Showing 6001 words to 9000 words out of 100889 words

Chapter 3 - Love Cycle Book 1 Complete Hausa Novel

Annafie   

10 Feb 2025

224

can ba aure ba.... Muhammad kau aiki yake sosai kudi sun zauna har yagama gida halimatu ma suna exams dinsu ta karshe ne yanaso ya gabatar da ita ga iyayen sa amma yana tsoro baze iya aure ya barta ba sbd besan yanda zatayi ba zata iya komawa ruwa Ranar kwatsam sega baffa shida Ibrahim a parlor suka iske Halimatu tana karatu... Wani kallo ya mata kafin ya daka mata tsawa yace mata daga da ina... Tsawar da baffa yy ita tafito da Muhammad daga daki... Cak ya tsaya ganin su Baffa... Baffa yace "me wnn take a gidan nan" kasa magana yy gaban sa na faduwa baffa ya girgiza kai yy yace well LA kyau ta to ta gaggauta barin gidan nn kai kuma kafin jibi na ganka a Nigeria amma ma bani kunya... Daga haka suka fice cike da fushi.... Zubewa Muhammad yy a wajen yana kallon Halimatu data rude cike da tsoro.. Yama rasa me zeyi kawai ya yanke shawarar ya tafi da ita ya masu bayani haka kau akayi a ranar suka wuce Nigeria da Halimatu da take cike da tsoro... Muhammad tawa baffa bayanin komai da kudinsa akan halimatu se baffa yace "Allah ze bashi lada amma baze yarda ya aureta ba dan baze iya hada jini da ita ba nan Muhammad yace shifa se ita dan baze iya auran wata ba baze iya rabuwa da itaba sbd shine silar rabuwar ta da iyayen ta nan Baffa yace sede yanemi wani uban bade shi ba... Hakan ya daga hankalin Muhammad gashi duk yan uwansa sun juya masa baya seda Muhammad ya hadasa da Liman da kuma wani malam hamisu snn ya yarda aka daura auren Muhammad da Halimatu sede me a ranar Baffa yace yabar gidan ya cire sa daga cikin jerin yaran sa baya bukatar ganin sa shide be masa baki ba amma baya son ganin sa kusa dashi.. Hankalin Muhammad ya tashi gashi cikin yan uwansa babu me masa magana se sa'adatu da Raheenah... Yana ji yana gani yabar gidan mahafinsa sukazo suka ci gaba da rayuwa da Halimatu tana yawan cewa su su koma su roki gafara yasan zasu hakura yace aa ta bari se sun haihu yasa baffa ze yafe masu... Halimatu bata haihu ba seda suka shekara hudu ta haifi yarta kyakkyawa ya sakawa yarinyar sunan mahaifiyar sa wato khadijah.. Daga nan suka dauko hanyar dawowa Nigeria cike da farin ciki da kuma sa ran baffa ze amshe su.. Lokacin yaran duk sun girma da dan wayonsu .snn an hafi suma mata yan jarirai dasu akwai yusrah, sumayyah, jidda, fareeda, da Hafsat.. Duk kwanaki ne tsakanin su.. .. Yanda Muhammad yy tunani ba haka bane dan baffa cewa yy ya bar masa gida baya bukatar sa baya bukatar ganin sa yacire sa daga jerin yaransa da haka yatafi ya basa waje... Kuma ko yan uwansa babu wanda ya nuna yy farin ciki da ganin sa kodan baffa ya nuna baya bukatar sa knn... Hakan ba karamin cin ran Muhammad yy ba yaji shiko baze kara zuwa wajensu inhar basu neme sa ba yaji kasar ma bayason ta... Tun daga nan suka dawo UK da zama suka cigaba da kula da khadeeja da suke cema fannah sosai Muhammad yake son fannah dan yana ganin bashi da wata dangi sama da ita se matar sa dake mugun yi masa biyayya yana matukar alfahari da ita mace ce mai roko da addini da sanin yakamata ya daga sosai wajen koya mata hausa ta kau rike kamar yarenta.. Snn wasu al'adun hausar ma duk sunayi dan yanaso Fannah ta san yaren ta kuma alhmdullah ta taso cikin sa.. Duk wata soyayyar su na kan fannah dan ita kade suke kallo a matsayin dangin su snn ita kade suka haifa se da ta shekara tara snn suka mata kani Aliyu suna ce masa hisam suke nan su hudu suke rayuwar su se abokanai na mutunci tun mummy na masa maganar komawa Nigeria harta dena dan tasan beso koda Fannah ta matsa tana so ta tasani dakyar yabata lvr ranar kau yini yy suku ku dan kamar an fama masa inda yake masa kai kayi.. Shekara goma shatara knn be taka kasar sa Nigeria snn be ga wani dan uwansu ba... Amma yana dan jin lvrin su kamar Ahmad yana US dan rabi rayuwar sa anan yake rabi kuma a Nigeria shida iyalansa rabiu ma yana dan zama sudan haka ma Ibrahim yakan dan zauna Us amma ba kamar Ahmad ba... Sede basu taba haduwa ba.. Snn babu wanda yasan gidan sa... Daddy yy arziki sosai kamar yanda yasan suma family dinsu sun kara akan dan familyn Radda ya kara bunkasa wurare dayawa ansansa shiyasa shi ya dena amfani da Radda sbd bayaso wani yaji lavarin sa koyasan inda yake haka ma su fannah baya musu amfani da Radda duk da wasu sun riga sunsan sa da Radda amma abin da sauki... Wnn knn
....
Dan lumshe idanu tayi a hankali bacci ya dauketa....
Se gab da azahar ta tashi snn tayi sallah ta tafi dakin mum can suka zauna har daddy ya dawo sukayi dinner tare.. Snn ta koma dakin ta tahau chat... Bata wani jima tanayi ba ta sake kwanciya wani baccin se safiya washe gari friday basu da lectures dama practical ne zasuyi ta an daga se Monday dan wani sabon doctor ne ze zo ya masu bayani akan wani surgery na ido... Weakend dinta maryam ce tazo sun dade suna fira da shirme a gida kafin su tashi suje gidan su Vaneesa daga nan suka fancama yawo cikin gari... Ranar Sunday kuma wuni tayi tana research game da surgery din da zasuyi gobe dan ita tanaso taga tana communicating a class Fannah yarinya ce me kokari da ko a department dinsu masu irin kanta kadan ne....
Monday...
Tsaf ta gama shirin ta ta dauki komai da take bukata ta dauki labcoat dinta ta fita.... Koda taje apartment din maryam har ta gama shirin ta a nan wajen maryam tayi breakfast daganan suka wuce a babban teaching hospital din dake sch din tayi parking suka shiga ciki sunzo gab da zasu shiga lab din ne ganin kowa da labcoat yasa ta fara zare idanu ganin babu tata a hannunta maryam ta kalleta tace "hey girly where is ur labcoat?" Dafe kai Fannah tayi "oh god na barshi a apartment dinki" maryam ta zaro idanu tana duba wrist watch dinta snn tace "huh is already tym bamu san halinsa ba kar mu fita ya shigo kokuma bari na kira maid dita seta shigo taxi ta kawo ko" gyada kai Fannah tayi tana tunanin Allah yasa kar ya shigo dan bata sani ba ze barta ta zauna ba labcoat koko... Bakin kofa suka tsaya suna jira da adduar Allah yasa tazo kafin doctor din ya shigo... Sede addu'ar ta bata karbu ba dan mutane ne suka fara shigowa ana natsuwa cewa gashi nan... Zuwa sukayi suka zauna gaban Fannah se faduwa yake mutane se kallon ta suke ganin bata da labcoat.... Tsit akayi sbd shigowar sa.. Yayinda lokaci guda gaban Fannah ya yanke ya fadi lokacin da ta daura idon ta akan guy dinta da ta gefawa tissues sanye cikin suit blue black da suka matukar amsar sa snn suka dace da fatar jikin sa gashin kansa da yake baki yasha gyara inda ya kwanta lufluf kyawawan idanunsa sanye cikin farin glass se yakara ma fuskar sa wani kyau lips dinsa da suke pink se ya kara wani haske... A tare maryam da Fannah suka kalli juna cike da tsoro.. Kallon sa sukayi jin cool voice dinsa na ratsa kunnen su... "Am Dr. Amah nice meeting you all" a tare akace "welcome sir"... Dan binsu ya rinkayi da idanunsa yana nazarin su kafin ya sauke su akan Fannah.. A lokacin ji tayi kamar ta shide sbd tsoro ko maryam da ba ita ake kallo ba dauke numfashi tayi.. Yana kallon ta da kyau yace "hey you".... Daga mayan idanun ta tayi ganin ita yake kallo yasa Muryar ta na rawa tace "si...sii.. Sir" yace "where is ur lab cloth" wani miyau ta hadiye ganin yanda kallo ya dawo kanta tace "sir.. I.. I.. Forget ..t..it but its on the..way.." Katse ta yy yana daga mata hannu kafin ya dubi sauran yan class din yace "class a medical student is coming into the lab for practical without lab cloth is that student a serious student" a tare akace "no sir"... Juyowa yy yana kallon ta tare da nuna mata kofa yace "out of my class" muryar ta na rawa tace "sir.. am srr... " "I said out my Frnd".. Ya katseta cikin tsawa... Da sauri ta fita tana danne kukan da ya taho mata... Bata son missn class din nan ko kadan ko daya batayi marhabun da cewa wnn shine doctor dinsu ba bata fi minti biyu da fita ba aka kawo mata labcoat din ta dawo tana kuyo cool voice dinsa inda yake bayani cike da kware.. Seda ta saita natsuwar ta kafin tace "permission to join the class sir".. Wani kallo ya juyo yana mata kafin ya dauke kai yace "come in but stay by the door and keep standing ur punishment for coming late".... Tsayawa Fannah tayi tanajin kamar ta tafi dai dai class din is very important da wlh bata zama.. Tana kallon yanda yake kowaya cike da kwarewa kuma ana ganewa ynx ana masu daga farko ne kafin sucida gaci... Ana masu bayani ne dallah da komai 4wks zasuyi sunayi snn su duba result...tym na kurewa yace "who is ur class rep"... Nunata akayi.. Hakan yasa ya kalleta shima kafin ya kallesu da mmki yace "did she deserve or have any qualities of being a leader?" Shiru duk akayi ta be baki yace "well I knw she don't even know her responsiblity so class we shall meet next week bye" daga haka ya shige wani office dake Lab din.... Fannah ce farkon fita tasamu wani waje ta zauna ta fashe da kukan da take dannewa... Maryan ce tazo tana lallashin ta sbd tasan she's is hurt ya dizgata over... Vaneesa ma ta fara bata hakuri.. Seda ta dena kukan ne maryam tace "mujeki basa hakuri tun kafin abun yy nisa babban course yake daukar mu rasashi matsalane... Gyada kai kawai fannah tayi tana danne bacin ranta zatajene kawai sbd tana tsoron caurse dinnan... A office din suka samesa tsaye yana gyara wrist watch dinsa suka gaisar dashi dage gira yy batare da ya amsaba yace "what?".. Maryam ta zunguri Fannah... Murya ba rawa Fannah tace "sir am..am sr...srry for the other and today pls forgive me is a mistake sir".... Ta fada kanta kasa... Budar bakin sa se cewa yy "can I have my way pls" ya fada cike da wulakanci ba shiri suka matsa ya fice ya barsu tsaye kamar gumaka.....
Juyawa Fannah tayi ta fice tana share hawayen ta da sukaki tsayawa suna fitowa maryam na iskota.. "Pls Fannah calm down everything will be settle ohk"... Cike da tsiwa Fannah tace "let it continue be like that I will not apologize again because I hate down grading i can't take it wlh"... Maryam tace "Fannah you knw this not the solution ryt just calm down lets find a way to settle this kinsan de kece a kasa ko" cike da masifa Fannah ta bude baki zatayi magana maryam tayi saurin rufe mata baki ganin Dr. Amah din yazo ze wuce ta saitin su.. Harara fannah ta zabga masa yayinda maryam tayi saurin gaisar dashi ganin ya juyo sun hada ido .... Kafin ya Amsa Fannah taja wata tsuka tabar wajen duk binta sukayi da kallo kafin ya juyo ya kalli maryam da take wani zare idanu cike da tsoro... Murmushi ya sakar mata wanda seda taji kamar ta shide itama ta mayar da yake snn tabi bayan Fannah da sauri......
A garden ta iske fannah ta kifa kai tana na kuka rungume ta maryam tayi kafin ta kama hannun ta sutafi wajen mota... Maryam ce ta jasu ita ta kai Fannah har gida rudewa mumm tayi tana tambayar meya faru... Maryam tace "kanta ne ke ciwo"... Dakin. Fannah ta shiga maryam na kallon Fannah tace "fannah just think of what you did kin kyauta knn" fannah ta tabe baki kafin tace "kawai bazaki gane ba maryam" shhhhhh maryam ta katse ta "naji but a matsayin ki na dalibar sa yakamata ki basa hakuri koda kau me ya maki dole ki sauke kanki kasa"... Tana gama fadin haka ta fice bayan ta aje mata key din motar ta.... dan tabe baki fannah tayi tanajin wani irin haushin Dr. Amah din.. Lumshe idanun ta tayi a hankali bacci ya dauke ta...se 2 ta tashi da sauri tayi wanka ta tayi sallah snn ta fito cin abinci... Mumm da hisam na parlor dining ta wuce ta zubo aplate snn ta dawo parlor ta zauna tana ci.... "Meya sakaki kuka a sch yau"... Ajiyar xuciya ta sauke tasan inhar tayi karyar ciwo mumm zata gane ta... Tace "mumm is just misundersterding nida wani lecturer"... Mumm ta gyada kai cike da daure fuska tace "I see can you start growing da har kika fara samun matsala da lecturers dinki so listing to me attentively kije kisamesa and apologize if not I will show you the real me ai naji tym din da maryam na maki maganar kinaso ki zama masiffiya ko?" Kamar Fannah zatayi kuka tace "am srry mom i'll apologize".... "Better"... Daki fannah ta koma idanun ta cike da hawaye wlh da ba dan mummy ba sede sucigaba da tafiya a haka......

More comments more typing...
✨✨✨
Urs
Nafisatu😍

.....
*💫❤LOVE CYCLE✨*


Written by

*@nnafie🖤*
(Smll but mighty😉)

*writer of*
Saif
Adaan
Wada mafita
Saboda duniya
Love cycle......


Bismillahir rahmanir raheem

💫❤Love cycle.. (4)✨
Washe gari kamar yanda tayi alkhawari sukaje lab din domin tambayar office dinsa.. Aka masu kwatance cikin teaching hospital din suka shiga direct inda office dinsa yake sukaje.... Hadadden office ne Wanda daga gani kasan meshi babba ne... A ran fannah tace "dole yy wulakanci yana jin kansa sama".. PA dinsa suka tambaya anan aka tabbatar masu be zo ba. bama ya zuwa se yana da aikin da zeyi kamar surgery ko zema student class da kuma yan minor things da ba'a rasa ba.... Haka suka juya jiki a sanyaye... Washe garima suka gama zagayen nemansa baya nan in takaice maku seda sukayi 4dys suna nemansa amma kome kama dashi babu ranar sun gama zagayen neman su sun gaji suka yada zango wani garden Wanda yake shiru suka zauna... Maryam ta dubi Fannah da take ta wani daure fuska dariya tayi tace "easy mana love saki fuskar mana" kamar fannah zatayi kuka tace "wlh nagaji sbd dalili biyu yasa nake neman afuwar sa"... Mekewa maryam tayi tace "let me get something for us dan nasan harda yunwa take cinki" ficewa maryam tayi yayinda ta dauko wayar ta tana dannawa ... Kamar ance ta daga kanta ta hangosa daga can zaune cikin shigar kananan kaya yana amsa call.. Juyowa yy waya kare a kunnensa suka hada idanu... Da sauri ta dauke kanta gaban ta na faduwa.... dan dakewa tayi tana ganin wnn ma wata dama ce for her to apologize.. Hakan yasa ta tattaro duk wani courage ta tashi ta nufin inda take.... A hankali take tafiya toward him yana kallon lokacin da ta taho seda ya bari tazo gab snn ya mike ya nufi hanyar fita.... Cak ta tsaya tana kallonsa har ya fice.. Jiki a sanyaye ta juya hawaye cike a idanunta.. Tunda take bata taba ganin dan wulakanci da rainin hankali ba kamar sa..... Zama tayi bayan ta gama share hawayen ta tana daure fuska tanaji a ranta ta gama bin wnn mutumi har abada da sunan bada hakuri.... Koda maryam ta dawo bata fada mata komai ba ta ware suka cigaba da firar su... Tundaga ranar Fannah bata kara neman sa ba
Monday...
Seda Fannah ta tabbatar bata manta komai ba snn ta taho ta biyawa maryam sann suka taho yauma kamar wancan karon sun shiga bada jimawa ba ya shigo sanye cikin suit sede be sanya rigar saman ba se ya daura lab coat a sama.... Gaisar da class din yy duk suka amsa kafin ya fara bin yan class din kallo da lumsassun idanun sa har ya daura a kanta... Gabantane ya shiga faduwa amma seta dake ta daure fuskar ta... Cikin cool voice dinsa yace "class rep ryt?" Gira daya ta dage tana kallonsa cike da jin haushin sa.. Ya tabe baki kafin yace "any way come and stand by the door ur permanent position in my class"... Bnx tayi batace komai ba... Har seda ya juyo cike da isa yace "am I not talking to khadeeja".... Ba shiri fannah ta dawo inda yace cike da mmkin wnn bawa to ina ma yasan sunan ta... Harde hannu tayi tana zuba masa harara tana kallon yanda yake masu bayani gabadaya class din take da yanda kowa ke cooperating amma ita kam tayi shiru dukda kuwa ta sani shima kuma be tambaye ta ba be ma kalli inda take ba... Allah ya gani bata son tsayuwa amma ya zatayi ta nuna kamar be dameta ba..... A haka har ya gama ya fice .... Tabe baki tayi snn ta fice ko jiran maryam batayi ba taje inda inda suka saba zama ta tsaya.... Maryam taxo tana dariya tace "uhmm gsky mutumin nan yaci kai keda kowa ke kaffa kaffa yake ji dake shine shi yace ba haka ba wow I love this game can't wait naga karshen sa.."fannah da take danna wayar ta bata dago ba tace "i will be the winner while him the loozer" maryam na zama tace "uhm then after that what will be the next thing" tabe baki tayi tana mikewa tsaye "let me get us something"... Gyada mata kai kawai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login