu su sallama ya ce zai koma tunda Gana ya na nan ne ya sa Zainab dan samin sauki cikin ran ta.

Bayan tafiyar shi su ka shiga tattauna auren Zainab, in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login