Showing 33001 words to 36000 words out of 58720 words

Chapter 12 - Auren Shehu Book 1 Hausa Novel Complete

25 Jan 2025

463

ta ba, dan kuwa ba na jin zan iya tunkarar ta da wannan maganar ta tashin hankali cikin dare haka. Can turkar shanu na na je, Nan na kwana amma ban runtsa ba, yanda na ga rana haka na ga dare, sai da asuba ta yi sannan bacci ya fara dauka ta, ban kai ga runtsawa ba korarin Bello da ya zo ya na tashi na ne ya katse min baccin.

Yanda ya ke maganar ya na mai nuni izuwa gida ya sanya ni kara tsanar Baffa Mudi, kiri kiri ya nakasa yaro karamin dan kawai san mulki da san zuciya, ban san sanda na fara zubar da hawaye ba, shi kuwa Bello da yayi tunanin sakon da ya isar min ne ya sa ni hawaye tuni ya fara kokarin lallashina, ya na mai dafa kafada ta, kafin daga bisani ya fara jan hannu na.

Sai a sannan na fahimta lalle akai wani abun tashin hankali da ke faruwa a gida, da sauri na tashi, ko silifa ban saka ba. Bello na janye da hannu na mu ka isa gida. Mutane ne fal bakin kofar gidan wasu na alwala wasu kuma tabarma su ke shimfidawa, ganin Baffa zaune dirshen a kasa ga Tanko gefe ya na matsar kwalla, jama'a na ta min sannu da sai hakuri ya sanya na karasa cikin gidan da sauri.

Cikin gidan ma tashin hankali na tarar, kuka da kurarin mata ne ke tashi, haka ina tsallake mata na isa ga bukkar Iya ta, Nan na iyi idu biyu da gawar Cangwai kwance, gefe kuwa Iya ta ce ri?e da jinjirar da ta haifa, cikin dare rai yayi halin sa bayan ta haifi diyar ta mace. Kalaman Cangwai ke dawo min sanda ta ke rokan karda na halaka ta, za ta hade kayan ta tabar Rugar Shehu ba za ta sake dawowa ba, Wana sanin barin ta ita kadai da tsohon ciki ya mamaye ni, haka tsananin tsanan Baffa Mudi da shi kan sa mulkin da ya ke kwadayi har ya kai ga saka diyar shi cikin halak.

Bayan an shirya Cangwai ana shirin a fito da ita, sai ga Baffa Mudi ya shigo, ya nemi a bar masa gawar zai gana da ita kafin a fito da ita. Tun da ya kebe da gawar hankali na ya kasa kwanciya. Ya dan jima ciki kafin ya fito ya ce za a iya fito da ita.

Hankali na ya kasa kwanciya dan haka, kafin a kai da fito da ita na ce da su su dakata, Iyar Cangwai ta ce ban isa ba, tun dazu me ya hana na zo na mu yi sallamar karshe sai yanzu? Iya ta da sauran kishiyoyin ta ne su ka sa baki, haka ba a san ran Iyar Cangwai ba na shiga dakin. Ranar na yi abin da ban taba tsammanin zan iya ba, Yanda gaba na ke faduwa da hawayen da ke kwaranya daga idanuna be sa na fasa kunce suturar da aka yiwa Cangwai ba, hannun ta na hagu na yi arba da wani abu dunkule an daure shi da bakin kyalle, na yi sauri na sunce, daga waje ina jiyo Iyar ta na kuka da kururuwan na ki fitowa a tafi a rufe Cangwai.


Cikin azama na tura abun cikin wandan saki na, hakan yayi daidai da shigowar Iya ta, ganin na bude Cangwai ta hau ni da fada, tare da taimakon ta mu ka yi sauri mu ka rufe ta, cikin kankanin lokaci aka sallace ta, mu ka je aka rufe ta.


Cikin dare na sami Iya ta zaune dakin ta rike da jinjirar da Cangwai ta bari, ganina ta yi yunkurin bani yarinyar, Amma na ki karba. Hakan ba karamin tunzura Iya ta yayi ba, a zatan ta zafin mutuwar Cangwai ya sa na tsani jinjirar da ta bari. Nan kuwa kwashe komai na sheda mata, har da abinda aka kunsa hannun gawar Cangwai.

Mamaki da takaici ne ya rufe iya ta, kuka ta ke cike da takaicin zaluncin da aka yiwa Bello. Tare mu ka kunce abin da na ciro daga hannun gawar Cangwai, laya ce mai dauke da sunana da sunan baro baro da rubutun ajimi, an rubuta

"Kamar yanda gawar nan ta bar duniya, haka za ka bace a doran kasa Usman , kamar yanda wanan gawar ta ba za ta taba shakar iskar duniya ba, haka kai ma na za ka taba zama Shehun Rugar Shehu ba Usman"

Ko da na gama karantawa Iya ta ba karamin tashin hankali da rudani ta shiga ba, da kyar na samu na kwantar mata da hankali, na kuma umarce ta da kar ta shedawa Mahaifina halin da ake ciki, ta bari mu sami mafita a tsakanin mu, dan kuwa halin da Baffa Mudi ya nuna zai aikata komai dan ya cima burin shi na san rai da san duniya.

A wannan daren Iya ta ta yanke hukuncin da ya sa yayi sanadin bari na gida har na ke zaune tare da ku a yau, Iya ta ta umarce ni da na sakarwa Baffa Mudi Shehuntakar Rugar Shehu, ta Umarce ni da tunda a nashi tunanin ya birne gawar diyar sa da surkullen watsa ni uwa duniya, matukar ya ga ban tafi ba zai fahimci asirin sa ya tonu, ya kuma cigaba da kulla zalunci har ya kai ga cin nasara, da na bi uwa duniya ba a cikin hayyaci ba, gwara na tafi da niyar neman ilimi, dan haka ta na so na hada kaya na, na shiga arewacin Nigeria, duk gidan da na ga Malami na tabbatar na nemi ilimi daga gare shi, haka kuma duk sanda na canza sheka na sami hanyar sanar da ita ko da kuwa hakan ya na nufin ziyartar ta ta shigar batda kama, ita kuma muddin ta san in da na ke za ta turo min Bello duk sanda bukatar haka ya taso. Ina ji ina gani haka ta hade kaya na, ba tare da na yiwa Mahaifina sallama ba na baro Rugar Shehu na shiga uwa duniya..."

Usman ya nisa, ya na mai duba Malam ya kara da

"Hakan ba karamin ciwo ya yiwa Mahaifina ba, a tunanin shi mutuwar Cangwai ya sa na bi uwa duniya, tun ya na cigiya har ya sadakar ya fawwalawa Allah. Shekara goma sha biyu kenan da barin Rugar Shehu, kamar yanda Iya ta ta umarce ni, na kan ziyarce ta duk sanda na sami dama cikin bat da kama, haka kuma duk in da na ke tana da masaniya akai, ina barin mata bayanin wajan a rubuce, ta kan aiko Bello duk sanda bukatar haka ta taso. Allah yayiwa Mahaifina rasuwa bayan shekara uku da barin Rugar, yanzu haka Baffa Mudi ne Shehun Rugar"

Usman ya kare maganar cikin kewar Iyar sa da bakin cikin mahaifin sa ba tare da sun samu sun gana ba. Gaba daya falon babu wanda be tausayawa Usman ba, Musammam Halitta wacce har hawaye ta zubar saboda hakan. Cikin jimami Malam ya nisa ya ce

"Da farko dai ina ma ka ta'aziyar rashin mahaifin ka, da kuma matar ka. Ba kai kadai ka ci amana ta ba, hatta yar ciki na ta ci amana ta, idan kuwa haka ne na yafe ma ka duniya da lahira......"

Karar wayar Malam ne ya katse maganar da ya ke, ko da Malam ya duba ya ga makocin sa kuma daya daga cikin amintattun abokan sa ne Alhaji Sidi, ya daga wayar, bayan sun gaisa ya ce da shi ya jira ana zuwa. Bayan da ya aje wayar ya umarci Jauro ya je ya budewa Alhaji Sidi gate, ya shigo da shi ciki. Cikin himma Jauro ya fita, in da Malam ya dakata da jawabin shi har lokacin da Jauro ya shigo biye da shi Alhaji Sidi tafe.

Alhaji Sidi na mai bawa Malam hannu yayinda ya zauna kusa da Malam ya ke tambayar abin da ke faruwa cikin al'ajabi, Da safiyar nan ya ji dan sa ya shigo da wani labari hakan nan babu dadin ji, wai an kama wata yarinya ta na haurowa daga gidan Malam, shin menene gaskiyar maganar?

Murmushin yake ne ya maye fuskar Malam, hannun sa cikin na Alhaji Sidi ya ce

"Zan ma ka bayani Alhaji Sidi, Amma kafin nan na ji dadin zuwan ka har rai na, domin kuwa ina da bukatar shedu, zuwan ka ya cika min shedun na ke bukata"

"Shedu? Na me kuma Malam?"

Alhaji Sidi ya tamabaya cike da mamaki.


"Kar ka damu Alhaji, a sannu za ka fahimci komai, ina kai Usman matso nan kusa da ni"

Cikin shakku Usman ya taso ya zauna gaban Malam in da ya nuna masa. Malam na mai dafa kafadar sa ya ce

"Usman a daren jiya ka yi min abinda babu wani mahaluki da ya taba yi min cikin duniyar nan, ka rufa min asirin da diyar cikina ta so tona min a duniya, ba zan yi butulci akan jarabawar Allah ba, Allah ya jarabci annabin sa, annabi Nuhu AS ta hanyar dan sa, sa bare ni da ba ko wan kowa ba, Amma akwai alfarma daya da na ke so ka min...."

Ya karasa maganar ya na mai duban Usman. Cikin girmamawa da kaskantar da kai Usman ya ce

"Malam duk abinda ka ke so ni mai yi maka ne, wanda ya ba ka ilimi nan duniya ai ya ma ka komai"

Cikin jin dadin amasar da Usman ya ba shi Malam ya ce

"Ina so ka taimaka ka auri diya ta Zainab..."

A firgice Usman ya dago ya kalli Malam, haka ma Halitta da su Ammy, gaba daya falon babu wanda be girgiza da maganar Malam ba, Zainab kuwa ji ta yi gaba daya dodon kunnan ta ya toshe tsabagen yanda maganar ta doki kunnan ta. Cikin in'ina Usman ya furta

"Ma...l..am"

Alhaji Sidi kuwa mamaki ne ya sanya shi furta

"Me ke faruwa haka? Wata Zainab ka ke nufi ne haka?"

"Diya ta ta ciki na, ka ga wannan bawan Allah da ke zaune gaba na? Shi ne kadai zai iya rayuwar aure da waccar yarinyar asiri na ya rufu, dan kuwa ya rufa min asiri a yau fiye da tunanin ka! Wannan dalilin ya sa na yanke hukuncin daura ma sa ita ta zame masa halak malak ko mutuwa na yi na san na fita hakkin ta"

Jin haka tuni Zainab ta fashe da kuka mai tsuma zuciya, fadi ta ke

"Dan Allah Dady ka yafe min kar ka yanke wannan danyan hukuncin a kai na, dan Allah Ammy ki sa baki, dan Allah Halitta ku taimaka min, Alhaji ku sa baki"

Hawaye ke zuba daga idanun Halitta daya na bin daya, kiri kiri ta na ganin mahaifin ta na shirin mata yankar kauna tsakanin ta da masoyi abin kaunar ta. Cike da kishi Jauro ke duban Usman, da ya san Malam zai yanke hukuncin haka da shi ma ya ce Zainab matar shi ce, yanzu gashi Usman da ya zo ya tarar da su cikin gidan ya sami garabasa kara zube.

"Malam dan Allah kada ka yanke hukunci cikin gaggawa haka, Yakura jinin ka ce, kada ka bata rayuwar Yakura"

Ammy ce ke magana cikin magiya. Idan Malam ya ji Ammy toh sam be nuna alamun da shi ta ke ba. Ya na duban Usman ya ce

"Kai na ke tsimayi Usman, shin ka karba? Za ka iya auren diya ta?"

A hankali ya daga idanu ya kai kallan sa ga Zainab wacce ta ke kuka mai fitar da sauti, har ga Allah be taba jin wani abu na so game da ita ba, bare yayi tunanin aure zai shiga tsakanin su. Yanda ta ke kallan sa ne ya sa shi saurin kau da kai gefe

"Usman?"

Malam ya kira sunan sa da kakkausar murya.

"Na'am Malam, na yarda na amince, sai dai matsalar abu biyu ne"

"Ina sauraran ka Usman"

"Banda kudin sadaki, haka kuma banda muhallin da zan iya aje mata Malam"

Jin haka Malam ya dara tare da fadin

"In dai wannan ne matsalar ka toh Alhamdulillah, na tabbatar ka haddace Riyaadul Saliheen?"

Cike da girmamawa ya gyada kai alamar eh.

"Toh Alhamdulillah, na yanke maka wannan littafin a matsayin sadakin Zainab, ina so ka koyar da ita wannan littafai, batun muhalli kuma ga BQ nan babu kowa da ciki, zan sa a gyara maka ku zauna, Allah bashi idan ka yi na ka sai ku tashi ku koma can ko?"

Baki bude Ammy ta ke duban Malam har ya kare jawabin sa, ba ta taba tunanin Malam zai iya kaiwa matuka wajan wulakanta ta da yaran ta ba sa sai a yanzu.

"Innalillahi wainnailaihi rajiun yau! Innalillahi wainnailaihi rajiun! Innalillahi wainnailaihi rajiun!"

Salatin da Zainab ke yi kenan cikin kuka, dan kuwa ji ta ke kamar rayuwar ta ce ta zo karshe. Halitta ma kukan ta ke haka ma Falmat wacce tausayin yar uwar ta ya maye zuciyar ta. Alhaji Sidi na mai gyaran murya ya ce

"Malam ran ka a bace ya ke, ka tuna yanke hukunci cikin fushi....."

Hannu Malam ya daga masa, ganin haka Alhaji Sidi yayi shiru. Kana Malam ya ce

"Malam Usman dama kai namiji ne, kai kan ka mai karSa ma kanka aure ne a kaidar shari'a ka isa ka karbarwa kan ka aure, ga shedu uku nan, Jauro, Isa da kuma abokina Alhaji Sidi, dan haka idan ka shirya sai a hanzar ta a daura auren ko?"

Kai Usman ya gyada abun ya zo masa kamar almara. Haka kuwa Zainab ta na ji ta na gani Malam ya daura mata aure da Usman, akan sa dakin koyar da ita littafin Riyaadul saliheen. Ana shafa fatiha Zainab ta zube mu su nan sumammiya.Auren Shehu

11



Ganin Zainab a sume da kururuwan kukan su Ammy sam be sa Malam ya motsa ba. Alhaji Sidi ne ma ya kawo doki ya na mai umartar Usman yayi maza ya dauko ruwa daga cikin fridge din Parlour. Ammy da Falmat ne ke jijjiga kafadun ta, Halitta kuwa kasa motsawa ta yi, hukuncin da Malam ya yanke ba Zainab yayiwa ba, gani ta ke tamkar ita Malam yayiwa gwale gwale, ta na ji ta na gani wanda ta ke so, ta ke kauna ya zamanto miji ga yayar ta uwa daya uba daya.

Yayyafin ruwan sanyin da ya sauka fuskar ta ya sanya ta farfadowa, a hankali ta bude idanun ta.

"Alhamdulillah, Malam ta farfado ka yiwa Allah ka warware auren nan, Alhaji Sidi ka sa ba ki!"

Ammy ke magana cikin magajiya ta na mai rungumo Zainab wacce ta ke ji kan ta na sarawa tsabagen ciwon da ya ke ma ta. Maganar da Ammy ta ke yi ne ya sa ta farga ta tuna da halin da ta ke ciki, kuka ta saki mai tsuma zuciya ta na fadin

"Dan Allah Dady na tuba, ba zan kara ba, Dan Allah Dady kar ka daura min wannan nauyin a kai na Dady!"

Idan dutse na motsi toh Malam ya motsa, ko nunawa ya san da shi ta ke bare ya amsa mata be yi ba. Usman wanda kamar yanda Zainab ke kukan bakin ciki shi ma har ga Allah wannan auren da aka daura ma sa be so ba, shi ya fara zamewa ya fice daga parlour, Jauro da Isa su ka bi bayan shi. Ammy kuwa Alhaji Sidi ne ya ce su dan ba shi wuri su zanta da Malam in Sha Allah za a sami mafita. Zainab kwance jikin Ammy kamar mai jinya haka su ka fice ya rage daga Malam sai Alhaji Sidi.

Alhaji na duban Malam ya ce

"Malam kai fa mai sani ne, ka sani cewa yanke hukunci cikin fushi da gaggawa na tare da dimbin danasani, shin me wannan yarinyar ta aikata da har za ka yanke wannan hukuncin mai nauyi akan ta Malam?"

Ga mamakin Alhaji Sidi sai ga Malam ya na zubda hawaye.

"Ya hayyu ya qayyum! Munin abun ya kai haka?"

Cewar Alhaji Sidi cikin alajabi. Kai Malam ya girgiza, kana ya ce

"Alhaji Sidi ka na daya daga cikin amintattuna na, abokin arziki da amana, Alhaji Sidi ba zan boye ma ka komai ba. Na kasance mai rauni aka 'ya'ya, musammam ma Zainab. Allah ya jarabce ni da diya, sai dai na ce Alhamdulillah. Amma Zainab ba ta min adalci ba, ina nan idanuna kan 'ya'yan wasu, Wai ni Malami mai wa'azi ashe tawa diyar wacce na fi yarda da ita ta nan ta na barna a bayan ido na, Innalillahi wainnailaihi rajiun.....!"

Nan Malam ya kwashe komai ya fadawa Alhaji Sidi, ya kare maganar da

"Yaron da zai kare mutunci na haka, wanda zai rufa min asiri haka me zai hana na bashi ita? Yanda ya ke da kyawawan halayya ina kyautata zaton idan har Zainab ta zauna karkashin sa, ta nemi wannan gatan ta take da shi ta rasa za ta nutsu Alhaji Sidi, haka kuma Na yi imanin Usman zai ruke ta da amana"

Cikin jimami Alhaji Sidi ke jinjina kai, kana ya nisa tare da fadin

"Innalillahi wainnailaihi rajiun! Zainab ba ta kyauta ba, duk da dai har da sakacin ka Malam, ai ba a shedar dan yau Malam, ka yarda da Zainab da yawa, haka kuma Hajiya ta yi sakaci duk dai rabin rayuwar yarinyar nan ba a gida ta ke yi ba, Amma da ana bibiyan ta duk sanda ta dawo da duk wannan masifar ba ta afku ba Malam, yardar ta yi yawa, sakacin yayi yawa!"

"Ka duba yanda na tsani kare Alhaji Sidi, har karnuka na debo na sa a gidan nan tun sanda mu ka fara zargin ana hauro mana gida, ashe dai tawa karyar ta gida ce......"

"Waiyazubillah!"

Alhaji Sidi ya katse Malam cikin hanzari, be gushe ba ya kara da

"Ka kausasa harshe da yawa Malam, Amma wani hanzari ba gudu ba, yarinyar nan haura katanga ta ke, ta na fita yawan dare, shin ka tambaye ta ina ta ke zuwa? Shin iya ka yawan abun ya tsaya? Ta na nan matsayin ta na budurwa ko kuwa dai istibiraqi ya hau kan ta?"

"Diya ta ba mazinaciya ba ce! Na yi imani diya ta ba za ta aikata zina ba kamar yanda ni ma ban taba aikata zina ba "

Malam ya bashi amsa kai tsaye. Kai Alhaji Sidi ya dafe, cikin nuna bacin rai ya ce

"Ga ba irin ta ba! Ka na shedar gaibu kai tsaye! Ka taba tunanin Zainab za ta iya tsayuwa da wani da namiji? Bare kuma har ta na yawan dare? Amma yanzu ina gari ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login