Showing 45001 words to 48000 words out of 58720 words

Chapter 16 - Auren Shehu Book 1 Hausa Novel Complete

25 Jan 2025

464

kashe ya ba ka, dan kuwa ga amaryar ka can a tafe zuwa dakin ka, ka ga da ni ne sai na ga abin da ya turewa buzu nadi, cargwadi! Sunan wani abinci wai rahadada! Za ka huta fa dancirani! Mats??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????alar dai kila ba kai za ka fara....."

Ji ka ke "Tas" Usman ya sauke yatsun sa biyar bisa kuncin Jauro har sai da ya ji ya dena ji na wasu dan sakanni baya ga jinin da ya shiga gangarowa daga hancin sa tsabagen karfi da zafin hannu na Usman, ya na mai nuna Jauro da yatsa ya ce

"Idan ka na cin kasa, ka kiyayi na shuri! Sakarai mara daraja!"
Ya juya a fusace ya nufi ciki ya bar Jauro hannu bisa kunci in da ya ke fadin

"Ya kurmartar da ni, Isa ka na kallo ya raftama min gatari a fuska! Aradu ya mayar da ni kurma Isa"

Fuskar Isa cike da jin dadin marin da Jauro ya fusha, ya na darawa ya ce

"Ba gatari ba ne, wallahi hannun sa ya sa ya kwashe ka da uwar mari"

Jauro na susa kunci ya ce

"Kai dan manzo wai hannun mutum ne haka? Kai wannan ba dai basamude ba!"

"Ka ma godewa Allah ba sandar nan ta shi ya rafta ma ka ba, ina fada ma ka ba ka ji Jauro! Ka dena rai na mutumin nan ga shi ka fari gani"

Zafin marin da ya sha, da kuma maganganun Isa ne ya tunzuro Jauro, nan ya fara kurari ya na masifa, fadi ya ke

"An rai na shi din, shi dan uban wane! Da ya isa da ya tsaya mana sanda ya mare ni! Tsoro ya sa shi shigewa ciki da sauri! Da mana ya tsaya!"
Isa na mai taba kafadar Jauro ya furta

"Idan ka gama ihun da ka ke bayan hari don Allah ka sheda min, bari na tai ta kunto karnukan nan da munafunci ya hana ka yin aikin ka"

Jauro ya rikice nan ya fara ruwan ashar, In da Isa ya maishe shi mahaukaci, Nan ya bar shi ya na hayaniyar shi shi kadai.

Ko motsin Usman ba ta ji ba, bare ma ta ga giftawar shi, garden ya je yayi zaman sa bisa kujera ya na mai neman tsari daga tafasar da zuciyar sa ta ke yi, Dan kuwa be taba jin zafin magana kamar wanda Jauro ya fada masa a yau ba. Yanda ba ta sami cikakken bacci ba a daren ranar gudun kar Usman ya zo ya fada mata duk da dai ta san ta rufe kofar. Gashi taurin kai irin na Zainab ya hana ta sake komawa ta lallabi Ammy ko ta hakura ta barta cikin gida. Haka ita Ammy, wacce tashin hankalin ko a wani hali Zainab ke ciki ya hana ta bacci.

Sai da aka kira sallar asuba sannan bacci mai nauyi ya sace Zainab, ba ita ta tashi ba sai wajan karfe goma sha biyu na rana. Bandakin cikin dakin ta shiga, duk da bandakin fes ya ke sai da hankalin Zainab ya tashi matuka, dan ko fitsari ma ta kasa tsugunnawa ta yi, dan haka ta lallaba ta koma dakin ta cikin sanda, nan kuwa ba ta san Ammy ta gan ta ba.

Wankan ta fara sannan ta hada asuba da azahar ta yi, ta na shirin haye gadon ta ta mike sai ga Ammy ta shigo, ta na mai salati ta ce

"Lahaila me zan gani Yakura? Me ki ke min a cikin gida?"

Cikin marairaicewa Zainab ta tashi zaune. Idanu na kawo kwalla ta ke fadin

"Ammy ki rufa min asiri wallahi kyamkyamin BQ din na ke, wallahi Ammy...."

Cike da takaici Ammy ta ke duban ta, ka na ta ce

"Ba ki ji kyamkyamin rayuwar ki ba sai na BQ? BQ yanzu yanzu za ki iya gyara shi? Karkari ya sha shara da guga? Ki tashi ki fitar min daga gida, bana san ganin ki Yakura! Idan har abin ya mi ki ciwo toh ki zage ki gyara BQ din, Amma kar na sake ganin ki kwance cikin dakin nan, wallahi sai na sabar mi ki!"

Cikin fushi Zainab ta tashi ta fice fuuuu ta na mai doka kofa. Sai da Ammy ta kai zuciyar ta nesa dan ji ta yi kamar ta bi ta ta kara nakada mata na jaki ko ta huce.

Tsakanin 'ya da mahaifa aka ce sai Allah. Ammy ce da kanta ta hade abincin na cin mutum biyu, cikin dan kwando ta jera kulolun ta ce da Iya ta kaiwa Zainab, Amma kada ta ce ita ta saka ta.

Halin da Iya ta ga Zainab ya sa ta tausaya mata matuka, ta yi ta yi Zainab ta ce abinci ta ce ba ta ci, ta koshi. Iya ce ta sa hannu ta wanke mata bandaki har ma da shara da gugan daki, ta tsaftace mata ko ina tsaf sannan ta kyale ta. Bayan tafiyar Iya Zainab ta farma abincin, ta ci ta koshi sosai dan kuwa daurewa ta yi ta ki cin abicin gaban Iya dan ta fadawa Ammy ko ta tausaya mata.

*****

Da nadamar yanda ta bijerewa Malam Ammy ta kwana ta tashi, tunanin ta be wuce na yanda za ta yi ta nemi afuwan Malam, daga baya ta yanke hukuncin kiran sa. Sai da ta shiga dakin ta, cikin faduwar gaban yanda zai amsa mata, da kuma abin da za ta ce masa, ta kira har sau uku ba ya shiga, sai ta yi tunanin ko in da ya ke ne ba network mai kyau. Ba ta dade da aje wayar ba sai ga kiran Hajja Dudu. Da kamar ba za ta daga ba dan kuwa ta kullaci Hajja Dudu, gani ta ke ita ta dauko Hajja Kilishi ta kawo ta Kano har ta tafi da Malam. Ta na kallo har wayar ta tsinke. Ganin ta sake kiran ta bayan tsinkewar wayar Ammy ta dauka, muryar Hajja Dudu taji cikin kuka ta ke fadin

"Aleesha ki hado yara maza ku taho Maiduguri komin dare! Malam sun yi hatsari hanyar tahowar su Kano!"

Cikin ihu Ammy ke fadin

"Innalillahi wainnailaihi rajiun! Innalillahi wainnailaihi rajiun! Ya jikin na sa? Me ya same shi? Lafiya ya ke?"

"Ku dai taho Aleesha, abin dai sai kun gani!"

Ta na gama fadin haka Hajja Dudu ta kashe wayar ta, Ammy ta saka kuka mai tsuma zuciya, hijabi ta saka gaba a baya, ta na surutai kamar zaucacciya fadi ta ke

"Ya Allah kar ka raba ni da miji na ba tare da na nemi gafarar shi ba, ya Allah kar ka dau ran miji na ba tare da na nemi tafiyar shi ba! Innalillahi wainnailaihi rajiun!"





*Khadija Sidi*
Auren Shehu

15



Yanda Ammy ta fito afujajan da kuma sumbatun da ta ke ne ya sanya su Halitta rudewa, kamar yanda ta ke kuka, haka su ma din kukan su ke. Cikin kankanin lokaci su ka shirya, gaba daya sun manta da Zainab da ke can BQ, sai da su ka shiga mota, dukan su uku gidan baya su ka zauna, direba na shirin tayarwa sannan Halitta ta furta

"Yakura, Ammy ba a fadawa Yakura ba"

Ammy na share hawaye ta furta

"Ai kuwa dai, kai na yayi zafi wallahi! Halitta je ki sanar mata"

Halitta ba ta so Ammy ta aike ta wajan Zainab ba, haka babu yanda ta so ba ta fita ta same ta ta yi dai dai ta na bacci hankali kwance. Yanda Halitta ta tashe ta cikin gaggawa fada fada, da kuma sakon da ta fada mata na hatsarin Malam ya sanya ta tashi a gigice har ta na neman fadowa daga kan godo. Fadi ta ke

"Innalillahi na shiga uku! Ina Dadyn ya ke? Yaushe za mu tafi Maidugurin?"

"Idan har kin iya shiryawa da wuri za ki iya tafiya da mu, dan kuwa har mun shiga mota Allah ya sa aka tuna da ke..."

Halitta ta bata amsa tare da juyawa ta fice, ta na jiyo kukan Zainab wacce ke fadin

"Tsabagen wulakanci ni din ce za a mance fisabilillahi! Dady be da lafiya har ku shiga mota sannan za a tuna da ni? Wallahi kin yi da yar halak Halitta! Duk wannan munafuncin da ki ke kulla min za ki gani a kwaryar cin tuwan ki....."

Sai da kusan minti goma sha biyar ya shude suna jiran Zainab, Ammy ta kule har ta ce da direba ya ja mota su tafi, sai ga ta nan har da yar jakar ta da ta tsaya shiryawa, idan aka dauke Zainab wacce ta shirya tsaf cikin bakar rigar abaya, daga Ammy har su Halitta hijabi ne jikin su. Kafar nan ya sha takalmi mai tsini kamar mai zuwa club. Taikaici ne ya sa Ammy kau da kai gefe yayinda ta karaso, boot ta bude ta aje jakar kayan ta, sannan ta dawo jikin mota daidai saitin Falmat, ta na mai nuna ta da dan yatsa ta ce

"Malama kin san dai ba za ki sani zama tare da Direba ba ko? Gwara ma ki fito ki bani waje!"

"Kun ji irin halin sakarcin na ta ko? Sai da na ce mu tafi mu barta ku ka ce ah ah! Dan uban ki idan ba za ki shiga mu tafi ba ki sha zaman ki! Kai Malam Habibu ja mota mu tafi!"

Cewar Ammy a fusace ta na mai watsa ma Zainab harara. Ganin direba ya tada mota ya sa ta bude gidan gaba ta zauna ta na zumbure zumburen baki da guna guni babu wanda ya tanka mata. Su Jauro na mu su Allah ya tsare hanya, tare da fatan Allah sa Malam be ji rauni sosai ba su ka dauki hanyar Maiduguri.

Gudu direba yayi sosai dan kuwa Ammy ji take kamar ta rufe idanun ta ta bude ta ganta a Maiduguri. Tafiyar awa biyar sai gashi sun yi ta a awa hudu, dan kuwa baikwai daidai a Maiduguri ta mu su. Sun tarar gidan Malam da ke New GRA babu kowa sai mai gadi, gun shi su ka sami labarin mutuwar Direban da ke jan motar Malam, cewar Maigadin take Direban ya rasu be ko shura ba, haka kuma ya sheda mu su cewa Malam ma ya na can kwance rai a hannun Allah a nan UMTH (University of Maiduguri Teaching Hospital).
Asibitin Ammy ta ce a kai su ba tare da ta tsaya jin sauran bayanan tashin hankali da Maigadi ke fada mu su ba. Tun kafin su isa asibitin ta ke kiran number din Hajja Dudu amma ya ki shiga, da kyar bayan isar su asibitin sannan ta sami numbar Gana, shi ya sheda mu su suna Emergency and accident.
Tun daga nesa su ka hangi Hajja Dudu, Hajja Kilishi, Madu dan Malam na biyu sai kuma 'yayan Hajja Kilishi mata guda biyu, Zinaru wacce ita ke bin Madu, sai kuma Kori wacce ita ce sa'ar Zainab. Kukan da su ka tarar Hajja Kilishi da sauran yaran na yi ba karamin daga mu su hankali ya yi ba, Gana da Madu ne kawai su ka iya daurewa duk da dai su ma din idanun su cike ya ke fal da kwalla, musammam Gana wanda gaba daya jinin Malam ya bata gaban farar rigar sa sanadiyar rungumosa da yayi sa'ad da aka dauko su daga wani dan karamin asibiti kusa da kauyen da su ka yi hatsarin.

"Menene wannan jikin ka Gana? Ina Malam? Kar ka ce min jinin Malam ne haka jikin ka!"

Cewar Ammy ta na mai ruko hannun Gana. Kai kawai ya girgiza mata dan kuwa tsoro da tashin hankali ya sa ya kasa magana, a kan idanun sa Direban Malam ya cika, haka kuma har lokacin salatin Malam ne ke masa yawo cikin kunne. Salati ya ke yi da karfi wanda duk wanda ya ji ya san Malam na cikin tsananin ciwo, Malam be dena salatin nan ba har sai da su ka iso Maiduguri, sai kuma tsit. Har Gana ya fasa kuka a tonanin shi Malam ma ya cika, shigar su asibitin aka sheda ma sa Malam na raye, sai dai yayi doguwar suma ne mai kama da mutuwa, wato ya shiga "Coma"

"Gana ku fada min mana, ku amsa min dan Allah wani hali Malam ke ciki!"

Ammy ta sake tambaya ta na mai fashewa da kukan da take ta kokarin dannewa.

"Malam ya na ciki, kusan awa hudu kenan da aka shige da shi, Amma har yanzu dai shiru, hana rantsuwa dazu wani likita ya ce da mu suna iyakan kokarin su, Bayan wannan ba mu kara ji daga gare su ba Hajiya"

Madu ne ya amsa mata ganin Gana be da niyar magana. Jin haka su Halitta su ma su ka kara saka na su kukan, waje ya kaure da koken iyalan Malam kai ka ce Malam ya cika, tun Madu na kokarin tsawatar mu su, har ya gaji ya sa mu su Ido, sai jama'ar wajan ne ke ba su baki.

Su Ammy ba su jima sosai da zuwa ba Likita ya fito, ganin sa gaba daya su ka yo kan sa kowa da tambayar da ya ke masa, hakan ya sa ya nemi ganin Hajja Kilishi da Gana a Office, Ammy ta ce ba ta san zance ba kafar ta kafar Likita, ita ma din matar Malam ce. Su uku su ka dunguna zuwa Office din Likita.

Bayan Likita ya yi kokarin kwantar mu su da hankali ne ya sheda mu su cewar sun yi iyakar kokarin su domin ganin Malam ya farfado daga doguwar suman da yayi Amma abin ya ci tira, dadin dadawa kuma ya sami "Spinal cord" injury, ya ji ciwo kashin bayan sa

"Innalillahi wainnailaihi rajiun!"
Cewar matan Malam suna mai fashewa da kuka. Cikin dakiya Gana ya furta

"Haba mana dan Allah! Ku shiru ko ma ji bayani daga bakin sa, yau ko mutuwa Malam yayi kukan nan na ku ba zai amfana masa sa komai ba sai ma azabtar da shi da zai yi!"

Jin haka duka su ka yi kokarin yin shiru, Gana na mai kallan Likita ya ce

"Yaya kenan? Menene shawara ko fitar da shi za mu yi zuwa karsar waje?"

Likita na duban Gana ya ce

"Zan ba ka shawara tsakani da Allah, kada ku wahalar da Malam, ku bar shi nan gida Nigeria, a kuma masa addua, sauki na Allah ne, Allah ya yassare masa"

Jin haka gwiwowin Gana sun yi sanyi kwarai, dan kuwa jiyayi tamkar likita na fadin Malam ba zai tashi ba. Da sanyin gwiwa su ka yi sallama da likita, in da ya ce a bar Malam ya kwana emergency ward suna monitoring din shi ko Allah ya sa a dace.

Madu da Gana aka bari za su kwana wajan Malam. Duk yanda Ammy ta so ganin Malam ba a bari ta gan shi ba saboda gudun abin da ganin na shi zai haifar mata ta, haka duka su ka koma gidan Malam. Kamar yanda aka saba duk sanda su ka zo hutu Maiduguri, bangaran da aka ware na musammam domin saukar baki su Ammy su ka sauka. Manyan dakuna uku ne kowannan su da bandaki ciki, sai kuma madaidaicin Parlour mai dauke da kanan kujeru ruwan kasa. Halitta da Falmat dama tare su ke zama duk sanda su ka zo, Ammy da na ta dakin da ta saba sauka, sai kuma karamin ciki Zainab ke kwana ita kadai.

Idan aka dauke Zainab babu wanda ya iya runtsawa daren ranar, Musammam su Hajja Kilish da su Zinaru, mutuwar Direban nan ya tsaya mu su rai dan sun saba sosai. Mutum ne mai kirki da haba haba da mutane. Daren ranar sarkin Musulmai ya sanar da ganin watan Ramadan, aka kwanta da niyar tashi sahur domin daukar azumi.

Washagari da sassafe su ka koma asibiti, ba a mayar da Malam patient ward ba, Amma an bar su sun ga Malam. Ganin yanda aka daure kirjin Malam, ga robar samar da numfashi baki, hannun sa makale da robar ruwa, ga kuma na fitsari nan wanda yar robar ta fito ta cikin jallabiyar da su Gana su ka sanya masa daren jiya. Gashi fuskar Malam kumbure sosai goshin sa an daure da bandaje saboda tsayar da jinin da ke zuba da gan kan shi da ya fashe, babu wanda be zubda hawaye ba, lalle mutum ba a bakin komai ya ke ba.

Matan sa duka biyun hannun shi su ka ruke, Ammy ke furta

"Malam dan Allah ka warke ko na nemi yafiyar ka, na yi nadama, dan Allah ka yafe min"

Zainab kuwa kallo daya ta yi masa ta fashe da kuka mai tsuma zuciya, Wai Dadyn ta ne kwance haka kamar mutum mutumi! Yanda su ka mayar da dakin tamakar gidan makoki, ya sanya Gana tsawatar mu su, tare da fadin

"Duk wanda ya san zai zo mana asibiti ya mana kuka dan Allah yayi zaman sa gida, ba ma bukatan zuwan sa!"

Hakan ya sa duk wanda kuka ya zowa sai ya fita yayi kayan sa waje gudun fadan Gana. Yan uwa da abokan arziki, ciki har da daliban Malam, Wanda ke sauraran tafsirin sa duk sanda aka fara azumin Ramadan, sun yi cincirindon zuwa duba Malam, Amma babu damar ganin shi likitoci sun hana. Asibitin nan babu wanda be san da kwanciyar Malam Birma ba, haka lungu da sakon Maiduguri haka labari ya zaga ko ina.

Sai da Malam ya kwana uku Emergency Ward aka mayar da shi Aminity 4. Jikin sa dai ba canji, ya na kwance sai an tayar sai an kwantar, su Gana kullum suna cikin wanke kayan jinyar sa, da yi masa wanka idan ya kama. Satin Malam uku a asibiti aka fara shirye shiryen fita da shi India. Ammy da 'ya'yan kuwa hado nasu ya na su su ka yi su ka tare a Maiduguri karo na farko da kan iyalan Malam ya hadu sosai, kowa ya dukufa wajan ibada da rokawa Malam sauki alfarmar wata Mai girma.

Ranar da aka akai azumi ishirin da biyar, Ammy ce a wajan Malam, ita ta karbi Gana da Madu ta ce su dan je gida su huta.

Zaune ta ke kan kujera, ta kurawa fuskar Malam Ido ta na mai kukan zuci. Sam ba ta lura da motsin da hannun Malam ke yi ba tsabagen nisan da zuciyar ta ta yi na tunani da begen Malam. Ganin murfin idon Malam ya motsa ya sanya ta kara matsawa kusa da shi da sauri yayinda bugun zuciyar ta ya karu. Kamar gizo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login