Showing 75001 words to 78000 words out of 100889 words
ya bata tausayi itama setaga duk ya rame tasan shi kansa yana cikin damuwa sosai dauriya ce kawai irin tasa.. A hankali tace "duk ka rame kayi rashin lpy ne".. Ya kalleta se kuma ya girgiza kai.. Yace "just pray for us pls pray for us".... Idanun ta ya cika da kwalla.. Wayar ta ne yy ringing duk suka kalla sultan ne... Amoon ya ringa kallon wayar zuciyar sa na tafarfasa yanada wani mugun kishi inde akan Fannah ne... Lura da hakan da Fannah tayi ne yasa ta dauki wayar ta kashe gaba daya.. Dan sauke ajiyar zuciya yy se kuma ya kalle ta.. Ta langwabar da kai "srry..". Yy murmushi tare ta kamo hannun ta a hankali yace "I love you".. Ta dan lumshe idanu a hankali se kuma ta bude kamar zatayi kuka tace "am afraid".. Shafa gefen fuskar ta yayi a hankali yace "do you love me?". Gyada kai tayi tana hawaye.. Kafin a hankali tace "yes I love you.. I love you Aliyu.. I don't knw how to say it but you're the only person I love"... Se kuma ta fashe da kuka...rungume ta yayi cike da farin ciki "I love you too, I love you more and more dear".... Ya fada cike da tsananin sonta.. Da bayajin akwai wani mahaluki dayake mata kalarsa kuma bayaji ze iya bari wani ya mallaketa ba shi ba sede idan babu ransa sede idan mutuwa zeyi".. Fannah tanajin yanda zuciyarsa ke bugawa.. Gashi sosai ya rugumeta ... A hankali ya dago ta yana share mata hawayen.. Ta danyi murmushi tare da janyo jacket dinsa ta rungume tace "I love this jacket".. Yace "really zan kawo maki irinta".. Ta girgiza kai.. "No wnn nake so.sbd taka ce", yayi murmushin dake Kara masa kyau yace "abuna naki ne".. tace "thank you".. "Ba thank you ba abinci zaki zo ki ci and ni zan baki da kaina".. Fannah ta noke kafada.. Dauka yayi aje mata a cinya "I'll watch you eaten.. One day I will feed you my self".. Fannah tayi masa gwalo.. Murmushi kawai yayi yana kallon ta happily... Ita kanta Fannah duk setaji ciwon kan ya tafi rabon data samu tym dashi irin haka har ta manta...... Koda ze tafi ji tayi kamar karya tafi.... Yana tafiya maryam ta shigo tana kallon ta Fannah tace "yade kallon fa".. "Dole na kalleki ai har kinji sauki sbd maganin ki yazo".. Murmushi kawai tayi "kinga laifi na?"..
Ranar Fannah ta ware.. Ita kanta mummy tasan dalilin ware war tata kuma taji dadi kullum Addua take ma diyar tata Akan Amoon ita kanta tayaba da hankalinsa dakuma irin kaunar da yake wa Fannah. Tana kuma adduar Allah yasa rabon ta ne"..... Koda dare ranar bnd chart da Amoon babu Abinda take.. Ko a rayuwar su tada bata taba sakewa dashi ba irin yau..". Ita kanta bata taba sanin haka yake ba seyau data sake dashi.. Da kyar ya bari tayi bacci... Suna tashi daga lectures ya tura mata message wai ta jira inda suka saba haduwa.. Duk yanda tayi da maryam ta bita kin zuwa tayi.. Hakanan ta wuce.. Tana zuwa seta gansa a zaune.. Ta karasa tace "ashe kana nan shine kace na jiraka..". Ya aje wayar sa yana kallon yanda tayi kyau.. Yace "wancan karon nine nazo na sameki so today I decided kixo ki sameni"... Dan murmushi tayi seta tuna ranar daya fara samun ta anan wajen ranar da yace zasu zama frnds..... Zaunawa tayi tana murmushi.. Yace "it all started here anyway yaushe zaki rakani hand ball"... Ta kallesa tana ware idanu fuskan ta dauke da murmushi tace "naje ka kara buga mun handball ka ki bani hakuri. Idan kuma nayi magana kace zan saka maka ciwon kai".. Ya danyi dariya.. Dan yana sane ya buga mata ball din nan.wancan lokacin." Ta hade rai "oh dariya ma na baka ko karfa ka manta ko hakuri baka bani ba wancan tym din". Ya ware hannu yace "hakurin me bayan kin rama you throw a tissue for me ko kin manta"... Dan hararansa tayi "kai abubuwa nawa kayi mun see you".. Yace "srry ynx de yaushe zamuyi an jima ku shirya sena nazo muje" ta gyada masa kai... Kamar yanda yace hakan kau akayi suka shirya suka shirya harda hisam.. Yazo ya dauke su.. Fannah ta rinka satan kallon sa ganin yanda kayan suka mugun yi masa kyau.. Dan hada ido sukayi ya kashe mata.. Suna isa su maryam suka bude suka fita zata fita yayi saurin kamo hannun ta.. Ta juyo tana kallon sa yadan kashe mata idanu yace "se satar kallona kike nayi kyau ne".. Tace "zero bakayi ba".. Dariya yayi sosai har seda ta shagala da kallonsa.. Yace "ba'a son karyata babba amma karya kike".. Fashewa tayi da dariya.. "Tace "oh. Hakama zakace".. Bude kofar yayi ya fita...itama fita tayi.. Tuni dama maryam taja hisam sun tafi wasan su.tare sukayi komai dashi se wani langwabe langwabe take shikam ya biye mata karshe ma cewa tayi batayi shima tace bazeyi ba.. Dole ya hakura ya siya masu kayan ciye ciye.. Se yamma sosai snn suka koma gida.. Su maryam na fita daga motar yace "I will be living tomorrow" ta kalle sa da sauri "zuwa ina" yace "America dama ai just squeeze amma inada aiki dayawa".. Tace "se yaushe knn".. Ya dube ta.. Da sallah kawai mu hadu a katsina"... Ta ware idanu "har sallah".. Dan ita har tsoran komawa take baffa ya bata wanda yace.. Kuma tsoro takeji kamar yasan tunanin da take knn ya kamo hannun ta "inshaallahu wnn karon baza'a samu matsala ba babu dadewa saura 2weeks ramadan and ga waya nan koda yaushe kuma tare kinji".. Gyada masa kai tayi jikin ta a sanyaye yace "I love you".. A hankali tace "love you too"... Yadan langwabar da kai kamar zeyi kuka "to ki saki ranki mana".. Budewa tayi ta fita.. Dan zata iya fashe masa da kuka. Dan murmushi yayi jikinsa a sanyaye ya yaja motar.. Fannah ta daure batayi kuka ba...ta zauna gefen gado tayi folding hands dinta trying hard batayi kuka ba.. Duban wayar ta dayayi kara tayi alamar shigowar sako.. "Don't cry pls I love you" shine abinda ya turo mata se hawaye sharrr maryam tace "to me arhar hawaye me kuma ya faru".... Nan ta fadawa maryam yanda sukayi ta karasa da fadin tsoro nake ji maryam".. Maryam tace ki kwantar da hankalin ki inshaallahu komai ze zo da sauki..
Hankalin Fannah ya kwanta sbd yanda maryam ta kwantar mata da hankali.. Ranar da daddare sun dade suna waya kuma hankalin ta yadan kwanta... Washe gari Amoon ya wuce America Fannah sam sam bataji dadin tafiyar sa ba..
Tunda yatafi be yarda ya barta da kewar sa ba kullum suna waya wani lokacin harda vedio call... Wnn karon shakuwar su tafi ta da... A haka har a aka shiga watan azumi... Kowa ya maida hankalin sa kan ibada.. Ana saura sati sallah su Fannah suka koma Nigeria.... Koda taje kamar yanda tayi tsammani ne su jiddah babu wanda yabi ta kanta.. Itama bata bi ta kansu ba sbd tasan wanda suke domin shi ita yake so ba su sede tanajin tsoro sbd bata manta da maganar baffa ba akan cewa ze sama mata wani kuma taga alamar har ynx sultan na kan bakansa...
Yanda chucu ke nan da nan da Fannah kade ya isa ya nuna maka cewa tana son yayan nata da ita.. Itama sun kulle sosai da farouq.. Ana saura kwana biyu sallah ne tafiyar su kt shiyasa kowa ya fara shiri dan dama duk sallama acan sukeyin ta a mota ci duk suke tafiya kowa ze sami motar da ze shiga su tafi..sultan ya turo mata message akan cewa su tafi a motar sa.. Amma ta share batayi masa reply ba.. Ranar da zasu tafi duk suna gidan Baffa sun fito duk za'ayi tafiyar tana ganin sultan se kallon ta yake amma ta nuna kamar bata gansa ba.. Baffa na fitowa dasu Abie kowa ya mike duk suka fita.. Da abie da baffa da daddy mota daya suka shiga.. Fannah ta rinka kallon motar Amoon dake wajen da tunanin Ko wani ne ze tafi da ita.. Bata gama tunanin da take ba taga ya bude ya fito.. Babu shiri ta ware idanu cike da mmki.. Dayawa ma kallon sa suke da mmki.. A wajen daga dad se mammah da saleem suka san ya dawo jiya amma ko chucu bata sani.. Ya karasa wajen iyayen nasa ya gaisar dasu snn yaje yana mikawa su sadeeq hannu harda sultan.. Su chucu suka gaisar dashi.. Yadan kashewa Fannah idanu ta dauke kai tana murmushi dayawa a wajen sun gani amma babu wanda ya kula dad dinsa ya girgiza kai kawai.. Mammah tace "kai da suwa zaku tafi".. Yadan sosa kai.. "Mammah zan tafi da chucu da Fannah or chucu su tafi da farouq I will go with Fannah and fareeda".. Kowa a wajen kallon sa kawai yake harda Fannah dan har kunya taji.. Karasawa yy ya bude front seat yana kallon Fannah yace "get in".. Kanta kasa taki dagowa Abbu ne yace "jeki mana mamana".. A hankali ta karasa fareeda ma tabita".. Dadi kamar ya kashe chucu domin taga yanayin reaction din su jiddah da sultan bana farin ciki bane.. Murmushi kawai Dad yayi yana kara mmkin dan nasa.. Be kara bi takan kowa ba ya bude motar sa ya shiga.. Yayi reverse snn ya dago suka hada ido da sultan kashe masa ido yayi snn yaja motar ya fice da mugun gudu.....
More comments more typing...
Urs
✨✨✨
Nafeesatu...😍😍
......
*💫❤LOVE CYCLE✨*
Written by
*@nnafie🖤*
(Smll but mighty😉)
*writer of*
Saif
Adaan
Wata mafita
Saboda duniya
Love cycle......
Bismillahir rahmanir raheem
💫❤Love cycle❤ (28)✨
Sultan ya runtse idanu zuciyar sa nayi masa wani irin zafi.. Ya dubi su yusrah da take ta sauke ajiyar zuciya kasan kadan take jira ta fashe.. Farouq ya budewa chucu mota zuciyar ta fess ta shiga se kanwar sa wacce ke bima Jiddah.... Jiddah kam tare dasu mamie ta tafi.. haka ma yusrah motar su mom tafi dukan su babu wacce bata kuka.. Hafsat dama tafiyar su daya da Sadeeq..
Fareeda ta gaisar da Amoon ya kalleta ta mirror yace "fareedan umma ya sch".. Tace "Alhmdllh".. A hankali Fannah ta gaisar dashi.. Ya noke kafada "bazan amsa ba"..ta Langwabar da kai "why".. Yace "fareeda baki ji me tace ba wai good morning haka ya kamata mata ta gaisar da mijin ta kamar ma batayi murnan ganina ba".. Fareeda kam murmushi kawai take Fannah ta ware hannu "but you didn't tell me you're coming".. Yace "umm na koma knn".. Tayi murmushi batace komai ba...yace "zaki gane kurinki kika sani ma ko acan kafin mu dawo za'a daura auren"... Fannah ta ware idanu yadan kashe mata ido... Yace "kinga daga can kawai fit... Duk inda zanje tare zamu tafi yarinya".. Fannah de tayi shiru batace komai ba.. Ita kanta fareeda se murmushi takeyi.....
Tun basu yi nisa da barin Abuja ba suka fara bacci.. Ta mirror ya dubi fareeda ganin bacci take yasa ya maida idonsa a Fannah yanda take bacci se tayi masa kyau.. He just can't wait suyi aure yaga tana bacci tare dashi.. Dan kwantar mata da kujerar yayi yanda zataji dadin kwanciyar.. Snn ya shafa gefen fuskar ta a hankali... Dan bude idanu tayi se kuma ta lumshe..... Seda sukazo kaduna snn ta farka.. Tana kallon garin yace "kaduna".. Taita kallon garin.. Daga nan duk garin da suka wuce seya fada mata sunan sa.. Taita kallo cike da nishadi.. Idan kuma ta gaji seta koma bacci ... Zuwa 4 suka shiga cikin garin katsina... Fannah ta rinka kallon state din tata.. Ganin yanda take kallo yasa ya kamo hannun ta yace "kin gaji ko".. Gyada masa kai tayi ga azumi yace "anan za'a daura Auren mu".. Ya fada hankali yana dan murza hannun ta.. Fareeda setaji duk sun bata tausayi.. Hakika suna son junan su tasan idan akace za'a raba su zasu wahala... Tunda take tun tana yarinya ma bata taba ganin koda wasa Amoon ya nuna yana son wata ba.. Amma yau ko yanda ya rikayiwa Fannah a motar nan ya isa ta tabbatar cewa Amoon nason son fannah.....ita kanta ynx da sultan yaci ace ta ciresa a ranta amma ta kasa....
A babban family hause din nasu suka sauka.... Kafin ta fita Amoon yace "don't stress ur self wajen gaishe gaishen nan ki bari se ansha ruwa kinji"... Ta gyada masa kai snn ta fita... Duk yawan mutanen wajen da sultan ta fara hada idanu tana fita a motar dan kusan duk a tare suka isa.. Dauke kai tayi.. Tana kallon mutane dayawa da aka firfito sbd murnar ganin su.. Barin ma ita da kowa keson gani.. Kowa se zuwa yake yana rungume ta da yaba girman da tayi.. Fannah de se murmushi take ganin yanda kowa ke farin cikin ganin ta .. Dan daga kai tayi suka hada ido da Amoon yadan langwabar mata da kai... Alamar ta wuce daki mana.. Sede ta dauke kanta.. Ta cigaba da amsa gaisuwar da wata tsohuwa ke mata da tambayoyi se murmushi take ganin yanda tsohuwar ta hakimce saman kujera tana bayani da alama de kanwar baffa ce.. Chucu ce tazo ta kama Fannah tana fadin "Adda bari muje ta huta dan Allah kinsan ta gaji bakuma ta saba wnn doguwar tafiyar ba".. Adda tayi mata dakuwa "kinci ubanki Amadu haushi fa take ji bn kula ta ba".. Chucu ta murguda baki taja Fannah suka wuce wani daki daban... Fannah ta zuwa ta baje saman gado tana lumshe idanu "wlh na gaji ga wata irin yunwa".. Chucu ta harareta tace "bayan soyayyar da kukasha a mota se kuma kice kinajin yunwa na dauka a koshe kike".. "Ke da kika taho tare da yaya farouq kin koshi knn".. Chucu ta ware hannuwa "full wlh".. Fareeda data shigo ynx tace "itama a koshe take.. Dan yau nasha kallo nasan na biyo motar masoya ko kunya ta fa basaji"... Tashi Fannah tayi ta shige toilet tana dariya.. Ganin wani tsalle da chucu tayi ta rungume fareeda wai se ta bata lvri.. Ita kanta tun tanajin kunyar fareeda har ta ware ta rika biye Amoon a motar.. Kuma tasan daba dashi bane kila da tafi haka gajiya....
Adda ta dubi yusrah da idanun ta suka kumbura tace "ke kuma lpy keda baki rabo da fitina".. Yusrah ta murguda baki ta tashi ta shige dakin da mom ke ciki.. Adda ta tabe baki tana fadin "kyaji dashi nasan Aliyu ne ba wani ba".. Amoon da yadan kalleta ta gefen idon suka hada ido.. Dauke kai tayi ta nuna kamar ma bata gansa ba.. Dan murmushi yayi ya tashi ya koma kusa da ita tare da bata side hug. Ture sa tayi "kai nifa tsoro kk bani".. Daidai kunnen ta ya rada mata.. "Nifa na samu mata Adda".. Ta dan ware idanu.. Tayi masa alama da hannu akan wacece "ya rada mata "yanda tayi da fuska seda yayi saurin rufe mata baki dan karma ta daga zancen.. Ganin haka yasa tayi masa alama da zasuyi magana.. Tashi yayi ya fita yaki yarda ya kalli mammah ya yasan kallon sa take...
Fannah na idar da sallah ta kara kwantawa duk tsokanar dasu chucu suke mata bata bi takansu ba dan wlh ta gaji.. Quranin data gani ta dauko ta fara karantawa se gab da magrib snn ta aje .....
Fannah fareeda ce ta shigo masu da kayan shan ruwan su sukayi snn suka fita tarawi...
Washe garin ana idar sallah seda suka sha baccin su na gajiya snn suka tashi.. Ana yin azahar suka fara aiki kasancewar gobe sallah duk da akwai yan aiki dole su saka hannu sbd ayyukan dayawa.. Duk tare sukayi aikin amma babu wanda ya kula wata tsakanin ta dasub jiddah.. Sallah ce kade ke tashin su.. Chucu ta mikawa Fannah wasu kaji da aka gama gyarawa.. "Ki yiwa yaya dambun nama me yaji snn ki saka tafarnuwa".. Dagowa tayi suka hadu idanu dasu yusrah.. Taci fuska ta karba ta fara sarrafa ta... Tana gamawa ta saka a inda chucu ta miko mata ta dube ta tace "ina za'a aje".. "Kai dakin mu".. Fannah ta mike ta fita.. A parlor ta iskesu shida wani wanda da alama shima ba'a nan yake zaune ba jiya yazo "sageer" taji suna ce masa.. Dan gaisar dasu tayi ta wuce zuwa dakin su.. Ta aje .. Tana juyowa taga Amoon tsaye jikin kofa har ya bata tsoro.. Ta ja baya da sauri.. Se kuma ta shagwabe fuska tace "ka ganka ko" yace "nimene".. "Ka bani tsoro".. Ta gyara tsayuwa "to mene Acan".. Ta ware idanu "ina ruwanka".. Ya langwabar da kai "ke kikayimun da kanki".. Ta girgiza kai... Yy murmushi yace "just can't wait to teste it idan ansha ruwa zaki bani".. Fannah ta noke kafada.. Ya harde yace "sageer".. Ya amsa.. Ya dubi Fannah yace "come with me".. Bin bayan sa tayi bayan sun fita parlor yace "sageer waini za'a ma rowar nama".. Sageer ya ware idanu "wnn da kike gani maye ne mayen dambun nama ne ko bayan aure da kinyi ki boye".. Fannah tayi murmushi ta shige kitchen bama ta dauka sageer nada magana ba..
Koda aka sha ruwa duk yanda Amoon yaso cin naman nan kin yarda su hadu tayi karshe ma cikin mutane ta shige inda baze iya zuwa ba.. Se can da daddare tayi shirin bacci ya tura mata message "just craving for it amma kin hanani".. Tura masa tayi "srry".. Yace "no bad hope it will be the first thing I will eaten tomorrow after eid".. Ta tura masa da inshaallah.. Daga haka ta kashe wayar ta ta kwanta bacci".. .
Washe gari eid.. Sukayi duk wasu dabiun daya kamata .. Snn kowa ya shirya cikin kayan sa masu kyau..Fannah ta rinka kallon yanda su chucu sukayi kyau kamar wasu larabawa.. Chucu tazo saitin kunnen ta tace "you look so take away