Showing 27001 words to 30000 words out of 135959 words

Chapter 10 - Namijin Zuma Book 1 Complete Hausa Novel

masa, kmr zararre ya mike ya nufa hanyar cikin gidan Yana fadin ''wlhi ina sanki mommy! '' kaf ma'aikatan gidan seda suka fahimci meke faruwa A halin yanzu. Cikin hanzari Daya daga sojojinsa na hannun damansa adamu, ya karasa cikin hanzari ya riko Aeezad ganin Yana kokarin shiga cikin gidan, gudun kada yashiga cikin gidan asamu matsala yasa adamu rikosa sosai, Aeezad ya dago ya kalli adamu,Yana fadin ''ka bari naje na gan mommyna, wlhi ina santa,....kaji tana cewa bata sona kou? Wlhi karya takeyi tana sona gashinan tanata kuka kmr yadda nima nake kuka,..." Sune kalaman dake fitowa daga bakin Aeezad Cikin kidimewa tamkar mahaukacin daya jima a dawanau. Hawayen tausansa suka wanke fuskar Adamu, Yana kwallar yace "Tana sanka itama sir Dan Allah ka kwantar da hankalinka pls, kaifa babban soja ne, be kamata kadinga kuka a gaban mu ba pls sir!'' "bazan iya controlling kainaba, ta lalatamin ruhina da kaunata, wlhi ko a gaban waye zanyi kuka,,, ina santa ne wlhi ! mutuwa zanyi!!' ya karashe Yana wani irin kuka, Hadi da dafe saitin zuciyarsa. Dai-dai adamu ya karaso bakin motar da Aeezad, wasu sojojin guda uku suka bude motar adamu yasa Aeezad a ciki, shima ya shiga bayan ya zauna kusa dashi, dreva din yayi lock din motar, sauran sojojin Kusan su arba'in suka shiga tasu motocin guda biyu, wasu duk a tsaitsaye duke da bindigogi, dukkaninsu cikin tausayi da tausayawa na Aeezad suke, suka tada motocin suka fice a gidan , Aeezad se kuka yakeyi Yana buga kansa a kan glass din motar Yana kuka Yana Kiran sunan mommynsa, mommynsa! adamu Daya zauna gefen Aeezad ya shiga rarrashnsa cikin girmamawa da dadin lafazi, yana basa baki kuma Yana tofa masa Addu'ur'i Amma sam Aeezad ya kasa samun nutsuwa sede abinda baza a rasa ba, Aeezad ya jawo wayarsa yayi typing message jikinsa na rawa fuskarnan tasa ta kukkumburo bakinsa ya kumbure yaci kuka ya koshi Yanama kan kuka n domin be koshi da kukanba,bejinma ze koshi da kukan. "Ina sanki Dan Allah mommy ki rufamin asiri kamar yadda Allah ya rufa miki wlhi ina sanki!!..." Shine abinda yayi typing ya tura mata yayinda kafin ya gama tura mata message din tini kwallarsa ta wanke wayar tasa tass, yana gama typing message din ya wurgar da wayar kasan motar,yaci gaba da kuka tamkar karamin yaro, ya rasa ina zesa rayuwarsa yaji sanyi, ga sanyin AC a motar Amma shi se zufa yakeyi. Direct hanyar Kano suka nufa daga garin katsina,. Dai-dai suna Shirin fita daga katsinar,a Wani daji,kawai se gani sukayi motar sojojin ta gabansu tayoyin motar sun fita duka a lokaci daya, Nan da Nan motar ta mirgina gefe ta kifa, kan kace kwabo motar ta kama da wuta! Ta kone kurmus da mutanen cikinta. Ji kake kiiii dreva din dake tukin motar da Aeezad yake, yaja burki Hadi dacewa " Akwai matsala an kawo mana hari!'' cewar dreva din dake tukin motar da Aeezad yake cikin tashin hnkli Yayi maganar. Nan take hankalin Aeezad ya kara tashi kan wanda yake ciki, kwakwalwaraa ta dauki charge! kan kace kattt aka fara bude sojojin dake motar baya wuta, Nan suma suka zage suka shiga bata kashi da mutanen, Nan mutanen sukayi musu Circle, kusan mutane hamsin,, duk fuskokinsu a rufe da bakin kyallle, bindigogi dake hannunsu na fitar hankali. ,Nan hankalin sojojin ya kara tashi suka shiga bude ma Mutanen wuta, ina Ai sarkin yawa yafi sarkin karfi a kallah su sojojin basufi su ashirin ba. "Fito mu gudu sir.... Kai akeson kashewa mu gudu jawai..." Cewar adamu da hnklinsa ya tashi Ainun, yayinda se harbin motar dasuke ciki akeyi,dande motar batajin harbine, Amma sede tini sun kashe tayoyin motar da harbi yadda bazata tafiyu ba. Tini Aeezad ya fito ya Ciro bindigoginsa kananu guda biyu ya shiga Harbin mutanen dasuka zagayesun. Nan suka shiga Aiko masa harbi Yana kaucewa Amma ina kafin su ankare tini ya kashe mutane goma. Sarkin yawa yafi sarkin karfi nan suka karar ma Aeezad da mutane suka rage mutum biyu,. "Sir mu gudu Dan Allah pls..." Adamu ya fadi da karfi yayin daya jawo Aeezad da karfi, Aeezad na turjewa ina dole seda Adamu ya jawosa suka ruga a guje sbda basu da mafitar data wuce gudun domin zuwa yanzu kaf mutanensu an kashe musu daga AEEEZAD se adamu se Bashir suka rage, Bashir tini ya gudu ya fada daji. Sam Aeezad beso gudu ba dande kawai dande adamu ya matsa ne. Tini hankalin barayin ya dawo kan Aeezad da adamu dake gudu,Suma suka fara binsu a guje, suna binsu suna harbinsu, cikin Sa'ah suka harbi adamu a kafa Nan ya fadi kasa Yana ihu Yana fadin "ka gudu kawai sir..." Aeezad ya tsaya ze dauko Adamu, Nan suka samu nasarar Harbin Aeezad din, seda suka sakar mata bullet kusan goma yana kaucewa dayar ce ta samesa Nan ya zube kasa warwas,idanuwansa suka kulle ruf bakinsa da kalmar shahada. Jin jiniyar motar Yan sanda ga jirgin daya fara zagaye ta samansu, ai tini Bashiri barayin sukayi saurin guduwa , cikin farin ciki sbda sun tabbar sun samu nasarar kashe Aeezad.



Ayi hkri da rashin editing tsoffin fans Dina sun San baba editing book.



Wannan littafin na kudi ne 08101626484.
💖🐝NAMIJIN ZUMA PAID PAGE12🐝💖
*Wannan littafin na kudine 1k only 08101626484*

A bangaren nabeelah tana shiga cikin gidan a daddafe ta zube kasan tiles din falon kawai ta fashe da Wani irin kuka, abinda yasa kenan take ja baya da AEEEZAD sbda batasan mgnr Nan ta rashin kunya ta shiga tsakaninta dashi, ji takeyi tamkar yayi zunubi ne a gareta me girma. "ta yaya d'a zece yanason uwarsa kuma Yana sha'awarta!..." Nabeelah ta fadi a zahiri tana meci gaba da kuka tamkar ranta ze fice daga jikinta."wannan raini ne me tsanani!'' nabeelah ta fadi a zahiri tamkar zararriya, gani takeyi Tamkar ma Aeezad ya gama rainata ne tass, kuma karya yakeyi ba aurenta zeyi ba, kawai danyaga tana kasansu ne shiyasa ya bijiro mata da hakan saboda ya lalata mata tarbiya, sanin kanta ne tasan Aeezad mazinaci ne, to tabbas shima zinar yakeso yajata da aikatawa, ta tabbatar Sha'awarta yakeji so yakeyi ya lalata mata tarbiyarta, tin tini Ashe kallon da yake mata kenan nasan yayi Zina da ita, tabbas duk wanda ze iya fadin gatsal Yana sha'awarka a gaban mutane tabbas ze iya aikata komi gashi ko ya aikata Zina da ita bata da yadda zatayi dashi cewa za ayima ta masa sharri sbda shi d'an gata ne ita Kuma bata da gata sena ubangiji. Koda ace ma aurenta zeyi ita Sam bazata iya aurensa ba koda ace za a kasheta, Aurensa tamkar zata Kai kanta ne ga wahala inma yanaso kenan, domin a duniyar Nan nabeelah na azabar tsoron Hajiya rafi'ah tazauna dasu bataji dadin ba Sam, balle ace wai ita zata zauna kishi da na'eema ai ta tabbatar sena lahira yafita jin dadih duniya, har kwarama ta mutu da hakan ya faru, bama wannan ba tabbas ko ta rasa mesonta a duniya bazata iya auren Aeezad ba, koda za a kasheta sede a kasheta. "Har abadan!'' ta fadi tana meci gaba da kukanta,ta dago hannayenta data dinga marinsa dasu ta kallah, Wani irin tiriri zuciyarta ta dauka me azabar zafin Daya haifarwa da jikinta ketowar zufa, haka kawai taji bata kyautaba saboda marirrikan data masa, Nan take fuskarsa ta fado mata idanuwa a yayin data masa kallon karshe kafin ta shigo cikin gidan, duk hannayenta sun kwanta a kn fuskarsa , gashi ta fasa masa baki da marirrikan data dinga masa, kukan da yakeyi kmr ze haukace ya kara fadowa tunaninta, taga tamkar yana gabanta ne, ji takeyi kmr ynzu abubuwan ke faruwa, Nan take ta kara zama kmr mahaukaciya tace "meyasa na masa wadannan marirrikan? Kawai danyace Yana sona Yana shaawahta!!" Ta kara fashewa da kuka Hadi da kwanciya a kasan tiles din falon, "Dan Allah kayi hakuri Dan gatan Nabeelah...dan Allah ka yafemin ,kwata-kwata baka chanchanci abinda na maka ba, kawai dankace kana sona? Shine na maka wadannan marirrikan .... Kwata-kwata baka can-can-ci abinda na maka ba Jarumina! Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!! Ya Rabbih!'' ta shiga sambatu cikin gigitar fitar hayyaci, se yanzu take nadamar marirrikan data dinga masa,,, a matukar zabure ta dafe kuncinta yayinda takejin tamkar zafin marirrikan data dinga masa ne takeji a kan tata fuskar. "Ka yafemin....bazan Kara marinka ba, nayi nadamar marinka Dan Allah kazo ka rama...ka rama please!'' ta fadi a rude kaf bata cikin hayyacinta, ta mike a zabure ta fito kofar harabar gidan takai dubanta inda ya tsugunna yanata kuka, daman tasan tini sun bar gidan sbda taji ficewarsu a gidan. Nan kasan datake tsaye ta zube kan guiwowinta tana kuka me tsuma zuciya yayinda kaf siffarta seda ta chanza sbda kukan datasha, Kanta ko hula babu tini hular kanta ta fadi a falon, uwar sumar nn kanta ta barbaje tsakiyar bayanta. "Ka dawo Dan Allah,! Aeezad kadawo Dan Allah, Dan girman Allah kadawo ka rama marirrikan danai maka Dan Allah!!!'' ta fadi tamkar zatayi hauka,takai hannayenta kan fuskarta tashiga Marin kanta da karfi,,dakanta taji zafin marin datakema kanta ina magashi, Nan ta kara fashewa da kuka tana Marin kanta tana fadin. "na tabbatar zafin da Aeezad yaji yafi zafin da nakeji ynzu haka A Marin da nakewa kaina...wlhi Bazan yafewa hannayena ba dasuka mararmin kyakyawar fuskar Aeezad dina ba....'' ta fadi se sambatu takeyi kaf ta zare, ma'aikatan gidan suka taru suna kallonta su a zatonsu ko iska ne suka tashin mata,. mata kuwa ma'aikatan suka shiga kokarin riketa a mata rukiya, kusan su goma nabeelah ta zubar dasu ta nufa cikin gidan a guje tashige dakinta suka biyota tasawa dakin key, suka dinga mata Addu'ur'i Hadi da kiran sunanta zuwa can har suka gaji suka watse. ita kadai tasan meke damunta, kwara ace aljanun ne da ita suka tashi, da tashin hankalin datake cikin,Nan kasan tiles din dakin ta zube Hadi daci gaba da kukanta tanata bubbuga hannayenta a kasan tiles din dakin, tamkar zata zare , yayinda zuwa yanzu takejin zuciyarta kamar zata buga sbda azabar bugun datake mata. "Wani Abu ya samu Aeezad!!'' ta fadi a matukar kidime,tabbas in tanajin wannan bugun zuciyar to Wani Abu ze ze samesa, a yau bugun zuciyar datakeji baze misaltuba bata tabajin irinsa ba, ko ciwo zeyi setaji a Jikinta kuma makusancin bugun zuciyarnan takeyi in Wani Abu Ze samesa, Amma ta yau ta shahara domin har jikinta rawa kawai yakeyi kmr zararriya, ta haukace yau tuburan, tako ina zafi takeji a jikinta, hatta jinin jikinta ya dauki zafi se azabar zufa kawai takeyi, . Kmr an tsunguleta ta tashi ta nufa bedside tanata tangal tangal jiri na neman dibarta, Wayarta ta dauko wadda ke ajiye a bedside kirar Samsung ce wayar, tin kafin ta bude wayar taga sunansa dauke da messages a kan wayar, jikinta nata kakkarwa tashiga kokarin bude wayar, Nan wayar ta fadi kasa sbda jikinta daketa kakkarwa, wayar ta bugu da kasan tiles, jiki na rawa tabi wayar ta dauka, abinka da Samsung ashe faduwar da wayar tayi taci screen, farr-farr wayar tayi, tayi wasu layi layi, kuka nabeelah ta kara fashewa dashi yayin data zube Nan kasa ta ajiye wayar a kan cinyoyinta tana fadin "meyasa zakici min haka, banga messagee dinsa dayaminba, inaso in kirasa inji ina yake inaso in gansa! Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un! Ya Rabbih ka rabani da mummunar kaddara..." Nabeelah ta karashe tana kukan dayafi kaf kukan datayi a fari, jikinta se kakkarwwa yakeyi, ta kara dago wayar, taga ta Dan rage layi-layinn datayi, jiki na rawa ta karkata wayar gefe, tashiga kokarin cire wayar a lock daman Sunansa ne security din wayarta AEEEZAD! da kyar tasamu wayar ta fita daga lock Sam bata gani SOSAI seda kyar wayar nayi tana far-far, a haka tashiga taga messages din da kyar ta iya karantawa. Tana GAMA karanta sakon ta kife taci gaba da kuka yayindatake Nemo lambarsa tayi dealing taji a kashe, ta kira kusan sau talatin Amma a kashe wayar take, (tinda ya wurgar da wayar kasan motar ta mutu)
nabeelah ta kara fashewa da Wani irin kuka tana fadin "Wayyo Allah na! Wayyoh Allah na! Wayyoh Allah na! !! Wayyo rayuwata!'' sune kalaman daketa fitowa daga bakinta yayin datake kuka kmr zatayi hauka, bugun zuciyarta na kara kidima jikinta, se buga kanta takeyi a kasan tiles din dakin Sam ko zafin hakan bataji, abinda takeji a zuciyarta ya wuce tunanin duk Wani me tunani, se dealing number dinsa takeyi Kamar hauka Nan take tayi masa kira yafi kira dari biyar Amma duk a kashe.

**
A bangaren Aeezad.
tini jirgin Yan sanda dana sojoji sukama dajin saukar angulu, tako ina ma'aikata suka cika dajin tini Yan ta addan sun tsere. Bashir ne yasamu damar Kiran Wani abokin Aikinsu ya sanar dashi halin da suke fiki, kasancewar Aeezad ba karamin mutum bane a Nigeria, tini aka sanar da shuwagabannin sama, shine aka shiryo wadannan tawagar jirage guda biyu, motocin Yan sanda da sojoji Kam sunfi motoci hamsin. Nan wasu suka fada dajin domin dubo Yan ta addan Amma ina ai babu su babu dalilinsu. Yayinda tini aka dauki aeezad dake kwance kmr matacce aka sashi a cikin jirgi kana aka dauki Adamu na aka sashi a jirgin, a cikin jirgin harda chief of army, ba karamin kaunar Aeezad yakeyi ba sbda kokarinsa a hukumar sojojin, ganinsa kwance kmr ba Rai seda yayi kwallah,. "Jarumin maza.. Namijin fama..." Chief of army ya fadi Yana me kallon Aeezad a kwance tamkar matacce,kowa jikinsa ya sare gani sukeyi da wuya Aeezad ya rayu,dukda basu sanma a ina aka harbesa ba, kawai de jini se kwarara yakeyi a hannunsa jinin me dumbin yawa ya zuba daga jikinsa,hkn ne yasa suke tunanin da wuya Aeezad ya rayu sbda jinin daya zubar yayi yawa., har kwara Adamu ma yana iya rayuwa sede kafarsa da wuya ta moru. Cikin hanzari jirgin ya tashi sama aka nufa cikin garin Kano dashi domin Nan yafi musu saukin zuwa, direct babban asibiti aka nufa dashi, tini Yan jarida sun fara watsa labaran hakan a gidajen Redio da gidajen TV, domin tini Suma sun hallara dajin tin kafin a dauke Aeezad da adamu suka samu nasu rahotannin,, Nan da Nan Nigeria ta kideme da zallar tashin hankali, iyalansa dasukeda tabbacin a cikin sojojin dasuka rasa ransu akwai nasu suka hau koke koke.

** ** **
Dai-dai Alhaji sunusi dake zaune falonsa Yana kallon news wannan Labarin ya fado masa, aka nuna konewar motar sojojin sannan aka saka picture din Aeezad Dana adamu, cikin tashin hankali daddy ya tashi tsaye, sbda tini ya gane dansa ne tilo dayafi kauna a fadin duniyar Nan, ko daga bacci ya tashi ze gane d'ansa koda a cikin dubu dubu ne. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!'' alhaji sunusi ya dauki salallami kusan sau uku a jere cikin ihu tamkar ze fasa falon nasa, ya jawo wayarsa ya fara kokarin neman number din shugaban sojojin nigeria, Yana Shirin kiransa yaga Kiran shugaban sojojin yashigo wayarsa. Nan gabansa ya yanke ya fadi Yana dagawa yace "Ina d'ana? Da gaske ne abinda ya faru da Aketa yad'awa a labarai..." Daddy ya fadi a rude yayinda yakeji kmr zeyi hauka dai-dai hajiya rafi'ah ta sakko daga upstairs cikin tashin hankali sbda karar dataji mijinta nayi, ta iso ta taddashi cikin tashin hnkli Yana waya. Nan shugaban sojojin ya tabbatar masa da abinda ya faru, ya sanar dashi yanzu suna babban asibitin dake cikin garin kano,. "Ka gayamin Dan Allah D'ana ya rasu ne?" Shine abinda daddy ya fadi yayinda idanuwansa tini suka kad'a sukayi jajawur. "Ka kwantar da hankalinka, be mutu ba..." Alhaji sunusi yace "Karya ne!! Karya ne!!" Ya fadi kmr zatautacce,jikinsa kawai ya basa d'ansa baya raye. Jin abinda yake cewa yasa rafi'ah shiga tashin hankali itama, Nan tashiga Fadin "meya faru wani d'an kake nufi? Bade Aeezad ba mijin y'ata... " Rafi'ah ta fadi cikin tashin hankali da rudewa. Katse wayar daddy yayi domin baya fahimtar me nacikin wayar ke fadi, cikin tashin hankali yashiga kokarin Kiran sakataransa bugu daya ya daga,. "Ase mana fly zuwa kano..." Yana fadar hkn cikin tashin hnkli ya katse wayar, ya ajiyeta gefe Nan kiran jama'ah ya fara shigowa wayar Ciki harda Kiran shugaban kasa, Nan take Alhaji -sunusi ya tabbatar da dagaske abinda idanuwansa suka gani ya samu tilon dansa. Rafi'ah dake tsaye se tambayarsa takeyi meya faru ya kasa mgna dukyabi ya fita a hayyacinsa, se zufa kawai yakeyi, duk sanyin AC dake falon baya ji a karshe ma zafi yaju AC na sakarwa,. Nan take kwallah ta wanke masa kunci, duk dauriyarsa seda kwallar suka subuce masa. Hankalin rafi'ah ya kara tashi ganin abinda bata taba gani ba a cikin idanuwan mijinta ba wato kwallah se yau, yanada dakiya da dauriya. "Meya faru Alhaji ko mutuwa Aeezad din yayi?'' ta tambaya a matukar rude. "Yan ta adda ne suka Kai masa hari, sun samu nasarar harbinsa,sun kashe kaf masu tsaronsa se mutane biyu ne suka tsira......" "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!'' hajiya rafi'ah ta dauki salati cikin gigita, tace "Bade ya mutu bade ko!?"cewar hajiya rafi'ah da hankalinta ya tashi Ainun Nan take yarta ta fado mata Rai watta take Egypt, rafi'ah ta tabbatar in yarta tasamu wannan labarin seta kusa hauka sbda kaunar datakewa Aeezad, uwa uba ma ita tunaninta karya mutu da wuri ya maida mata yarta Karamar bazawara. "Jeki Sako hijjabinki yanzu zamu tafi kano..." Alhaji sunusi ya fadi murya a rikice yayin daya kagu yaga d'ansa ko hnklinsa ze d'an nutsu. Ba bata lokaci hajiya rafi'ah ta Sako hijjabinta Alhaji sunusi dagashi se jallabiya ya fito harabar gidan, kaf ma'aikatan gidan duk sunyi jungum jungum domin sun gani a TV wasu kuma sun sauran. Ba bata time suka shiga mota dreva yajasu zuwa Airport, ba bata lokaci suka shiga jirgin ya daga zuwa garin Kano a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login