Showing 66001 words to 69000 words out of 100889 words

Chapter 23 - Love Cycle Book 1 Complete Hausa Novel

Annafie   

10 Feb 2025

241

dauke ta sbd harda maganin bacci.tasha.
Washe gari sega maryam.. Cike da mmki maryam ke tambayar ta abinda ke faruwa.. Sosai maryam tayi mmki.. Maryam tace "knn dama can yasan ke wacece yake tare da ke acan".. Fannah ta tabe baki "shide ya sani"... "To ke ynx yazaki knn dasu jiddah".. "Maryam I don't knw".. Ranar a gidan maryam ta wuni se gab da magrib snn fannah ta rakota.. Har wajen estate din fannah ta rakota suna tafiya a hankali babu kowa a cikin estate din. Yanayin yayiwa fannah dadi se tafiya suke har sun kusa gate din wata mota ta wucesu.. Slow motar tayi se kuma se kuma ta fara dawowa da baya.. Fannah ta rinka kallon motar dan bata taba ganin ta ba kuma bata ganin wanda ke ciki.. Seda yazo daidai su snn ya tsaya a hankali ya zuge glass din yana kallon su da dan murmushi.. Seda gaban fannah ya fadi ganinsa... maryam ta ware idanu "wow Dr Amah".. Dan murmushi yayi.. Yace "Amoon".. Maryam tace "oh hakane fa ynx ka zama Amoon".. Yace "har an kiraki an fada maki"... Maryam tace "ai kai din ne kafin abun mmki".. Yace "anyway ina zuwa" tace "zan hau taxi ne na wuce gida"... "Nayi dropping dinki mana".. Maryam tace "kaida zaka fita ka barshi kawai".. Yace "babu damuwa sako kawai zan karba airport".. Ya karashe maganar yana kallon Fannah da taki kallon sa.. Yace "madam am I new to you".. Dan murguda baki tayi batare da ta yarda ta kallesa ba.. Ya danyi murmushi "need ur accompany" noke kafada tayi.. Ya dubi maryam "bata son rakaki fa.." Maryam tace "muje Fannah" kamar fannah bazata shiga ba se kuma ta shiga gaba ganin maryam ta shiga baya.. Ita kanta motar kamshin ta daban ne ga wani sanyi.. Suna shiga yaja motar yace "maryam.. This ur frnd is ignoring me kamar bata sanni ba tamaki bani tym dinta."... Maryam tace "anya kaine de ka nuna baka santa ba".. Dan kallon Fannah yayi ta dauke kai... Yy murmushi yace "haka ta fada maki knn.. Kuma kin yarda".. "aa to nide bazan yanke hukunci ba".. Ya dubi fannah "madaam kinyi shiru.. Kode jan class ne". Maryam tace "fushi muke"... Ya ware idanu "ai ni yakamata nayi fushi wasu fa ta kula ganin bana nan har ta yanke shawarar auren wani bani ba.. Nikam bazan iya aure wacce ba ita ba bayan gata a raye"...maryam ta rinka murmushi fannah kam juyawa tayi tana kallonsa.. Hararan ta yayi ta dauke kai tana murmushi.. A haka har suka kawo gidan su maryam.. "Dama kasan gidan mu" da mmki yace "kina mmki ne".. Dan murmushi tayi ta bude ya dubi fannah yace "bari nayi sallah".. Fita tayi tabi maryam.. Shi kuma fito zuwa massalacin unguwar su maryam.. Suna shiga gida maryam ta rungume fannah "wow fannah wato Aliyu daban ne snn cike yake da abun mmki".. Fannah ta marairaice "ni wlh tsoransa nake ji".. Maryam tace "common dallah ni nan bakiji dadin da nake ji ba"

Bayan ya fito ya aika a kira su.. Har gate maryam ta rako fannah tana daga masu hannu... tunda suka fara tafiya bece da ita kala ba har suka iso airport din.. Wayar sa ya dauka yy kira "waiting" kawai yace snn ya juyo yana kallon Fannah ita de bata dago ba duk da taji yana kallon ta .. Knocking glass dinsa akayi.. Zugewa yayi yana kallon gayen jan gashinsa yayi.. Amoon yace "ohch ishak kaifa mugune".. Ishak yana kallon Fannah yace "ur sister cos naga kuna Kama".. Amoon ya kalli fannah "anya kuwa sede kamar na fita kyau ko". Ishak ya yamutsa fuska "ina babu ma hadi tafika".. Fannah na murmushi ta gaisar da ishak ya amsa shima.. Amoon yace "khadeeja".. Ishak ya ware idanu "don't tell me cewa tazo Nigeria".. Amoon ya hararesa "gata ma kana gani"... Ishak yayi saluting fannah "I salute you.. Mace ta farko data sace zuciyar sa".. Murmushi kawai Amoon yayi tare dayima ishak sallama snn suka bar airport din bayan ya karbi sakonsa.. Dan kallon ta yayi.. Yace "why are you silent".. Ta gefen ido ta kallesa ta dauke kai.. "Am I new to you?.. Am still the Amah you knw"... Kallonsa tayi ya dage mata kafada.. kamar bazatayi magana ba se kuma tace "dama ka sanni ne?".. Murmushi yayi.. Ita kuma ta tura baki yace "wai fushi kikayi? But you knw I love you ryt?".. Fannah ta sauke ajiyar zuciya.. Yace "I miss you".. Kallon sa tayi taga hankalin sa nakan driving ta dauke kai.... Yace "so you're not missn me ryt ko dan kin samu wasu".. Kallosa tayi idanun ta cike da kwalla can kuma ta rufe idanun ta tafara kuka.. A hankali yasa hannunsa ya kamo nata yana muzawa a hankali.. "Srry dear".. Tace "what about yusrah and jiddah".. Dan kallon ta yy se kuma ya maida hankalinsa a driving "I love only you". Fannah ta lumshe idanu. Tana jin yanda yake murza hannun ta a hankali.. Zare hannun tayi tare da folding dinsu.. Yace "why". Dan tura baki tayi batare da tayi magana ba.. Yy murmushi yace "but do not worry one day, a day is coming that not only ur hands but the whole you and is soon inshaallah".. Rufe fuska tayi.. Se ta tuno moment dinsu na baya....yanayin parking a gate dinsu ta fita da sauri.. Yace "Fannah".. Da sauri ta juyo tana kallon sa sbd yanda yakira sunanta.. Yace "coming back to ur lyf not just as ur teacher.. I'm ur brother and just knw that Amoon loves you".. Da sauri fannah ta shige tana murmushi..shima murmushin yayi sann ya karasa gida..
a cikin yan kwanakin nan idan kaga su yusrah har wata rama sukayi gaba daya sun tashi hankalin su cikin kankanin lokaci har kowa yasan meke faruwa kowa ya boye sbd kowa abinda ke damunsa .. Farouq ya shiga dakin Mom yana kallon yusrah da kullum batada wani aiki se kuka sannu yayi mata bayan sun gaisa da mom.. Yusrah tace "yaya farouq, yaya Amonn fa". Farouq bece komai ba dan shi kansa Amoon wahalar gani yake masa be sani ba ko fushi yake dashi ko aikine ya masa yawa.. Oho.." Juyawa yayi ya fita.. Can lambu ya nufa sbd ya hango sultan ta window,..
Jin motsin tafiya yasa sultan ya juya ganin farouq yasa ya dauke kansa farouq ya karasa kusa dashi yana kallon sa da dan murmushi.. Yace "sultan Raddah".. "Yes" sultan ya amsa batare daya bude idanunsa dake lumshe ba... Farouq yace *"is either me or you, and that beech ta take fadin tabama zuciyar ta.. Kai ni wann bana ma zancen sa cos ina ganin kamar baya existing ne"*....hope ka tuna maganar da kayi now the beech is back and nasan ze tabbatar maka da yana existing". Sultan ya bude idanunsa da suka canza kala yana kallon farouq.... "Dawowar sa ko rashin dawowar sa be isa ya canza ni akan ra'ayina ba koshi Amoon din ubanane da zanji tsoransa".. Murmushi farouq yayi "ba ubanka bane am telling kar ka shiga gonar daba taka ba".. Sultan ya gyara zama yana kallon farouq.. "Kana tunanin zanji wani darr sbd Amoon ne Amahn da take fada.. Akan me zanji darr dame yake takama ne kyau? Kudi? Ko asali duk abinda yake ji dashi inaji dashi".. Tabe baki farouq yayi kafin yace "babu ko daya sede ka manta abu daya cewa shi ya mallaki zuciyar ta wanda nasan ko digon space baka dashi".. Sultan ya dunga kallon farouq dan maganar ta masa ciwo se ya ware hannu "wnn bani kade ya shafa ba har da kai and I will soon take action on that".. Wani kallo farouq yayi masa.. "Kaide ya shafa I want the best for her.. And after that ma inada chucu kuma dama can inasonta kawai na dauka shi don't have interest on me but now Alhmdllh.. I will just watch you guys".. Daga haka ya fice yabar sultan....
...
Alh. Ahmad ya gama sauraren er uwar tasa.. Tas Mom ta fada masa halin da ake ciki.. Suna gama wayar ya canza akalar kiran zuwa Amoon yana dauka yace "I want see you in the next 2mns".. Daga haka ya katse wayar sa.. Yana kallon mammah yama kasa ce mata komai.. Amoon ya shigo da Sallama..Dad ya dunga kallon dan nasa cike da mmki shi har tsoro ma yake basa idan yana wani Abun. Yana kallonsa da kyau "Ina kasan Fannah".. Shiru kawai Amoon yayi ba tare da amsa wa mahaifin nasa ba.. "Wait knn de duk abun nan dake faruwa kaine Amah din da Fannah ke magana".. Amoon ya gyada kai.. Shi kansa Dad girgiza kai yayi dan yama rasa tunanin da zeyi.. Yasan wane dansa ze aikata abinda ma yafi hakan bn mmki can yace "tashi make sure gobe by 9am kana parlorn Abie".. Gyada kai yy snn ya tashi ya tafi.. Dadd ya bisa da kallo wani lokaci tausayi dan nasa ke basa Amma abunsa se shi...
....
Urs
✨✨✨
Nafeesatuh...😍😍
.....
*💫❤LOVE CYCLE✨*


Written by

*@nnafie🖤*
(Smll but mighty😉)

*writer of*
Saif
Adaan
Wata mafita
Saboda duniya
Love cycle......


Bismillahir rahmanir raheem

💫❤Love cycle❤ (24)✨
Kamar yanda aka sanar masu by 9 duk sun hallara a parlon Abie.. "Iyayen nasu ma duk sun hadu.. Kowa kansa na kasa cike da ladabi.. Daddy ya bude masu taro da Addua... Abie yayi gyaran murya yayi sallama snn ya fara magana kamar haka.. "Nasan kowanen ku yasan dalilin wnn taron.. Wato akan wasu abubuwa da suka faru kuma suke kan faruwa..kuma idan aka barshi yacigaba da faruwa za'a iya samun matsala.. Kamar yanda kuka sani munan duk iyayen ku kuma mun dauke ku a matsayin abu daya.. Akwai wadan da muka sani dama tun can wasu kuma se ynx suke faruwa kamar kamar maganar Jiddah, yusrah da kuma kai Aliyu, sann hafsat dakuma Sadeeq.. A yan kwanakin nan kuma abubuwa dayawa sun faru tsakanin Farouq, sultan, kadeeja, fareeda da kuma sumayya, muna cikin hakan kuma sega wata wato Kai Aliyu da kuma khadeeja still,.. Shin dama can kasan ta ne?"..kan Amoon kasa yace "eh Abie".. "But for how long kuke tare wait a ina ma kasanta tun yaushe kasanta".. Amoon yayi kasa da kai "10yrs back".. Bama su Abie kade ba har su sultan seda suka dago suna kallonsa.. "Amoon" Dadd ya furta a kasan labban sa cike da mmkin dan nasa.. Daddy ya ringa kallon Amoon.. Mom kau tagumi kawai tayi tana kallonsa.. Abbu ne yace "ynx kana nufin tun shekara goma da suka wuce kasan inda Muhammad yake but bamu sani ba".. Amoon yace "Abbu tun lokacin da daddy yabar nan I put that on mind that inshaallahu sena san inda yake but i was just at the age at the age of 11... First surgery dina dana farayi a uk.. Na naga Abba yazo dubiya.. Before then nayi kokarin duba duk inda nasan zeyi aiki amma bn samesa ba.. Se luckily yazo duba patient din and nagansa shi kuma be ganni ba... Na bisa har na gane inda yake zaune da kuma inda yake aiki anan na gane cewar ya dena amfani da komai na family din nan dan kar a ganesa ya kuma toshe duk wata hanya da family din nan zasu gansa.. Naso na bayyana hakan amma har lokacin na fuskanci daddy yana cikin radadi sosai shiyasa nabar zancen lokaci lokaci kuma ina dubawa to make sure they're fne..nasan duk fushin da ze dauka dole ze sakko kuma yaji yana bukatar yan uwansa kodan sbd fannah hakan yasa na shiga rayuwar ta ina bibiyarta har ta shiga aji uku a jami'a.. Anan ya kwashe duk abinda ya faru ya fada masu snn duk rayuwar da sukayi ya kara da fadin..sugery din da nayi a spain wanda aka samu matsala shine yasa nabar uk.. Ganin ta hadu dasu farouq yasa koda nagama aikin yasa bn sake neman ta ba tunda nasan zan dawo I don't knw it will take me long kamar haka".. Duk kallon sa suka ringayi tabbas bakowane zeyi abunda yayi ba domin Amoon mutum ne me hikima.. Dadd yayi farin cikin abinda dan nasa Yayi shiyasa a koda yaushe yake alfahari dashi... shi kansa daddy se yaji Amoon din ya birgesa yayi abinda iyayensa basuyi ba ... Abba (Alh Aminu) yace "Amoon kayi kokari hakika kai abin Alfahari ne sede abinda muke so mu sani shine shin kana son khadeeja ne kokuwa sbd wnn family din ne ka shiga rayuwar ta.. ".. Kan Amoon a kasa yace "ina sonta Abba".. Abba ya jinjina kai "to kasan kuskuren ka anan".. Shiru Amoon yayi.. Abba yace "ka tafi kabar ta babu wani kiran waya.. karkaga laifin sultan da farouq dan sun so ta snn ita baka tunanin zata iya canxa ra'ayi akankan ka, ka tafi batare da ka waiwayeta ba ba tare da kayi tunanin wane hali zata shiga ba". Amoon de yayi shiru bece komai ba.. Abba yacigaba "and nasan de kasan da maganar su yusrah da jiddah ko.. Kasan de tun yaushe suke jiran ka anyi maka maganar amma kayi bris damu har ynx bamuji wani feed back daga gareka ba.." Shiru Amoon yayi bece komai ba.. Abba yace "snnku su farouq ya kuke ciki akan batun wnn yarinya" farouq yace "Abba ni na hakura zan auri sumayya inasonta".. Abba ya jinjina kai domin yaji dadin maganar farouq.. Ya dubi sultan.. Kan sultan kasa yace "ina sonta Abba.." "Toh fareeda fa?".. "Zan aure su duka Abba.." Sultan ya fada yana kallon Amoon da shima ya dago yana kallonsa da idanun sa da suka rikide.. Dauke kai sultan yayi yanajin duk abinda za'ayi sede ayi kodan sbd maganar da ya gaya masa ranar da fannah bata da lafiya da kuma farouq ranar a lambu... Abba yace ku tashi kuje zamuyi magana dasu yaran sede inaso dan Allah kada wnn yasa ku samu matsala da junan ku.. Duk godiya sukayi... Amoon ya fice ba tare da ya kalli kowa a cikin su.. Sadeeq ne yayi kokarin kiran sunan sa.. Juyowa Amoon yayi ya kalli sadeeq da Farouq karasawa sukayi inda yake sadeeq sadeeq na kallon Amoon yasan tabbas tunda yayi wnn dawowar yana cikin damuwa.. Yace "brother pls take it easy.. Kar wnn ya zama silar daze kawo matsala tsakanin mu".. Murmushi Amoon yayi sede baya son magana dan ransa a mugun bace yake.. Farouq yace "kayi hakuri da duk abinda ke faruwa inshaallahu everything will be settle..".. "Settle".. Amoon ya maimaita . . se ya danyi murmushi "everything will be settle amma idan wancan ya cire fannah a ransa... Sbd fannah tawace ni kade ba'ayita dan wani mahaluki ba"... Ya fada yana nuna sultan da fitowarsa knn.. Sultan ya karaso yanawa Amoon wani kallo snn yace "kai kana tunanin zanbar fannah ne sbd ina tsoranka let me tell kai baka isa ba kasan da kana sonta zaka tafi ka barta har tsawon lokutan nan kuma snn kana zuwa lokaci daya sena barma bayan muma muna sonta kamar yanda kk sonta".. Amoon ya dunga kallon sultan boiling from inside ya nuna sa yace "sultan Raddah na kula rigima kk nema nasan kasan nine Amah tuntuni but because of ur selfish ka tusa kanka, but get in to ur head idan ka cika shigewa fannah duk abinda nayi maka kaikaja".. .. Daga haka yabar wajen.. Sultan ma tabe baki yayi yabar wajen ....
Koda Amoon.. Ya shiga gida bebi takan kowa dake parlon ba yayi hayewar sa sama.. Chucu ta dubi mammah "mammah yaya yana cikin damuwa sosai".. Mammah ta lumshe idanu sosai take tausayin dan nata be cika saka abu a raiba wanda be damesa ba tunda taga ya damu tasan tabbas yana tsananin son fannahr nan.. Tasan ynx haka ko abinci da wuya yaci.. Dadd ne ya shigo.. Nan yake fada masu duk yanda sukayi da yan uwan nasa ... Mammah tace "I don't want to involved my self but yakamata a duba Amoon yana cikin damuwa sosai". Dadd yace "suma sauran ai kinsan suna cikin damuwa sbd farin cikin sa a baza'a kuntatawa wasu ba".... Ranar tunda Amoon ya shiga daki be fito ba babu yanda mammah, saleem da chucu basuyi dashi ba akan ya bude kofa amma yaki da kyar mammah ta samu ya bude shima ita kade ta shiga su chucu tsoran shiga suke sbd abinda zeje ya dawo..
Tashi chucu tayi gidan su Fannah taje a dakin ta tasameta .. Tana ganin chucu ta saki murmushi.. Chucu ta zauna daga gefen gado.. "Duk kin manta damu ko kamar duk fushi kike damu".. Fannah ta girgiza kai ko daya wlh kawai bana jin dadi ne".. Chucu tayi tagumi tana kallo fannah "yanxu dama all this while wnn Amah din da ake magana ba wani bane yayanane".. Dan murmushi fannah tayi se kuma tace "and that same Amah shine Amoon din da Yusrah da jiddah suke magana akai".. Chucu tace "kinsan yaya yasha fadamun cewa akwai khadeejar da yake so wlh yaya ke kade yake so".. Fannah tace "chucu ina cikin rudani". Chucu tace "Fannah yaya Amoon yana cikin damuwa sosai tunda yayi wnn dawowar yaki sakewa da kowa ko ynx yana can ya rufe kansa a daki"... Fannah ta kurawa chucu idanu can kuma tace "me kikeso nayi to nima fa kaina Allah kade yasan damuwar dake zuciyata".. Chucu ta mike pls koyaya ne kizo muje ki gansa nasan ze rage damuwar sa wlh duk yau bnga ya fito ba dan Allah kizo muje kila idan kece ya bude dakin.. Gaban fannah ya rinka faduwa tana tunanin wane hali yake ciki kuma.. Girgiza kai fannah tayi "srry chucu bazan iya zuwa ba". Chucu nason brother dinta sosai tana matukar damuwa idan har yana cikin damuwa tasan ze iya shiga wani hali... Chucu ta share hawayen ta "dan Allah fannah wlh tsoran damuwar yaya Amoon nake".. Fannah ta girgiza kai tana jin yanda zuciyar ta ke beating.. Mikewa chucu tayi zata tafi har ta kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login