Showing 1 words to 3000 words out of 61846 words
Chapter 1 - Nakasa B Kasawaba Book 2 Complete Hausa Novel
[9/9, 9:04 PM] +234 806 222 4030:
Cikin tsananin tsoro da mamaki. Maryam ta rumtse idanunta da azaban k'arfi tare da cewa.
"Innalillahi waInna'ilaihirajiun. Zaleeha kashe kanki zakiyi baki da hankali ne?."
sai kuma duk falon ya ricab'e sabida. Ihun da Zahira keyi tanayi tana tsalle da burburwa tare da cewa.
"Shike nan ai an huta."
Aunty Lubna kuwa da Ziyada ruggume juna sukayi tare da rumtse ida nunsu,
Ganin yadda Zaleeha tasa knife d'in ta yanke wuyan hannunta tare da kurma ihu mai gigitarwa, tuni jini yaketa tsiyanyowa yana zubowa har k'asa.
Cikin wani irin tsoro da al'ajabi da firgici ya Ahmad yayi sauri ya k'arasa gabanta, tare da sa hannu ya fizge knife d'in data saitashi kan jijiyar mak'ogoronta.
Ihun Mama da Yayarta Ruda da Zahira ya cika gidan gaba d'aya.
Mamy da Aunty Lubna da Ziyada ma kukan sukeyi mai cike da tsoron ganin Zaleeha zata aikata kisan kai.
Ga kuma ihun da itama Zaleehan takeyi tanayi tana tsalle tana.
"Wallahi zan kashe kaina! gwara in mutu kowa ya huta! In yaso in na mutu a raba gawata biyu a kai musu dukansu biyu kowa a bashi tsagi d'aya."
Ya Ahmad kuwa hannunta data yanke yaketa kamowa dan ganin yadda jini ke zuba alamun ta yanke sosai.
Baba Malam kuwa tun sanda yaga ta yanke kanta,
ya juya ya bar wurin yana tafe jiri na fizgarshi sabida tsananin tashin hankali da b'acin rai.
A gabanshi a gidan shi ƴarshi ke kirari da tutiyar kashe kanta, a kan mijin da itace tace ya turo iyayenshi.
Gaba d'aya idanunshi basa gani, sabida wani fitinennen duhu daya mishi k'awanya kan kwayar idanunshi, babu abinda yakeyi sai sunan Allah yake ambato,
Wai yau shi Malam Bashir Sulaiman Dukku shine za'ayi kisan kai a cikin gidanshi, kuma yarsa ce ta cikinsa, lallai fulani sunyi gsky da sukace, (Te'ud'o laddefu and'i dayan sabere) kowa ya auri daji tofa yasan tabbas wata rana zai haifi Saura/lampo.
Jiki na rawa ya zauna dirsham a bakin gadonshi tare dasa hannu duka biyu ya tallabe kanshi kana yaci gaba da zancen zuci.
"Eh tabbas yau dai yaga zahiri, ashe ba banzaba Fulani keda k'abilanci a fagen neman aure da bada aure, yau gashi yaga illa da kuma dafin gwamutsa zuriya, sabida ai dai kowa ya sani abinda d'iyarshi Zaleeha take inkarin zata aikata koma yace ta aikata kafurcine wanda addinin musulunci yayi tir dashi, kisan kai ko kashe kai al'adace ko d'abi'ace ta kafurai marasssa imani da tawakkali wanda basuyi imani da Allah da manzonsa ba, bare suyi imani da k'addara mai kyau ko akasin haka."
Wani irin fitinennen kukane mai cushe zuciya da numfashi ya kwabcewa dottijon nan mai cikar haiba da kamala,
mik'ewa yayi cikin tsananin kuka ya d'auki yar karamar jaka,
Qur'an da wasu littafan ya saka a ciki, sannan yasa ATM nashi da carbinshi kana ya d'auki car key d'inshi.
A hankali ya nufi cikin gidan inda yake jiyo ife-ifen na k'ara tsananta,
Dib-dib-dib haka zuciyarshi ke bugawa da tsananin k'arfi da firgita Kardai ta kashe kan nata ne?.
Yana isa ya samesu gaba d'aya suna tsaye a tsakar gidan, sai Zaleeha daketa kwaso akwatunan da yan uwan Abdussalam suka kawo tana ta watsosu tsakar gida,
gaba d'aya tayi kaca-kaca da komai ta birkice ta zama kamar mai shafar al'janu.
Ya Ahmad ne keta kamota tana zillewa duk ta birkice gashin kanta yayi biji-biji ya hargize ta zama kamar zarerriya
Wani k'aton akwati ta jawo wanda wlhi ko maza zai sunyi da gaske zasu jawoshi sai gashi ta figoshi ta turoshi waje,
Ahmad ne yayi sauri tareta cikin gigita da kid'ima ya kamo hannunta dake zubda jinin tare da cewa.
"Wallahi al'janine a jikinta, sune suke sata yin komai."
Da sauri ya sake hannunta ya kalli Ziyada data ruga a guje ta nufi mahaifin nasu,
tana zuwa ta durk'usa gaban Baba malam hannu duka biyu ta d'ago cikin tashin hankali ta saki kuka mai sauti tare da cewa.
"Dan Allah Baba Malam kayi hak'uri, kada ka tafi, in ka tafi ka barmu ya zamuyi, dan Allah Babana kayi hak'uri, wlhi gwara ka kori ita Zaleeha tunda bazatayi maka biyayya ba."
sai kuma ta kifa kanta bisa rumfar sawunshi cikin neman al'farma.
Hakama Maryam da gudu tazo gabashi ta durk'ushe murya na rawa cewa.
"Wayyo Allah na wayyo Ya Ahmad ka bar Zaleeha kaga zata kashe mana mahaifinmu da bak'in ciki."
Sai kuma ta matso gab dashi cikin tsananin kuka take magiya.
Tuni Ahmad ya mance da Zaleeha bare matsalarta yazo tsakiyar k'annenshi suka durk'usa gaban Mahaifin nasu suna kuka mai tada hankali.
Zaleeha kuwa sam bata cikin nitsuwarta bare tasan illar abinda take aikatawa asirin da uwarta tayi mata ya shafe nitsuwarta burinta kawai ta firgita kowa a fasa batun aurar da ita.
Ido Baba Malam ya rumtse ganin Mamy ta motso gareshi cikin kuka take cewa.
"Kada laifin mutun d'aya ya shafemu baki d'ayanmu, idan ka tafi ya zanyi da rayuwata? ina zan shiga? Me ya rage min da zaman gidannan? Dama d'ana kwaya d'aya tak Allah ya bani, shi kuma ba'a gidan yakeba, dan k'ashin Kanka ne da aurenka nake zaune a gidan nan, ni banyi maka laifiba Maryam batayi makaba hakama Ziyada da Habu da Zakiriyya to meyasa zakayi nesa damu akan laifin da bamu aikata ba?."
ta k'arishe mgnar tare da durkushewa gefenshi kana ta kamo hannunshi murya na rawa tace.
"Duk in da zakaje sai ka tafi damu, in kuma laifinsu ya shafemu ne, wlhi kana fita nima zan bar gidan nan."
kalamam Mamy sunyi matuk'ar k'ara gigita su Maryam kawai sai suka saki sabon kuka.
Mama kuwa da Ruda da Zaleeha ihu sukeyi wai bak'in ciki ya haukata Zaleeha.
Daga bakin Gate Habu ke jiyo ihu da hargitsin dake cikin gidan nasu,
Ko parking bai gama dai-dai tawa ba ya fito cikin motar, a guje ya nufi cikin gidan nasu gaba d'aya jikinshi kerma yakeyi.
Wani irin tsayuwa yayi tare da zaro idanunshi baki d'aya, kuka da magiyar dasu Maryam keyi ya ganar dashi abinda ke faruwa.
Wani irin tafasa da harzuk'a zuciyarsa keyi, juyowa yayi tamkar zautacce,
Zaleeha da ta Kikimo wani akwatin ne ta harboshi, dai gaban Habu, kana ta juya tayi hanyar shiga parlour da niyar kwaso wani.
Wani irin razanannen k'ara ta saki jin wani irin azabebben naushi da Ya Habun nata ya d'irka mata a tsakiyar gadon bayanta har saida tayi tangal-tangal zata fad'i k'asa,
bata gama gigitar naushinba taji yasa k'afarshi ya tareta daga fad'uwar da zatayi ya naushi k'irjinta wanda saida ta bada sautin hak.
bata ida tsayuwarba tayiji yasa k'afarshi ya tad'eta ta yi k'asa, ji kake gib ta bugi k'ofar parlour tayi gaba ta dawo baya,
sai kuma ya zaro belt d'in k'ugunshi ya juya kan belt d'in dai-dai inda k'arfen yake ya fara tsula mata tamkar Allah ya aikoshi.
Ihu da karaji ta sake tare da fara mirginawa tamkar macijiya tana.
"Wayyo Ya Ahmad ya Habu zai kasheni! Wayyo goshina ya fashe! Wayyo k'uguna ya karye, wayyo Allah na na mutu na lalace".
Shi kuwa binta yakeyi a baya yana had'a mata naushi da gula da zana tare da magana cikin haki dake nuna tsantsar tafasar da zuciyarsa keyi.
"Shegiyar yarinya. tsinenniya mara amfani a doron duniya, kiyi ihu da kyau ki fad'a da k'arfi kasheki zanyi, tun kafin ki kashe mana mahaifinmu, kasheki zanyi koda ma rage mugun iri, shegiya mai zuciyar arnan kan duwatsu. Shegiya mai gadon bak'ar zuciya."
Ina Ahmad, Maryam, Mamy, Ziyada su bata Zaleeha sikeyi ba bare su ceceta daga bugun gardi da Ya Habu keyi mata.
Ganin alamun habu zai kasheta ne yasa Mama tayi tsalle tare da shiga tsakaninsu, da k'arfi ta ingiza Habu baya tare da cewa.
"Dan ubanka kai farar zuciyarce da kai? Nace kai ɗin farar zuciyar ce da kai? da kake cewa tayi gadon bak'ar zuciyar a ina ta gado kenan?."
Kan Zaleeha ya kumayi sunkuyowa yayi yasa hannu ya damk'o wuyanta tare da shak'ewa da k'arfi kana ya kalli Mama tare da cewa.
"Eh nima bak'ar zuciya gareni kuma, data kashe mana uba gwara na kasheta, bak'ar zuciyar kuwa a ina zamu gada banda wurin bak'ak'en arnan iyayenkin can dake bautar gumaka."
Aunty Lubna ce tayi k'arfin halin kamo hannun Habu da niyar cotar rayuwar Zaleeha daketa kakarin mutuwa tuni idanunta sunyi zuru-zuru a woje,
sai kuma ya jiyo muryar Baba Malam na cewa.
"Abubakar ka dawo haiya cinka, kisan Kai ya sab'awa addinin musulunci."
jin haka yayi matuk'ar sace mishi zuciya hakan yasa ya hankad'e Zaleeha, kana yazo ya durk'usa gaban mahaifin nasu cikin rauni yace.
"Dan Allah da al'farman manzon rahma Baba Malam kayi hak'urki ka gafarcemu ka rufa mana asiri kada kayi nesa damu."
Ita kuwa Zaleeha wani irin azabebben tari takeyi tun sanda Habu ya sake mata wuya tarin takeyi tare da kuka,
Aunty Lubna ce ta ruggumeta sukaci gaba da kuka a haka,
Ruda kuwa tunda Habu yazo ta silale ta bar gidan dan tsoron yaron take.
Ita kuwa Mama akwatuntan su Abdussalam d'in ta fara tattarewa tana maidasu parlournta.
Shi kuwa Baba Malam kanshi ya jujjuya tare da rab'awa gefen su da nufin zai fita,
ganin hakane yasa fargabansu ya ninku sama da sau d'ari,
Maryam ce ta kife kanta a k'asa cikin kuka tace.
"Kaito na! Kaiton rayuwata da bani da damar share hawayen mahaifina,
Yau da ace bani da aure wallahi da na sharewa maka hawayenka baba malam Kodako Saifuddeen kurmane makahone gurgune kuturune wallahi matuk'ar zakayi farin ciki tabbas da zan zauna dashi.
Inama ana rabuwa biyu wallahi da na kasu biyu."
Ziyada ma kukan takeyi tare da kamo hannun Baba Malam cikin rauni tace.
"Baba kada ka tafi ka barmu, in yana sona ni zan zauna dashi."
Gaba d'aya sun rud'e da kuka hatta habun kuka yakeyi bare kuma Maryam da Ahmad masu rauni.
Wani irin Murmushi Ahmad yayi still hawayenshi na kwaranya, kai ya jinjina ganin Zaleeha na rarrafe tamkar yarinya k'arama a hankali ta isa gaban Baba Malam hannu ta had'e wuri d'aya cikin yanayin neman gafara, murya na rawa jikinta na kar-kar-wa numfashinta na ficewa ba komawa,
cikin shak'k'k'iyar murya a disashe tace.
"Na amince Baba Malam na yarda ayi auren ka aura min Saifuddeen d'in na amince. Ka yafe min Babana ka gafarta min ka rufa min asiri kada in hallaka sabida fushinka na amince ayi auren na yarda."
Da sauri Maryam da Ziyada suka ruggumeta.
Ahmad da Habu kuwa ruggume juna sukayi,
Mamy kuwa kamo hannun Baba Malam d'in tayi ta nufi side d'inshi dashi, shi kuwa ba musu ya bita. Ahmad da Habu sukabi bayansu,
Aunty Lubna kuwa kamo hannun Zaleeha tayi ta nufi Side d'in Mamy kana Ziyada da Maryam sukabi bayansu.
Zahira kuwa da sauri tabi bayan Mama.
A gidan Saifuddeen kuwa, Ummi ce zaune a parlournta ita da.
Su Bappa Ali da Malam Ashiru.
Cikin nitsuwa tayi musu bayanin dalilin nemansu da tayi ta k'ara da cewa.
"Hankali na ya tashi tun zuwansu na forko, yarinyar ta nuna bata son auren da Saifuddeen ta gaggaya musu bak'ak'en maganganun da suka gigitasu suka tayar musu hankali, anan Ahmad ya dawo yana kuka cur-cur da hawayenshi dan wulak'ancin da tayi musu ita da aminanta.
basu b'oye min komai ba, sai dai shi Saifuddeen baiso su sanar min ba sabida tsananin son yarinyar yakeyi ita kuwa bata sonshi ina tsoron kada tazo ta cutarmin shi."
Ta k'arishe maganar cikin yanayin tsantsar karaya da tsoro.
Bappa Ali ne ya gyara zama tare da fuskantarta da kyau kana yace.
"To yanzu me kike so ayi?."
Nannauyan ajiyan zuciya ta sauk'e tare da cewa.
"Ni dai auren ya fita raina, ku kira Saifuddeen ku taushi zuciyarshi ya rabu da yarinyar ya janye batun auren, kana kuje ku sanarwa iyayenta cewa an fasa batun auren tunda yarinya bata so gwara a bari kawai, magnin bari kadama a soma."
Baba Ashiru ne ya katseta da cewa.
"A,a sam bamu da hujjar janye batun auren nan, da girmanmu da mutuncinsu munje munyi magana gemu da gemu sannan dan zancen baya muce zamuje muce mun fasa auren. Sannan keda kankifa kika ce mana Saifuddeen yana son yarinyar matuk'a gaya."
Cikin sanyi ta girgiza kai tare da cewa.
"Ba zancen bayan kadai bane. Ko shekaran jiya Hayatuddeen yaje gidan kakarsu wurin Abokinshi k'aninta ya sameta can tanata kuka, wai ita bata son auren gurgu kurma. Tayi al'washin in dai aka aura mata shi zata kashe kanta.
Kuma jiya ma dasu Saifuddeen d'in sukaje nanma ta ciccimusu nutunci sun dawo nan suna mgnar basu san na jisu ba."
A hankali Bappa Ali yace.
"Ba komai! In sha Allah babu abinda zai faru sai al'khairi! Ke dai kiyi ta addu'a kin san addu'ar uwa karb'eb'b'iyace domin bata da hijabi,
Tunda kin sani mun sani Saifuddeen yana sonta tofa mu bisu da addu'a.
in har bata so ai iyayenta zata sanarwa kuma in bata sonshi baza bashi izinin turamu ba."
kasake tayi tana jinsu, suna bata k'arfin guiwa, cikin kula Malam Ashiru yace.
"Kinga fa du-du-du kwana biyar ne ya rage bikin ta yaya zamu fito da wata matsala ta b'angarenmu, muyi hak'uri in har bata so d'in su sa fito da matsalar."
Kai ta jinjina tare da cewa.
"To tunda kunce haka ba matsala, amman ni naso Saifuddeen ya nemi matar aure a cikin tarin matan dake bibiyarsa da soyayyarsu. Amman ba komai Allah yasa hakan shine mafi alkairi."
Amin Amin sukace baki d'aya, kana sukace to su zasu koma dukku.
nan suka sallemi juna suka tafi.
A can gidansu Zaleeha kuwa, shiru gidan ya koma kamar gidan zaman makoki, kowa da abinda ke ransa, su Ahmad da Mamy da Maryam dai sunyi ta magiya da rok'on Baba malam da bashi hak'uri. Har saida suka ga alamun ya samu sassaucin tashin hankalin da yake ciki.
Bayan anyi sallan isha ne. Malam Adam da Ya Aminu suka shigo gidan a jere.
Kai tsaye parlour Baba Malam suka nufa,
Bayan sun gaisa ne ya musu bayanin abinda ya faru.
kwaffa ya Aminu yayi dan tabbas da yana nan to da tuni ya karya Zaleeha.
Shi kuwa Malam Adam kai ya jinjina cikin tsananin mmki da tsoron yaran zamani yace.
"Aminu je ka kirawo min Zaleehan."
To yace kana ya mik'e ya nufi part d'in Mama.
Ita kuwa Zaleeha zuwa yanzu dai tayi kuka har hawayenta sun kafe.
Da kyar Aunty Lubna da Maryam suka sata tayi wonka kana tayi salla, sannan suka bata magani ta sha, domin tuni wuyanta ya kumbura haka fuskarta ,gaba d'aya jikinta ciwo da tsami yake mata duk farar fatar nan tayi jazir ga tsami da yankan da tayiwa kanta yayi duk da anyi mata dressing.
Rumtse idanunta tayi lokacin data rab'a jikin Ya Ahmad da yanzu ya shigo, wasu zafafan hawaye ne masu k'una suka kwaranyo mata.
sosai ta zama abar tausayi dan duka iya duka Habu ya jibga mata gashi ita da kanta can ƙasan zuciyanta take jin zafin abinda ta aikatawa mahaifinta.
cikin sanyin murya da tausayawa tare da lallashi Ahmad yace.
"Zaleeha!." bata amsa ba sai wasu sabbin hawaye ne suka fara sintiri a fuskarta.
Lubna ce tasa tafin hannunta ta share mata hawayen, yayinda Maryam ma idanunta sukayi rau-rau alamun zasu zubdo kwalla,
muryar Ya Ahmad d'in nasune ya katse musu shirun nasu.
"Dan Allah Zaleeha na rok'eki da girman Allah kiyi biyayya ga umarnin mahaifinmu, kiyi koyi da Maryam, ki kare mana mutunci da martaba da darajar gidanmu dana mahaifinmu."
A hankali ta bud'i baki cikin disashewar murya tace.
"Ya Ahmad bana sonshi wallahi na tsaneshi ji nakeyi kamar zan mutu in na tunoshi."
kanta ya shafa tare da cewa.
"Zaki soshi, zaki daina jin komai, in kin rabu da aljanin dake jikinki. Ni nasan Zaleeha tana son farin cikin Babanmu."
Shiru tayi dan ta fahimci ya Ahmad dai ya maidata mai aljanu so bazai tab'a fahimtar matsalarta ba,
shi kuwa d'agota yayi suka fuskanci juna cikin tausaya mata yacee.
"Dan Allah Zaleeha kiyi biyayya ga auran da Baba Malam zai miki ki zauna d'akinki, nayi miki al'k'awarin zan miki duk wani abu da kikeso a duniya matuk'ar baifi k'arfina ba, kuma bai sab'awa shariya ba,
ki gaya min duk abinda kikeso zan miki shi k'anwata, ni dai fatana a miki auren ki zauna lfy da mijinki."
cikin zubda hawaye tace.
"Ka saya min sabuwar mota, motocina su zama biyu."
da sauri Maryam tace.
"Ai yanzuma motocinki biyu ne, ai kayan aurenma da motarki sabuwa fil Saifuddeen ya had'o miki."
Ido ta rumtse da k'arfi dan wani d'aci da takaicin jin sunanshi da Maryam ta kira cikin had'e fuska tace.
"Bana son wannar, abin gori abin dangin miji".
murmushi Ya Ahmad yayi tare da cewa.
"Zan saya miki k'anwata sabuwa fil zan saya miki, motocinki su zama uku."
sosai taji dad'in amincewar da yayi zai saya mata mota,
ganin taji dad'i yasasu jin dad'i suma.
Ahmad ne ya rik'o hannunta tare da cewa.
"Da me kuma kike so?."
cikin jin dad'i tace.
"Sabuwar system." cikin jin dad'i fa da ganin yarintarta yace.
"Kin samu."
kayan d'aki kuma wanne iri kikeso."
jim ta d'anyi tare da cewa.
"Ko wannema." a tunaninta me zata ce a kan kayan d'aki abinda ko sun kashe kud'i sun mata bazata soshiba.
haka fa sukayi ta lallab'ata.
Ya Aminu kuwa yana isa parlour Mama ya samu, Habu cikin had'e fuska yace.
"Ina Zaleeha tazo, Baba malam na kira."
"Tana part d'in Mamy."
"Je ka kira min ita."
to yace kana suka nufi parlour Mamy,
daga bakin k'ofa ya tsaya tare da cewa.
"Ke Zaleeha maza ki zo, Baba Malam na kira."
jin muryar habu yayi masifar razanata, da sauri ta mik'e ta nufi parlour.
Ahmad d'inne yabi bayanta.
ganin Ya Aminu da Ya Habu a parlour'n ya k'ara firgitata.
nur-nur tayi gaba sana suka bita a baya,
tana tafe tana d'ingisa k'afarta.
har suka isa parlour.
kana Ahmad na biye dasu a baya,
A hankali ta isa gaban Baba Malam d'in jiki na rawa ta durk'usa ganin yadda ya Aminu ke watsa mata harara yasa tayi maza tayi k'asa da kanta, murya na rawa tace.
"Baba Malam gani."
shiru yayi yana k'are mata kallo,
gaba d'aya jikinta rawa yakeyi,
Malam Adam ne ya kalleta tare da gyara murya wanda sai lokacin ta ganshi,
cikin rawan murya tace.
"Daddy ina wuni." ido ya lumshe tare da cewa.
"Lafiya lau Zaleeha."
daga nan sukayi shiru na tsawon 55 seconds sannan Malam Adam ya kira Zaleeha wacce tsoro ya hanata salama.
"Na'am". A hankali ya fara magana.
"Naji abinda kikayi,