Showing 27001 words to 30000 words out of 100889 words

Chapter 10 - Love Cycle Book 1 Complete Hausa Novel

Annafie   

10 Feb 2025

360

sa"... Tsam daddy ya mike jikin sa na wani irin rawa... "Bana son ganin kowa".... Daganan direct ya nufi kofar fita.. Seda yakai daidai kofa snn yace "banajin zan koma garesu... Sun gujeni a lokacin da nake bukatar su... Dan haka nima na barsu har abada kamar yanda suka bukata.. Ku yarana ne kuma ko da yaushe ina maku barka da zuwa nan gidan ku ne zaku iya zuwa a duk lokacin da kuka so but ni.. Bazan taba komawa wajen wadan da suka kyamaceni ba nagode da ziyara"... Daga haka ya fice.... Fannah ta fashe da kuka taje ta rumgume mummy "mummy kibasa hakuri dan Allah".. Shiru kawai mummy tayi amma bata iya tace komai ba.... Su fannah suna gani su farouq zasu fita.. Fannah tayi saurin shangabansu su.. Tace "au tafiya zakuyi ashe dama ba neman mu kuke da gske ba" sultan ya girgiza mata kai "no sister we're coming back"... Daga haka yaja hannun farouq suka fice.. Fannah na kallon su kamar wata shashasha... Tana gani sun fita ta fashe da kuka tare da zuwa ta rungume kanin ta.. Da take ji shine kade dan uwanta a duniya....
Kirane ya kara shigowa wayar farouq na kusn bakwai... Dagawa yy "hello abie".. "Farouq yaushe na zama tsaran wasan ka.. Ina Muhammad da nagani ta video call".... "Abie...... " nan ya kwashe duk abinda ya faru ya fada masa..
***
... Abie ya kashe wayar bayan yagamajin abinda farouq ke fada masa... Jiki a sanyaye ya dubi matar sa da ta mike tana son tabbatar da cewa Muhammad ya dawo... Tace "meya faru yana ina shi Muhammadun".. Ya dube ta "mamien yara Muhammad har ynx fushi yake damu"...mamie tace "yakamata kuyi wani abu tunda wnn damar ta samu kar mu bari ta subuce mna" ya gyada kai cikin gamsuwa kafin ya dauki waya yakira Ahmad dake America "hello Abie".. Abie yaji muryar diyar dan uwan nasa sumayya ta daga "Chucun abie"..."abie good morning" Abie ya saita muryar sa "morning chucu ina dad".. Mika masa wayar tayi.. Alhaji Ahmad ya amsa tare da sallama.. "Ko gaisuwar kirki basuyi ba ya fara sanar dashi dalilin kiran... . Alhaji Ahmad be san sanda ya mike ba zuciyar sa na masa wani irn rauni.. Jin abinda Muhammad din yafada ne yasa lokaci daya ya yanke shawarar ynx Idan ya samu flight din Nigeria ze taho zuwa gobe se suje London din snn yace a a fadawa Alh Aminu da Alh Rabiu.. Bayan nan kar a fadawa kowa dan basa so Baffa yasan da maganar har se komai ya dedeta.... " kafin azahar su Alh Aminu da Alh Rabiu duk sun san da maganar kuma suna cikin farin ciki Rabiu da yake sudan yaso ya yanke aikin da yake ya taho amma Abie yace ya bari zasuje. Haka ya hakura dan yasan duk da shine suke uwa daya uba daya da Muhammad yasan baze nunawa sauran yan uwan nasa kaunar sa ba.. Dan dama tuni shi Muhammad kowa yafi sonsa a gidan sbd shi Allah yayi sa da sauki da hakuri ba kamar sauran ba... Hajiya.. Maimuna ma da take Lagos danta sultan ya kirata ya fada mata... Dan haka itama tuni ta kira Abie kuma ya sanar mata da inshaallah gobe zasu je....
**
Fannah shiryawa tayi ta tafi wajen maryam.. Bata fada mata komai game da ganin family din nata ba.. Ita kuma maryam ta dauka duk dan zata tafi ne da yake duk in zata tafi haka suke barin ma hutu me tsayi irin wnn.. Haka de taita lallashin ta... Karshe ma fannah kuka ta fashewa maryam dashi... Abubuwa da yawa sun mata gana Amah gana Family dinta ga kuma maryam ma Zata tafi.... Da kyar maryam ta lallaba ta dan itama seda ta sakata kukan ....
Fannah ta rakata har airport din snn ta juyo ta dawo gida.. Mummy ta iske a parlor tayi shiru.. Zuwa tayi ta kwanta saman cinyar mummy kafin tace "mummy pls do something"... Shiru mummy tayi bata san dalilin daddy nayin haka ba but tasan cike yake da son ganin yan uwansa ita ynx hankalin ta duk a tashe yake sbd bata san wane hali yake ba a ynx....
Tashi fannah tayi ta koma daki.. Tana zuwa ta ciro sakon da Amah ya barmata ta karanta.. Tana hawaye kafin a hankali ta furta I love you.. Pls come back to me"...
Ranar gidan babu wanda yabi ta kan lunch har dinner ma seda mummy ta mata da gske snn tasakko kuma har lokacin daddy be dawo ba... Gaba daya hankalin su a tashe yake... Suna gamawa yana shigowa... Suka masa sannu da zuwa ya amsa ciki ciki snn ya haye Sama... Fannah kara fashewa da kuka tayi snn ra wuce dakin ta... A haka ranar suka kwana kowa da abunda yake damunsa a rai..
washe gari andade da gama breakfast amma babu wanda ya sakko yy har wajen 12... Da kyar mummy ta lallaba daddy yasakko snn ta kira fannah a waya... Har suka kusa gamawa fannah bata sakko ba.. Daddy ne na kansa ya dauki waya ya kirata... Tana dauka yace "I want to see in lessthan 2mnts" daga haka ya kashe wayar... Ai kau se gata dakaga idanun ta kasan tayi kuka.. Abubawa da yawa sun mata yawa to... A hankali ta zauna tare da gaisar da iyayen nata mummy ce kawai ta amsa amma daddy sede kallon ta yy ya basar... Har cikin har sa bayason yanda ya ganta... Kodaya bayason ganin ta a damuwa... Itace babban farin cikin sa a duniya shiyasa a duk lokacin da yaganta cikin damuwa zuciyar sa take karaya...
Juya abincin kawai take har lokacin ta kasa kai ko tea bakin ta... Ganin abinda take ne yasa daddy fadin.. "Kar ki bari na gama break ba tare da kin cinye abinda ke gabanki ba you better behave ur self" gyada masa kai kawai tayi tana tura abincin tana hawaye.. Suna cikin haka ne sukaji an danna bell.. Daddy ya umurci maid dinsu akan ta bude...
Tana budewa.. Farouq ya shigo da sallama cikin shiga hausawa wacce ta fito da anahin kyaunsa.. Sultan ma ya shigo cikin shiga irn ta Farouq sunyi matukar kyau da kagansu kaga kyawawan asali.... Da sauri fannah ta mike cike da farin cikin ganin yan uwan nata.. Sede kafin tayi step daya.. Idanun ta ya sauka akan wani kyakkawan dattijoh cikin shiga ta alfarma kamannin sa da daddyn ta sun bayyana haka kuma suna tsananin kama da Farouq... Wanda ya shigo daga bayan sa seda gabanta ya fadin ganin shima kamannin sa da daddy sun fito a fuzge kuwa da Dr. Amah dinta yake kama.. Next ma wani ne ya sake shigowa kammanin sa sak da daddy... Ai ba ita kade ba harta Daddy da mummy seda suka mike..... Gaba daya daddy jiyayi jijiyoyin jikin sa na saki ganin yan uwan nasa gabansa bayan tsawon shekaru 19 se yake ganin kamar a mafarki... Ko a yanda numfashin sa ke sauka kasan yana cikin wani yanayi... Sauran yan uwan nasa da hawaye ya cika idanun su ganin little kanin nasu kamar a mafarki.... Cikin raunanniyar murya Alh. Ibrahim yace "Muhammad"... Fashewa da kuka daddy yy ya nufi dan uwan nasa da sauri ya fada jikin sa suka rungume juna.. Cikin rauni da kewa daddy yace "ya..ya..na" ya kara fashewa da kuka.. Alh. Ahmad ma da kukan yaci karfin sa ya rumgume su hakama Alh. Aminu... Kuka suke cike da kewar juna.. Idan ka gansu a yanda suke se sun baka tausayi sbd da kagani kasan suna matukar kaunar junan su to be separated from each other is something else musamman ma idan kuna kaunar junan ku.. Koda baku kaunar juna kuka rabu irin haka for years bakwa ganin juna se kunji kuna kewar juna ballantanama wanda kukeson juna.. Fannah ma rungume mummy tayi tana kuka watching her parents crying.. She's can't believe cewa daddy dinta take gani tare da yan uwansa... She have been dreaming this for so long tunda tasan kanta.. But nayau is different.. Na yau is reality.. Idan ma mafarki take bazata so ta farka ba let her continue dreaming till her last breath.. But her Dr. Amah should be included she can't wait to go back to Nigeria taga yan uwan ta.. Kilama acan zata hadu da Amah dinta.....
so how is it? .... Is it sweet?. If yes se ku karamin yawan comment and ku danna mun vote.. . Bakuga komai ba inde a littafin love cycle ne.. I knw you will enjoy it more than ur expectation.se kunji kamar karna gama just need ur support more comments dan hakan na karawa duk wani writer kwarin guiwa.. So more comment more typing..... Kar ku manta nice taku Nafeesatuh😘 popularly as...
✨✨✨
*ANNAFIE😍*


......

*💫❤LOVE CYCLE✨*


Written by

*@nnafie🖤*
(Smll but mighty😉)

*writer of*
Saif
Adaan
Wada mafita
Saboda duniya
Love cycle......


Bismillahir rahmanir raheem

💫❤Love cycle❤ (10)✨
*Not edited*
Daddy yace "yaya I missed you so much kun gujeni without knowing halin da zan shiga" Abie ya dago dan uwan nasa yana share masa hawaye "we are srry lil bro muma munshiga halin rashin ka for so many years".. Daddy ya share hawayen sa yace "ina baffa na" Alh. Ahmad yy murmushi.. "Baffan ka yafi kowa damuwa da rashin ka tsawon 19yrs da be ganka ba yanacikin tsanin damuwa ynx ma besan mun taho ba da tare dashi zamu taho"...cike da farinki yace "ynx baffa yana son ganina Ina mamana ina umma da sauran yan uwana".. Daga ganin yanda yake magana kasan yana cikin farinciki da kewa Alh. Aminu yace "eyee is that how you miss us shine ka barmu".. Dan langwabar da kai daddy yy kamar yanda ya saba masu kasancewar sa karamin su yace "I don't think zaku sake kewa ta sbd yanda har nayi 4yrs na koma amma baku bukatar gani na.. I thought sona ya fita a ranku.. I thought kun barni har abada bazaku sake yafemun ba"..yafada a raunane Alh. Ahmad yace "common bro we loves you kasani kawai de lokacin idanmu ya rufe ganin yanda ran baffa ya bace but kafimu gskiya".. Abie ya shafa kansa yace "se bayan ka tafi muka fahimci cewa kafi mu gsky liman ya samu baffa yamasa nashiha ya nuna masa abinda kayi daidai ne.. baffa ya shiga damuwa tun yana saka ran zaka dawo har ya cire but kullum yana maka Adduar gamawa da duniya lpy.. Kullum kaine mafarkin sa ... Kuma be taba cire ran zaka dawo ba duk kyautar dayamana har da kai".. Daddy da farin ciki ya ishesa se juyawa yy ina matarsa da yaran sa suke.. "Halimatu. Mamana kunga yan uwana sun dawo hisam zo".. Duk tahowa sukayi kowa idonsa na zubar da hawaye... Abie na kallon fannah yace "masha Allah yarinya ta ta girma".. Murmushi tayi kanta kasa.. Alh Aminu yace "come to ur parents we really miss you".. Suka rungume hisam ita kuma suka shafa kanta.. Daddy is so excited he can't believe ranar nan zata zo... He can't wait yaga mahaifinsa sa ji yake kamar yy tsalle ya gansa a Nigeria yaga mammansa da sauran yan uwansa....
Bayan komai ya lafa aka gabatar masu da abinci sun roki kafarar mummy da shi kanshi daddyn har fannah da take jin kunyar su sun roki tata kafarar kuma duk sun yafe mata.. Daddy ya shige cikin yan uwansa se fira suke yana tambayar yan uwansa da yaransa.. Aka kira haj. Maimuna da Alh. Rabiu bade a kira su sa'adatu ba sbd suna son surprising dinsu amma sauran ya gaisa dasu a waya kuma yaji kalar farin cikin da suke.. Se daddy yaji duk be kyauta ba dama ya koma da be zauna cikin kadeci na shekaru ba.. Fannah kau se kallon daddyn take ganin yanda ya sake da yan uwansa kamar bashi ba dan is hardly ya sake da jama'a inhar basu ba.. Ynx ko koyanayin maganar sa ya chanza se yar shagwaba yake masu dade kagani kasan dama shine karamin su kuma dan gata... Fannah kasa sakewa taci abinci tayi sbd yanda idanuwan sultan da Farouq ke yawo akanta.. Kara daga ido tayi suka hada idanu da Farouq.. Ta ware masa idanu shi kuma ya sakar mata murmushi tare da kashe mata ido daya.. Ta dauke kai tana murmushi.. Suka hada ido da Alh. Ahmad.. Da sauri tayi kasa da kai dan hakanan taji tanaji matsanaiciyar kunyar sa fiye da kowa a wajen... Wayar Alh. Ahmad ne tayi kara yana dubawa ya kalli daddy yace "danka ne kekira" "me sunan baffa".. Daddy ya fada yana murmushi... Alh. Ahmad ya dauki wayar bayan sun danyi magana kadan ya mikawa daddy suka gaisa snn mummy.. Daga nan ta mikawa Alh. Ahmad se yace "ga kanwar ka ku gaisa toh"... Shru yy kafin can yace "ohk to Allah ya kaimu ya bada sa'a".... Ya kashe yana kallon fannah "wai dan uwan naki busy yake but idan ya zama free ze kira ku gaisa"... Gyada kai fannah tayi kawai a ranta tace "wato shine kade baze gaisa da ita ba bayan kowa dokin yake abasa ita su gaisa yaji yanda ta girma.. Amma shi busy yake...."
... A ranar su abie sun dade kafin suce yaushe ze koma.. Daddy ji yayi kamar ya bisu but yace "gobe inshaallah kasata zata amshi bakuncina nida iyalina"... fannah couldn't find it but smile... Jin cewa gobe zataje Nigeria abun kamar a mafarki.. Kowa se kallon juna suke suna murmushi sun kasa magana.. Alh. Aminu ne yy karfin halin fadin "lallai gobe munada manyan baki lallai gobe ilahirin family din Radda suna cike da farin cikin dawowar dan uwansu bayan tsawon shekaru".. Duk murmushi sukayi Farouq yace "su wata za'a bar kauye aje birni".. Fannah ta tsuke fuska tana hararan Farouq sultan yace "Allah yasa karta mana kauyanci dukda nasan ma wnn aje take".... Abie yace "rabu dasu daughter ne ai sune yan kauye keke birni bakiga idan zasuzo bude ido nan suke zuwa ba".... A hakade sukai ta wasa da dariya daddy ya zagaya dasu cikin gidan sa ya fada masa nasarori da arzikin da ya samu bayan barinsa gida.. Sun jinjina masa kuma sun saka masa albarka...
Gabadaya tare suka rakasu airport fannah kamar ta bisu haka take ji dan gani take kwana dayan nan kamar shekara daya ne.. Ganin yanda jikin ta yy sanyi yada sultan kamo hannun ta yace "lil sis are you ohk?"...kamar zatayi kuka tace "I just can't wait jinake kamar na biku"... Yy murmushi "see you inde Nigeria ce seta isheki"... Itama murmushi tayi ya kashe mata idanu.. "Keep smiling cutie you look more beautiful".. Kasa tayi da kanta ganin yanda ya zuba mata manyan idanu....
Kiran su da aka farayi ne yasa bama fannah kade ba hatta daddy seda jikinsa yy sanyi dan gani yake kamar baze kara ganin su ba ya rungume su.. Fannah ta kalli Farouq dake kallon ta ya girgiza mata kai alamar kartayi kuka.. Itama seta gyada masa kai tana masa murmushi.. Ya kashe mata idanu... Yanda yayi din seya mata kama da Amah... Suka daga masu hannu suna gani har suka shige snn suka juyo...
Fannah ta dubi daddy dake driving tace "daddy ynx Nigeria zamu koma".. Yace "sure daughter gobe zakiga baffa ba da mamana da umma and other of ur relatives" farin ciki kamar me....
Suna komawa gida suka fara shirye shirye daddy yace ba wasu kaya dayawa zasu dauka ba idan sunje duk zasu siya nacan Nigeria.. Ranar suka gyara gidan komai aka ajesa a inda ya dace wanda ze lalace suka bayar dashi daddy ya masu booking flight.. Kafin dare sun gama shirya komai .... Ranar ma duk basuyi wani baccin kirki ba daddy hankalin sa gaba daya ya koma kan iyayen sa.. He just can't wait ya gansa tare da mahaifinsa mamansa da sauran kannensa...
Fannah ma murna da farinciki da dauki ya hanata bacci.. Ta rungume pillow tana tsara yanda zatayi surprising maryam.. She wish ace ta hadu da Amah acan tasan zeyi mmki..A haka de bacci ya dauke ta...
Washe gari jirgin su ya daga zuwa Nigeria.. Fannah tana cike da doki daddy kau da mummy tunanin su daya ne babu wanda ya manta last tym da suka hau jirgin Nigeria shekara 19 knn lokacin fannah na jaririya.. Gaban mummy se faduwa yake musamman ma da tasan itace silar komai fahimtar hakan da daddy yy ne yasa ya kamo hannun ta.. Ta kalle sa ya girgiza mata kai kafin yace "inshaallah komai yaxo karshe".. Ta gyada masa kai.. Ya juya ga Fannah da tayi bacci with smiling face... Yace "kinga diyarmu bacci take cikin farin ciki.. Wancan tym din da muka baro da ita bata san komai ba.. But now she's happy"... Mummyn ta kalli diyar tata cike daso da kauna tana murmushi.. "Inason yarana yaya iyayen mu sukaji da suka rasa mu"... Daddy ya kwantar da ita a shoulder dinsa yana dan buda bayan ta.....
*⭐⭐NIGERIA⭐⭐⭐*
Nnamdi Azikiwe International Airport Abuja...
A hankali fannah ta lumshe idanu tana shakar iskar kasar tata wani irin farin ciki yana lullubeta she can't believe itace tayi stepping in a Nigeria.. Iskar yammacin tana dan kadawa a hankali taitabin jama'ar wajen da kallo inda take ganin kamar mafarki take... daga inda sultan yake yana hango su tunda suka fito sunyi wani kyau da kagansu kasan suna cikin hutu .. Ya sauke idanun sa akan fannah.. Tayi matukar yi masa kyau acikin arebian dressing dinna ta seta fito sak balarabia kyawunta is unique ta hada komai sede abinda ba'a rasa ba.. Fannah a bangaren kyau babu macen da bazata iya gogawa da ita.. Gashi kallo daya zaka mata ta shiga ranka... Sultan yadan lumshe idanu yana kara jin son fannah acikin ransa wanda tun randa ya fara ganin ta yakejin sonta... A hankali ya bude motar ya fita yakarasa inda suke... Hisam ne ya fara ganin sa yaje ya rumgumesa... Duk su daddy suka juya gare su... Ya gaisar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login