Showing 54001 words to 57000 words out of 58720 words

Chapter 19 - Auren Shehu Book 1 Hausa Novel Complete

25 Jan 2025

466

gudun da su ka yi, karfe uku a Giwa barracks ta mu su, har aka shiga barikin be san in da ya ke ba, illa bayan da aka sauko da shi, sun dan yi tafiyar kasa mai tsayi, sannan su ka tsaya, ya ji kamar ana bude kofa, ya na ji su ka caje shi tas, su ka cire duk wani abu da ke jikin sa, ciki har da takardar da yar tawadar sa da ya ke rubutu duk sanda bukatar haka ya taso, daga bisani aka hankada shi cikin wani waje da shi kan sa be san yanda wajen ya ke ba, ya ji an mayar da kofa an rufe. Sai a sannan wani sabon tsoro ya rufe shi, ya fashe da kuka cikin ran sa ya na mai ambaton ubangiji da ya kare shi daga sharri wannan mutanan da su ka dauko shi ba gaira babu dalili. Jiki da jini be jima ba baccin azaba ya dauke shi nan zaune.

Tun sassafe labarin dauko Usman ya sami Zainab, ba karamin nishadi da annashuwa ta tashi da shi ba, musammam idan ta tuna umarnin da ta bayar na a tabbatar Usman ya ji a jikin sa sannan a gaggauta tilas ta masa sakin ta, dan kowa ko zuwa in da ya ke ba za ta yi ba, ita dai kawai a karbo mata takardar saki. Babu wanda ya san wainar da ta ke tauyawa daga Anty Sauda sai Anty Hannah dan haka hankalin ta kwance ya ke.

Saukar ruwan sanyin da ya ji ya sanya shi tashi a gigice, be gama warewa ba ya ji saukar mari bisa kuncin sa, wanda hankan ya sa shi komawa ya zauna ya na mai ware idanu. Wanda ya watsa masa ruwan ya fara bi da kallo, Soja ne, daga gani sojan ma karamin wanda ake kira kurtu, sanye cikin kaki, ya tsare shi da jajayen idanun shi.

"Dan uban ka an ce ma ka nan gidan bacci ne?"

A tsorace ya shiga girgiza masa kai alamar "ah ah"

"Ba ka da baki ne? Open your mouth and talk to me friend!"

Maimakon ya bashi amsa, sai ya cigaba da girgiza masa kai, hakan ne ya kara tunzura kurtun, ledar abinci da ke aje bayan sa ya janyo, ya bude kosai ne da biuredi, da ke rabon sa da abinci tun jiya da rana tuni zuciyar shi ta kwadaitu da kosai da buredin. Ganin yanda ya ke kallan abincin ya sanya kurtun murmushin mugunta, ya ce

"Duk sanda ka budi baki ka yi magana a ba ka abinci! Giwa barracks ka ke dan uban ka, ma'ajiyar tsinannu irin ka! Wai dan ka mushe mu yar da kai ba wani abu ba ne!"

Ya na gama fadin haka ya ja bakin kyallen zai rufe masa fuska. Kai ya ke girgiza masa, kokarin rokan sa ya bar shi yayi sallar asuba ya ke amma babu dama dan kuwa yana ji ya na gani ya kara sanya bakin kyallen ya rufe masa fuska sannan ya ja kofar ya rufe ba tare da ya ba shi abinci ba.

Da yammacin ranar Zainab ta ci ado kai ka ce gidan biki za ta je jin Kori da Falmat na tsokanan Halitta akan za ta yi bako. Sanye ta ke cikin material baki mai duwatsu ruwan zuman, dinkin goguwar riga ne da ya amshi jikin ta sosai. Karamin mayafi ta saka dan ta burge Sudais ganin shi din ma da alama wayayye ne, haka kuma ta shafa tsadaddun turaren ta masu tafiya da hankalin jama'a.

Ta na zaune falo Madu ya shigo shedawa Halitta isowar Sudais, in da ya ce ta same shi falon da Malam ke saukar baki kafin Allah ya masa cikawa. Jin haka Zainab ta faki idon Halitta ta fice, sai ga ta falon baki ta tadda Sudais zaune ya na jiran Halitta.

Fuskar ta kunshe da fara'a ta masa sallama, ganin ita ce maimakon Halitta da ya ke tsammani be sa ya fasa mata fara'a ba, tare da amsa sallamar ta. Cike da kissa ta ce

"Ka ba ni izini na shigo? I'm welcome?"

Zuciyar shi daya ya murmusa, murmushin da ke kashe Zainab dan kuwa sai da bugun zuciyar ta ya karu. Jin ya furta

"Why not? You're welcome babbar Yaya"

Zainab ta dan tsuke fuska,
'wato har wani yaya ka ke ce min ko? Wai kai mijin kanwa ta! Ka yi ka gama ni ce matar ka! Da ni ka dace'

Abin da ta ke fada cikin ran ta kenan yayinda da ta karasa shiga falon, tana taku dai dai, ta sami kujera dab da shi ta zauna, wanda hakan ya sanya shi daga Ido ya kalle ta, ita kuwa ta sakar masa murmushin da ta san ba karamin jan hankali da rikita maza ta ke da shi ba. Sai a sannan ya lura da irin adon da ta yi, sai dai kuma sama Sudais ba abocin son ado irin na Zainab ba ne, sam ba ta burge shi ba. Ga mamakin ta sai gani ta yi ya dauke kai, yayinda ya kunna wayar hannun sa ya shiga dube dube. Cikin kulewa ta ce

"Ina wuni?"

"Lafiya lau Alhamdulillah"

Ya amsa ba tare da ta daga Ido ya kalle ta ba. Zainab na mai cije lebe, ta kara da

"Ya ku ka je gida rannan?"

"Lafiya lau"

Ya ba ta amsa a taikaice, har lokacin hankalin sa kan wayar sa ta ke. Ran Zainab ya fara baci, ta saba maza ke bin ta kamar jela, Amma ga wannan ita da kan ta ta zo wajan shi, ya share ta kamar ma be san da zaman ta a wajen ba. Jikin ta be yi sanyi ba sai da ta ga yanda fuskar Sudais ta sauya cikin kankanin lokaci yayinda ya ji sallamar Halitta, da kuma yanda ya bi ta da kallo tamkar zai cinye ta.

Ta ga dai hijabi ne jikin Halitta, har kasa ma kuwa, haka kuma fuskar ta sam ba kwalliya kai ka ce ita ce ma mai takaba ba su Ammy ba, Amma hakan be sa Sudais fasa kallan ta da tarerayan ta ba har ta zauna kujera can nesa da shi. Yanda ya ke kokarin yiwa Halitta hira bayan sun gaisa, ya tambaye ta ko ta na cin abinci da kyau kuwa, tare da rokonta da ta rage damuwa cike da kulawa ne ya sanya Zainab ta shi ta fita ba tare da ta yi masa sallama ba.

Dakin ta ta koma dan bacin rai ji take kamar za ta yi hauka. Gaba daya fushin ta ya fi karkata kan Usman, gani ta ke duk auran sa ne ya ja mata, dan ba dan Malam ya daura mata aure da Usman ba, da Sudais ne mijin ta, babu yanda za a yi ya kalli Halitta, har ma ya kulata bayan ga mace kamar ta gaban shi, idan har ta na son jan hankalin Sudais dole sai Usman ya sauwake mata auren masifar da aka daura mata. Ta na kuka ta kira Anty Sauda, fadi ta ke

"Anty Sauda na gaji da nauyin auren almajirin nan kai na! Dan Allah ku karba min takarda ta ko na huta!"

Jiki sanyaye Anty Sauda ke rarrashin ta, cewar ta

"Ki yi hakuri Yakura, tun da ya shigo hannu zai sake ki ne ai, ba dan taurin kai irin na shi ba ai da tuni an wuce wajan, kin san kuwa yanzu na ke shirin kiran ki, yaran General sun ce mutumin nan tun da aka kawo shi ya ki yayi magana, babu irin horan da ba a masa ba, Amma sam ya ki nunawa ya san abin da ake magana a kai, bare ma ya furta komai, ya zama beben karfi da ya ji, an ya kuwa ba a yi kuskure ba wajan dauko shi?"

"Zai ci uban shi kuwa! Wallahi sai ya sake ni! Babu kuskuren da aka yi tsabagen taurin kai ne irin na almajiri!"

Cewar Zainab a fusace. Daga dayan bangaran Anty Sauda girgiza kai ta yi ta ce

"Ah ah dai Yakura, gwara dai mu je mu gan shi da idanun mu, dan kuwa hotan da General ya nuna min na ga kamar ya dan canza akan ran da na gan shi a fili, ke kuma ba wayar arziki ba bare na ce zan turo mi ki ki gani, ko Halitta zan turowa....."

"Halitta fa!"

Zainab ta katse ta da saura, ba ta gushe ba ta kara da

"Ai Anty Sauda Halitta ba za ta rufa min asiri ba, na dade da ganewa ba ta kauna ta, gwara dai mu je din kawai, da ban yi niyar kara ganin wannan kazamin mutumin ba wallahi, amma ya zan yi!"

"Da dai ya fi din, gwara dai mu je. Ni ina ganin Halitta mai hankali me ya faru haka?"

Zainab na mai girgiza kai ta ce

"Kishi, envy, bakin ciki! tun da take kishi ta ke dani, na fita komai shi ya sa"

"Kai amma ko kuna ciki daya? ba ta kyauta ba, toh sai ki shirya zan zo na dauke ki karfe goma. Zan kira Hajja Aleesha na sheda mata za ki raka ni"

Cewar Anty Sauda cikin ran ta tana mai Allah wadar da halin Halitta. Da haka su ka yi sallama. Zainab ba ta kara bari sun hadu da Halitta ba tsabagen kishi da bakin cikin yanda Sudais ya mata.


Washagari da safe wajen goma Anty Sauda da Direban ta su ka zo daukan Zainab, duk yanda Falmat ta so bin su, kiri kiri Anty Sauda ta hana. Haka su ka tafi, Zainab da Anty Sauda zaune a gidan baya, direba da sojan da ke kula da Anty Sauda zaune gidan gaba, ba su zame koina ba sai Giwa barracks.

Ganin wacce ke tafe ba su sami damuwa wajan shiga barikin ba, kai tsaye aka wuce da su in da Usman ke kulle. Ana bude kofar wani warin datti ne ya buge su har sai da Zainab ta ja baya ta na mai rufe hanci da gefen mayafin ta, haka ma Anty Sauda wacce ta furta

"Huum! Hammatar mijin Yakura ke wari haka?"

"Ayya mana Anty Sauda!"

Cewar Zainab yayinda ta danna kanta cikin dan karamin dakin, ita dai burin ta Usman ya sake ta su bar wajan. Gaban ta ne yayi mummunar faduwar ganin wanda ke kwance hajaran majaran sai nishi ya ke da alama ya sha duka, idan aka dauke shekaru, tsayin sa, fadin sa, yanayin tufar sa da fuskar yayi kama da Usman sak, dan duk wanda aka fasaltawa Usman ya ga wannan zai ce Usman din ne, Amma ban da Zainab wacce ta san Usman sosai kamar yunwar cikin ta. Ta na mai duban shi ta ce

"Na shiga uku! Wannan ba Usman ba ne Anty Sauda! Wannan ba Usman ba ne! Wallahi ba shi ba ne!"

"Toh matsala! Ai nima na yi tunanin haka wallahi, kila tsabagen kama ne, bari na kira General din na sheda masa"

Cewar Anty Sauda cikin damuwa. Nan da nan ta kira General ta sheda masa halin da ake ciki. Waje su ka fito Zainab sai safa da marwa ta ke dan ta kasa nutsuwa. Suna cikin wannan yanayin ne wasu sojoji su ka zo su ka shige in da bawan Allah nan ya ke kwance, bayan wani yan mintini daya daga cikim sojojin ya fito dauke da takarda ya mikawa Anty Sauda, ka na ya ce

"We are very sorry Madam, an sami matsalar ne daga wanda su ka dauko shi, kamar yanda mu ka yiwa General bayani wannan ko magana be yi ba, sai yanzu da ku ka tabbatar mana ba shi ne wanda ake bukata ba, sannan mu ka gane da gaske ba ya maganar ba wai pretence ba ne, sanda mu ka caje shi mun ga takarda da tawada, hakan ke nuna mana hanyar maganar shi kenan, Ashe tun da alamar mu bashi ta kardar ya ke mana mu kuma ba mu gane na sai yanzu, gashi yayi rubutu jiki amma kuma rubutun da larabci yayi ban sani ba ko za ku iya karantawa"

Ya karasa maganar ya na mai mikawa Anty Sauda takardar. Zainab ce ta yi saurin karba ganin abin da ke rubuce jiki ji ta yi kamar ta kurma ihu yayinda ta mikawa Anty Sauda takardar.

"Muhamad Bello daga rugar Shehu, Dan Allah kar ku kashe ni, na zo kiran dan uwana ne jikin Iyar mu yayi tsanani, ku taimaka ku sake ni ban san me ku ke magana akai ba..."

Anty Sauda ta karanta a fili. Ta kara da

"Yakura wanene Muhammad Bello kuma? Ina ne Rugar Shehu"

"Ni ina zan san wanene shi! Na dai san Rugar Shehu sunan rugar su Usman ne, ya ma za su aikata wannan kuskuren dan Allah!!!"

*Khadija Sidi*Auren Shehu


18



Anty Sauda na Mai duban Zainab ta ce

"Yakura ni fa ganin yanda wannan ke kwance rai a hannun Allah gwara a sake shi kafin ya mace mu su a nan"

Cikin nuna rashin tausayin Muhamad Bello Zainab ta zunbura baki tare da fadin

" A sake shi? Idan aka sake shi sai a je a dauko shi almajirin ko Anty Sauda? Wallahi ni auren nan gaba Waya na tsana har rai na!"


"Ah ah ba sai an dauko shi ba, wannan horon da aka yiwa dan uwan sa ma ya isa ya sake ki muddin ya na da hankali"

Cewar Anty Sauda, ba ta gushe ba ta kara da
"Su dauke shi yanda ya ke su kai mayar da shi Kano..."

"Anty Sauda......"

Zainab ta katse ta cike da damuwa. Murmusawa Anty Sauda ta yi, ba ta gushe ba ta kara da
"In dai almajirin nan ne wallahi sai ya sake ki, yanzu dai a mayar da wannan kada ashahadun mutuwar shi ya rataya kan mu!"

Haka ba a son ran Zainab ba ta na ji ta na gani kafin su tafi, Anty Sauda ta ba da umarni a mayar da Bello Kano gidan Malam in da aka dauko shi.

A ranar aka wuce da Bello Kano, hajaran majaran, gaban gidan Malam su ka ajiye shi a wulakance, su ka juya su ka yi tafiyar su. Hayaniyar mutane ne ya sanya su Jauro bude kofa, ganin mutane sun yi cincirindon ya sa Jauro kutsawa cikin su domin ganewa idunun sa abin da ke faruwa, masu salati na yi, ma su Allah wadar da kasar nan na yi.

Kallo daya Jauro ya masa ya san ko shakka babu wannan bafulatani na da dangantaka Usman, dan haka da sauri ya koma ya yi kiran Usman, wanda jin abinda kr faruwa ya sanya shi fitowa kafa ko takalmi babu.

"Innalillahi wainnailaihi rajiun! Bello? Bello!!!"

Cewar Usman yayinda idanun sa su ka sauka kan Bello. Tuni idanun sa su ka kada su ka yi jajur tamkar garwashi, cikin kankanin lokaci gaba daya ya sauya kamanni. Tsugunnawa yayi gaban sa tare da daura hannu bisa kirjin Bello, jin ya na bugawa be tsaya bata lokaci ba ya dauke shi cak ya daura a bisa kafada, Haka kafa babu takalmi, Isa biye da shi su ka dauki hanyar da zai sada su da titi, Allah ya so kafin su karasa sai ga dan sahu, Isa ne ya tsayar mu su da shi, su ka shige, Usman na mai umartar dan sahu ya kai su asibiti mafi kusa.

Sun je asibitoci ya kai biyar, Amma duka sun ki karbar su, cewar su halin da Bello ya ke ciki ya kamata su zo da police report. Da kyar su ka samu aka karbe su wani karamin private hospital da ke cikin Tarauni, me suna Iklima Clinic, su ma din sai da Isa ya koma ya hado gaba daya abin da ya mallaka na kudi tare da wanda Usman ke da shi, su ka ba su sannan su ka yarda aka ba su gado, likita ya shiga duba Muhamadu Bello.

Bayan wasu mintina Likita ya fito, Nan ya ke yiwa su Usman bayanin yanayi yunwa da kishin ruwa da Bello ya ke ciki, bayan haka ga dukkan alamu an bashi kashi sosai, jikin sa zane ya ke da alamun shatin belt. Allah ya sa be sami karaya ba ko daya ba.

"Yanzu likita ya za a yi? Dan Allah ka taimaka ka ceto ran dan uwana"

Cewar Usman, cikin ran sa ya na mai cin alwashin ramuwar gayya ga duk wanda ya aikatawa Bello tsananin azaba haka, ko da kuwa wanene.

"Ka da ka damu, in Sha Allah za mu yi iyakar kokarin mu"

Cewar likita, wanda tun shigowar Usman Allah ya dora masa tausayin sa, musammam ganin yanda hankalin Usman ya tashi akan abin da ya sami Bello.


In da Usman ke zirga zirgan nemawa Bello lafiya, Zainab kuma a na ta bangaran tunanin yanda za ta kawo karshen auren ta da Usman ta ke, dan kuwa yanda ta ga ana maganar auren Halitta Sudais ba karamin daga mata hankali ya ke ba. Gashi duk wani dabarar da za ta ja hankalin Sudais ta yi, Amma ina kamar ta shuka dusa dan kuwa dai ha?onta ya kasa cimma ruwa.


Bayan sati Waya da sakin Muhammad Bello Anty Sauda ta zo gidan Malam. Ta yi rashin sa'a Ammy ba ta nan, Halitta da Falmat sun raka ta asibiti a gwada jinin ta, dan ta na yawan fama da ciwon kai. Zainab ce ta saka Anty Sauda gaba a kan auren ta da Usman. Cike da Mamaki Anty Sauda ta ce

"Wai ke wannan saurin ina zai kai ki ne? Na ga ke kan ki makaranta za ki koma, ki fita harkar almajirin nan, ki hada na ki ya na ki ki koma makaranta, duk ran da ya gaji zai sake ki, Ni na san bayan abin da ya faru da dan uwan sa zai sake ki Yakura, dolen sa ma"

Zainab na kallan Anty Sauda ta kada baki ta ce

"Anty Sauda idan kuma na sami mijin aure fa? Shikenan ina ji ina gani sai na bari ya wuce ni?"

"Ina ki ka taba jin mijin wata ya wuce ta?ai matar mutum kabarin sa, toh tunda abin haka ne bari Hajja Aleesha ta dawo sai ki fada mana dan gidan wanene, in ya so duk yanda za a yi almajiri ya sake ki sai a yi, wancan din ya fito a hada auren da na Halitta"

Cewar Anty Sauda hankali kwance. Kamar daga sama ta ji Zainab ta ce

"Ba fa kowa ba ne face Sudais, dama ni Dady ya ce zai daurawa tun farko, kuma dani ya fi dacewa......"

"Zancen banza zancen hofi!"

Ammy ce ta katse ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login