Showing 30001 words to 33000 words out of 58720 words

Chapter 11 - Auren Shehu Book 1 Hausa Novel Complete

25 Jan 2025

610

baya, kafin daga bisani Malam ya nisa tare da fadin


"Menene dalilin ka na rufa min asiri bayan ka bari ana barna a bayan ido na?"

Shiru Usman ya kasa amsawa, Malam be gushe ba, ya kara fadin

"Shin wani abu na ma ka da na cancanci wannan abu biyu daga gare ka? Cin amana da kuma rufin asiri? Ka ci amana ta, daga baya ka zo da rufin asiri? Ka na da wata manufa ne na yin haka?"

Usman na mai girgiza kai ya ce

"Ina neman yafiyar ka Malam, dan Allah ka min yafe min, ban da wata manufa da ya wuce kare mutuncin ka da gujewar tashin hankalin ka, na yi kuskure, ka yafe min"

"Kai wanene?"

Malam ya kara masa tambaya mai rikitarwa. Cikin nuna rashin fahimta ya ce

"Ni Usman ne, ban taba tunanin cin amanar ka, ko kuwa zaluntar wani daga cikin iyalin ka ba"

Malam na mai duban shi cikin nazari ya ce

"Iya binciken da na yi akan ka kai bafulatani ne dan cirani, ka fito daga wata ruga da ake kira Rugar Shehu, bayan abin da ka min a yau ya sanya ina tsoran zamantakewa ta da kai, dan kuwa idan har za ka iya ganin diya ta cikin halaka haka ka kawar da kai, to ko shakka babu za ka iya halaka ni kai na! Wannan ya sa na ke son jin cikakken tarihin rayuwar ka, wanene kai, da wata manufa ka zo gida na?"

Maganar Malam ta sanya zuciyar Usman rauni, cikin kokarin kare kan sa ya furta

"Allah ya sani ban zo da cuta ba tun ranar da na sa kafa ta gidan nan, haka ma yanzu da na ke zaune gaban ka. Kamar yanda ka sani tun a baya, Sunana Usman, Usman Tanko, na zo ne daga rugar Shehu, in da maihaifina shi ke da sauratar Shehuntakar rugur, Ya gada ne tun kaka da kakan ni. Ba mu da takamamman wajan zama, dan haka yawo mu ke daji daji, mukan yada zango a duk dajin da Allah ya nufa, muddin akwai ruwan da shanun mu za su sha, haka ciyawa da da harawar da za su ci. Babban abin da Rugar Shehu ta yi suna akai kuwa shine surkulle dan haka ba ma zama a daji sai an yi surkulle an kafe dukkannin dajin kaf ciki da waje ya zama mallakin mu.............."





*Khadija Sidi*AUREN SHEHU

10.

Khadija Sidi



Cikin daji mai suna santali wanda ya ke arewa moso gabashin mararrabar Nigeria da Nijar ne Rugar Shehu su ka yada zango. Babu laifi akwai ruwa da 'yayan itatuwa wadatacce hakan ya sanya su jimawa a dajin. Rugar Shehu ba su da wani yare face fulatanci, kaWan daga cikin jama'ar rugar wanda su ke fita suna cudanya da hausawa ne ke jin hausa.

Babu laifi mahaifina ya yi aure aure da yawa, duk a dalilin neman magaji kasancewar duka matan sa 'ya'ya mata su ke haifa masa wanda da sun kai shekara goma sha uku zuwa sha biyar ake mu su aure. Sai da ya haifi 'ya'ya Ashirin duka mata, har ya fitar da rai dan kuwa shekaru sun ja ya bawa arbain baya, sannan Allah ya amsa masa ya azurta matar sa ta hudu wacce dama ita ta fi kuwa karancin shekaru da haihuwar da namiji.

Murna gun mahaifina ba a magana dan har kyautar shanu biyu mace da namiji yayiwa unguwar zoma da ta karbi haihuwar. In da mahaifina ke murna samun magaji, Dan uwan shi wanda ya ke cikin ummansa, shi maihaifina ya sha nono ya bar ma, babban abin bakin ciki ya zame masa dan kuwa ya ci burin kujerar da mahaifina ke kai, rashin magajin mahaifina shi ne babban takobin da ya rike.

Kamar yanda Baffa Mudi ke bakin cikin jaririn da aka haifa, haka ma sauran matan gidan su ka nuna bakin ciki karara, dan sam babu wacce ke hubbasa wajan taimakawa mai jego, haka ta yi jegon ta sai dai 'ya'yan ta mata ko kuwa dai mokota su agaza mata, idan kuwa an ga sauran matan kusa to lalle mahaifina ke kusa, ana yi ne dan ganin idanun sa. Haka a daddafe sati ya zagayo, ranar suna aka sanya min suna Usman, mahaifina ke kira na "Magaji" wannan kalma ta zamo tamkar wuka a kirjin Kawu Mudi.

Baffa Mudi ne dan uwa daya tilo da su ke ciki daya da Mahaifina, su biyu kacal Mahaifin su ya haifa a duniya. Matar Baffa Mudi daya, haihuwar matar shi goma sai dai biyar daga ciki sun rasu, biyar kadai ke a raya, duka mata ne. Bayan an haife ni da sati biyu matar Baffa Mudi ma ta haifi dan ta namiji, yaro ya ci sunan Mahaifina amma ana kiransa da Tanko.

Gata da soyayya karara da mahaifina ke nuna min ba karamin bakin jini ya jawowa Iya ta da ni kai na ba. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, ana jifa da surkulle domin halaka mu, Allah kuma na kare mu.

Tun kafin na cika shekara biyu a duniya na yaye kai na na ki nono, Wanda hakan ya nunawa Iya ta alamun cikin da ta ke dauke da shi. Murna gun mahaifina ba a cewa komai, shi dai fatan sa Allah ya maimaita a haifa ma sa da namiji. Cikin da Iya ta ke dauke da shi ya sanya Mahaifina dakatar da canza shekar da ake da niyar yi duk da kuwa ruwa da kayan itatuwa sun ja baya. Wannan ya bawa Baffa Mudi damar yiwa mahaifina zagwan kasa ta hanyar hore mu su kunne akan wannan hukuncin da mahaifina ya dauka saboda a cewar shi hakan na nuna rashin adalcin Shehun rugar. Da ya ke jama'ar rugar Shehu amintattu ne, kalilan ne su ka dauki zugan Baffa Mudi dan haka hakan sa bai cimma ruwa ba, Nan dajin Santali Iya ta ta sake haifo dan ta namiji, da mako ya zagayo aka sanya masa Muhammadu Bello.

Sai da Bello ya dan yi kwari sannan aka tasanma barin dajin Santali, nan mu ka niki gari, mu ka hada kwan mu da kwarkwatar mu, mu ka shigo Nigeria, mu na tafe muna tare da shanun mu su na kiwo, duk in da dare ya mana mu yada zango. Duk yanda mu ka so kiyaye shanun mu kar su shiga gona, yau da gobe sai sun shiga, dan haka ko da yaushe cikin fada mu ke da manoma, wani sa'in har a kai da bata kashi. A haka Allah ya isar da mu wani yanki da ke cikin kungurmin dajin falgore. Bayan dube dube da Maihaifina yayi na surkulle ya ce a kafa bukkar rugar Shehu a nan dajin. Cikin sati daya aka kafe dajin nan kaf ya zama babu mahalukin da ya isa ya dumfari rugar Shehu da kowani barna ko mugun nufi.

Toh rayuwar ruga dai haka mu ke yin ta, babu wutan lantarki, babu asibiti, babu makaranta babu ko wani irin taimako daga gwamnati dan kuwa idan ba dai wani tarzoma ta hado mu da manoma ba gwamnati ba ta waiwayan mu bare ta ba mu agaji, dan haka ban san wani abu wai shi boko ba. Ina da shekara hudu a duniya matar Baffa Mudi ta kara haihuwa, ta haifi diya mace wacce aka sa mata suna Ummakaltime, ana kiran ta Cangwai.

Kasancewar mahaifina shi ne Shehun rugar dama shi ke koyar da yara da samarin ruga karatu wanda ya hada da kur'ani, littafan addini, sai kuma rubutu da karatun ajami. Soyayyar da ke tsakanin mu, da Kuma ganin ni ne magajin shi wanda ya ke sa ran zan zama shehu ya sanya shi ya fara ba ni ilimin surkulle tun ina dan shekara takwas a duniya, duk yanda ya so ya jawo Bello jiki a koyar da mu tare hakan ya gagara saboda lalurar bebantaka da ta sami Bello sanda ya na da shekaru biyar a duniya.

Ba na manta ranar ta kasance wata juma'a ne aka tashi da rashin ladanin Rugar Shehu, bayan an masa sutura, aka kai shi kushewa aka rufe mu ka dawo gida mu tadda Bello na ta kurari da kuka, juyin duniyar nan an yi ya fadi abin da ke damun shi, amma ya gagara sai dai gwalangwalanto, wanda hakan shi ne karshen maganar sa kenan duniya.

Sanda na cika shekara goma na fara kora shanu nawa na kai na, Mahaifina ya ba ni mace da namiji wanda su ke aure, cikin shekaru kalilan su ka hayayyafa sosai Allah ya albarkaci kiwo na sai gani da shanu har guda koma, sanda na cika shekara shabiyar a duniya shanu na tuni sun kai ishirin.

Ba yaban kai ba, tarbiya da kuma yanayin karatu da na ke samu daga wajan Mahaifina ya sa na fita daban daga sauran matasan rugar mu, idan ka dauke Baffa Mudi da iyalan sa babu wanda ba ya girmama ni a rugar Shehu. Sam ba ma ga miciji da Tanko dan Baffa Mudi, dan kuwa yayi kauran suna wajan fiti na da neman fadan manoma, hakan nan babu gyara babu dalili ya ke kora shanu cikin gona su yi barna su bata amfanin gona ba dan komai ba sai dan neman fitina. Da ta fara fitinar mutane ne Mahaifina ya Umarci Baffa Mudi da yayi wa Tanko magana, ko dai ya canza hali, ko kuwa ya bar masa rugar baki daya. Maganar da ta kara kawo rashin jituwa tsakani na da Tanko kenan, har ta kai ba ya amsa sallama idan na masa.


Idan kuwa batun amana ne sau dayawa jama'ar rugar Shehu na bani amanar Shanun su duk sanda su ke da uzuri, cewar su duk rugar Shehu ni kadai zan kora shanun jama'a na kiyaye mu su kamar yanda zan kora nawa, kafin ka ce menene tuni na kasance kamar mataimaki gurin Mahaifina wanda shekaru sun ja sosai, hidimomi da dama ba ya iya yi, duk yanda Baffa ya so ya ja ragamar shehuntakar kuma Mahaifina ya ki sakar masa, sai dai ya sanya na wakilce shi, cewar sa tunda ina da nutsuwa zaifi na fara gwada mulki tun ya na raye.


Ba zan manta da wata ranar labara ba, lokacin ina da shekara goma sha bakwai, na dawo daga kiwo Mahaifina ke fada min shawarar da su ka yanke na daura min taubashiyata, daya daga cikin 'ya'yan Baffa Mudi, wato Cangwai. Cangwai dai yarinya ce mai hankali da nutsuwa, wajan kyawu ma babu laifi, idan aka dauke kiyayyar da mahaifin ta ya ke min sam bata da laifi, dan haka na yi na'am tare da godiya da wannan hadin.

Iya ta kuwa nunawa ta yi sam ba ta yarda da wannan hadin ba, a cewar ta ba hadin alkhairi ba ne, yanda Baffa Mudi ba ya kaunar mu me zai sa ya so ya kulla wannan kulli haka? Sai da rai ya baci sosai tsakanin ta da Mahaifina, ni na zaunar da ita, na nusar da ita ce komai nufi ne na Allah, muddin ba ma nufin kowa da sharri to kuwa Allah ba zai bari a jefo mu da sharri ba, ta kwantar da hankalin ta, khairan in Sha Allah.

Da haka da haka aka daura min Cangwai. Daya daga cikin bukkokin da ke wajen gidan Shehu mu ka tare cikin yarda Allah. Bayan sati daya da auren mu Cangwai ta fara laulayi, Iya ta ce ta fara lura da cikin da ta ke dauke da shi, za ta yi surutun yayi wuri na ce da ita babu komai ni da iyali na mun yi tarayya tun a daran fari, dan haka ba wani abu ba ne dan ta na dauke da juna biyu.

Abu dai kamar wasa cikin kankanin lokaci cikin Cangwai ya bayyana sosai, Ni kai na na kanyi mamakin shin watanni nawa da auren mu da har abu zai fito sarari haka kamar kwarya? Gashi mu ba asibiti ba bare bokan ture ya duba ya fada min adadin watannin cikin.

Dangantakar mu ya sanya ban yi kokarin neman warware wannan sarkakkiyar ba, na rufa asiri mu ka zauna haka, ko da wasa ban taba nuna mata wani damuwa ko bambamci ba, ina kula da ita kwatankwacin yanda na ke ganin Mahaifina ke kula da Iya ta, sai ita ce ma da na ga kamar ta na cikin damuwa, duk sanda na so na ji dalilin ta kan ce min babu komai.

Iyar ta kullum ta na hanyar gidan mu, haka ma Baffa Mudi, ni kuwa sam ban taba kawo wani abu cikin rai na ba. Cikin wannan halin mu ka kai wata shida tare da Cangwai. Wata ranar lahadi da daddare na dawo daga hirar dare na tarar Cangwai ba ta bukkar mu, na yi tsammanin ta zagaya bayan gida, ni kuwa dama na debo gajiya sai na yi kwance bisa gadon karar mu bacci na diba na sama sama


Ban yi cikakken minti goma da kwanciyar ba kamar daga sama na ke jiyo muryar su, a bakin kofar bukkar na ji mahaifiyar Cangwai na tambayar yaushe zan dawo. Cangwai ta ba ta amsa??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????r da sai can cikin dare ai wajan hira na je, Bukkar su ka shigo, Cangwai na niyar kunna futular acibalbal Iyatar ta ce ta bari saboda ba ta san jama'ar gidan su san da zuwan ta.

Ina shirin mu su gyaran murya dan su san da ni kenan na ji Iyar Cangwai ta ce

"Ba dai ki tona mana asiri ba ko?"

Mutuwar zaune na yi jin amsa Cangwai na cewa

"Ah ah Iya, Amma wallahi a tsorace na ke, gani na ke kamar fa ya san ba cikin shi ba ne, dama Baba ya sani ya bari sai da na zo gidan na sami cikin halak, ai ya fi......"

Wani irin zufa na ji ya na keto min, Ashe dai duk yanda na so kar na zargi baiwar Allah nan ashe hainta ta su ka yi. Babban abin taikaici shi ne amsar da iyar ta ta bata, cewar ta

"Ke yiwa mutane shiru! Wa ya ce mi ki Baban na ki ya na so ki haifa masa jika da wannan la'anan nan yaron? Ko kin manta dalilin da ya sa ki ka tare da sangami har ya mi ki ciki?"

"Sangami"

na maimaita cikin rai na, Sangami na daya daga cikin fitattun matasan da ke wata ruga kusa da rugar Shehu, mahaifin sa yayi suna kwarai wajan tarin shanu, haka kuma abokin fitinar Tanko ne. Iyar Cangwai ba ta gushe ba ta kara da

"Kar ki manta yarjejeniyar da aka yi tsakanin Mahaifin Sangami da na ki, na farko dai ki samu ki haife dan nan, wannan wawan mijin na ki da Shehu su gama azazzabin samin magaji, sai a sheka su barzau, kin ga kenan burin Mahaifinki na zama Shehu ya tabbata, ke kuwa mu aurar da ke ga Sangami, tare da bawa baban shi rabin shanun rugar Shehu kamar yanda aka yi alkawarin matukar ya taimaka aka dauke Shehu da magajin su daga doran kasa, shi wancan beben dan na sa da mu ka lakasa tun shekarun baya be Isa ya aiwatar da komai ba, ina Bebe zai iya shehuntakar ruga? Ina ya ga bakin magana?....."


"Usman mutumin kirki ne Iya, ba ki ga yanda ke mutunta ni ba, ya na kula da ni....."

Cewar Cangwai cikin nuna damuwa, cikin hantara Iyar ta ta ce

"Ke rufawa mutane baki! Ko dai kin fara son shi ne?"

"Ah ah"

"Toh idan kin fara sai ki zaba ko shi ko uban ki! Dama abin da ya kawo ni kenan! Na ja kunnan ki! Sakarya kawai na ji kin tona mana asiri uban ki ne a rana ai"

"Zan kiyaye!"

Da wannan Iyar Cangwai ta tafi, Cangwai ta fita ta dan taka mata. Jiki sanyaye na tashi zaune, dan tashin hankali na ma rasa abin yi bare na motsa. Zuciyar ta daya ta dawo, ashanar da na mata tsaraba da shi sanda na fita kiwo ta kesta haske ya gwauraya daki hakan ya bata damar ganina zaune na doka tagumi fuska fal zufa kamar wanda ke zaune gaban wuta.

A razane ta ke dubana yayinda jikin ta ya dau kyarma, saura kirin ta wulgar da acibalbal din da ke rike a hannun ta Allah ya sa na tashi da sauri na riko shi. Gefe in da mu ka saba ajiyar shi na aje. Ina mai bata baya dan sam ba na kaunar ganin ta, na ce

"Me ku ka yi ku ka nakasa kanina Bello?"

Murya na rawa da alama ta fara kuka ta amsa min da cewa

"Dan Allah kar ka tona min asiri, ka rufawa Mahaifina asiri na maka alkawarin kare lafiyar ka da mahifin ka...."

"Ba wannan na tambaye ki ba!"

Na katse ta cikin tsawa, juyowa na yi na karasa gaban ta, hannaye na biyu bisa kafadar ta ina mai jijjiga ta ba tare da na yi la'akari da tsohon cikin da ta ke dauke da shi ba na ce

"Me ku ka yiwa kanina ya dena magana?
Ko ki fada min ko na halaka ki da cikin shegen da ki ke dauke da shi nan take kafin na je na riske azzalumin uban na ki"

Yanda ta ga na rikide cikin kankanin lokaci ya sanya ta kara tsorata da lafazan da ke futowa daga baki na, tana kuka ta ke fadin

"Lokacin da abin ya faru ina da karancin shekaru, Amma dai na san surkullen da aka yi masa da tare da gawa aka hada aka birne, yanda gawar ba za ta kara magana a duniya ba, haka shi ma Bello ba zai sake magana a duniya......."


Tas na dauke ta da mari kafin ta kai da karasa maganar ta, ta yi baya sauran kiris ta fada na riko ta da sauri cikin danasanin marin ta da na yi, dan kuwa tun da na zo duniya ban taba dukan wata diya mace ba, face Cangwai.

"Dan Allah ka yafe min, kada ka halaka ni, zan hade kaya na, na bar rugar Shehu ba zan sake dawowa ba har abada"

Takaici ya sa na kasa magana, kallan ta na ke cike da tsana karara cikin idona. Mun kai kusan minti biyar cikin wannan halin kafin na sake ta, rai na na kuna fice da bar mata Bukkar gaba daya gudun halin zuciya.


Bukkar Mahaifina na nufa, ganin babu alamar haske ya sanya na sake shawara, na juya na fice ba tare da na dubi bukkar Iya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login