Showing 9001 words to 12000 words out of 58720 words

Chapter 4 - Auren Shehu Book 1 Hausa Novel Complete

25 Jan 2025

457

fadin haka ta fice a fusace tare da buga masa murfin mota. Zuciyar ta na bugu ko wani taku ta yi, wayar Halitta ta shiga kira, ta yi ringing ta gama ba ta daga ba, hannu na rawa ta kira Falmat, ita ma din ba ta daga ba, isar ta gate din ta dan tura ta ji a rufe, sai da ta dan yi jim sannan ta yi karfin halin bugawa. Har ta fitar da rai da bude gate din, ta na shirin juyawa sai ta ga an bude hujun da aka yi jikin gate din domin ganin na waje.

Idanun ta ta tsinta cikin na sa, tuni ta tsinci kanta cikin mummunar faduwar gaba, yayin da bugun zuciyar ta ya karu, sai da yayi sakanni ya na kallan ta, ta na mai cuna kumatu cike da tsiwa ta ke mayar masa da martanin kallan, dan kuwa tsoro baya hana Zainab rashin kunya..

"Malam dalla ka bude min gate! Ka zuba min na mujiya ba ka taba ganina ba ne?"

Ga mamakin ta sai kuwa ya bude, shigar nan dai da ta gan shi da ita jiya da daddare, shi ne jikin sa, Goran nan dai be aje ba, ta na rike hannun sa na hagu, hannun sa na dama kuma ruke da rediyo ya na jin labarai.

Ko kallan sa ba ta kara yarda ta yi ba, bare su hada idanu kai tsaye ta wuce ciki kamar dai yanda Bobo ya ce ta yi, addua ta ke Allah ya rufa mata asiri kar ta hadu da Isa ko Jauro, sa'ar da ta yi da an idar da sallar asubahi su ke komawa su yi baccin su tun zuwa Usman gidan, shi kadai su ke bari da gadin safe, karnuka kuwa ana kiran sallar farko ake daure su, saboda kar su dami masu sallah masallacin gidan da haushi, duk da dai ta waje masallacin ya ke.

Sai da ta kurewa ganin sa, zuciyar sa cike da tunani kalala wanda duk yanda ya so ya cire daga zuciyar sa ya gagara, ya mayar da gate ya rufe.

"Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun! Babu shakka Allah ya jarabci Malam da diya kamar yanda ya ke jarafta salihan bayin sa cikin ikon sa! Ya Allah ka kare Malam daga sharrin wannan Bingel!"

Cewar shi a zahiri, yayinda ya koma mazaunin shi bisa benci, ya kishingida ya na mai cigaba da sauraron labaran shi a tashar BBC hausa.

Cikin sanda takalman ta a hannu ta ke tafiya, ta kitchen ta bi ta shiga falon, dab da zata karasa dakin ta muryar Halitta ya daki kunnan ta

"Yakura daga ina ki ke?"

Jiki na rawa ta saki takalman su ka zubi kasa, Kallan Halitta ta ke ta na mai waige waige ta ga ko ita kaidai ce. Ita kadai din ce sanye cikin hijab har kasa, hannun ta ruke ta carbi dan Halitta ba ta komawa bacci bayan sallar asuba, zama ta ke ta yi zikiri da adduo'i har gari ya waye rana ta fito, sannan ta shiga kitchen ta taya iya abin karin kumallo. Ta fito za ta kitchen din kenan su ka yi kacibus da Zainab ta na sanda za ta shige dakin ta.


AUREN SHEHU

5.



Wani irin sassanyar ajiyar zuciya ta saki, ta na mai duban Halitta murya kasa kasa ta ce

"daga ina na ke kuwa? Dage exercise mana!"

"Exercise din tun karfe 4:45 na dare Yakura? Ki ji tsoran Allah! Ammy ta turo ni tashin ki sallah Yakura, na san ba gidan nan ki ka kwana ba, daga ina ki ke?"

Halitta ta kara tambaya ta na mai tsare ta da idanu.

"Daga yawon ta zubar na ke ko da yanda za ki iya ne? Ki na da abin yi ne? Kuma Allah ya mana katangar karfe da saidawa!"

Kafin Halitta ta bata amsa ta yi saurin kwasar takalman ta, ta yi wuf ta shige dakin ta. Jim ta yi ta na maimaita kalaman Zainab cikin ran ta

"Daga yawon ta zubar na ke......"

Ta kara maimaita.

"Shin anya kuwa shirun nan da na ke akan abin da Yakura ta ke yi Allah ba zai tambaye ni ba? Ko dai Ammy zan fadawa? Ko da ya ke in har na fadawa Ammy kamar na fadawa Dady ne, Allah kadai ya san halin da Dady zai shiga muddin ya sani, Allah ka ga zuciya ta, Allah ka mana magani"

Kitchen ta wuce, ganin Iya har lokacin ba ta fito ba sai ta wuce dakin Iya domin ta ga ko lafiya.

Zainab kuwa ta na shiga bandaki ta shige ta yi wanka, fitowar ta daga wanka ta tarar Ammy tsaye tsakar dakin, abin ku da mara gaskiya sai da zuciyar ta ta dan yi rawa. Ta na kame kame ta ce

"Ammy, aw ashe ke ce"

"Ni ce jiki yayi sauki kenan, ai na turo Halitta ta tashe ki sallah da asuba...."

"Eh mun hadu ai"

Ta yi saurin katse ta. Kallon ta Ammy ta ke kamar mai nazari, kafin daga bisani ta ce

"Me ki ke cewa ne? Kamar yaya kun hadu?"

Zainab na mai sosa kyeya ta ce

"Ah ah ina nufin na gan ta, da ta zo tashi na, eh ta tashe ni din"

"Oh toh, Ni ce min ta yi ba ta gan ki ba, ta na tunanin kin tashi tuni har kin shiga toilet"

"Eh ai ina toilet din na jiyo shigowar ta, haka na ke nufi Ammy"

Kai Ammy ta gyada, sa'annan ta kara da

"Ya ciwon kai?"

"Ciwon kai? Aw Alhamdulillah na sami sauki, Ina kwana Ammy?"

Cewar Zainab yayin da ta zauna bakin gado, Allah Allah ta ke Ammy ta fita ko ta samu gaban ta ya bar faduwa.

"Lafiya lau Alhamdulillah, ashe ba mu gaisa ba, Allah ya kara sauki, sai ki yi maza ki fito mu karya ko?

"Wallahi Ammy ba zan iya cin abinci yanzu ba, wani irin bacci na ke ji, rabona da bacci tun jiya da safe, kin san bacci ba a cin bashin sa "

Ta na mai duban ta cikin nazari ta ce

"Wannan baccin na ki kuwa anya Yakura? Me ya hana ki bacci? Nan fa na shigo na tarar ki na ta bacci?"

"Ah ah, wai ina nufin ban yi ishasshe ba, ina yi ina tashi saboda ciwan kai"

"Toh Allah ya sauke, ki daure dai ki ci wani abu kafin ki kwanta"

Zainab ta amsa mata da toh, dan dai kuwa ba ta da buri da ya wuce Ammy ta fita ta samu ta ji hakarkarin ta bisa katifa. Illai kuwa ta na fita ko mai ba ta iya shafawa, ta dauko wata yar riga iya gwiwa ta sanya, ba batun sallar asubahi ta bi lafiyan gado abin ta. Nan da nan bacci ya dauke ta.

***

Haka rayuwa ta cigaba da gudana. Zainab ta kasa hakura da club ta bari sai ta koma makaranta kamar yanda ta saba, saboda sabon saurayin ta Mike, shi ne ke zuwa daukar ta ya dawo da ita.

Ba komai ne ya bata lasisin wannan shagalin na ta ba face shawarar Mike da ta bi na siye daya daga cikin masu gadin gidan. Cikin masu gadin uku ta san Isa da tsattsauran ra'ayi ko da wasa ba zai amince da ita ba, Usman kuwa shi tsoran sa ma ta ke ji, dan haka sai ta kama Jauro ta rike gam. A kulli yaumin ta kan tabbatar ta masa alkhari na safe daban na yamma da daban, ta haka ta samo hanyar shawo kan sa. Ta masa karyar cewa akwai kungiyar bitan karatu da su ka hada ne ita da yan makarantar su da ke zaune Kano, kafin su koma makaranta, Amma da daddare ake yi, ta na tsoran kar ta fadawa su Ammy ne su hana ta gabadaya, shi ya sa ta yanke hukuncin ta na bi ta bayan kasa, har su koma makaranta.

Duk da Jauro ya san maganar Zainab yashesshen zance ne, da ke ido a kabo ne da ta bashi sai ya sa hannu ya karfe, idan dare yayi sai ya tabbatar Usman da Isa ba sa kusa sai ya bude mata kofa, haka idan ta dawo shi ne ke bude mata.

Duk wannan hidimar da ya ke yi akan idanun Usman, tun ya na Wauke kai har ya gaji wata ranar Juma'a da yamma, ana saura sati daya Malam ya dawo Usman ya sami Jauro kishingide karkashin bishiya ya na shan rake, dan kuwa tunda Zainab ta fara bashi kudi kullum cikin kudi ya ke.

Sallama ya masa tare da zama kusa da shi. Tayin rake Jauro ya masa bayan ya amsa sallamar. Usman na mai godiya, cikin maganar sa mai cike da nutsuwa, yanayin yanda ya ke fito da kalmomin hausa daga bakin sa ne ki kara jaddada kasancewar sa na kabilar fulani, ya ce

"Alhamdulillah, na gode Jauro ka sha raken ka, dama akwai yar magana da na ke so mu yi da kai"

"Toh Madallah dan cirani, da me ka zo"
Cewar Jauro bai fasa shan raken sa ba. Shiru ne ya biyo baya, kafin daga bisani Usman ya ce

"Ka yi hakuri zan ma ka shisshigi, wala'alla za ka fahimce ni"

Jauro na mai fuzar da totuwar rake daga bakin sa ya ce

"Uhum, ina sauraron ka.

"Zancen fitar dare da Bingel din nan ke yi, diyar wajan Malam"

Cikin halin ko in kula Jauro ya ce

"Uhum? Menene na ka a ciki?"

"Akwai, Malam ya ba mu gadin gidan sa bisa amana, ni da na ke gani ina dauke kai ba tare da fadawa mahaifan ta ba, ina da alhaki, bare kai kuma da ka ke ba da gudunmawa Jauro!"

Jauro na mai tashi zaune ya ce

"oho! Ashe dai ka na gani, kuma ka san ka na da alhaki! Tun da ka ke gani ba ka san ka na da alhaki ba sai yanzu da ka ga ina dan samu ko fillo? Ni za ka yiwa halin na ku na fulanin daji ko? Dan bakin ciki!"

Usman na mai dafe kai ya ce

"Ya ilahi! Ba ka fahimce ni ba Jauro! Ba dan komai ya sa ban iya fuskantar Malam akan wannan batun ba sai dai dan kunya da nauyin sa da na ke ji! Da wani ido ko baki zan iya kallan Malam na ce masa diyar sa na haura katanga? Ko kuma duk dare ana zuwa ana daukar ta? A dawo da ita da safe?"

"Dan sa ido! Da Idon da bakin da ka zo ka tinkare ni yanzu mana! Yarinya na fita bitar digiri(Degree) din da ta ke yi a jami'a, ko da yake kai fa ko zo na kashe ka da turanci ba ka sani ba bare ka san kalmar Degree! Kai Allah dai ya raba mu da jahilci!"

Duk zuciya irin na Usman sai ya tsinci kan sa ya na mai murmusawa, ka na ya ce

"Ban da cin fuska mana Malam Jauro, na zaci za mu iya samin fahimtar juna shi ya sa ma na tunkare ka da maganar, amma tun da abin haka ne, Allah ya ba ka hakuri!"

"Ni kuma na taimaka da Aameen! Eh amen, kuma Allah ya raba mu da munafukai da yan bakin ciki"

Usman na murmushi ya amsa da amen, tashi yayi tare da yiwa Jauro sallama duk da dai be ji dadin yanda Jauro ya kasa fahimtar ta shi, sam be ruke shi a rai ba, shi dai fatan sa Allah ya bashi ikon kawo karshen wannan masifar da ke faruwa gidan Malam, duk da kamar yanda Jauro ya fada be san "digiri" ba, Amma koma menene wannan digirin in dai haka ake yin sa toh lalle ba alkhairi ba ne.

***

In da Usman ke kokarin neman mafita akan iftilakin da ke faruwa gidan Malam, ita kuma Halita soyayyar Usman ce ta sami wajan zama cikin zuciyar ta. Zaune su ke a falo, sun gama cin abinci kenan su ka zauna zaman hira. Falmat sanye da atamfa koriya dinkin doguwar riga, Halita kuwa kananan kaya ne cikin ta, riga da sikit jajaye, kanta daure da jan mayafi.

"Ni kuwa Halitta ina mamakin yanda ki ke kaunar Usman din nan, dan kuwa dai sai dai na kira shi kauna dan ya fi karfin so"

Cewar Falmat yayinda yanayin fuskar ta ke gasgata lafazan ta. Sanyayyar ajiyar zuciya Halitta ta saki kafin ta ce

"Daga Allah ne Falmat, Ni dai kawai ki taya ni addua"

"Toh zan taya ki, Amma duk randa Ammy ta san Usman ki ke so Halitta, I mean not just Usman o, but Maigadin gidan nan wallahi akwai kura...."

"Shhhhh"

Halitta ta katse ta, ta na mai kasa da murya ta ce

"Ke fa matsala ta da ke Falmat handsfree! Ki rufa min asiri kar Yakura ta ji....."

"Ji kuma na nawa?"

Da sauri su ka juya su na kallon ta, ba wanda ya san da shigowar ta bare ya san adadin mintunan da ta yi tsaye ta na sauraran su. Sanye ta ke cikin bakin material, doguwar riga ta yi daurin nan da ake Kira tura ka tsiya. Idanun ta kan Halitta wacce har ga Allah ba ta so maganar ya je kunnan ta ba ta ce

"Yanzu ke Halitta ki rasa wanda za ki so sai wannan Maigadin? Yo to menene abin so a wannan kazamin bafulatanin hammata fal gashi?"

In da Halitta ta fusata, ita kuwa Falmat mamakin yanda aka yi Zainab ta ga hammatar, ba ta san sanda dariya ta kwace mata ba, wanda hakan ba karamin tunzura Halitta yayi ba. Yakura ba ta gushe ba ta kara

"Ke anya kuwa bakin wannan ya san brush? As in kafin na so mutum I first imagine things people do when they're in love, as in can you imagine yourself with him? Like imagine kissing wannan dagageggen bakin na shi?"

"Wayyo Allah Ammy!"

Falmat ce ta saka ihu ta na mai dariyar mugunta, ita kuwa Halitta iya kulewa ta kule. A fusace ta ce

"Malama ina ruwan ki? Kin manta ba kiss ba! Abin da ya fi kiss! Idan ma auren shi na ce zan yi ina ruwan ki!"

Ta na mai daga hannu sama yayinda ta zagaya ta shigo falon sosai, kujerar da ke kusa da Falmat ta zauna, sannan ta ce

"Babu fa, babu ruwa na ko kadan, aw kin san abin da ya fi kiss ashe, yo ai na zaci uztazanci ya hana ki sani, Sha it's your life, Bari na ja baki na!"

"Alhamdulillah tunda kin san haka, da fatan za ki yi aiki da shi...."

"Ke fa ba kunya gare ki ba Halitta!"

Zainab ta katse ta cikin tsawa, ta kara da

"Kar ki ga kin yi tsayin kafa wallahi ina iya doke ki, mara kunya fitsararriya"

"Toh sarkin tsiwa! Tun daga daki na ke jiyo hayanoyar ku! Anya kuwa Yakura? Ke da waye kuma?"

Ammy ce wacce ihun Falmat ya sanya ta fito da sauri ta ke tambaya.

"Babu komai Ammy"
Halitta ta fada gudun kar Yakura ta mata tunan asiri, ilekuwa sai cewa ta yi

"Da komai fa Ammy, ai dai gaban ki yarinyar nan ta gama azazzabi da rawan jiki wajan jaddada bayani akan wannan dan bokon haram din, toh dai ruwa ba ya tsami banza, ga shi nan na ji tana managanar son shi ya kamata..."

Ta karasa maganar ta na yar dariya tare da girgiza kai. Daga Falmat har Halitta mutuwar zaune su ka yi, sun san Zainab da barin zance amma ba su taba zatan za ta tonawa Halitta asiri hakan nan kara zube ba.

Ammy na dariyar yake ta ce
"Ke kuwa Yakura ba dai zolaya ba, ina Halitta ina kula wani da namiji? Har kuma ki ce Maigadi? No wonder na jiyo ku tun daga daki, ah ah ni ma ban goyi bayan wannan wasan ba!"

"Atoh Ammy ke dai kya fada"

Cewar Falmat ta na mai fatan rufe asirin Halitta. Zainab kuwa ba ta damu da irin sakon da Halitta ke aika mata ta ido ba, sake cewa ta yi

"Wallahi Ammy ba wasa na ke ba, Halitta soyayya ta ke da Maigadin gidan nan"

"Lailaha ilallahu Muhammad a rasulillahi!"

Cewar Ammy ta na mai tafa hannu cikin tashin hankali ta ke duban Halitta wacce ita ma din kallo daya za ka mata ka tabbatar da damuwan da ta shiga.

"Halitta me na ke ji haka? Wannan wani irin mummunar labari na ke ji Halitta? Duka tarbiya, kulawa da soyayyar da mu ke baki abin da za ki saka mana da shi kenan Halitta?"

Tuni hawaye ya shiga fita daga idanun Halitta, ta na girgiza kai ta ke fadin

"Ah ah Ammy, wallahi ba haka ba ne Ammy...."

Cikin bambami Ammy ta ce

"Ba haka ba ne uban ki ne? Yi min shiru! Wallahi kin ba ni kunya kin yi asara Halitta! Yanzu idan Malam ya ji wannan tozarcin da cin amana ya ki ke tunanin zai ji. Dama aka ce tsintacciyar mage ba ta mage! Hakan nan mutum daga sama ya zo gidan ka ka karbe shi har da bashi wajan kwana, gashi nan zai masa sakayya ta hanyar hure ma diyar sa kunne ai! Toh kuwa zaman shi a gidan nan ya zo karshe"

Jin Ammy na batun zai bar gidan wani dadi ne ya mamaye Zainab, dan kuwa burin ta ke nan.

"Atoh ai tun da na fara ganin sa na san ba za a wanye lafiya ba, na yi magana a ce na fiya kyaman yan kauye, ga dai irin ta nan!"

Cewar Zainab ta na mai daga kafada tare da saukewa. Falmat ce ta saka baki ta ce

"Ammy ba ki fahimta ba, wallahi ba haka ba ne, shi wannan bawan Allah sam be ma san da Halitta ba, bare ma ya hure mata kunne, ba soyayya su ke ba, kawai dai Halitta na yawan maganar sa ne ya sa ke tsokanar ta da shi, Amma babu komai tsakanin su Ammy!"

"Ki ji wani yashesahen zance idan babu rami me ya kawo rami?"

Ammy ta tambaya a fusace, in da Zainab ta taya ta da atoh. Halitta kuwa ta ma kasa magana sai hawayen takaici da ge gangarowa daga idanun ta.

"Allah Ammy gaskiya na ke fada mi ki, in kuma ya kama a kira shi ne ki tambaye shi ki kira shi Ammy"

Shiru ne ya biyo baya na dan sakanni, Zainab sai adduar Allah ya sa kar Ammy ta yarda da zancen Falmat ta ke cikin zuciyar ta. Jin abin da Ammy ke fadi ne ya sanya ran Zainab yin baki. Tana mai ajiyar zuci ta ke fadin

"Toh ni fa in ce, jinina ba za ta taba san Maigadi mara asali ba, haba har na dan ji sanyi cikin rai na, toh wallahi kar na sake jin maganar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login