Showing 12001 words to 15000 words out of 58720 words

Chapter 5 - Auren Shehu Book 1 Hausa Novel Complete

25 Jan 2025

456

nan ko da wasa!"

Ta na mai duban Halitta ta kara da

"Ke kuma Halitta na kara jin maganar Maigadin nan bakin ki sai na sabar mi ki"


Kai Halitta ta gyada kafin ta tashi ta fice da ga falon, dan kuwa gani ta ke muddin ta cigaba da zama zafin rai zai sa ta iya tonawa Zainab asiri akan yawan daren da ta ke, ita kuwa ba ta so ta biye mata garin ramuwar gayya su jawa mahaifiyar su matsalar hawan jini.

Ta na jiyo Zainab na cigaba da sukar zaman Usaman a gidan. Ita kuwa Falmat mamakin yanda Zainab ta hakikance ta na bata Usman da karya da gaskiya wajan Ammy, har ta kai ga ta na tunanin shin me ya taba hada su ta ke masa wannan tsana haka?

Duk yanda ta so a kori Usman a gidan, ranar ha?on ta ya kasa cimma ruwa, duk da dai ta ci nasarar tusawa Ammy kiyayyar sa cikin zuciyar ta, ko ba komai yau da gobe in dai Ammy ta tsane shi tabbas sai zaman gidan ya gagare shi. Ta sha alwashin sai ta san yanda za ta yi ta sa Malam ya kori Usman daga gidan.

****

Ana sauran kwana biyu Malam ya dawo Kano, haka kuma wata daya ya rage a fara azumin watan ramadan, bayan sun idar da sallar isha'i gidan Malam da ke Maiduguri, Malam ya karbi bakwancin aminin shi, Shiek Ahmad Suraj.
Kamar yanda Malam ya ke babban Malami haka ma Shiek Ahmad ya ke sananne a cikin garin Maiduguri, ba dan malamtakan sa kadai ba, har dama tarin dukiya da Allah ya ba shi. Duk da dai shi asalin sa dan Chad ne. Ba karamin farin ciki masa tarba na ban girma kamar yanda ya saba masa duk sanda ya zo.

Babban Falon Malam su ke zaune, falo ne ya kayatu kwaran gaske. Bayan sun gaisa tare da hirar bayan saduwa, Shiek Ahmad ya ce

"Ya Shiek dan wajan ka Sudais fa ya hada karatu, mu na sa ran dawowar shi gida Nigeria farkon shauwal da an kammala azumi"

Malam na mai washe baki ya furta

"Toh Alhamdulillah, ka ce Sudais ya zama cikakken likita, kuma mahaddaci wannan labari abin alfahari ne, Allah ya masa albarka, ya albarkaci ilimin da aka samu, ya sa a yi aiki da shi, ya kawo abokiyar rayuwa ta gari"

"Allahumma amen, abokiyar zaman kuwa Ya Shiek gidan ka na ke so a samu, dan kuwa sami 'ya'ya masu tarbiya irin 'ya'yan ka mata sai an duba akaramallah"

Cewar Shiek Ahmad wanda ke maganar har cikin ran sa da zuciya daya. Hakan ya sanya farin ciki bayyana a fuskar Malam, idanun sa har sheki su ke, ya na mai ruko hannun Shiek Ahmad ya ce

"Jazakallahu khair, jazakallahu khair, jazakallahu bi jannah da wannan sheda ta ka Shiek, Ni kuwa na maka alkawarin bawa Sudais diya ta mafi soyuwa a rai na, cikin su tafi kuwa nutsuwa, ga ladabi da biyayya, ga rukon addini, ga kunya, ga...ga...ga....sai Zainab! Ta na aji uku a matakin karatun jami'a, in da take karantar Microbiology anan American university of nigeria da ke Yola"

Cikin gamsuwa da jin dadi Shiek Ahmad ya ce

"Madallah da wannan diya da ta sami shaida mafi daraja daga wajan mahaifin ta, muna so"

Malam na mai murmushi ya ce

"An ba ku"

Hannun Malam Shiek ya rike cikin musabaha ya ce

"Mun karba, mun gode, Allah ya saka da alkhairi, in Sha Allah da yaron nan ya dawo sai a turo a sa ranar daurin auren ko?"

"Su waye za su saka rana da ya wuce mu? Ai kawai tsaya ka gani ya Shiek"

Malam ya dauko calendar ya na dubawa, ranar Juma'a ya zagaye wanda ya kama shabiyu ga watan juli Malam ya ce

"Ga rana nan duba ka ga, idan har ya maka, sai mu yi fatan Allah ya kai mu da rai da lafiya"

Shiek Ahmad na duba calendar da Malam ya nuna masa ya ce

"Hamdan ya yi Ya Shiek, Allah ya nuna mana da rai da lafiya"

Malam ya amsa da Allahumma amen.
AUREN SHEHU

Biyu

***

Kamar ta san abin da ta ke ayyanawa cikin ran ta, ta na mai duban idanun ta ta ce

"Falmat na yarda ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?da ke, Amma ki sani matukar na ji wannan maganar ta zaga wajan Ammy ke zan tuhama.."

Cike da nuna rashin gaskiya Falmat ta shiga girgiza kai tare da fadin

"Kin san dai ni mai rufa mi ki asiri ce Halitta, amma wannan abun da ki ke shirin yi ba daidai ba ne, ki tuna fa Dady ya ce ko saurayi bai yarda mu kula a waje ba ko mu kawo masa gida ba tare da yana da masaniya akai ba, Amma yanzu kin shirya dan baya nan ki ce mu yi karya ki ga namiji Halitta?"

Hannun Falmat ta saki, ta na mai dafe kai ta furta

"Ya Ilahi! Ya iIlahi! Ya Allah ga Falmat! Dalla wa ya ce ma ki zance zan yi da shi? Kawai fa yi za mu yi kamar za mu fita ne idan Allah ya sa yana waje sai na Wan gan shi..."

Cike da mamaki gami da tausayin halin da yar uwar ta ke ciki Falmat ta zura mata idanu. Ganin haka Halitta ta kara da

"Haba mana yar ?anwa ta, in ba ki taimaka min ba wazai taimake ni? Kin san dai Yakura is a snob, ji da kanta ba zai bari ma ta saurare ni ba balle ma taimaka min sai dai ma ta tona min asiri idan dai wannan ce, please Falmat! Zan baki wannan abayar tawa da ki ke so"

Jin batun abaya sai ga Falmat ta mike tsaye, ta ce

"Da ga yau shikenan gaskiya ba zan kara yin karya dan kawai ki ga Usman Mai gadi ba Halitta..."

"Usman! Sunan shi Usman ba Usman Mai gadi ba"

Halitta ta gyara mata cikin jaddadawa. Fita Falmat ta yi tana mitar kar Halitta ta takura mata wallahi sai ta fasa raka ta. Haka ta lallaba ta, bayan ta Wauko mayafin ta, su ka yiwa Ammy karyar za su je gidan wata kawar Falmat, dan kuwa cikin su Falmat ce kadai mai kawa a cikin unguwar. Sai da Ammy ta yi mitar dama jira su ke Malam ya tafi su sami kafar yawo, tare da kashedin kar su dade sannan su ka kama hanya.

Tun da su ka kama hanyar fita gaban Halitta ke faduwa, fatan ta Allah ya cika mata buri ya sa Usman na nan farfajiyar gidan. Ai kuwa su ka ci sa'a can kusa da gate ta hango shi tare da abokin gadin shi. Zaune su ke bisa teburi ga ledar dafaffiyar gyada gaban su, suna afawa a baki su na hirar duniya.

Tun da ya hangi fitowar su idanun sa ke kan su, kokari ya ke ko zai iya gano wacce ta diro daren jiya cikin su. Sam Halitta ba ta lura da yanda ya saka mu su Ido ba domin kuwa ta yi kasa da na ta idanun tun fitowar su, Falmat ce dai ta ke kokarin kare masa kallo tun daga nesa ta na mai mamakin yanda yayarta ta fada ma san dankauye irin shi. Ganin yanda ya tsura musu ido Falmat ta ja tsaki

"Mtsw ashe ma mayen kallo ne! Ji fa yanda ya tsura ma mutane idanu sai ka ce mujiya! Wallahi ya ci sa'ar ki da sai na tsawatar masa!"

"Kai Falmat ke da wani ido ki ka san ya na kallan ki? Bare kuma ai ban da burin da ya wuce ya lura da ni nima..........."

"Hajiyoyi za a fita ne?"

Cewar abokin gadin Usman yayin da ya tashi ya nufi gate din gidan domin bude musu kofa.

"Eh sannun ku da aiki"

Falmat ta furta ta na mai kai kallon ta ga Usman wanda fuskar sa ke Wauke da fara'a, haka ma Halitta wacce tunda ta sauke idanun ta bisa fuskarsa mai kwarjini da dumbun annuri gaban ta ya shiga faduwa.

"Toh Allah ya dawo da ku lafiya"

Ya fada sa'ad da ya bude kofar ya na jira su fita ya kulle. Ganin yanda Halitta ta yi kasake ta na duban shi ya sanya shi fadada fara'ar shi, cike da girmamawa ya sunkuyar da kai alamar gaisuwa, ba Halitta ba hatta Falmat sai da hakan ya burge ta, ganin Halitta na shirin ba da su ya sanya ta jan hannun ta su ka yi waje ta na fadin

"Amen Isa, godiya mu ke"

Isa na mayar da kofar gate ya koma wajan zaman shi ya zauna, tare da fadin

"Ina ruwan Falmat, 'ya'yan Malam ne ai, kila ba za ka san su sosai ba saboda ba sa fita, in za su fita kuma fuskarsu kullum a rufe, na yi mamaki ma yau ka ga ba su rufe ba"

Kai Usman ya gyada masa da ke mutum ne da be fiya magana ba, tunanin Falmat ya ke dan ko shakka babu ita ma ta yi kama da wacce ta diro daren jiya, sai dai kuma yanayin kibar Falmat ce ke karyata ita ce din. Duk da waccar hijabi ne jikin ta har kasa, Amma ba ya Jin ta kai Falmat kiba. Nisawa yayi kafin ya furta

"Isa ina da wata tambaya domin Allah"

"Ina jin ka"

Cewar Isa ya yayinda ya bare gyada ya afa a baki.

"Shin Malam ya na da 'ya'ya mata da yawa ne,?"

"'ya'yan sa uku ne, wannan biyun da ka gani, sai guda, ita ba ta fiye zama a gida ba, jami'ar kwana ta ke ai"

Isa ya amsa masa zuciya daya ba tare da ya kawo wani abu cikin ran sa ba. Shiru ne ya biyo baya, Isa bai fasa cin gyadar sa ba, shi kuwa Usman zaton shi ne ya tabbata, Zainab ita ce diyar Malam da ya gani jiya ta hauro kan katanga.

'ita ko wannan Bingel me zai sa ta haura katangar gidan su tsakar dare haka?'

Tambayar da yayiwa kan sa kenan, ji yayi duk duniya be da muradin da ya wuce ya san musabbabin wannan lamari na diyar Malam.

Halitta kuwa tun bayan fitar su take washe baki kamar wacce aka ma bushara da gidan aljanna. Ba ta bari sun dade gidan da su ka je ba ta ringa azalzalal Falmat su tafi gida, dan kawai su dawo ta kara ganin shi. Su ka yi rashin sa'a kafin su dawo Usman ya tashi sai Isa kawai su ka tadda. Haka ba yanda ta so ba su ka wuce ciki.

Dakin ta tayi kwance, bayan ta sallami Falmat da abayar da ta yi mata alkawari. Da kwanciyar ta ishe ta ne ta leka account din ta na Instagram, nan ta ci karo da hotunan Zainab na club, tun tana dauke kai har ta kai hotan da tayi tsakiyar maza ta na busa hayakin shisha, ka na gani ka san sababbiya ce a harkar. kasa zama ta yi, zuciya na zafi ta tashi ta nufi dakin ta.

Kai tsaye ta bude kofar dakin ta shiga batare da ta buga mata ba. Bisa gadon ta tarar da ita ta yi kwanciyar rub da ciki, sanye cikin wando "bump short", da yar riga wacce ko cibiya bai rufe mata ba. Ba komai ya dauki hankalin Halitta ba face wata yar zanen fulawa da ta gani kugun Zainab, dab da mazaunan ta, ta na mai tafa hannu ta furta

"Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun Mai Zan gani jikin ki Yakura kamar Tattoo?"

Jin maganar kamar daga sama ya sanya ta sakin wayar hannun ta ta tashi zaune da sauri ta na duban Halitta.

"Haba Halitta! Ya za ki shigo min daki haka ba sallama! In aka yi magana you claimed Ustaziya ke diyar Dady! Yes Tattoo ne jiki na so what?"

"Tattoo fa Yakura? Ki na diyar musulmai ki yi tattoo? Ba ki ji tsoran tsinuwar Allah? Yanzu dan Allah idan Dady ya gani ya ki ke tunani zai ji....?"

"It's not meant for Daddy's view shi ya sa na yi shi kusa da ass dina ok?"

Cewar Zainab ta na mai sake nunawa Halitta inda zanen tattoo din ya ke. Halitta kamar za ta yi kuka dan takaici. Zainab kuwa ko a jikin ta, sai ma ta kara mata da yi da

"Toh dan ma na yi tattoo na kafirta ne? Tsinuwar Allah kuma ai tsakani na da Allah na ne, bare ke da ki ke claiming ki na tsoran tsinuwar Allah na ga ai kina make up once in a while, kuma in za a zana mi ki gira sai an aske...."

"Auzubillallah! Allah ya tsare ni da aske gira, ban taba ba, kuma ba zan taba ba in Sha Allah"

Halitta ta katse ta. Komawa ta yi, ta yi irin wannan kwanciyar ta rigingine, ta na duban Halitta ta ce

"An yi rashin sa'a ban sami wanda su ka iya permanent one ba ne, wannan iyakan sa shekara daya, Amma ya na gogewa zan fita US a yi min permanent, after all jiki na ne ba naki ba, oya me ma ya kawo ki daki na?"

Shanye bakin cikin da ya taso mata cikin ranta ta yi, wayyar ta ta daga mata, nan hotan nan ya bayyana a idanun Zainab, Halitta ta ce

"Wannan wani irin shiga ne Yakura? Yanzu har kya iya zama cikin maza da wannan shigar ta ki? Har ki dauka ki sa a social media? Kuma ki na busa hayaki Yakura! You smoke? You are smoking in the picture! Me mutane za su yi tunani akan Dady muddun su ka san ke diyar shi ce?"

Zainab na kallan ta irin kallan nan na hadarin kaji ta ce

"Wai ke Haliita ba za ki fita harka ta ba? It's my life, my personal life! Ko kin ga na sa sunan Dady jikin sunana? Ina ruwan Dady da rayuwa ta a waje? Cikin gida na ke diyar sa, ina shiga irin wanda ya ke so a cikin gida in da ya ke gani na, ina masa ladabi da biyayya and he is satisfied! a school da social media I'm the person I chose to be, I don't use his name! mahaifina kenan bare ke da kike kanwa ta! Dan Allah ki fita harka ta Halitta!!"

Ta dan tsagaita ta na mai jan wayar ta, Instagram ta shiga ta dubo sunan Halitta, ta ce

"Alright ga shi nan na yi unfollowing din ki, I expect you to do the same in dai ke ba mayya ba ce! Wannan masifar har ina!"

Ran Halitta idan yayi dubu ya baci, cikin zafin rai take kallan Zainab, ta ce

"Ki tuba Yakura! Ko dan darajar mahaifin mu ki tuba, kuma ki sani idan babu mutuwa akwai tsufa, ke mace ce, Rayuwar diya mace kalilan ce, Me za ki ce da 'ya'ya duk randa su ka wayi gari aka yi musu nuni da wannan hoto aka ce ke mahaifiyar su ce? Da wani ido za ki kalle su?......"

"Get out of my room! Ba na bukatar wa'azin ki, ki bari sai Dady ya hau mambari ki ja masa baki! Nonsense!"

Ta katse ta cike da masifa. Jiki sanyaye Halitta ta juya, ko da ta kai kofa sai ta sake juyowa ta da dubi Zainab da ke kallan ta kamar zakanya, ta ce

"Ba zan fasa mi ki wa'azi ba Yakura, ba zan fasa mi ki addua ba, Allah ya shirye ki"

"Mtswww"

Amsar Zainab kenan, yayin da ta tashi ta rufe kofarta da key bayan fitar Halitta. Idan ran ta yayi dubu ya baci dan kuwa a rayuwar ta ta tsani sa ido, gani ta ke duk duniya babu wanda ya sa mata ido kamar Halitta, shi ya sa ma sam ba sa shiri.


*Khadija Sidi*
AUREN SHEHU

3

Ta na zama bisa gado ta Wau wayarta ta kira abokin zuwa club din ta da ta ke kira Bobo, bugu daya ya daga tare da faWin

"Zeee oh Zeee the slay mama the club mama, diyar Malam ta ki halin Malam! Ai ni na san baki fushi Zeeena....."

"Eh en fa Bobo!"
Ta katse shi, ba ta gushe ba ta kara da

" Kar ka wani dame ni da dadin baki! Da ka san masifar da ka kusa jawo min jiya da ka ji tsoran Waga waya ta!"

"Toh yanzu dai Allah ya baki hakuri, ko da ya ke tun da ki ka kira ni ma na san kin huce, wetin dey sup? Malam don commot?"

Cewar Bobo cikin muryar zolaya.
"Ehen na, him don go Maid, toh ya za a yi? Any happening tonight? Amma dan Allah kar ka kai ni club din talakawa, ka san I can't stand them!"

Ta fada ta na mai yamutsa fuska. Dariyar kyeta ya saki, fadi ya ke

"Heheheheh Zeeena na daWe ban ga wanda ya ke kyamkyamin talauci kamar ki ba, babe don't worry I got you, ki shirya 12 daidai ta yi mi ki gaban gate din ku, na san dai yau ba batun haurawa tunda Malam baya nan"

"Ba ka da matsala, su Isa ne ai wa'inan, in su ka sa shayi gaba har na wuce ma ba lalle su sani ba, sai ka zo"

Ta na maganar ne yayinda Usman ya fado mata rai, ta na mai adduar Allah ya mata katangar karfe da shi, su ka yi sallama da Bobo ta aje wayar.

***

Kamar yanda ta saba duk sanda ta san ta kulla harkallar ta, ana isha'i ta fara kukan ciwon kai, daga Ammy har Falmat babu wanda ya kawo wani abu cikin ran su, sai ma tararraya ta da su ka din ga yi, musammam ma Ammy. Halitta kuwa ko kallan in da take ba ta yi, dan cike fal ta ke da Zainab. Ammy ce ta bata magani ta sha, ta ce lalle ta je ta kwanta, amma Zainab ta ce ah ah, gwara ta zauna jikin su za ta fi jin dadi.

Sai da ta bari goma da rabi yayi sannan ta ce ciwan ya ci karfin ta, bari ta kwanta dan Allah kada wanda ya shigo ya tada ita, dan idan aka tada ita ba lallai ta iya komawa bacci ba, gashi kuma dama ciwon kai ta ke. Ana bin ta da sannu haka ta mu su sallama, ta koma daki ta yi kwanciyar ta har da kashe wuta.

Da ya ke uwa uwa ce wajen sha daya Ammy ta kasa hakuri, sai ga ta a dakin, ganin wutan a kashe ya sanya ta yin sanda zuwa ga gadon Zainab, wacce jin shigowar uwar ta saki jiki ta yi lum kamar mai bacci. Hannun ta dora bisa goshin Zainab ta na mai hamadala, fadi ta ke

"Alhamdulillah ta sami

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login