Showing 51001 words to 54000 words out of 58720 words

Chapter 18 - Auren Shehu Book 1 Hausa Novel Complete

25 Jan 2025

614

tsinci kanta ta na mai shigowa Falon da sauri gudun kar sauran yan falon su lura da halin da ta tsinci kan ta ciki. Cikin ran ta fadi ta ke

"Innalillahi kar dai wannan shi ne mijin da Dady ya so aura min? Ya ilahi Allah wallahi da ni ya fi dacewa! Wayyo ya hadu! He should be mine! Da ni ya dace!"
Da kyar ta iya daurewa da gaishe da Shiek ya amsa tare da mata gaisuwa, sannan ta kashe da Sudais, wanda ya amsa ya na mai duban ta da kyau. Tun shigowar ta ya so kare mata kallo, Amma yanda ta ke kallan sa ya sa shi kasa tsayawa ya kalle ta da kyau har sai bayan da ta shigo ta zauna kusa da Falmat. Ko shakka babu ya amince da abu daya, Zainab ta amsa sunan kyakkyawar mace ta ajin karshe, kuma ga dukkannin alamu wayayyiya ce kuma yar gayu, sai kuma akwai abinda ya ke so da be gani a tattare da ita ba, shi kan sa ya kasa gane menene abun, haka kuma ya tsinci kan sa ya na mai fatan Allah ya sa ba ita ba ce matar da Shiek ya zaba masa ba.

Gaisuwa ya mata, ta na cikin amsawa yaji sassanyar muryar Halitta ya ziyarci kunan sa ta sigar sallama wanda shigowar ta yayi daidai ta furucin Ammy na

"Wannan ita ce Zainab, wanda mu ke kira Yakura ita ce babbar su"

"Allah sarki ita ce Malam ya sheda min maganar auren ta ranar da na masa ganin karshe, Allahu akbar duniya kenan"

In da Zainab ta ji kamar ta kurma ihu jin furucin Shiek akan auren ta, Sudais kuwa wani dadi ne ya ziyarci zuciyar sa yayinda ya zubawa Halitta idanu, sanye ta ke cikin hijabi fari kal har kasa, kan ta sunkuye har ta shigo falon ba ta kalli Sudais ba bare ta lura da kallon da ya ke mata

"Alhamdulillah for you, Alhamdulillah, she so MashaAllah! Na gode Abba da wannan zabi na ka"

Cewar Sudais cikin zuciyar sa, wanda ya fadada fara'ar sa dan kuwa ya kasa boye farin cikin sa na ganin Halitta, ta yi masa har cikin zuciyar sa.




*Khadija Sidi*
Auren Shehu


16


Cike da ladabi ta gaishe da Shiek, Wanda ya amsa cikin ran sa ya na mai yabawa da nutsuwar Halitta. Ta'aziya ya mata, sannan ya kara da

"Ga dukkan alamu wannan ce matar da Malam ya bawa Sudais"

Halitta ta sunkuyar da kai yayinda bugun zuciyar ta ya karu, dan tun da ta dunfaro falon ta ji kamar ana mata kallan kurulla, haka kuma jikin ta ya bata wannan da Shiek ya ke magana ne duk da ita ba ta daga ido ta kalle shi ba. Zainab kuwa wani irin bakin kishi ne ya dasu cikin ran ta, ai dama ita Malam ya yi niyar ya bawa Sudais ba Halitta ba, dan haka sai in da karfin ta ya kare.

"Halitta ba, eh ita ce, ya ko yi dace da diya mai mutunci, Halitta ta san darajar manya"

Cewar Hajja Kilish iya gaskiyar ta, hakan ya sa Zainab w???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?atsa ma Halitta harara ta wutsiyar idanu.
"Ai daga gani ma, Allah ya tabbatar mana da alkhairin sa, ya sa a yi damu, in Sha Allah lokacin da mu ka saka da Malam ba za mu saba ba"

Duka su ka ce "Amen" ban da Zainab wacce ta ke ta sakar yanda za a yi Sudais ya zama mamallakin ta.

"Halitta ban ji kun gaisa da angon na ki ba"
Hajja Kilish ta fada ta na mai duban Sudais wanda ya saka ma Halitta idanu ba tare da ya ji kunyar kowa ba. Cike da kunya Halitta ta kai kallan ta gare shi, sai ga idanun ta cikin nasa, ta yi saurin yin kasa da na ta idanun sannan ta furta

"Ina wuni?"

Zainab ta kauda kai dan kishi ji take kamar ta tashi ta bar mu su wajan. Babu abinda ya dada kona mata rai fyace yanda Sudais ke washewa Halitta baki sa'ad da ya amsa gaisuwar ta, tare da mata ta'aziya, dan kuwa rabin fara'ar da ya ke yiyiwa Halitta be yi mata ba. Kasa daurewa ta yi, ita ta fara tashi ta mu su sallama ta shige ciki. Shigar ta ba da dadewa ba Shiek ya mu su sallama, har sun fita sai ga Zara ta dawo, gun Halitta ta je ta dan tsugunna cikin rada ta furta

"Ya Sudais ya ce na karba masa number dinki"

Ta mika mata wayar, da kamar ba za ta karba ba, ganin yanda Ammy ke kallan ta ya sa ta karba ta saka numbar. Cikin jin dadi Zara ta karba tare da fadin

"Na gode Anty Halitta, Allah ya ba mu alkhairin sa"

Ta tashi ta fita. Kamar yanda su Zara su ka tafi da Halitta a baki, haka ma su Falmat da Kori su ka ta yaban Sudais. Har daki Falmat ta bi Halitta. Da ke tun tafiyar Shiek da iyalan sa ta komawar ta daki ta kwanta. Falmat ta shiga da gudun ta, ta fada kanta

"Alhamdulillah wani hani ga Allah baiwa, Allah ya hana ki Usman dan ya ba ki mafi alkhairin sa!"

A hankali ta dago ta na kallan Falmat, sai a sannan ta lura da jajayen idanun Halitta da hakuma hawayen da ke kwance kunci ta. Cike da mamaki Falmat ta ce

"Ya salam! Kukan na menene? Ina dai fatan na rashin Dady ne a wannan rana ta farin ciki"

"Na komai ne Falmat, komai ya cushe min, komai babu dadi, rayuwa babu dadi, rayuwa ta chanza, rayuwa ta zo min ba yanda na ke tsammani ba! Falmat ba na san shi...."

Halitta ta fada ta na mai zubda hawaye, baki Falmat ta bude ta na kallan ta. Ba ta gushe ba ta kara da

"Kin fi kowa sanin burin rai na miji ne gurin yaya ta, ina ji ina gani aka sanya tazara a tsakanin mu. Na daukar wa Dady alkawarin auran zabin shi, kuma ba zan saba alkawarin ba ko da kuwa hakan na nufin rasa farin ciki na, gashi yau an wayi gari babu Dady Falmat......"

Ta karasa ta na mai fashewa da kuka. Tausayin Halitta ne ya rufe Falmat. Rungume ta ta yi cikin rarrashi ta ke magana, ta na fadin

"Ki yi hakuri Halitta, rashin abin da rai ke so ba karamin rashi ba ne, sai dai kuma wani sa'in hakan shi ya fi alkhairi a gare mu, daga ganin Sudais alkhairi ne Halitta, wallahi hankalin kowa ya kwanta da shi, darajar biyayya Allah ba zai bari ki tabe ba Halitta"
"Allah ya sa Falmat, Allah ya sa"

Cewar Halitta ta na mai kokarin tsayar da hawayen da ke zuba daga idanun ta. Haka Falmat ta cigaba da ba ta baki har sai da ta sami nutsuwa ta dena kuka.

Da tunanin Sudais Zainab ta kwana cikin ran ta, washagari da safe ta kasa dakewa, sai ga ta dakin su Halitta ta ci sa'a Halitta ce kadai zaune bisa gado ta amsa wayar Sudais kenan, ta zauna tunani.

Ganin Zainab da yanda ta zo mata mamaki ya rufe Halitta, musammam da ta ga ta zauna kusa da ita har da riko hannun ta, ta ce

"Halitta, dama wani shawara na zo da shii"

Kallan ta ta yi na wani dan sakanni, sannan ta ba ta amsa da

"Toh Yakura, ina jin ki"

"Dama batun Sudais ne, na san ba kya san shi, Kuma idan har ba kuskure na yi ba, na san kin jima da saka wannan almajirin da Dady ya aura min a ran ki....."

Daf! gaban Halitta yayi mummunar faduwa, ta yi saurin zare hannun ta daga cikin na Zainab ta na fadin

"Auzubillallah! Wannan wani irin magana ne Yakura!"

Murmushi Zainab ta sakar mata, kana ta ce

"No kwantar da hankalin ki, ba wani abu ba ne dan kin so shi, ni yanzu ma hakan rahama ya za me min, domin kuwa Allah ya sa min san Sudais, wallahilazim Sudais shi ne mijin da na ke burin samu a rayuwa ta, sam be dace da ke ba, Kuma duka kwamacalar nan Dady ya hada, Allah ya masa rasuwa, kin ga kenan hankali kwance za a iya warware komai. shi wancan almajirin sai ya sake ni, in ya so ya aure ki, ni kuma na auri Sudais....."

"Allah ya sauwake mi ki Yakura, tur da tunani irin na ki!"

Halitta ta katse ta cikin dakiya duk da har ga Allah zuciyar ta ta kwadaitu da zance Zainab. Ba ta damu da irin kallan da ta ke mata ba, ta kara da

"Ina hankalin ki ya tafi ne? Wai yaushe za ki gyara hali ne? Toh ki saurara ki ji ni da kyau, zabin Dady shi ne zabi na, hawainiyar ki ta kiyayi rama na, Sudais miji na ne In Sha Allah, gwara ma ki ruke mijin ki ko Allah ya sa ki dace...."

"Ke dallah malama rufa mana baki! Yen! Yen! Yen!"

Zainab ta daka mata tsawa ta na mai kwatanta yanda Halitta ta yi maganar, ba ta gushe ba ta kara da

"Har ke kin sa! Wani rama gare ki! Ki asuwa cikon benci da ke? Na tabbatar aka jera mu ni da ke ba Sudais ba ko wani da namiji a duniyar nan sai ya dauke ni sau dubu kafin ya dube ki! Ki na nan banza a banza kashi a leda! Nunan rana da ke har kin samu ina shawara da ke! Toh ki saurara ki ji Halitta idan har ban mallaki Sudais ba ban cika diya mace ba! "

Ta tashi fuuu ta fice ta na mai buga kofa. Tagumi Halitta ta yi idanun ta na kallan kofa, tun da take a duniya ba ta taba ganin mutum irin Zainab ba, in dai san kai da san zuciya ne, a komai ita kan ta ta sani sam ba ta tunanin kowa a cikin lamarin ta fyace abin da zai dada mata.

Dakin Ammy ta nufa, ta tarar da Ammy ta fito daga wanka kenan ta zauna za ta shafa mai. Babu gaisuwa babu komai kai tsaye ta ce

"Ammy akwai maganar da na ke so mu yi"

Fasa shafa man ta yi, ta na duban Zainab ta ce

"Ina sauraran ki"

Zainab ta matso gaban Ammy ta zauna, hannayen ta bisa cinyar Ammy, hawaye na zuba daga idanun ta ta ce

"Ammy dan Allah ki yafe min, na yi kuskure, dan Allah ki yafe min, Ammy dan Allah...."

"Na yafe mi ki Zainab, na yafe mi ki duniya da lahira, bayan rasuwar Malam Zainab idan ban yafe mi ki ba me ya rage min a rayuwa? Na yafe mi ki"

Zainab na murmushin jin dadi ta furta
"Ammy na gode, Ammy dan Allah ina neman alfarma"

"Ina jin ki"
Cewar Ammy yayinda ta fara shafa mai.

"Akan auren da Dady ya daura min Ammy, Ammy dan Allah ki raba aure na da.... "

"Ba zai yiyu ba! Auren ki Malam ya daura shi, ba zan taba kashe shi ba Yakura, idan har kin ga auren nan ya mutu toh Usman ne ya sake ki da kan shi...."

"Ammy dan Allah...."

"Yakura!"

Ammy ta katse ta cikin nuna bacin rai, ta kara da

"Kada ki tsaya jayayya da ni!"

Jiki sanyaye Yakura ta amsa da

"Toh Ammy, Allah ya huci zuciyar ki"

Tashi ta yi ta fita ran ta na radidi ba ta taba zaton Ammy za ta juya mata baya haka ba. Ta kasa zaune ta kasa kwance daga karshe hukunci kai maganar dangin Ammy wanda ta tabbatar za su mara mata baya akan kashe auren na ta tayi, dan kuwa babu wanda ya goyi bayan auren, duka sun nuna bakin cikin su karara akan auren Zainab da Usman.

Jin za ta tafi gidan Babbar yayar su Ammy, Anty Sauda. Ammy ba ta hana ta ba, ta dai ce mata kada ta yi dare.

Ta ci sa'a ta tarar da kanwar Ammy wacce su ke kira Anty Hannah ma ta je gidan. Nan Zainab ta saka mu su kuka, ta hada karya da gaskiya duka ta fada mu su. Cike da takaici Anty Hannah ta ce

"Toh shi Malam ma fisabilillahi ya ma zai dauki yar sa, jinin mu ya aurar da ita ga almajirin sa! Dan ruga! Ai ya san tsadar mu, kila ya manta wahalar da ya sha kafin ya auri Hajja Aleesha ne!"

"Toh da ke Allah ba azzalumin bawan sa ba ne ai gashi ya dauke Malam a doran kasa, ke bar kuka wallahi babu wanda ya isa ya sa ki zama da almajiri! Dangin mu ko talaka ba su taba aure ba bare almajiri!"

Anty Saude ta ara ta yafa. Cikin jin dadi Zainab ta shiga share hawayen ta, ta kara da

"Ammy ta ce matukar ba shi ya sake ni da kan shi, ita ba za ta kashe auren ba, Kuma wallahi na san da kyar ya sake ni Anty...."

"Ke rabu da wannan Ammyn ta ki, kila zafin mutuwar mijin na ta ne ya toshe mata kwakwalwa, in ba haka ba ya sha giyar wake ne da za a aura masa kyalleliyar diya, jinin shuwa da Kanuri kuma ya sake ki dan kan sa? Mu nan za mu sa a kawo mana shi tun daga Kano har barracks, dan uban shi sai ya sake ki!"

Cewar Anty Saude da ke mijin ta soja ne mai babban matsayi "General". Anty Hannah da Zainab su ka sa sowa, su na mai fadin

"Yayi matar General"

Zainab ta kara da

"Wallahi shi ya sa na ke kaunar ki Anty Sauda, Allah ya ja da tsayin rai!"

Anty Sauda na mai darawa ta furta

"Ku ji yarinya fa! Ai yiwa akai ne! Yanzu ki na diyar mu sai mu bar ki da auren almajiri? Allah ya mana sutura! Ai ke din matar manya ce, san kowa kin wanda ya rasa, babu talauci a jinin mu, Kuma in Sha Allah ba za mu gan shi ba, ina ki ka ce shi almajirin ya ke yanzu"

"Amen Anty Saude, ai ya na nan gidan mu, shi dan masu gida ba! Wai fa BQ Dady ya ce na koma, wai nan ya ce Ina kwana da shi...."

"Lailahailallah! BQ!"
Su ka fada a tare, Anty Hannah ta kara da

"Yanzu ita Hajja Aleesha sai ta mike kafa ta na bacci diyar ta na kwance da almajiri a BQ?"

Zainab ta rangwabar da kai ta ce

"Wallahi Anty, har ma ta sa na kwashe kaya na, ana gobe Dady zai yi accident ma fa can na kwana...."

"Kin kwana da shi???"

Anty Hannah ta tambaya cikin tsawa.

"Ah ah kofa na rufe ina zan yarda na kwana da shi"

"Atoh yanzu na ji batu, yar tselan uwa da kin yabawa aya zakin ta ki ka shiga hannun wannan gardin!"

Cewar Anty Saude ta na mai hango Usman a idanun ta sanda ya zo ta'aziyar Malam. Sai da Anty Saude ta yiwa Zainab alkawarin za a yi duk yanda za a yi Usman ya sake ta, ko da kuwa hakan ya na nufin za a je har kanon a dauko Usman ne, sannan Zainab ta dawo gida zuciyar tas, dan ta san auren ta da Usman ya kare, sai kuma batun soyayyar da ta ke shirin kullawa tsakanin ta da Sudais.



*Khadija Sidi*
Auren Shehu


17



Da ya ke mijin Anty Sauda a barracks ya ke General, cikin gida kuwa sai yanda ta yi da shi, tuni ya dorar da bukatar ta, in da yayi waya Bokabo barracks ya ba da umarnin dauko masa Usman a daren ranar, ya bayar da adireshin gidan Malam, tare da fasalta kamannin Usman kamar yanda Zainab da matar shi su ka fasalta ma sa shi, ya ce a kawo shi Giwa barracks da ke Maiduguri. Dan haka wajan goman dare sojojin da aka tura su ka nufi gidan Malam.

Bakin gate su ka tadda shi tsaye da alama jira ya ke a zo a bude masa kofa, kamar yanda Zainab ta fasalta yanayin shigar shi, sanye ya ke da riga yar shara, wando wanda shi wanda shi ba gajere ba, shi kuma be kai masa har kasa ba ke kara nuna daudar da kafarsa ta yi, dan kuwa yayi futu futu da shi tsabagen tafiyar kasa da ya sha kafin ya isa gidan Malam. Haka kuma kan sa dauke da rawani da ya zaga har fuska.

Yanda su ka delle shi da hasken mota ya sanya shi saurin kai hannun ga fuskar shi ya na mai kare idanun sa. Su uku ne cikin motar dukan su sanye cikin shiga irin ta sojoji. Biyu da cikin su ne su ka diro daga cikin mota, su ka nufo shi gadan gadan hannayen su dauke da bindiga, dan kuwa yanayin shigar sa, tsayin sa da komai na sa ya tabbatar mu su da shi din ne wanda su ka zo tafiya da.

Sai da su ka karasawa dab da shi sannan ya ankara da yayayin shigar su, hakan nan gaban sa yayi mummunar faduwa musammam ganin bindiga tsirarara a hannun su, ya zabura zai gudu daya daga cikin sojojin ya sa kafa ya tade shi, sai gashi tim ya fadi kasa wanwar

"Gidan uban wa za ka je!"

Cewar Soja yayayinda ya dago shi, ya na mai tisa kyeyar sa ta hanyar hanakada shi da bakin bindiga, be gushe ba ya kara

"Dan uban ka ko tarin ka na ji sai na ci uban ka wallahi! Dan haka salin a lin ka wuce mu tafi!"

Be yi mu su musuba, haka su ka tasa shi gaba su ka sanya shi bayan mota, shigar shi ke da wuya su ka hade hannun sa biyu a baya su ka daure, sannan su ka fidda bakin kyella su ka rufe masa idanu kai ka ce sun dauko dan fashi da makami. Motar su ka tada, hakan yayi daidai da lokacin da Isa ya bude gidan Malam dan kuwa ya ji sanda ake bugawa bawali ya ke, kuma shi kadai ne kusa shi ya sa be bude da wuri ba.

Ganin tashin motar sai yayi tunanin ko na ciki ne ke bugawa su ka gaji su ka tafi, dan haka yayi kokarin tsayar da su, Amma ganin yanda su ka figi motar ya sanya shi fadin

"Toh ko lahira za ku ai sai haka! A sauka lafiya!"

Ya mayar da kofa ya rufe. Suna isa Bokabo barracks aka shedawa General isowar su. Yanda Anty Sauda ta matsa a kawo Usman ya sa General ba da umarnin a kawo shi Giwa barracks a daren. Cikin wani motar sojoji aka saka shi, wajan shabiyun dare su dauki hanyar Maiduguri. Tsabagen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login