Showing 48001 words to 51000 words out of 58720 words

Chapter 17 - Auren Shehu Book 1 Hausa Novel Complete

25 Jan 2025

467

haka ta kara ganin murfin idanun Malam sun motsa, haka ma yatsun hannun sa. Cikin ihu ta ke kwallawa su Zainab wanda ke zauna daga waje kira.

Da gudun su su ka shigo ciki, Ammy na goge kwalla ta ke fadin

"Ku duba ku ga yau Malam ya motsa, Alhamdulillah Malam ya motsa! Maza ki kira likita ku fada masa Malam ya motsa"

Ganin hannun Malam na motsawa Halitta ta fita da sauri sauri gudu gudu kiran likita, Zainab da Zinaru kuwa hannun Malam su ka ruko, daga mai fadin

"Alhamdulillah Daddy dama na san za ka tashi"

Sai mai fadin

"Malam ya tashi, Alhamdulillah Malam ya tashi"

Likitoci uku ne da Nurses biyu su ka biyo Hilitta jin motsawar Malam, a zahirin gaskiya sun ma fitar da rai da tashin sa. Cike da mamaki iko na Allah su ka umarci su Ammy su ba su waje. Nan su ka bar su ciki suna duba Malam, su Ammy kuwa sai kiran yan uwa da abokan arziki su ke suna sheda mu su Malam ya motsa. Sai da su ka dau kusan awa daya sannan su ka sami damar ganin Malam, su Gana da Hajja Kilish tuni su ka karaso jin labarin farin ciki.

Rashin baki be hana Malam aika ma iyalan sa da murmushi ba ganin yanda su ka zagaye shi. An cire masa rubar taimakon numfashi, sai na fitsari da na ruwa ne kadai ya rage jikin sa. Kowa burin sa ya ruke Malam, ko kuwa Malam ya kai kallan sa gare shi. Hajja Kilish kadai farfadowar Malam da kuma ganin sa ya dan kashe mata gwiwa musammam rashin maganar sa, duk da likitoci sun tabbatar mu su cewar a hankali Malam zai fara maganar.

Sai da la'asar su ka yiwa Gana da Madu Sallama domin su koma gida a yi girkin bude baki.

Ana gobe Sallah da sassafe Usman da Isa su ka dauki hanyar Maiduguri, Dan tun da Malam yayi hatsari ba zo sun duba shi ba. Shadaya da rabi su ka isa Maiduguri kai tsaye asibiti su ka wuce. Likitoci sun hana yan dubiya ganin Malam sai dai iyalan sa kadai, Amma Gana yayi magana su ka shiga. Duk da Malam ba ya iya magana, ganin su Usman sai gashi ya na fara'a sosai.

Shi kuwa Usman ganin yanda Malam yayi fari sosai ya kara tsayi ya sanya shi zubda hawaye, cike da mamakin hawayen Usman Gana ya ce

"Ai Malam Usman jikin Malam Alhamdulillah, yayi kyau fa sosai Malam ya sami sauki, ji fa yanda yayi fari sol da shi, kashin bayan sa ne ya sami matsala shi ya sanya ba ya iya zama ko tashi, ba ya iya motsa kafafun sa, Amma ka ga ai yana dan motsa hannun sa, da kuwa ko hannun ma ba ya motsawa wallahi!"

"Allahu akbar, Allah ya bawa Malam lafiya"

"Allahumma amen, in Sha Allah sauki ya fara samuwa, bayan sallah da sati daya ma za a fitar da shi India, mun sami wani asibiti na kwararrun likitoci a can"

Madu ya amsa mu su, ya na duban Usman ya kara da

"Na gane Malam Isa sosai, shi dai Malam Usman ne ban waya ba, ko shi ne sirikin namu ne? Mijin Yakura?"

Dab! Gaban Usman ya fadi jin an ambato auren da ya ke kwana da shi ya ke tashi da shi a kulli yaumin. Gana na mai murmusawa

" Ya ce eh fa shi ne, Malam Usman wannan shi ne Madu, shi ne ke bi na"

Nan Usman da Madu su ka kara gaisawa, in da Madu ya masa nasiha akan hakuri, a cewar sa zama da mace irin Yakura sai hakuri, dan kuwa mace ce mai taurin kunne. Sai da Gana ya dan zungure shi sannan yayi shiru, Usman kuwa cikin ran sa fadi ya ke be da buri da ya wuce a sauwake masa wannan karfen kafan da aka daura masa, wato auren Zainab.

Ana yin azahar su Usman su ka yiwa Gana da Madu sallama, ga mamakin su sai ga Malam ya na ta motsa hannu kamar ya na son yiwa Usman magana, hakan ya sa Gana fadin

"Tun da Malam ya kwanta ban taba ganin yayiwa wani mahaluki yanda ya ke ma ka ba Usman, ka ga fa kamar so ya ke ya ma ka magana"

Cike da tausayawa Usman ya matsa gare shi, yana mai duban Malam ya sanya hannun shi cikin na sa, ganin har lokacin Malam be dena motsa hannun ba Usman ya ce

"Malam Gana shin ko za a sami takarda da biro? Ina ga kamar akwai abin da Malam ya ke son ya fada min"

Gana be ki ta Usman ba ya nemi yar takarda da biro, ya bawa Usman. Hannu na rawa Usman ya sanya biro cikin yatsun Malam, sannan ya dura hannun Malam bisa takardar. Ga mamakin kowa sai ga Malam na kokarin rubutu, amma ina rubutun ba ya fita tamkar na yaro dan koyo. Sai da Usman ya taya shi ruke biro, da ikon Allah sai ga Malam yayi dan rubutu da ajami sanin Usman be iya boko ba. Kalma biyu ya rubuta

"Zainab.... Amana..... "

Ya na rubuta haka ya saki birun, Usman ya daga rubutun da ya fi kama da jagwalgwalon yara, da kyar ya iya karantwa, hanun sa cikin na Malam ya furta

"Na ma ka alkawarin Malam, Ni da Zainab mutu ka raba"

Cikin nuna jin dadi Malam ya murmusa. Jiki sanyaye Usman ya tura takardar da Malam yayi rubutu cikin aljihun sa, su ka yi sallama su ka tafi. Tafiyar su ba da dadewa ba Ammy da Falmat su ka ta zo. Ganin yanda Malam yayi fari sai murna ya kamata, fadi ta ke

"Kai Alhamdulillah ji yanda jikin Malam yayi fari, yayi kyau wallahi"

Madu ya ce

"Wallahi fa Hajiya, Amma tunda ya kwanta ba mu taba ganin fara'arsa ba kamar na yau da wannan bawan Allah Usman ya zo"

"Allah sarki ashe ya zo"

Cewar Ammy cikin faduwar gaba, dan kuwa ji ta yi ba za ta iya jiran Malam ya warke ba, gwara ta nemi yafiyar sa ko ta sami sauki cikin ran ta. Kamar yanda ta kudiri niya, sai da ta nemi gafarar Malam kafin ta tafi, ta na magana ta na zubda hawaye hakan ya sa Malam girgiza mata kai, sai da ta ga ya na murmushi sannan ta gamsu. Duk sanda ta dan gifta ta wajan gadon sa sai ta ga ya ruko hannun ta, hakan ba karamin dadi ya ke mata ba, ta san ta isa matar so, tunda ciwo be hana Malam nuna mata so da kauna ba. Cikin so da kewar Malam ta yi masa sallama, har ta juya za ta tafi ya kara ruko hannun ta. Ammy na mai darawa ta furta

"Ka yi hakuri Malam, da sassafe zan dawo na kawo maka tuwan sallah in Sha Allah"

Malam na darawa yayinda kwalla ya dan gangaro daga idanun sa ya dan motsa kan sa. Ita ma Ammy kwallan ce ta fara cikowa idanun ta, ta yi saurin zame hannun ta ta fita, idanun Malam na kan ta har ta fice.

Daren ranar da ke daren duba watan sallah ne gari sai hidima ake. Gana da Madu ma zaman hira su ka yi bayan sun sha ruwa, hiran Usman da auren shi da Zainab su ke. In da Madu ke nuna jin dadin shi akan hukuncin da Malam ya yanke na auren Zainab, cewar shi

"Ka san Allah Gana da ka san yanda yarinyar nan Yakura ta lalace a Instagram da sai ka koka, ai na nuna maka wani hotan ta ka musa min ka ce ba ita ba ce, har da kwaba ta kar da na bari Malam ya ji, ai ga irin ta nan, yanzu da komai ya fito zahiri wa gari ya waya? Bari ma ka ga na nuna maka wasu da ga ciki"

Ya shiga Instagram ya na neman shafin Zainab, Amma ga mamakin sa babu shi babu alamar shi. Cikin cije ya yatsa ya ce

"Kash yar banza ashe ta yi deleting, Shi ya sa Hajiyar mu ta birgeni da ta hana su Zinaru kowani Social Media! Wallahi ba karamin jan hankali yara mata ya ke ba, musammam masu rawan kai irin Yakura!"

Gana na mai mikewa bisa carpet din da su ka shimfida tsakiyar daki ya ce

"Toh sai dai Allah ya dada kare mana su, ba dai an aurar da ita kowa ya huta ba, Madu bari na dan mike kadan, dan Allah ka sheda min idan an ga wata, Allah ya sa ba talatin za a yi ba, azumin asibiti babu dadi"

Madu ya amsa da "toh" yayinda ya cigaba da danne dannen wayar sa. Cikin yardar Allah aka sanar da ganin wata, gobe sallah. Madu ne ya kira su Hajja Kilish ya fada mu su, tare da jaddada mu su lalle a kawo mu su karin kumallo da wuri.

Ranar Sallah rana ce da iyalan Malam ba su taba manatawa da ita ba. Motsin Malam ne ya tada Gana da asubar fari, ganin halin da Malam ke ciki, jiki sankare idunun sa sun kafe ya sanya shi ihu ya na salati ya ke fadin

"Madu Malam! Innalillahi wainnailaihi rajiun! Madu Malam, Madu kira likita!"

Hakan ya sa Madu fita a guje. Hannun Malam Gana ya ruko, ya na hawaye ya ke fadin

"Innalillahi wainnailaihi rajiun! Lailahailallah Muhamadur rasulillahi! Lailahailallah Muhamadur rasulillahi!"

Malam na mai damke hannun Gana ya tsinci kan sa ya na mai amsawa da karfi ya furta

"Lailahailallah Muhamadur rasulillahi sallahu......"

Sai tsit, Gana ya na ji ya na gani an zare ran Malam, kullu nafsin zaikatul maut


*Khadija Sidi*



*Khadija Sidi*Auren Shehu

(15 continuation)




Kafin likita ya karaso har Gana ya sa tafin hannun sa bisa fuskar Malam, ya na mai karanto adduar neman rahama ya rufe idanun Malam, tare da jan zani ya rufe fuskar sa, sannan ya zauna a kasa dirshen ya na kuka kamar kankanin yaro.

Ko da Madu da likita su ka shigo, Madu ya ga Malam rufe sai ya rufe Gana da fada, akan wani dalili Gana zai rufe Malam! Yaushe ya zama likita! Shikenan ya kashe mu su Malam!

Gana ya cigaba da kukan sa ba tare da ya kula Madu ba, wanda sam ba cikin hayyacin sa ya ke ba. Likita be fasa yaye zanin da Gana ya rufawa Malam ba, ya sanya safar hannu na roba, ya dan kara duba gawar ya tabbatar ya cika da gaske, sannan ya zare robar ruwan da ke hannun Malam, ya fara kokarin zare na fitsari wanda ba a yi cikakeken awa daya da saka shi ba, Amma azarbar fitar rai ya sa shi cika har ya na komawa sama.

Ganin likita ya kara mayar da zani ya rufe Malam nan Madu rungume gawar Malam, ya na fadin

"Hasbinallahu wani'imal wakilu! Allah ya yafe maka kurakuran ka Malam! Allah ya ji kan ka! Allah ya sa annabi ya san da zuwan ka!"

Cikan kankanin lokaci aka hade komai na Malam. Gana ne ya kira Hajja Kilish ya ce kada su kawo mu su abinci, ga su nan ma an sallami su, Malam ya sami sauki, gida za su taho. Ita dai ta amsa da toh, azahiri kuma jikin ta ne ya dau rawa yayinda bugun zuciyar ta ya karu, dan kuwa jikin ta ya bata akwai abin da ya faru, hakan nan ba za a sallame su ba, in ba dai saukin mutuwa ya samu ba. Aikuwa zatan ta ya tabbata sai ga su Gana da gawar Malam, sun shimfide mata tsakar falo.

Hajja Kilish neman kuka ta yi ta rasa, ta na zaune daidai kan Malam ta ke tsawatar su Ammy da yara, wanda su ne su ka fi kowa ihu da kuka, fadi ta ke

"Kul kada ku kara mana ihu a nan! Sakayyar da za ku masa kenan? Ku dena mana kuka na ce!! Yanzu Aleesha har da ke? Malam fa ya na jin ku!"

Zinaru kuwa aljanu ta ringa tayarwa. Hajja Kilish tare da Gana da Madu ne su ka wanki gawar Malam, su ka masa sutura. Ko da aka dauki Malam za a fita da shi Hajja Kilish ta tashi da sauri za ta ruko makarar amma ina tuni ta yanki jiki ta fadi sumammiya, ba ita ta farfado ba sai bayan da aka sallaci Malam aka kuma kai shi gidan gaskiya. MashaAllahu Malam yayi mutane matuka. Su Usman da daliban Malam ba su sami janaiza ba, dan kuwa sai da aka yi awanni da birne Malam su ka iso. Sun zubda hawayen rashin Malam kwarai sanda aka kai su kabarin Malam su ka masa addua.

Kamar yanda Malam ya ke yawan fada idan ya mutu kar a masa zaman makoki, su Gana sun yi kokarin hanawa amma ina hakan ya ki yiyuwa, kullum gidan cike ya ke fal da jama'a, yan unguwa, yan uwa da abokan arziki abin takaici shi ne yanda gidan mutuwar ya so ya zama gidan biki, iyalan Malam da su aka yiwa rashi ne kadai ke cikin bakin ciki da kuka, in da ake bikin sallah su kuma su ke fama da bakin ciki da alhinin rashin Malam. Ranar da Malam ya cika kwana uku su Usman su ka nemi yiwa su Ammy gaisuwa, duka iyalan Malam sun fito an gaisa, ban da Zainab wacce a cewar ta zafin mutuwar Malam daya ya ke da zafin ganin fuskar Usman. Ganin ba ta fito ba Usman be tambayi ina ta ke ba, yayiwa su Ammy gaisuwa su ka juyo Kano ya na mai tunanin yanda rayuwa za ta kasance akan alkawarin da ya daukarwa Malam.

Ranar da Malam ya yi bakwai Ammy ta so komawa Kano, yan uwan Malam ne su ka ruke ta da ta zauna nan gidan Malam ta gama takaba tare da yar uwar ta Hajja Kilishi, tunda ko ta je Kano ma gun wa za ta koma? Duk yan uwa suna nan Maiduguri. Da wannan ta hakura ta zauna.

Sai da Malam ya yi sati biyu da rasuwa, jama'a ka dan dauke kafa. Gidan ya fara shiru, gashi babu wanda ya ke cikin walwala musammam mutum hudu, kusan za a ce mutuwar Malam ta fi duka, wato Hajja Kilish, Madu da Gana, sai kuma Halitta. Gaba daya ta rame ta lalace, sai ta kara fari da manyan idanu.

Zainab kuwa bayan mutuwar Malam, babban burin ta shi ne a gama alhinin mutuwa a zo a raba auren ta da Usman, dan kuwa ko sama da kasa za ta hade ba za ta yarda da auren ba, musammam yanzu da aka wayi gari babu Malam a doran kasa.
Da la'asar sakaliya Madu da Gana su ka karbi bakwancin Shiek tare dan shi Sudais da kanan sa mata biyu, Zara da Ummi, kasancewar sanda aka yi rasuwar ba sa nan suna Saudiya. Bayan sun yiwa su Ghana gaisuwa ne Madu ya shigar da matan cikin gidan wajan su Hajja Kilishi, tare da sheda mu su cewar Shiek da Sudais na Falon waje, idan sun shirya za su shigo su yi mu su ta'aziya.

Ya ko ci sa'a Hajji Kilishin zaune ta ke tare da Ammy. Kanan Sudais su ka mu gaisuwa, tare da neman su Zinaru wanda dama su su ka sani, duk da dai suna kwadayin ganin amaryar yayan su da aka ce diyar amaryar Malam ce da ke zaune birnin Dabo. Zinaru da Kori ne su ka fito jin zuwan su Zara. Suna cikin gaisawa ne Madu ya dawo biye da shi Sudais da Shiek ne.

Bayan sun yiwa su Hajja Kilish gaisuwa, Shiek ke tambayar Ammy ina su Halitta su ke, da fatan ba su koma Kano ba ko. Ammy ta ce
"Eh suna nan tare da ita, Kano ai ta yi mana nisa in ba dai Zainab wacce ke da miji a can ba, bari a kira su, Kori kira yan uwan ki"

Kori ta tashi ta shiga kiran su. Tun tashin ta gaban Sudais ke faduwa, ya zubawa kofar da Kori ta fita idanu, da ke shi ne ke zaune kurar da ke kallan kofar, Shirin ganin matar da Shiek ya zaba masa ya ke cikin zulumi.
Jim kadan Kori ta dawo biye da ita Falmat ce sanye da hijabi har kasa, kallo daya Sudais ya mata ya tabbatar ba ita ba ce amaryar ta sa tsabagen kuruciya da fuskar Falmat ta nuna karara duk da kiban da ta ke da shi. Cike da ladabi ta durkusa har kasa ta gaishe da Shiek da Sudais. Su ka amsa tare da mata gaisuwa. Ammy ta gabatar da Falmat a matsayin autar ta.

Zainab wacce har cikin ran ta ba ta yi niyar ganin baki yau ba, da kyar ta tashi daga kan gado, bakar abaya ta ja ta dora bisa yar karamar rigar da ke jikin ta, ta ja mayafin abayar ta rufe kan ta. Za ta wuce ta hango Halitta cikin dakin su, bisa sallaya. Tun da ta ji sakon isowar Sudais ta ji wani bakin ciki ya kara ziyartar zuciyar ta, ta ma kasa tashi bare ta fito su gai sa.

"Malama wanda aka bawa ke ya zo,, you better bring your ass to the parlour, aha bari na je na ga wani local champion Daddy ya bawa"

Cewar Zainab cikin tsoka na, ta wuce ta na yiwa Halitta yar dariyar mugunta. Tun kafin ta karasa falon ta fara jin wani irin ni'mantaccan kamshi, zuciyar ta daya ta sanya kafar ta hakan yayi daidai da hada idanu da shi, gaban ta yayi mummunar faduwa har ta tsinci kanta ta na mai fadin

"Hasbinallahu wani'imal wakilu!"

Ta sha ganin maza wanda su ka amsa sunan su maza ma su kyau, Amma ba ta taba ganin wanda ya tafi da imanin ta kamar Sudais. Sudais wankar tarwada ne mai duguwar fuska da ke dauke saje da gemu baki wuluk har sheki ya ke, ba wani dogo ko siririn hanci gare shi ba, girma da tsayin hancin sa yayi dadai da fasalin fuskars sa, haka kuma idanun sa da ke manya dan ko ita Zainab ba za ta nuna masa kyawun idanu ba. Kasancewar zaune ya ke kan kujera be boye tsayi da fadin da ya ke da shi ba, sai ma kwarjini da ya mata. Idan ko gayu da wayewa ne kallo daya za a yiwa Sudais a san gidan shi aka zo, murmushin da ya sakar mata, gefan kumatun sa biyu su ka lutsa wato alamun dimpol ne ya dada rikita Zainab wacce ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login