Showing 69001 words to 72000 words out of 100889 words

Chapter 24 - Love Cycle Book 1 Complete Hausa Novel

Annafie   

10 Feb 2025

245

kofa fannah ta dakatar da ita.. Sbd yanda zuciyar ta ke bugawa bazata taba natsuwa ba setaga halin da yake ciki....
Saleem kade suka iske a parlor yana ganin su yace "yauwa gwanda da Allah ya kawoki Pls dan Allah yana daki". Kallon sa Fannah tayi snn ta kalli chucu.. Chucu tace "mammah na gidan Baffa".. A hankali fannah ta fara hawa stairs gabanta na mugun faduwa.. Kofar dakin da take tunanin nasa ne ta tsaya jin kamar kafar ta bazata iya daukar ta ba yasa ta dafe bango.. Can de ta aro jarumta tayi knocking.. Jin shiru yasa ta tura kofar dakin a hankali.. Dan lumshe idanu tayi jin daddan kamshin turaren sa wanda ke mugun kwantar da hankali.. Bude idon tayi ta daura akan bayansa.. Yana zaune ya juya baya yana kallon window.. Kafin tayi magana taji yace "welcome wife".. Fannah ta jingina da kofa tana sauke ajiyar zuciya "what's wrong with you".. Juyowa yayi ya zuba mata idanunsa da gabadaya suka rikide wanda seda ta tsorata.. Yace "kece".... "Ni kuma?".. Ta tambaya "yes you're".. Ta zuba masa idanun ta.. Ya mike tsaye.. "Sbd ke din tawace ni kade amma ana a shiga gonata".. Fannah ta dauke kai "am srry to say amma ni dukan ku babu wanda zan aura na hakura da ku duka".. "Kin hakura damu kikace?.. Dama mu din har yawane damu? Ai inde ina raye babu wanda ya isa ya aure ki sbd ke din mallaki nace".. Idanun Fannah suka cika da kwalla "no Amoon kayi hakuri Amma bazan iya auren ka ba sbd ko badan sultan ba akwai jiddah sann akwai yusrah inason kwanciyar hankali da zaman lafiya kuma rabuwa da dukkan ku shine ze sama mana zaman lpy".. Bata san ya akayi ba kawai se gani tayi ya fizgota idanun sa sun rikide sosai "farin cikin su, kade kike so bnd nawa?, kwanciyar hankalinsu kade kikeso bnd nawa?, tell me ki fada mun Fannah talk to me...".. Fashewa da kuka Fannah tayi dan ya mugun bata tsoro a yanayin da yake magana.. Rugume ta Amoon yayi sosai ta kara karfin kukan ta.. He hug her very tight.. Muryan sa so broken ba kamar dazu ba yace "I love only you, I love you Khadeejah you're my peace of mind, don't say that again pls kasancewa dake shine kwanciyar hankali na pls love only me.. Zuciyata bazata iya daukar ganin ki da wani ba you are irreplaceable pls don't say that kin hakura dani again pls Fannah".. Yanda yake maganar kade ya isa ya tabbatar maka har zuciyar sa ne.. Tace "you didn't consider halin da zan shiga ka tafi ka barni no phone call nothing nothing bayan kasan inda nake".. Ya kwantar da kansa saman nata still hugging her a hankali yace "srry love pls love only me".. Kokarin turesa ta farayi jin yanda ya matse ta ga yanda zuciyar sa ke bugawa.. Muryar sa can kasa yace "no pls no Khadeejah".. "It's haram.."... Dan Murmushi yayi yana kara kwanta da kansa a nata yace "really haka fa.. Ashe ba'ayi auren ba... But suna so su rabu mu why not ayi a wuce wajen kawai kinga dole su auramin ke"... Sosai Fannah ta turasa yy baya ita kuma ta matsa tana zare idanu dariya Amoon yayi wanda har seda Fannah ta tsaya tana kallon sa.. Can kuma seta juya zata tafi yayi saurin kamo hannun ta.. "pls karki tafi".. Noke kafada tayi shi kuma ya langwabar da kai "love wai har ynx baki so na ne".. Kamar zatayi kuka tace "mummy fa batasan ina nan ba".. Ya ware idanu "harda satan hanya ko kin kasa natsuwa"... Da sauri ta rufe fuskar ta da tafin hannun ta.. Hakanan kawai taji wnn moment din da suke tare ya mata dadi but she have to go.. Yace "ki bari naci abinci se mu tafi"... Ta ware idanu "no pls kar mummy ta nemeni". Ya harareta "se kice kina dakin wanda zaki aura".. Fannah ta wani zaro idanu "wanda ma zan aura tabb".. Yana kallon ta with smile yace "umm mene a ciki".. Nide gsky tafiya zanyi.. Ya kamo hannun ta ta fizge.. Yace "ohk muje na karaki".. Fannah taji dadi da taga babu kowa a parlorn shikam Amoon haka kawai yaji ajikin sa ana kallon su kuma yasan su chucu ne.. Layin babu kowa daedae gate din gidan su Fannah motar su sultan ta wuce su da gudu su bama su kula ba.. Yana can yana tuna mata da farko haduwar su.... Yusrah ta dubi sultan dake driving ya nuna kamar ma bega su Amoon ba tace "yaya, ya Amoon ne fa nagani tare da Fannah nashiga uku knn da gske yaya Amoon son ta yake.. Wayyo Allah na wlh bazan yarda ba.". Sultan de ko kallon ta beyi ba bare tasaka ran ze bata amsa

More comments more typing......
Urs
✨✨✨
Nafeesatuu....😍😍
.....
*💫❤LOVE CYCLE✨*


Written by

*@nnafie🖤*
(Smll but mighty😉)

*writer of*
Saif
Adaan
Wata mafita
Saboda duniya
Love cycle......


Bismillahir rahmanir raheem

💫❤Love cycle❤ (25)✨
Da kuka ta yusrah ta fada jikin mom.. "Yau na bani yusrah lpyn ki kuma"... Sultan ne ya shigo mom na kallon sa tace "me tayi maka".. Ya ware hannu "mom babu ruwana ita da Amoon ne fa"... Mom ta fitar da iska tace "wani abu yayi mata ne". "Wlh yaya Amoon son fannah yake shknn nide bayan kince na kwantar da hankali na amma wlh mom baki gansu ba yau wlh inason sa".. Tashi kawai mom tayi dan ita ynx babu abinda zatace akan wnn lamari.. ..
Amoon na idar da sallah gidan baffa ya wuce .. Dakin umma ya shiga har lokacin tana saman abun sallah zuwa yayi ya kwanta saman gado ya lumshe idanu.. Umma na gama addu'o'in ta ta juyo tana kallon sa "lafiya kazo ka hayemun saman gado nifa wnn karon bana gayyar ka dan na kula bada mutumci ka dawo ba".. Amoon ya tashi zaune "umma pls kima Abie magana wlh fannah nake so".. Umma ta tabe baki "kaini raba ni da shirmen ku.. Inade fada maku gara ku samawa kanku mafita tun kafin baffan ku yasan da wnn zancen dan inde fada zaku cigaba dayi to wlh sede duka ku rasa".. Yace "umma dan Allah ki dena sakamun zancen sa anan shima rigima kawai yake nema"... Umma tace "rigima? To naji su yusrah ai kasan baza'a barsu ashara ba".. Amoon ya bata fuska "umma nazo maki da maganar fahimta kina kawomin wata magana.. Akwai wacce nace ta jirani ne... Kum.. " Maganar sa ta katse sbd shigowar Mom.. Tana kallon sa da kyau tace "bakace su jiraka ba ko? Ai ba kaine ka dora masu sonka ba.. Me ka dauki kanka ne Amoon to wlh baka isa ba bazaka maidamu shashashai ba. Maganar fannah kuwa idan bakayi wasa ba gaba dayan ku seku rasa ta".. Tashi Amoon yayi ya fice a wajen kofar fita yaci karo da yusrah.. Kewaye ta yayi ya fice.. Shiga tayi da sauri.. Maganar da Mom takene yasa ta tsinci wani abu a maganganun nasu.. Juyawa tayi tabi bayan Amoon da sauri.. Tana zuwa gab dashi ta kirasa hakan yasa ya tsaya ta karasa kusa da shi.. "Yaya dan Allah kayi hakuri pls yaya".. Yana kallon ta da kyau yace "inaso ki nemi wani wanda kikeso bani ba" daga haka ya wuce ya barta a tsaye ta bisa da kallo.. Se kuma ta fashe da kuka.. "Wlh. Babu wanda nakeso se kai kuma kai zan aura"....
fannah tun ranar da yusrah tazo akan maganar Amoon bata kara ganin ta ba daga ita har jidda tasan tabbas suna fushi da ita fareeda kam ynx komai ya wuce.. Ana fitowa sallahr juma'a ta nufi gidan baffa tare da hisam da dawowar sa knn.. A parlorn ta iske hafsat.. Tana ganin ta tace "oyoyo ya jikin naki".. Fannah tace "da sauki..".. Jiddah ta dake ciki ta nuna kamar ma bata ganta ba.. Itama din wucewa tayi dakin mama ba tare data kula jiddah ba.. Bayan sun gaisa da mama ta wuce dakin umma.. Yusrah na ciki Amma ta nuna kamar bata ganta ba... Itama bata kula ta ba ta gaisar da umma dake tsokanar ta.. Ta gaisar da da Mom data shigo ynx.. Snn ta mike hafsat tace "daga zuwa" fannah tace "wlh ko" daga haka ta nufi kofa.. Haka kawai yanda jiddah da yusrah suka mata setaji abun yayi mata ciwo.. Kuma ita bata ga laifin ta ba sbd kamar yanda suke bata lvrin Amoon haka take basu na Aliyu dan kuma kawai ya zaman to duk Amoon ne se suji haushinta....
Tana fitowa compound ta hadu da sultan daya fito daga motar sa... Sanye da manyan kaya da alama dawowar sa knn tun fitar sa massalaci... Yana ganin ta ya karaso wajen ta.kanta kasa ta gaisar dashi.. Ya amsa yana kallon ta.. Har zata wuce yace "fannah"... Tsayawa tayi.. Ya karaso wajenta.. Yace "kawai tunda Amoon ya dawo kika kuma gane shine Aliyun ki kawai ki watsar damu ba tare da kinyi considering halin da zan shiga ba bayan kuma kinsan ina sonki".. Fannah ta sauke ajiyar zuciya.. Kafin tace "I've already made it clear that na fasa auren ka yaya sultan I think be kamata ace haryanzu muna wnn maganar ba".. Zeyi magana kawai aka bude gate.. Gaban fannah seda yayi wani mugun faduwa ganin motar Amoon ce ta shigo... Kasa fannah tayi da kanta hoping kar a samu wata matsala.. Yana zuwa saitin su yadan zuje glass din ya kalleta snn ya kalli sultan daya wani hade rai.. Snn ya Kara gaba yaje parking yayi..
Fannah ta dubi sultan.. "Se anima".. "Muje na rakaki"... Girgiza kai tayi.. Tana kallon Amoon daya fito.. Yana sanyen cikin mayan kaya da sukayi mugun karbar sa haka hular ta zauna daram akan kwantaccen gashin kansa.. Duk da yanda gaban ta ke faduwa be hanata ganin yanda kyawusa ya kara fitowa ba.. Sbd bata taba ganin sa da manyan kaya ba.. Se taga ya Kara wani kwarjini.. Yana karasowa ba tare daya kalli farouq ba yayi mata kas kas.. "Kallon fa? Nayi maki kyau ne". Fannah ta tsuke fuska.. Kamar zatayi magana seta tuna sultan na wajen dan tunda Amoon ya fito daga mota ta manta da tsatuwar sultan a wajen.. Tayi kasa da kanta tana wasa da fingers dinta.. Amoon ya dubi sultan da zuciyar sa ke tafarfasa.. Yace "sannu".. Dauke kai sultan yayi.sbd yasan wulakanci ne kawai irin na Amoon... . Amoon ya ware hannuwansa.. In don't care yace "anyway.. Pls give us space.. Zanyi magana da feature wife".. Sultan nayi masa wani kallo yace "kai awa naga tare ka ganmu".. Amoon yace "what tare na ganku? Are you not stupid of ur statement? Na ganka tare da fannah bn damu ba cikin hankali nayi maka magana and you're telling me tare na ganku?".. Sultan yace "yes Amoon na fada maka do ur worst ita fannahr auren ta kayi dazaka mun iyaka da ita.. Amoon bari na fada maka kai baka isa kasaka mun rules ba kaman yanda kk sonta nima haka nake Sonya"... Tuni idanun Amoon sukayi jawur yanaji kamar ya kaima Sultan duka..sbd yanda yake fadin yana son fannah.. Ya nunasa da yatsa "sultan am warning you for last tym wlh koda wasa ka kara furta kana sonta zakaga abinda zan maka. Fannah tawace ni kade.. Ina gargadin ka da ka dena shiga gona ta inde kanason zaman lfy.. Idan ba haka ba.. Se kuma yayi kwafa... Sbd yanda zuciyar sa ke tafarfasa.. Shi me danne abubuwane amma zuciyar sa ta kasa jure ganin fannah da wani.. Fannah kam harta fara hawaye ganin yanda duk suka harzuka suna fada da junan su a kanta.. A harzuke sultan yace "an shiga gonar taka Aliyu do what ever comes to ur mind do it pls kai baka isa kahanani abinda nayi niyya ba".. Yanda Amoon ke kallon sa da jajayen idanun sa kade ya isa kasan zuciyar sa a kusa take.. Ganin haka yasa fannah kamo hannun sa "pls yaya Aliyu stop it banaso".. Sosai kuka ya kwace mata.. Ko lura da Abbu da Abba basuyi ba sede ji kawai sukayi abbu na fadin "subhanallahi what's happening here" dukkan su huci kawai suke kamar zasu danbatu.. Yanda Amoon ke fitar da nufashi kade zakasan jira kawai yake sultan ya kara wata magana.. Abba ne yayi masu tsawa "wai ba magana ake maku bane"... Duk basu tanka ba har lokacin kallon juna sukeyi a kufule.fannah de na gefe kuka kawai take.. Su jiddah dake parlor duk sum fito suna kallon ikon Allah.. Dama yaya Amoon da farouq suna da wata irin zuciya sede kafin kagani se ransu yayi mugun baci.... Mom ce ta daka masu tsawa.. Tare da fadin duk shigo ciki.. A hankali duk suka juya suka nufeta babu jima wa segasu Abie duk sun dawo harda baffa.. Su farouq ma duk ynx suka shigo... Baffa daya gane ma idonsa ya bukaci yana son ganin su Amoon har da farouq da sadeeq ... Da ita kanta fannahr snn da duka yaransa.. Su jiddah de nacan na kuka dan hankalin su yayi matukar tashi...
Baffa ya bukaci jin duk abinda ke faduwa.. Sadeeq ne yayi masa bayanin komai... Baffa ya jinjina kai.. Snn ya dubi yaran nasa yace "so duk wnn abun na faruwa amma bn taba sani ba?.. Ya dubi Amoon yace "kana sonta Aliyu?".. Gyada kai Amoon yayi snn ya dubi sultan yace "kaima kana sonta? " sultan ya gyada kai"..... Wani dan murmushi baffa yayi.. "Good and shine kuka aje duk wata alakar dake tsakanin ku kuke fada da juna". Shiru sukayi babu wanda yace komai.. Ya dubi fannah da har lokacin take hawaye yace "khadeeja ki kwantar da hankalin ki inshaallahu babu me kara daga maki hankali a cikin su.. "To baffa".. Daddy de se kallon diyar tasa yake tayi mugun basa tausayi yasan tana cikin rudani sbd duk bata saba da irin wnn ba...... Baffa ya dubi su Amoon.. "Aliyu da kai da usman tunda abun haka ze zama dukkan ku babu wanda ze aure ta zan sama mata wani daban.". Dago kai Amoon yayi yana kallon baffa zuciyar sa na bugawa.. A zuciyar sa ya furta "wani.." Ita kanta seda taji wani jiri.. Ta dago idon ta tana kallon Amoon bama ta kalli sultan ba bare ma tasan halin da yake ciki.. Suna hada ido ta sauke idon ta a kasa jin wasu sabbin hawaye na zubo mata... Baffa ya cigaba.. Kai Aliyu ga yusrah nan da Hauwa'u kasan da zancen su .. Tunda haka ne abun se ku shirya soon za'ayi dukan ku baiko Usman ga fareeda nan farouq ga sumayya nan sadeeq ma ga hafsat nan.. Khadeeja kuma zan samo maki wani inshaallhu kinji.. Ta gyada kai.... Nan yace "na sallame ku"... Duka tashi sukayi suka fita.. fannah bata saurari kowa ba gida kawai ta wuce.. Bama ta kula da mummy dake parlor ba ta wuce sama.. Fadawa saman gadon ta tayi tana kuka sosai fuskar Amoon kawai ke fado mata.. Kuka take sosai ta rasa dalili......
Mummy bata tashi tabi fannah ba har lokacin tana parlor kawai ta barta ne tayi kuka me isarta.. Daddy ne ya shigo.. Mummy tace "wai daddy meke faruwa ne".. Zaunawa daddy yayi.. "Tana son Aliyu sosai nasani shiyasa take wnn kukan amma hukuncin da baffa ya yanke kawai is the best tayi hakuri da duk wanda ze zaba mata kokuma ta nemi wani fakat shine kwanciyar hankali.. Duk wani sauki daza'a samu daga gareta ne.. Inda abun yazo da sauki ma hutun nasu ba wani bane next week zata koma sch kila hankalin ta yafi kwanciya idan bata ganin su".. Mummy ta gyada kai.. Dan itama tana tunanin hakan shine zefi.. Kodan sbd su jiddah...
.. Maganar wanin da baffa ya fada ne take tayiwa Amoon yawo a ransa.. Sadeeq ya kama hannun sa.. "Pls take this easy".. Kamar jira Amoon yake yace "sadeeq I will not wlh wlh kaji na rantse babu me auran min mata kuma tabbas duk wanda yayi gigin haka sena batar da kowaye fannah tawace ni kade kuma babu wacce zan aura a cikin su babu wacce nace inaso dan haka babu wacce zan zauna da ita a cikin su kuma kowaye ake shirin bama fannah yazo ina jiransa"... Daga yanda yake magana kasan a he mean what he said.. Su jiddah dake parlor suna jin abinda ya fada duk suka juyo suka kallesa.. Nunawa yayi kamar be gansu ba har ze fita yaji muryar mom.. "To shugaban masara kunya.. Da ba'a fada maka abinda zuciyar ka bataso shugaban yan kafiya.. Dan Allah idan an aura maka su ka maido mana su a ranar.. Se musan ka isa.. Muga iya karshen takama.. Shashasha kawai.. Wlh tallahi Aliyu ka kiyayemu.. Wato kai idan ka kafe babu me tankwara ka.. Mu zuba mugani mu da kai".. Ko kala bece ba yayi ficewar sa ba tare daya kara kallon kowa dake parlorn ba.. Dad yabi dan nasa da Kallo.. Shide yasan yanada kafiya Amma Amoon ya takesa ya murje.. Dan duk family dinsu babu me kafiyar Amoon.. Be cika shiga abubuwa ba amma fa idan ya tsaya a A to dole A din nan za'a tsaya haka yake shi tun yana karami..
More comments more typing...
Urs
✨✨✨
Nafeesatuu...😍😍
.....

*💫❤LOVE CYCLE✨*


Written by

*@nnafie🖤*
(Smll but mighty😉)

*writer of*
Saif
Adaan
Wata mafita
Saboda duniya
Love cycle......


Bismillahir rahmanir raheem

💫❤Love cycle❤ (26)✨
fannah ta kalli wayar ta dake ringing... Numbern da Amoon ya tura mata message ranar nan ta gani..seda gaban ta ya fadi.. Ganin ta kusa tsikewa yasa ta dauki wayar tare da yin sallama.. Daga can ya Amsa tare da fadin "Aliyu Raddah".. A hankali tace "na gane ai" yace "good..why did you say yes akan batun Baffa?"... Tace "because that's the best for both of us"... Amoon yadan tabe baki yace "do you think cewa wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login