Showing 54001 words to 57000 words out of 100889 words

Chapter 19 - Love Cycle Book 1 Complete Hausa Novel

Annafie   

10 Feb 2025

371

sukayi zasu gaisa nrml.. Wnn ne yasa a hankali a hankali ta fara sakin jiki dashi suka koma kamar da.. Snn da wnn damar yy anfani ya fara sako mata da maganar soyayyar sa ita kuma tana kokari wajen basa tym tunda baya matsawa rayuwar ta.. A hankali a hankali har wasu daga cikin family din sun fara kula da yanda suka fara shakuwa da juna.. Jiddah ta dubi Fannah tace "ynx kin sami sultan kin manta da Amah ko".. Murmushi kawai fannah tayi domin kau ko daya son Amah be ragu a ranta ba.. Tasan de sun shaku da sultan amma bazatace ta fara sonsa ba.. Kawai de tasaka sa a matsayin wanda zata iya aure idan har bata sake haduwa da Amah ba.. Farouq ne ya fito daga dakin sa.. Fannah ta bisa da kallo rabon ta dashi tunda yaje gidan su ranar nan yau 6dys knn sede suyi waya shima befi sau biyu sukayi ba setaga duk ya wani rame..hannun sa rike da car keys dinsa ya nufi fridge ta dauki ruwa yasha har lokacin Fannah kallon sa take.. Yana duban ta yace "cutie kallon fa" ta langwabar da kai "2dys banganka ba and duk ka rame kode baka lfy ne"... Yace "ko daya fa wlh aiki ne kawai.. Jiddah de kallonsa kawai takeyi.. Fannah tayi masa sannu snn ya masu se anjima ya fita.....
Abu kamar wasa shakuwa irin ta soyayya se kara shiga take tsakanin sultan da Fannah kuma dayawa a fam din ynx ansan meke tsakanin Fannah da sultan.. Farouq ko idan kagansa duk ya wani rame haka ma fareeda sede kullum tace zazzabi na dare ga kuma karatu.. But ita tasan dalilin ramar ta dan da gasken ta rame wanda ta taso tana so tun yarinta tana ganin yana soyayya da wata ba ita ba.. Tana kokarin cire damuwar a ranta amma ta kasa.. Ynx ne ta fahimci abinda su yusrah keji..
Su fannah suna zaune a parlor dukan sa harda dady wayar ta ya dauki kara ganin sultan ne tayi silencing wayar.. Yana katsewa aka sake kira.. Mummy ta kalleta ta kalli wayar kafin tace "pick ur call".. Daukar wayar tayi ta tashi ta haye sama... Da kallo duk suka bita.. Daddy yace "I think mamana fa tasamu wani".. Murmushi mummy tayi tace "yeah ba wani bane sultan ne".. Daddy ya dan yamutsa fuska "I thought ma farouq ne sbd yanda naga closeness din su da ita".. Mummy ta girgiza kai "bashi bane but koni na dauka farouq din ne".. Murmushi daddy yy "hakan ma yayi inde hankalin ta zefi kwanciya ai Alhmdllh but hankali na ya kwanta da farouq sosai but sultan ma is ohk" daddy ya fada daka gani kasan yana farin ciki.. Sbd duk tym din da ya tuna daughter din tasa tana son wani wanda bama su san inda zasu sameshi ba se hankalin sa ya tashi......
Fannah na daga wayar tana murmushi tace "kai a gaban su dad fa kk ta kirana".. Sultan ya ware idanu "oh srry nasaka wata taji kunya but mene najin kunya nida soon zanyi wuff dake".. Murmushi tayi "see you ai kaine wuff din"... Ya dan langwabar da kai "you knw what." Tace "se ka fada"... "Gobe mom zata zo so tana dawo wa nasan maganar auren mu zataje kunnen baffa dan zata fadawa Abie snn su fadawa baffa dadd Ahmad ma naji ze zo wai"... Gaban fannah ya wani irin fadi.. Yace "kinyi shiru".. Dan murguda baki tayi se kuma tace "no nide ba ynx ba ka bari zuwa naje sch na dawo".. Yace "no nima bawai ina nufin ynx ba but ai bazamu rinkayin abu without their knowledge ba".. Ta gyada masa kai a sanyaye tace "hakane"... Jin yanayin ta se ya canza wata firar sbd baya son duk wani abu daze sa taji ya gundureta... Sun dan dade sunayi fira kafin suyi sallama shima hafsa ce tazo.. Jan ta tayi suka fita wai zata rakata.. Seda suka biya gidan baffa domin daukar yusrah dan a motar tama suka fita.. Yusrah dake cikin farin ciki tace "wlh har na kosa mom tazo gobe nasan wnn karon dole ayi magana kan yaya Amoon.. Hafsa tace "ke ta Amoon ma kike bata ita ba".. Yusrah tace noo bazaku gane ba wlh a duniyan nan bani da babban burin daya wuce naga na auri ya Aliyu nasan duk wnn da munyi aure komai ze zama nrml..." Hafsa tace "ita kuma jiddah fa".. Wata tsuka yusrah taja "malama dallah karki batamun mood dina idan ina abu ki dena sakamun ita a lissafina........ Washe gari kamar yanda sultan yace Hajiya Maimuna tazo mom knn.. Sultan ne yaje ya dauko ta tun a mota yake ta bata lvrin wacce yake so.. Ita de mom dariya kawai take dan ta kula dan nata yayi mugun kamuwa.. Har suka iso maganar ta yake mata...
A part din baffa ta sauka kamar yanda tasama part din umma.. Dayawa ana ta shigowa gaishe ta but ita bata kowa take ba se mummy data shigo ynz.. Sosai ta Rugume ta tana murnar ganin ta mom harda kuka.. Duk da tanada zafi amma tanada rauni... Sun dade tare da mummy kafin ta tafi wajen baffa acan ta samu daddy nan ma wani kukan ta ringa yi da neman gafarar daddy..
Zaune Mom take a parlor su umma da mama da wasu saura daga cikin fam din duk suna ciki.. Sultan ma yana ciki.. Babu jimawa sega sadeeq da farouq ma duk suka gaishe ta da murna.. Mom ta rike haba "oh ni farouq baka da lpy ne".. Murmushi yy ya daga kai suka hada ido da sultan kafin yayi magana sega su fannah sun shigo.. Da sauri yusrah taje ta fada jikin ta "mummy na"...... Mom ture ta tayi tana amsa gaisuwar su fareeda idon ta na kan fannah da kanta ke kasa tana gaishe ta..." Zonan kiji dumin Mom din ki"... A hankali Fannah ta karasa kusa da Mom and Mom tayi hugging dinta "masha Allah kin girma sosai Allah ya rayamana ke".. Sultan ya karasa daidai kunnen Mom yace "itace mom".. Da sauri ta ware idanu "sultan are you for real?" Ya langwabar da kai "yes mom" "why didn't tell me that Fannah ce surukar tawa".. Sultan ya daga idanu suka hado ido da farouq.. Baze gane expression din fuskarsa ba amma yasan a halin da yake ciki ynx bame dadi bane.. Da ace zega fareeda tym din seya fahimci wani abu. But bayansu kowa zaka gani a parlorn yy farin ciki da maganar sultan .. Mom tace "oh yakamata duk na aurar daku na huta farouq dana Kuma ku fito da mata sadeeq dama ga hafsa Amoon kau ze dawo ya sameni" umma tace "aikam nima maganar sa na raina yazo ya hadasu duka biyun ya aura atoh dan bazan yarda su maida mu shashasha ba"... Mikewa yusrah tayi "umma bn gane ba wane irin mu biyu wlh babu wadda zan hadata da yaya Amoon" umma ta mata wani kallo "oh da kika samu ma zan saka baki har kike wnn maganar idan kikayi wasa se in barku dashi inga uban abinda zaku iya".. Mikewa yusrah tayi ta fice fuuuuu...
..
Urs
✨✨✨
Nafeesatuu....😍😍


*💫❤LOVE CYCLE✨*


Written by

*@nnafie🖤*
(Smll but mighty😉)

*writer of*
Saif
Adaan
Wata mafita
Saboda duniya
Love cycle......


Bismillahir rahmanir raheem

💫❤Love cycle❤ (19)✨
Duk binta sukayi da kallo idan ka cire farouq fa fareeda da bazaka iya tantance yanayin da suke ciki ba... Umma tace "ji shashasha idan Na barta da Aliyu se kace akwai yanda zatayi.. Ko wace se bakin ciki take ma er uwarta bayan idan ma aka barsu dashi sede duka su rasa".. Mom tace "barni dasu harda shi din ma duk zanyi tym dinsu"... Yusrah Na fita takusa cin karo da jiddah dazashigo.... Tsayawa yusrah tayi on a serious note tace "look malama". Hakan yasa jiddah ta tsaya tare da juyowa tace "do you have any business with me".. Yusrah ta mata wani kallon tara saura kwata.. "Baki kai matsayin da zan zauna Ina magana dake I just want to pass you a warning.. Idan ma kina hangen kanki a matsayin wacce zatayi rayuwar aure da Amoon to ki dena dan bama ke ba babu wacce ta isa taso abinda nake so"... Wani dariya jiddah tayi tana nuna kanta "ke kina ganin kin kai matsayin da zan hada abu abu dake ballantana yaya Amoon".. Nan suka rinka gayawa junan su magana... Sadeeq da sultan ne suka fito.. Sadeeq ne yadaka masu tsawa.. Duk fashewa da kuka sukayi.. Kama hannuwan su yy suka fita.. Sultan duk kallonsu kawai yake but gaba dayansu tausayi suke basa... Farouq ne ya fito .. Sultan ya bisa da kallo.. Kafin ya matsa inda yake yace.. "Mr it seems lyk you're not happy for me". Farouq dake yana kallon sultan "ban fahimce kana farin cikin me".. Sultan ya tabe baki "ai ko baka fadaba nasan baka farin ciki kuma nasan ynx haka zuciyar ka cike take da damuwa da kuma kishi".... Wani murmushi farouq yayi.. "Abinda ba auren ta kayi ba".. Sultan ya ware hannuwa "me kuma yayi saura tunda ynx ta yarda zata aure ni wanda take mahaukacin so ma na cire mata tunaninsa sbd ni".. Farouq ya gyara tsayuwa yana wani murmushi "ta cire Amah sbd kai.. Amma de kasan duk son da take maka be kai wanda take masa ba ko.. Sultan ya tabe baki "to ynx yana ina"... Farouq yace "good to kamar yanda kasa ta fara cire Amah zan iya sakawa ta cire ka kasan de ba kusanci ka fini da ita ba and ba abin mamaki bane kaga na kasara aikin da kafara".. Daga haka ya fice yabar sultan.. Dan jim sultan yy se kuma yadan tabe baki ya koma ciki....
Fannah ce zaune a dakin jiddah ta lumshe idanu.. Jiddah data fito daga wanka ta dubi fannah.. Karasawa bakin gadon tayi "ke yaushe kika shigo." Fannah ta bude idanu "ban dade ba".. "To lpyrki naganki somehow"... Fannah ta tashi zaune fuskar ta da damuwa tace "mom na gidan mu kuma maganar mu suke da sultan".. Dan murmushi jiddah tayi se tace "kina jin wani iri ko kamar Amah ya dawo ko?" Fannah ta gyada kai "duk yanda naso na manta da Amah na kasa ina pretending ne kawai"..jiddah ta girgiza kai dukan mu se a hankali wlh fannah da zaki san yanda nake ji akan yaya Amoon sekin tausaya mun barin dawar mummy hankali na ya tashi sosai and babban tashin hankalin yaya Amoon ne wlh yanada kafiya.. Idan ya kafe akan abu ko Dadd da kyar yake tankwara sa".. fannah ta kwanta ta maida idonta ta lumshe.. Jiddah tace "bari na hado breakfast yunwa nake ji"... Doguwar riga ta saka snn ta fita ... Fannah ta maida idon ta ta rufe kamar me bacci...
Kamshin turaren da taji ne yasa ta bude idonta. Suka hada ido yace "baki da lpy ne"... Fannah ta tashi zaune kamar zatayi kuka tace "yaya farouq ina zaka" yace "kano. Baki da lpy ne.." Dan langwabar da kai tayi.. Ya dauki turaren jiddah ya fesa snn dawo kusa da ita yana dan murmushi yace "ko zaki bini ne" ta gyada masa kai da sauri... yace "kuma yaka mata ki dan zagaya kuma kafin ku koma sch"tace "wlh ko".. Yace "nayi busy these days da wata rana munje ko kaduna ne but me be idan kin dawo se muje but ynx tell me meke damunki kinsan bana son ganin ki a damuwa".. Tace "yaya mom tanayiwa Daddy magana na nida sultan hakanan se nake jin wani iri".. Murmushi yy yana dan langwabar da kai irn yanda tayi "wai dama shine damuwar" ta gyada kai.. Yy murmushi yace "to kode na dauke ki mugudu ne" dariya tayi sosai tace "wai idan bakya sonsa".. Tayi dariya.. Yaja hancin ta yana mikewa bari naje idan na dawo munyi magana.. Ta daga masa hannu har ya fice.. Snn ta marairaice fuska tana komawa ta kwanta.. "Haka nan kawai taji dama farouq ne ba sultan ba sbd yanda take nishadi idan tana tare da farouq bataji tare da sultan.. Maida idon ta tayi ta rufe har jiddah ta shigo da da tray din breakfast...
Gaba daya ynx Fannah se koda yaushe ta rinka jinta cikin damuwa duba da yanda kowa ynx na family din ya dauki maganar ta da sultan da mahimmanci da kuma yanda kowa ke farin ciki.. Shima sultan ya kula da yanda ta sauya masa shiyasa shima ya rage kiranta ko son kasancewa da ita sbd baya son duk wani abu da zesa taji ya gundure ta.. Kuma hakan dayayi se yama Fannah dadi.. Ko waya take idan kaga ta dade tana waya da wani to Farouq ne ko maryam... Sosai take sakewa da farouq dan yana sakawa ta manta duk wata damuwar ta..
Ranar da Dadd yazo ranar Mom tayi masa maganar Amoon akan auren su jidda da yusrah da kuma fannah da sultan se Sadeeq da Hafsat.. Su Farouq ma ana saka ran soon zasu fito da nasu... Yayi farin ciki sosai da wnn hadin kuma zeso hakan ta faru sede besan ta bakin Amoon ba.. Ya bada goyon baya dari bisa dari haka ma Abie... Da daddy shima yy farin ciki Abbu(Alhaji Rabiu) dama already ya koma sudan sede suka kira sa yy farin ciki sosai dama already yasan da zancen diyar tasa dakuma Sadeeq yy farin ciki sosai kuma ya bada goyon baya ....
Jiddah ta rinka kallon abbie din nata haka ma Farouq.. Da yagama sauraren Abie daya fada masa duk yanda sukayi da yan uwan nasa... Jiddah ta girgiza kai tare da fashewa da kuka.. "Abie mu biyu fa mu biyu kace shi yaya amoon dinne yace mu biyu ze aura mamie kisa baki dan Allah wlh bazan iya ba".. Mamie tace "bana son shashanci inde kau kina son sa dole ki zauna da ita gata ma mukayi maki da har zamu hada ku tare"... Jiddah ta mike "Abie dan Allah kuyi hakuri wlh inason yaya Amoon bazan iya jure ganin sa da wata ba".. Daga haka ta fice tana kuka wiwi.. Duk suka bita da kallo Abie yace "ji shashasha".. Mikewa farouq yayi jiki ya sanyaye shima ya fice abie ya bisa da kallo snn ya dubi mamie "what's wrong with him"... Shiru kawai mamie tayi batace komai ba Amma ita tasan abinda ke damun dan nata....
Gidan su fareeda yusrah ta tafi ta shige dakin fareeda duk da tasan bata nan tana sch.. Kuka tayi sosai... Fannah ce ta shigo dakin ta rinka kallon jiddah dake kwance saman gadon fareeda tana kuka. Hankali tashe ta karasa "jiddah are you ohk"... Da sauri jiddah ta dago ta rungume fannah "pls ki tayani da Addua wlh fannah duk da nasan yaya Amoon ba wani sona yake ba ina kishin ganin sa sa wata.. Ballanta har ya aure mu mu biyu what if yazo yafi sonta..".. Fannah ta dan bubbuga bayan ta kiyi hakuri nasan hakan dasu ka yanke shine dede...."... Girgiza kai jiddah tayi "you won't understand baki san wane yaya Amoon ba da Na cire ran samun soyayyar sa har sena samu damar auren sa amma kuma se ace mu biyu za'a hada nide kawai ki tayani da Addua"... Cike da tausayin ta fannah ta rinka buga bayan ta. .. Shigowar fareeda ce yasa suka daga kai Hafsa ma ta shigo... Kallon jiddah dake kuka suka rinka yi.. Fareeda tace "jiddah meya faru".. Hafsa dake zama gefen gado tace "ya wuce oga Aliyu".. Fareeda tace "naji Dadd dayazo yace yau Chucu take gama Exams inajin gobe fa zasu zo"... Da sauri jiddah tace "wai da gske"... Hafsat tace wlh.. Ko gobe zasu zo kinsan chucu da son surprising shiyasa babu wanda ta fadawa.. " Farin ciki wajen jiddah kamar me... "Wow just can't wait yaushe rabon danaga yaya Amoon ko last zuwana America bamu hadu ba".. Duk dariya sukayi ganin yanda ta rude... Daga haka ta tashi ta fice.. Sude kam se dariya suke...
Ita kanta yusrah data samu lvri kasa natsuwa tayi sbd farin ciki.. Fannah tai ta kallon ta tabbas ta yarda ba son wasa suke masa ba.. But so from side daya babu dadi... Yusrah Na kallon ta tace "don't mind me pls wlh bazaki gane ba . inason yaya Amoon fiye da tunanin ki tun bansan mene so ba nake son yaya Amoon the most painful is shi hankalinsa baya kaina" yusrah ta idasa muryar ta a sanyaye.. Fannah tayi murmurshi.. "Kar ki damu kila ma kawai dan yaga kin damu dashi ne shiyasa yake basarwa".. Yusrah ta "girgiza kai wlh baki sansa ba shi gaba daya daban yake ai gobe ze zo zaki fahimci duk abinda nake fada maki nide kawai rokon da zan maki tunda ke be sanki ba kila ku dedeta dashi inde har kuna shiri pls try to convince him a kaina dan Allah"... Fannah ta gyada kai "inshaallah I will try my very best kinji ai ke din babu wanda ze ganki yace bayaso".. Yusrah ta rungume ta "wlh da kin gamamin komai.".. Murmurshi fannah tayi tana kara mamkin su ita da jiddah... Yusrah ta dauki waya kinga bari na kira yaya Saleem naji karfe nawa jirginsu ze sauka... Yana dauka tace "uhmm yaya saleem tafiya babu sanarwa".. Dariya yayi daga can yace "we're srry".. Tace "ina yaya Amoon fa". ... Yace "yana cleanic" "yau kuma dama da aiki ne"... Yace "nop wata patience muka samu ne"... "To patience kuma ba gobe zaku taho ba". Yace "eh to dade gobe but ynx gsky bnd mu nida yaya se mammah da Cucu gobe suna hanya"... Kamar zatayi kuka tace "kai dan Allah ynx se yaushe".. Yace "I can't say but soon inshaallah"... Jiki a sanyaye yusrah ta sauke wayar ta juyo tana kallon fannah "kinji ko wlh ynx kadan daga cikin aikin sa knn"... Sun dade suna lvr da fannah wanda duk shima

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login