Showing 78001 words to 81000 words out of 100889 words

Chapter 27 - Love Cycle Book 1 Complete Hausa Novel

Annafie   

10 Feb 2025

253

kaman wata balarabiya zataje masallaci"....
Murmushi kwai chucu tayi.. Key fareeda ta amso masu na mota wajen Adda ita tayi drving dinsu zuwa masallacin.. Yanda Fannah taga musumai dayawa kowa nata addu'a se abin ya birgeta fisrt tym zatayi sallah a kasar ta cikin state dinta tare dakuma yan uwanta ga musulmai ta koina.. Dole ta godewa Allah daya nuna mata wnn rana"...
Seda fareeda ta zazzagaya dasu sosai snn suka dawo tunda tasan gari sosai tana zuwa... Sanda suka dawo kusan dayawa suna cikin compound din da alama kila duk dawowar su knn... Fannah ta rinka kallon Amoon dayayi wani irin kyau cikin manyan kayan snn ta dauke idanu ta maida kan dad dinta wanda kallo daya zaka mata kasan yana cikin matsanaicin farin ciki"..
Tana fita wajen dad dinta taje ta rungume sa cike da murna .. Kusan kowa wajen iyayensa ya tafi yana masa barka da sallah..
Daganan suka rinka yiwa junan su aka fara yin hotuna na wajen hotuna seda sultan yasan yanda yayi ya tsaya kusa da Fannah.. A hankali yace "Fannah are you doing the right thing".. Kamar bazatayi magana ba se kuma can tace "me nayi".. Yace "you're ignoring me".. Tace "hakan shine dede".. "Why" tace "baffa yace na rabu da dukan ku".. Ya danyi murmushi "but ai ni kade kika kyale bnd Amoon".. Fannah tayi shiru amma har ga Allah haushinsa take ji.. Yace "pls koda call dinane pls be picking".. Gyada masa kai tayi.. Sbd dagowar da tayi taga Idon Amoon a kansu.. Seda gaban ta ya fadi Amma ta dake.. Ganin ya bar wajen ma gaba daya yasa duk jikin ta yayi sanyi.. Dama shi be shiga hoton ba gaba daya..
Bayan an gama kowa ya shiga ciki.. Har aka fara hada hadar cin Abincin bataga Amoon ya shigo ba.. Gaba daya duk se taji ta kasa ci.. Kusan har aka gama Amoon be zo ba. Sageer ne kade taji ya tambayesa akace may be ya tafi wani wajen.. Amma ita ai tasan yana cikin gidan sultan ma ya sani amma beyi magana ba.. Ganin babu wanda ya kara maganar sa yasa ta tashi a hankali ta fita.. Hanyar data ga yabi nan tabi can ta hangosa zaune cikin wata er rumfa yana danna wayar sa.. Komawa tayi.. Seda taje daki ta dauko dambun sa snn ta wuce kitchen seda ta diba masa komai har zu drink snn tasaka a tray snn ta juya tabi ta baya.. Tana karasawa gaban ta na faduwa tayi sallama.. Ya amsa ba tare daya juyoba... Jin muryar sa kade ya isa ya tabbatar mata da yana cikin damuwa.. Kujerar dake kallon tasa ta zauna tace "why are you alone".. Ba tare daya kalleta ba yace "just".. Ta langwabar da kai.. "Is it because of sultan".. Yace "am just thinking of how to handle that guy"... Tace "but I love only you".. Ya zuba mata idanun sa da suka canza kala snn yace "I don't knw why but sultan nason shiga gona ta.. But idan beyi wasa ba se bakin ciki ya kashesa"... Kamar Fannah zatayi kuka tace "beb pls forget about that ga abinci". Dan murmushi yy.. A haka ta tsare sa seda yaci duk abinda ta kawo masa snn ta tashi.. Duk yanda yaso ta tsaya ki tayi.. Ta dawo parlo ynx duk babu iyaye se su yaran tare da Adda da alama labari take basu.. Fannah ta shigo ta zauna ba tare da Adda ta ganta ba ta boye bayan Hafsat... Babu jimawa sega Amoon ya shigo.. Duk suka bisa da kallo wajen farouq dake wani murmushi yaje ya zauna tare da dan tallabar masa keya...
Da yamma.. Sadeeq ya dauke su ya zazzagaya dasu cikin gari.. Basu dawo ba se dare shima sallah kawai sukayi suka kwanta.....
..
haka Washe gari ma wani fitan suka karayi tunda suka fita basu dawo ba se yamma.. Yanda Fannah taji dadin sallahr nan ba'a magana bata taba sanin haka ake sallah ba gashi har hawa sunje kallo duk da basu wani dade ba suka dawo amma abun ya kayatar da ita.. . A get suka hadu da Amoon da sageer zasu fito.. Tsayar dasu yayi yana kallon Fannah yace "ur bag.. Sbd kwai abinda yake son saka mata.. Da kamar ta cire wayar ta se kuma ta mika masa gaba daya... Ya tafi da ita.. Cikin motar sa ya shiga ya ciro wasu bngles masu kyau na gold ya saka mata a jakar. Snn ya dauko wayar ta sbd da tayi karar shigowar message.. Dubawa yayi ganin sultan.. "Dear pls lets meet by 8 pls don't ignore".. Amoon ya rinka kallon message din.. Da ynx yayi niyar maida mata da jakar amma se ya fasa ya shiga contact din sultan yana duba messages din yake tura mata bata reply".. Zuciyar Amoon wani irin tafarfasa kawai take.. Wayar ya saka aljihu jakar kuma ya barta cikin mota yacewa sageer suje... Suna dawowa sallahr ishai yaji wayar na ringing kara dubawa yayi ganin sultan ne.. Tuni idanun sa suka sauya kala.. Ya rasa gane me sultan yake nufi shi gaba daya.. Suna shiga parlor ya hango sultan dake zaune cikin wasu raw na kujeru yana danna waya.... Kiran ne ya sake shigowa Amoon yayi silencing wayar snn ta karasa kusa da sultan zuciyar sa na wani tafarfarsa a tym din ji yake ze iya yiwa sultan dukan tsiya dan ya kaisa bango.. Sultan be an kara ba se ji yayi an fizge wayar an bugata da kasa... Ya dago da sauri yana kallon Amoon da idanun sa sukayi jawur... Tsabar fitina da kishi dake cinsa a lokacin.. Cike da fusata sultan yace "what? Amoon, my phone," Amoon yace "an fasa do what ever you think you can do.. And if you did not stay away from Fannah I will do worst than this".. Sultan ya rinka kallon sa ransa a mugun bace.. Before ramadan ya siyi wayar nan amma ba wnn ne damuwar sa ba yanda Amoon yazo ya fasa masa and yana masa magana cike da isa kamar ya haifesa shi yafi komai bata masa rai.. Sultan yace "an kula ta din who are you to give me rules.. Wlh Amoon kai baka isa ka hanani abinda raina ke so ba yanda kake son fannah nima haka nake sonta kuma".. Ai be idasa ba Amoon ya shake wuyar sa "don't ever se that again Fannah tawace ni kade." Hakan yasa shima sultan ya kaimasa wata shakar... Tuni akazo ana kokarin raba su.. Amma yanda kowa ya harzuka da yanda kowa yake jin haushin dan uwansa se aka kasa raba su... Seda mom ta fito ta taka matsu tsawa snn suka rabu amma basu bar gayawa junan su magana ba... Wata tsawar ta sake daka masu.. Se ynx suka kula da Abie, abu, se daddy da kuma Abban sageer.. Da alama shigowar su knn.. Abie yace "you guys should meet me and Fannah should join".. Duk bin bayansa sukayi kowa fuska a hade..
Duk suna ciki mom ta shigo tare da Fannah.. Kanta kasa bata yarda ta kalli kowa ba se Amoon.. Kansa a kasa yake amma kallo daya zaka masa kasan a zuciye yake....
Abbu ya tambayesu a binda ke faruwa. Sultan ne yayi karfin halin yin bayani Amoon de be dago dan babu ma alamar zeyi magana.. Abbu ya dubi Amoon "why did you did that. Aliyu".. Ba tare da Amoon ya dago ba yace "he should stay away from Fannah".. Abbu yace "you're very stupid the two of you.. Fada akan mace.. And wait baffa yace you guys should both let her..nether one of you will marry her.. Oh kun manta.. Sbd kunga mun zuba maku idanu" ya dubi Fannah yace "mamana" ta dago idon ta yace "inshaallahu gobe zan sama maki wani daban basu ba inde har ya maki in few days time za'ayi maku baiko"... Fannah ta amsa idanunta cike da hawaye.. Yace "Allah ya maki albarka.. Duk wanda ya sake maki magana ki kawomin karar sa and I will deal with that person" ta gyada masa kai tana kallon Amoon da har lokacin kansa a kasa yake.. Snn ya koma gasu Amoon yace "and duk wanda ta kawomin zancensa a cikin ku wlh zaku sha mmki na inshaallah inde har wanda na kawo yayi mata ranar Friday za'a masu baiko kuma ku shirya cos tun ba yau ba nariga nayiwa su yusrah alkhawari dan haka Amoon ka shirya auren ka dasu babu fashi... And you sultan.. It seems lyk you're not on ur ryt sense.. Kaima ka sani har fareedan kafasa auren ta itama I will get her one and before Friday ka tabbatar ka fito da wacce zaka aura".. Kaji na rantse inde har kuka saba dokata zaku sha mamaki".. Sultan ya rinka kallon Abbu jin wai har fareeda ya fasa basa.. Shifa bece bayason fareeda ba.. Yana mugun sonta kawai de baya so Fannah ta subuce masa ne shiyasa amma yanason fareeda.. Yace "Abbu kuyi hakuri wlh na hakura da fannahr zan auri fareeda wlh. Inasonta.. Tsawa mom ta daka masa "will you shoutup my friend you're very stupid se ynx kasan da haka to wlh koda wasa inga ka kara kula fareeda da neman rigima ne yasa ka kyale ta".. Kasa yayi da kansa cike da tsoro dan yasan kila wnn shawarar mom ce dan ba wani ba... Abbu ya rika masu fada.. Sosai yaga karaya da nadama a idon sultan.. Amma ko daya be gani a idon Amoon ba.. Babu ma Alamar ze karaya.. Ana sallamar su Amoon ya tashi ya fice ba tare daya kara kallon kowa ba.. Sultan kau tsayawa yayi ze bata hakuri.. Abie ya masa wani kallo yace "get out".. Ya kalli mom dinsa ta zuba masa harara hakan yasa ya tashi jiki a sanyaye...
.....
Urs
✨✨✨
Nafeesatu....😍😍
....
*💫❤LOVE CYCLE✨*


Written by

*@nnafie🖤*
(Smll but mighty😉)

*writer of*
Saif
Adaan
Wata mafita
Saboda duniya
Love cycle......


Bismillahir rahmanir raheem

💫❤Love cycle❤ (29)✨
Amoon ya wuce dakinsa ba tare daya kalli kowa dake cikin parlorn ba.. Yanda yake hadiyar zuciya a lokacin kamar wani mayunwacin zaki.. Yana shiga ya daki banko kofar da karfi yana nishi tare da cizgar lips dinsa.. "He's just hoping to see tomorrow dan yaga wane isashshen ne ze shigo cikin family din nan da sunan wanda ze auri Fannahr sa"... Ya runtse idanu yanajin yanda zuciyar sa ke wani irin bugawa.. Bude kofar akayi.. Ya daga jajayen idanun sa yana kallon sadeeq daya shigo.. Dauke kansa yayi ya cigaba da sauke ajiyar zuciya da karfi.. Kallo daya zaka masa kasan ransa yakai kololuwar baci .. Bude fridge sadeeq yayi ya dauki bottle water ya mikawa Amoon bayan ya bude... Karba Amoon yayi ya daga...ya shanye tass snn ya juya yana kallon sadeeq yace "inde har Fannah ta auri wani baniba, to mutuwa zanyi that's the end of me"... Sadeeq yace "stop saying that.. Inde Fannah har Fannah matarka ce wlh seka aure ta idan kau kaga baka aureta ba to ba matarka bace that's ur destiny".. Dan murmushi Amoon yayi wanda daga gani kasan he's boiling from inside yace "Abbakar bazaka gane ba Fannah is my hope she's my future".. Sadeeq yace "just keep praying and kayi hakuri nasan wnn duk kishi ne kesa wnn abun ko a yanayin condition dinka ai ka kwantar da hankalin ka..ni nasan sbd yanayin condition din yusrah suka matsa seka aureta sbd idan aka barta zata iya shiga wani hali tunda ba lafiya ta gama isarta ba.. Kuma kaga tunkan tasan kanta takesonka. And babu yanda za'ai a hana jiddah kuma tunda tun suna yara suke sonka".. Amoon yayi shiru bece komai ba amma yasan zuciyar sa bazata daukar ganin Fannah da wanin sa ba...
Fannah kam daki ta shiga tasha kukan ta fuskar Amoon kawai take hangowa tasan bashi cikin yanayi me dadi..
Bayan tafiyar su sultan akayi kiran su fareeda.. Nan take ya fada masu duk hukuncin da suka yanke.. Abbu ya kalli fareeda yace "maganar sultan ki barta ga sageer nan inshaallahu nasan bazaki samu matsala dashi ba".. Gyada masa kai fareeda tayi gaban ta na faduwa.. Sageer din da bawani shiri suke dashi ba mutumin da yakeda mugun jin kai amma shine za'a aura mata.. Haka nan de kawai ta Amince zata aure sa amma zuciyar ta bnd bugawa babu abinda take.. Ita tana da mugun tsoro shiyasa ko Amoon bata shige masa... Yusrah kam farin ciki sosai jin Friday za'ayi baikon su da Amoon duk da harda jiddah Amma de tana farin ciki... Jiddah kam jikin ta yayi mugun mata sanyi.. Taga a yanayin da Amoon ya fito daki dazu hakama na Fannah hakanan kawai se jikin ta yayi sanyi... Chucu kam duk da tana farin ciki sede tausayin yayan nata da Fannah ya rufe hakan.. She wish ace itace yusrah da Jiddah data hakura yau kodan sbd farin cikin su da yanda suke son junan su...
A ranar dayawa basuyi bacci ba cikin wadan da Abun ya shafa wasu farin ciki wasu kam kwana sukayi kuka irin su Fannah da fareeda.. Fareeda na ganin yanda sultan keta kiran ta da kuma tura messages.. yana bata hakuri da kuma rokonta akan dan Allah kartayi accepting sageer.. Babu amsar data basa.. Duk da tasan a lokacin can ita taja sultan ya barta amma dole itama ta share sa kamar yanda ya share ta wnn karon sbd fannah.. Kuma dukda tanasonsa dole tayi hakuri tunda Abbu ya hadata da sageer...
Fannah kam taci kuka harta gode Allah chucu ce me lallashin ta... Amoon ya tura mata message amma bata duba ba bama tason dubawa sbd tanaso tabi umarnin iyayenta...
Washe gari kamar yanda Abbu yace sageer yazo ya samu fareeda.. Itade ta gamajin abinda ya fada mata a matsayin wanda ke sonta ko daya bama tajin zata fara sonsa.. Sultan kau kamar zeyi hauka sharesa tayi ta nuna kamar ma bata san yanayi ba ...
Can bayan la'asar Abbu yayi kiran Fannah... A hanyar ta ta zuwa ta hadu da Amoon dauke kai tayi zata wuce.. Yace "dama idan kika je kinuna beyi maki ba"... dan kallon sa tayi taga bama ita yake kallo ba ta dauke kai tayi wucewar ta.. Parlorn Abbu ta shiga ta same sa bayan ta gaisar dashi ya amsa ya danyi mata nasiha tare da fada mata ribar hakuri snn ya nuna mata parlon da yake ciki .. A hankali ta tashi ta shiga jikin ta duk a sanyaye tayi sallama ya amsa mata kanta kasa ta zauna.. Ta gaisar dashi ba tare data dago ba .. Ya amsa snn yace "khadeeja".. Dan dagowa tayi ta kallesa.. Shima matashi kamar su Amoon din duk wani abu daza'a soshi ya mallaka sede ina batajin zata iya son wani bayan Amoon duk maganganun da yake bama tajinsa.. Tade ji sunan sa Yusuf. Amma nan har ya gama surutun sa ba jinsa take ba..
itade seda yace ze tafi zuwa gobe ze dawo snn ta dago ta kallesa murmushi tayi snn tayi masa sallama.. Parlorn Abbu ta wuce ta yace "ya tafi mamana".. Ta gyada masa kai.. Yace "masha Allah ya kukayi dashi".. Tace "na amince Abbu".. Murmushi Abbu yayi "Allah ya maki Albarka" a sanyaye tace "Ameen".. Wnn karon bata iske Amoon ba se jiddah tare da farouq.. Babu wanda ta tankawa a cikin su ta shege daki sbd kukan dake cinta...
Yusuf yazo ze shiga mota knn aka yi masa sallama ya juyo yana kallon Amoon da murmushi ya mika masa hannu suka gaisa... fuskar Amoon babu yabo ba fallasa yace "nasan neman aure kazo ko".. yusuf na murmushi yace "sure khadeeja".. Amoon ya dake gira trying hard be fito da bacin ransa ba yace "advisibly kar ka kara zuwa imda sunan wajen ta kazo cos tanada miji".. Dan kallo sa yusuf yayi snn yace "but ni ba'a fadamun tanada miji ba".. Amoon yace "for ur on good kar na kara ganin ka da matata".. Daga haka ya juya yabar Yusuf daya bisa da kallo.. Can kuma ya shiga motar sa...
Fannah dake zaune jikin gado tana share yan hawayen ta ta daga ido ta dubi jiddah da farouq da suka shigo.. Dauke kai tayi ta cigaba da goge hawayen ta da sukaki tsaya mata... Jiddah ta zauna gefen ta farouq kuma ya tsaya jikin mirror yana kallon ta yace "jiddah is here to apologize".. Jiddah tace "kiyi hakuri for all what happened and still happening ina son yaya Amoon amma na hakura dashi because of you ke yake so bamu ba dan haka na hakura".. Ba tare da ta kalli jiddah ba tace "babu komai and maganar yaya Amoon kuma ni na hakura Abbu na hadani da wanda zan aura"... Jiddah ta dafa kafadar ta "Fannah nasan kina son Amoon and shima ke yake so.. Tunda nake bn tabajin yaya Amoon yace yanason wata ba se akanki nasan koda mun aure zuciyar sa na tare dake.. Ni ynx nayi wa yaya khaleefa magana and inshaallahu zuwa Friday zasu zo ayi mana baiko".. Fannah de batace komai ba sbd ita kade tasan yanda take ji... Mikewa jiddah tayi ganin Amoon fita sukayi farouq na bayan ta.. Duk da Fannah taji kamshin turaren sa Fannah bata dago ba.. Amoon ya karaso Yana kallon ta ganin yanda take kallon wani direction din yace "hope kin sallamesa".. Ba tare data kallesa ba tace "why will I do that bayan shine aka zabamun"..yace "aka zaba maki ai ba zabin kiba".. Ta juyo ta kallesa.. "Nima ynz zabi nane coz na riga na amince ma Abbu".. Amoon ya rinka kallon ta yace "look into my eyes and tell me kin amincema wani da aure bayan ni".. Kin yarda tayi ta kallesa.. Yace "khadeeja".. Fashe masa tayi da kuka "pls Aliyu let me ka kyale ni dan Allah na rokeka ka rabu dani".. Se kuma ta juya tana ta kuka sosai... Sosai ta basa tausayi amma yasan duk abinda take ji be kai rabin wanda yakeji ba ya fita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login