Showing 42001 words to 45000 words out of 58720 words

Chapter 15 - Auren Shehu Book 1 Hausa Novel Complete

25 Jan 2025

468

da Gana ke nuna rashin dacewar auren a nashi ganin auren zai iya zama wani barna maimakon gyara a rayuwar Zainab, in aka yi la'akari da yanayin wayewar Zainab da kuma ilimin ta. Ya ce zai yiwa Malam magana a san yanda za a yi a warware wannan aure tun kafin ya haddasa wata matsalar gaba. Maganar ba karamin dadi ta yiwa Zainab ba, duk da dai Hajja Dudu da Hajja Kilishi sun nuna rashin goyan baya akan hakan.

Sai dab da magrib Ammy ta iso dauke da akwatin ta, dan ko gida ba ta je ba bare ta ji labarin zuwan su Hajja Kilishi wanda ganin ta ba karamin bakan ta mata rai yayi ba. Ta tarar Malam ya na bacci amma ganin Hajja Kilishi tuni ta fara kalallame shi, daga ya dan motsa sai ta zabura ta matsa kusa da shi cikin nuna kulawa. Ita kuwa Hajja Kilishi ta na daga gefe ta zuba mata Ido kawai. Cikin ran ta mamakin yajin da Ammy ta yi ta ke ji.

Ko da Malam ya bude ido ya ga Ammy sam be nuna wani farin cikin ganin ta ba, sai ma idan ya na da bukatar wani abu ya ce da Hajja Dudu ko Hajja Kilishi ta masa. Hakan ba karamin musgunawa Ammy yayi ba. Haka kuma duk yanda Ammy ta so kwanan asibitin Hajja Dudu ta yi kyememe ta hana, cewar ta gwara Gana ya zauna da Malam ai jinyar namiji sai namiji.

Bayan kwana uku Hajja Dudu ta koma Maiduguri, Ammy na ji ta na gani Hajja Kilishi ta tare mata a gida, cewar ta babu in da za ta je sai Malam ya sami sauki sosai. Duk yanda ta so ta tunzura ta ta koma ta ki, haka ta hakura. Wasa wasa sai da Malam yayi sati biyu a asibiti, kafin a sallame shi sai da likita ya jaddada hutu da kwanciyar hankalin da Malam ya ke bukata wanda hakan ne ya sanya Gana yanke hukuncin wucewa da Malam Maiduguri bayan ya ji cikakken bayanin abun da ya faru daga bakin Jauro, wanda be boye masa komai ba. Sai ga Gana mai kudirin samar ma Zainab yanci na mai gargadin ta matukar ta kashe mu su uba ita da uwar ta wallahi ba su yafe mata ba.

Sai da su ka dawo gida Gana ya hade kayan Malam kaf, ga mamakin Ammy Malam be yi musu ba, shi ne ma ya ke fadawa Gana kalar kayan da zai zaba masa, in da ya ke cewa ya fi san farare saboda tafsirin azumi ya gabato, sati biyu ya rage a fara.

Bayan Malam ya sallami su Halitta, tare da mu su alkawarin zai dawo bayan sati biyu kafin azumi ya kamkama, ya na mai duban Zainab ya furta

"Yakura kin dai san ke matar aure ce, cikin sati biyun nan da na ke kwance asibiti ban sani ba ko kin cigaba da halin ki na haura katanga ki fita yawan lalace, toh ki budi kunnuwan ki ji ni da kyau, wallahilazim matukar ki ka kara aikata haka ba za ki gama da duniya lafiya ba, Allah ya isa ban yafe mi ki ba...."


Dagowa ta yi a gigice ta na duban Malam, hakan ya sa Malam jinjina kai, ya kara da

"Ware ido ki kalle ni da kyau, ba dan da karar kwana ba da tuni bakin cikin ki ya kashe ni Yakura, toh amma Alhamdulillah Allah shi ne zai jibanci lamura na, ba za ki tuzarta ni ba! Ba ki isa ba!"

Jiki sanyaye Zainab ta furta

"Ba zan kara ba Dady"

"Idan ma kin kara kan ki za ki yiwa, kin dai san ke matar aure ce. Bayan haka daga yau idan ki ka sake kwana a dakin da ba namijin ki ba ba tare da kwakkwarar hujja ko dalili ba Yakura shi ma ban yafe mi ki ba"

Jin haka ta saki kukan da ta ruke shi can kasan magoro, fadi ta ke

"Dan Allah Dady ka kawo min dauki ka sauwake min wannan nauyi da ka daura min, wallahi ba zan iya kwana daki daya da shi ba Dady, dan Allah Dady"

Cikin halin ko in kula Malam ya furta

"Ki ka iya kwana gidan rawa bare dakin auren ki? Kai Gana kana ina? Maza zo mu tafi ko Allah zai sa na dena ganin wannan yarinyar!"
Zainab na gani Malam ya shige mota ya barta da nauyi mafi tsanani a rayuwar ta. Haka kuma Ammy wacce duk yanda ta so ta sauke girman kai ta bawa Malam hakuri ta kasa tsabagen kishin zaman Hajja Kilishi, gashi ta na ji ta na gan ta ci nasararr tafiya da shi.
_



*A gafarce ni, in Sha Allah zan sake posting kafin Sunday.*
_


*Khadija Sidi*
Auren Shehu

14



Tun da Malam ya sa kafa ya tafi gaba daya ya dauki hidimar Ammy da 'yayan ta ya watsar. Washagarin ranar da ya isa Maiduguri ya kira Shiek, in da ya sheda masa sauyin da yayi na auren Halitta da Sudais a maimakon Zainab da su ka yi alkawari akai. Kamar yanda yayi na'am a wancan karan, haka wannan karan ma ya amsa cikin godiya ba tare da neman ba'asi ba, haka kuma ba a sauya watan auren da su ka sa ba.

Kamar yanda Malam yayi burus da su, haka ita ma Ammy ta yi da shi. Kwanci tashi asarar mai rai, haka Malam yayi sati biyu a Maiduguri, idan aka ga kiran sa to ya kira ne ya duba lafiyar su, haka kuma ya fadawa Ammy ya tura mata kudi, da kuma kudin na menene. Ammy na gani Zainab ta ki bin maganar sa na ta koma BQ amma sam ba ta damu da hakan ba bare ta tsawatar mata, sai ma tambayar ta lokacin komawar ta makaranta da ta yi, jin be fi wata daya ya rage ba Ammy ta yi hamadala, ita a na ta ganin komawar Zainab makaranta shi ne mafi a'ala a rayuwar ta, kila kafin ta dawo Malam ya sauka ya raba auren Zainab da Usman.

Ana sauran kwana biyu a tashi da azumin ramadana, da daddare Ammy ta idar da sallar isha'i a dakin ta, zaune ta ke kan dadduma ta doka uban tagumi dan kuwa gidan ya mata kunci, abin duniya ya ishe ta ji ta ke kamar ta hada nata ya nata ta sake barin gidan. Sallamar Halitta ya sanya ta dago a hankali tare da amsa mata. Ta na mai kallan Halitta wacce ta tsaya bakin kofa hannun ta dauke da waya, cikin yaran shuwa ta ce

"Halitta ya dai? Lafiya ko?"

"Lafiya lau Ammy, zan iya shigowa?"
Ta mayar mata da harshen hausa. Kai Ammy ta gyada mata, cike da nutsuwa Halitta ta shigo cikin daki, ta sami waje kusa da Ammy ta zauna. Sanye ta ke cikin shudiyar atamfa dinkin doguwar riga, kan ta tufke da dankwali. Ta na mai duban Ammy cike da tausayi ta furta

"Ammy dama akwai wani abun da na ke so na nuna mi ki, da kamar ba zan nuna mi ki ba, ganin yanda dangantakar ki da Dady ya zamu wani abu na daban ya sanya ni yanke hukuncin fada miki"

Ammy na mai tattaro dukannin nutsuwar ta, ta dubi Halitta cike da fargaba dan kuwa a cikin dan kwanakin nan ta ga abubuwa kala kala har ta gode.

"Ke kuwa Halitta wannan abu menene shi haka?"

Maimakon ta bata amsa, sai ta shiga danna wayar hannun ta, Instagram ta shiga har ta kai ga shafin Zainab, ta shiga hutunan ta, musammam wanda ta yi ba da jimawa ba a club, ta na mai nuna fuskar wayar ga Ammy ta ce

"Ammy kin gane wacece wannan?"

Wayar Ammy ta karba daga hannun Halitta, tare da fadin

"Waiyazubillah wannan rashin tarbiya har ina? Ke kuwa Halitta ina zan san wannan lalatacciyar yarinya haka? Ji tufar da ke jikin ta? Wannan ai arniya ce! Kai wannan a arnan ma ba dai tambatsastsiya ba!"

Halitta na duban Ammy cike da tausayi ta ce

"Ammy duba fa da kyau ki ga, ba ki gane ta ba....."

Ta na mai jefa mata waya ta ce

"Ke ni ban san shashanci ina na san wannan arniyar bare na gane ta! Toh idan ma kin san ta babu ke babu ita! Wannan lalalcewa har ina? Ji fa hayaki ta ke busawa....!"

"Ammy Yakura ce fa....."
Cike da mamaki Ammy ta ce

"Ki na nufin kawar Yakura ce? Ta taba kawo ta gidan nan? Ina Yakura irin kawayen da ta ke mu'amala da su kenan?"

Halitta na mai girgiza kai yayinda ta ke dada nunawa Ammy hotan Yakura da ke kan fuskar wayar ta, ta ce

"Ba ki gane ta ba ne, ba kawar Yakura ba ce, Yakuran ce da kan ta Ammy duba ki gani....."

"Zancen banza zancen hofi!"

Cewar Ammy yayinda ta fuzgi wayar hannun Halitta ta na mai kurawa hotan idanu a karo na farko. Kallan kurilla da ta yiwa hotan ya sanya ta furta

"Innalillahi wainnailaihi rajiun"

Hawaye ne bibbiyu ke fita daga idanun ta, fadi ta ke

"Halitta wannan diyar da na haifa ce haka? Wannan Yakura ce Halitta? Wannan me kama da Yakura ce....."

"Wallahi Ammy ita ce, idan kin yi gaba ma za ki ga sauran hotunan ta da videos din da ta ke sakawa"

Cewar Halitta wacce ita ma din kukan ta ke ganin yanayin da Ammy ta shiga. Ammy kuwa yanda Halitta ta ce ta yi hakan ta yi, ta ringa bi ta na ganin munanan hotuna da videos din da Zainab ta yi, har ta kai ta kasa jurewa ta na mai wulgi da wayar ta tashi a fusace ta fita ta na kwallawa Zainab kira.

A falo su ka tadda ta ta fito a tsorace, haka ma Falmat wacce ihun kiran da Ammy ke yi ya firgita ta.

"Ammy gani lafiya....."

"Tas" Ammy ta dauke kumatun ta da mari har sai da ta ga walkiya a idun ta. Kafin ta kai ga farfalowa ta kara daga hannun ta wanke kumatun ta da mari har sai da ta zube kasa tsabagen zafi, kuka ta ke mai kara kamar wacce ran ta zai fita, musammam ganin yanda Ammy ta rufe ta da duka kamar wacce Allah ya aiko. Cewa ta ke

"Na shiga uku! Ammy za ta kashe ni! Halitta ku taimaka min, Falmat ku ceci ni kashe ni Ammy za ta yi!"

Duk yanda Falmat ta so karbar Zainab daga hannun Ammy sai da abin ya gagara, dan kuwa garin haka ita ma sai da ta sami raban ta. Ganin Halitta ta tsaya gefe ta na kuka ba ta da niyar agazawa Falmat ta ce

"Halitta dan Allah ki taimaka ko Iya ne ki kira mana!"

Gudun kar ta kira Iya asiri ya dada tonuwa duk da ta na da yakinin Iyan ba ta nan, dan yanda Zainab ke ihu ya ci ace ta ji, Halitta ta taimaka, ita da Falmat ne su ka shiga tsakanin Zainab da Ammy, Ammy na haki ta ke furta

"Ku barni na kashe yar banza na huta, wallahi da haihuwar ki gwara barin ki Yakura! Innalillahi wainnailaihi rajiun! Da na sani na take kanki na mukurkushe ki sanda ki ka zo duniya da ba ki ja min wannan bakin ciki haka ba! Macuciya azzaluma! Allah ya........."

"Innalillahi Ammy ki duba girman Allah kar ki mata baki haka!"

Halitta ta yi saurin katse Ammy, yayinda Falmat ta ja Zainab kusa da kujera, kuka ta ke sosai dan kuwa ta daku kwarai.

"Wani baki kuma ya rage? Ai Yakura ko ban mata baki ba ai duniya ta mata, ace diya ta ta ciki na ce haka? Allah sarki Malam! Allah sarki Malam, ciki mai haife haife ya haifo mana masifa! Sai yanzu na fahimci hukuncin da ya yanke kan wannan lalatacciyar yarinya!"

Ta karasa maganar ta na mai nuna ta da dan yatsa. Jikin gurnanin kuka Zainab ta furta

"Ammy me na mi ki haka da na cancanci wannan la'anta Ammy?"

"Uban ki ki ka min! Har ki na da bakin magana? Kai wannan yarinyar kashe ni za ta yi ni Aleesha!"

Cewar Ammy ta na mai daura hannu biyu bisa kan ta, ta kai ta kawo, ta kai ta kawo ta dubi Halitta ta ce

"Dauko wayar nan Halitta, maza dauko ta!"

Cikin rawar jiki Halitta ta je ta dauko wayar ta kawowa Ammy, karba ta yi ta na mai jefawa kan jinyar Zainab ta ce

"Dauka ki goge duka hotunan ki da kazaman videos din ki dan uban ki!"

Hannun na rawa Zainab ta dau wayar, ko da ta duba ta ga dalilin da ya sa Ammy ta nakada mata na jaka, a hankali ta dago ta dubi Halitta, ta na mai kallan ta irin wannan kallan kin ci amana ta. Ganin haka Ammy ta ce

"Ki dena kallan ta! Dubin ki ya gama cika Zainab! Ke ma Halitta duk wannan masifun da laifin ki, ki sani duk yanda Yakura ta cutar da mu ki na da gudunmawa akai, dan kin sa kyamatacciyar rayuwar da ta ke yi amma ki ka ki sanar da mu!"

Cikin sanyin jiki Halitta ta furta

"Ammy....."

"Shhhhh! Kar ki ce min komai! Da kin fada min da duk haka be faru ba! Oh ni Aleesha me na mu ku haka Halitta? Me na muku?"

Cewar Ammy ta na mai ware hannu cikin alamar tambaya. Ta na duban Zainab ta daka mata tsawa
"Na ce ki goge me ki ke jira dan uban ki!"

Baki na rawa tsabagen tsoro dan ba su taba ganin Ammy cikin matsanancin bacin rai kamar haka ba, ta ce

"Ammy ai sai ta account dina, Kuma waya ta ta fashe, sai dai Halitta ta taimaka ta fita daga na ta account din...."

"Maza Halitta fita ta shiga nata, ta goge komai delete everything, son samu ma ta rufe page din gaba daya! Wannan idan Malam ya gani mun kade har ganyen mu!"

Ammy ta katse ta, ta na maganar ne cike da gaggawa. Halitta wacce sam ba ta yi danasanin tonawa Zainab asiri da ta yi ba, sai ma na yin jinkirin da ta yi. Hannu ta sa ta karbi wayar ba tare da ta damu da mugun kallon da Zainab ke watsa mata ba ta fita daga na ta account din, sannan ta mayarwa Zainab da wayar ita ma ta shiga na ta. Nan ta ringa bin duka hotunan da videos din da ta saka ta na deleting, sai da ta koke tas, sannan Ammy ta sa ta yi unfollowing kowa da da take following, ta na mai duban Ammy da jajayan idanun ta ta furta

"Ammy na yi abin da ki ka ce....."

"Saura delete! Ki yi deleting account din gaba daya ya dena aiki!"

Cikin rawar murya ta ce

"Ammy ban iya ba...."

"Za ki iya ne dan uban ki, dukan da na mi ki ne be ishe ki ba ina ga!"

Jin haka hannu na rawa Zainab ta bi yanda za ta yi, sai gashi ta yi deleting account din gaba daya. Sannan ta wulgawa Halitta wayar ta. A fusace Ammy ta ce

"Maza ki fasa mata wayar ki siya mata sabo gal, asararriya kawai! Ki sani a daren yau za ki hade na ki ya na ki ki tafi can inda Malam ya ce ki na kwana da mijin ki, har ki na shirin kashe min aure ashe na bar jaki ina can ina dukan tanki!"

"Dan Allah Ammy ki yafe min, kar ki ce na kwana BQ, Allah Ammy ba zan iya ba, Ammy dan Allah"

Cewar Zainab cikin sheshekar kuka. Cikin nuna halin ko in kula da kukan ta Ammy ta ce
"Wallahi sai kin koma! Na baki nan da minti talatin kacal ki hada naki ya naki ko na dan dena ganin ki na sami sarari cikin zuciya ta, kuma kada wanda ya saka mata hannu cikin ku! Idan ya so idan gari ya waye na ga kin sake haurawa kin bar gidan gaba daya! Shi ne zan san kin isa tabarayyi!"
Da wannan ta juya ta shige dakin ta tabar Zainab ta na mai watsawa Halitta a harara, ta kara da

"Na tsane ki Halitta, tsakanina da ke Allah ya isa ban yafe ba"

"Mtswww"

Halitta ta ja tsaki, sannan ta kara da

"Allah ya isan ki ba zai ci ni ba, sai dai ya ciki ke kan ki! Kin ga tafiya ta!"

Ta juya ta wuce na ta dakin ta na juyo zagin da Zainab ta ke sirfa ma ta. Falmat kuwa wacce dama jikin ta ya gama mutuwa waje ta samu ta zauna in da ta ke kallan Zainab cike da mamaki. Kallan da ta ke mata ya sanya Zainab tashi a fusace ta shige daki ta na mai doka kofa.

Yanda Ammy ta yi kwance ta na kuka, haka Zainab ta zauna na ta dakin ta ci kukan ta ta koshi. Minti talatin daidai sai ga Ammy ta zo ta na mata oya oya ta fito ta wuce dakin ta, haka da kuka da majina ta na cijewa Ammy ta ja ta, zanin gado da filo kawai ta iya dauka, ita ta kai ta har corridor din da shi ne zai fita da ita waje, tafiya kalilan ce tsakanin kofar corridor din da BQ. Hakan yayi daidai da gyaftawar Jauro, zai je ya kunto karnukan gidan. Ganin abin da ke faruwa jiki na bari ya wuce simi simi ba tare da Zainab ta lura da wucewar sa ba ya koma ba tare da ya je kunto karnukan ba

Bakin corridor ta zauna ta gama shan kukan ta, ganin sauro na shirin cinye ta ya sa ta lallaba ta karasa BQ din a tsorace hannun ta dauke da tsanin gadon ta da filo. Ganin Usman ba ya kusa ta shige dakin da ta fara cinkaro da, cikin sauri ta sakata da jam lock da kulle dakin gam.

Cike da kyamkyami ta ke duban dan karamin gadon da ke dakin. Farin zanin gado ne, tuni ta yaye shi ta yi wulgi da shi gefe, yayinda ta dan shifida rabin na ta, haka kuma ta rufa da sauran rabin, sai ajiyar zuciya ta ke yi tsabagen kukan da ta sha.

Jauro kuwa ko da ya koma wajan da ya bar Usman da Isa zaune kan benci, ya na mai dukan kafadan Usman ya furta

"Dan cirani ka tsinci dami a akala!"

Dukan su duban shi su ke cikin rashin fahimta, Jauro ya gyara tsayuwa ya ce

"Ai yau za ka sha gara dan cira ni, abin ba a cewa komai Allah ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login